KADDARARMU CE....4
by @nusybee143
馃 茦ADDARAR MU CE....馃憣
(Ta zo a haka)
鉁嶏笍Nusy bee
鉂わ笍*Young talented writers association (YOTA)*鉂わ笍
My TikTok account 馃憞
***
My Instagram account 馃憞
***
My arewa pen link 馃憞
https://arewapen.com/u/nusybee143
*TALLA!TALLA!!TALLA!!*
*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KU茒I 茦ALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA 茦WAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DA茒EWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTU苼A TA KAI TSAYE KU TUNTU苼E NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.
*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,*馃憞
***,
***
Page 4
Da yamma Saif yana zaune a parlourn gidan yana wani aiki da laptop 蓷in shi,wasu ayyuka yake so ya 茩arasa saboda gobe sammako zai yi zuwa 茩asar Cuba don suba wani aiki a companynsu na can
茦arar intercom ya ji,ya 蓷aga kyawawan idanunshi yana kallon 茩ofar parlourn,aka sake danna intercom,ya motsa 茩ananun le蓳蓳anshi kamar baya so ya furta
"Come in!"
A hankali 茩ofar ta bu蓷e, matashiyar baturiyar ta kutsa kai cikin parlourn a abinda bai wuce seconds biyu ba ya 茩are mata kallo
Sanye take da wata 蓳ingilar riga wadda ko cikinta bata gama rufewa ba,fara,sai wani mini skirt pink colour,gashinta ya sha gyara da colours purple and Pink,kafarta sanye da takalmi heels,hannunta ri茩e da mini bag
茒auke kanshi ya yi yana jan tsaki a ranshi,ya rasa gane me yake damun abokin nashi da har wannan abin ya burge shi,yana jin sanda ta furta masa "Hi!"ko kallon banza bata ishe shi ba ballantana na arzi茩i,itama bata damu ba ta shige 蓷akin baccin Ashraf
SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA
Da mamaki take kallon wayarta da take ta faman ruri, lokaci guda kuma murmushi ya 茩awata fuskarta,ta janyo wayar ta 蓷aga tana lumshe idanunta,cikin sanyin murya ta yi sallama
Lumshe idanunshi ya yi ya bu蓷e,yana murmushi ya ce"waalaykis Salam the most shining and adorable star,tabbas na yi missing wannan zazza茩ar muryar"
"FAISAL!is you?"ta fa蓷a tana murmushi cikin tsananin farin ciki
Shima murmushin yake yi,a hankali ya ce"is me my queen,jiya muka gama exam,yau in sha Allah zan shigo,har na yi booking flight ma,I hope you are doing good!"
"Alhamdulillah my Faisal,sai dai kewarka,ya su Mamie da aunty Zaitun?"
"Lafiyarsu 茩alau haibibty,ya su Ammi?"ya bata amsa
"Suma lafiya 茩alau, Allah ya kawo ka lafiya, Allah ya bada abinda aka je nema"ya yi murmushinshi mai kyau wanda ya 茩ara 茩awata kyakkyawar fuskarshi,ya ce"alright! I'm on my way in sha Allah!"
"Okay I'm waiting!ka gaida mutanen Abuja"拼ar dariya yayi yana fa蓷in"okay zan bi kowa a Abuja na ce queen tana gaishe su"itama dariyar ta yi ta ce"to shikenan,ni dai sai na ganka"ya amsa da "okay bye sweetheart!I love you!!"
"I love you more,sai na zo"ya kashe wayar ya na murmushi
Farin cikin Aneesa ya gaza 蓳oyuwa,tana matu茩ar son Faisal kamar ranta,a wani zuwa da ta yi kanawa park ita da 茩awayenta Meena da Deeja,tana ta danna wayarta bata ankara ba suka yi karo wayarta ta fa蓷i
Da sauri ta du茩a don 蓷auka, shima ya kai hannu har hannayensu suka ha蓷u,ta yi saurin janye nata hannun idanunta akan wayarta
茒agowa yayi yana sake sakin fuskarshi, hannunshi ri茩e da wayar yana fa蓷in "oh!am so sorry!nayi miki 蓳arna ko?"bata iya yin magana ba sai girgiza kai da ta yi kawai tana 蓷auke kanta daga kallonshi,ya mi茩a mata wayarta,ta kar蓳a ta wuce shi ba tare da ta sake kallonshi ba
A ranar da 茩yar ta iya bacci saboda tunanin wannan matashin ya tsayar mata a rai,ko yaya ta yi juyi shi take gani, tunanin shi ya tsaya mata a rai,a ranar da 茩yar ta iya bacci,shima cike da mafarkan wannan kyakkyawan matashi da suka yi karo cikin rashin sani
Tsawon watanni uku, lokacin har ta fara mantawa dashi,duk da cewa tana tuna shi lokaci lokaci,still ta je duba wata 茩awarta asibitin Aminu Kano ta ganshi shi da wani abokinshi, saboda tsananin yadda zuciyarta take kewar shi ta kasa daina kallonshi, lokacin ma bai kula da ita ba
Kasa daina waigenshi ta yi har sai da Meena ta fara gane akwai abinda yake 蓷aukan hankalinta,ta ce"Aneesa wai lafiyarki kuwa?"
Sai a sannan Aneesa ta yi fuska ta ce "me kika gani?"Meena ta ce"ina baki labari amma kamar hankalinki ba a kaina yake ba,sai faman waige waige kike yi,wai me kike kallo ne?"Aneesa ta 蓷auke kanta kamar ba ita ba suka cigaba da tafiya ba tare da ta tanka ba
Meena ce ta tsaya tana fa蓷in"ya Salam!na tuna,akwai wani baban 茩awata,kusan satinshi 蓷aya a asibitin nan, amma ban ta蓳a zuwa na duba shi ba, Please why not ki raka ni mu je mu ganshi tunda dai ba sake shigowa zamu yi ba?"babu musu Aneesa ta bi bayanta,suka koma asibitin,kai tsaye suka nufi ward 蓷in bayan Meena ta sake kiran 茩awartasu ta yi mata kwatance
Zuciyarta sai da ta kusa tsayawa ganin wannan handsome guy 蓷in a wajen tare da abokanshi,sai hira suke yi suna ta dariya,茩awar Meena mai suna Naina ta mi茩e cikin farin ciki tana yi musu Oyo,suka gida marar lafiyan da jikinshi ya yi kyau Masha Allah,ya amsa da fara'a,suka gaida su Faisal da shima ya sauke idanunshi akan Aneesa yana ta murmushi
Sun 蓷an zauna suna hira,ita dai Aneesa tun da ta ja bakinta ta yi gum bata sake magana ba,sai an yi abin dariya ta yi 蓷an murmushi
Faisal da kanshi ya bu茩aci number 蓷inta don su rin茩a gaisawa, Aneesa ji ta yi kamar ta yi tsallen murna saboda farin ciki, ita ma Meena 蓷aya daga cikin abokan Faisal mai suna Almustapha ya amshi tata number 蓷in
A ranar Aneesa kwanan farin ciki ta yi,ita kanta tana mamakin irin son da take yi wa wannan bawan Allah
Ranar da ya fara kiranta ta yi matu茩ar murna,anan ya gabatar da kanshi da suna Faisal,iyayenshi 拼an asalin garin Kano ne amma yanzu dukansu suna abuja,mahaifinshi Alhaji Nazir Ibrahim kura ministern ku蓷i ne,mahaifiyarshi professor Haleema Idris Garko lecturer ce a jami'ar Abuja,shi kuma 蓷alibi ne a jami'ar tecn贸logico University tilujuana a 茩asar Mexico,inda yake karantar Microsoft engineering,yanzu yana mataki na uku ne(300lvl),yana da yayye uku,babbar su mace ce,Hajiya Zaitun,yana mata la茩abi da aunty Zaitun, bazawara ce,sun rabu da mijinta shekaru shida baya,da farko ta kama hayar gida a cikin Abuja ta kwashe yaranta Na'im da Munaya ta cigaba da aikinta na jarida mahaifinta ya saka ta mayar da yaran ta koma gida ta zauna
Maza biyu ne masu bin ta,Musaddeeq sai Mu'ayyad, Musaddeeq shima lecturer ne a jami'ar NUN da ke abujan,shi kuma Mu'ayyad pilot ne
Bayan shi mahaifiyarsu ta sake haifar yara biyu,Husna da Mu'izza, Husna tana final year 蓷inta a Nigerian Turkish,ita kuma Mu'izza tana SS1
Ta girgiza da mamaki sosai da jin cewa shi 蓷in ba sa'anta bane ta ko'ina,amma hakan sam bai bar zuciyarta ta karaya ba,ita dai ta san shi take so,kuma zata cigaba da sonshi har zuwa ranar da za su kasance a inuwa 蓷aya ta aure,daga nan su sake gina tsaftatacciyar soyayyar da zata sada su da aljanna
Sun 蓷auki Tsawon watanni tara kenan suna tare, yawanci idan yana makaranta bata cika samunshi ko a waya ba saboda yadda ya mayar da hankalinshi kan karatu,ita dai ta sanar da su Ammi batun Faisal,amma shi bai sanar ba,sanin tsarin gidansu,dole sai ya kammala degree 蓷inshi ma sannan har zai fara tunanin neman wata budurwa ballantana a zo ga maganar aure,a tsarin gidan mazan ba sa aure sai sun gama masters,matan kuma degree,aunty Zaitun ma bata yi aure ba sai da ta ha蓷a masters 蓷inta,tana yin aure ta juya PhD
鉁ㄢ湪
Wunin ranar cikin farin ciki Aneesa ta yi shi, saboda zuwan Faisal,ta je aka yi mata lalle ja da ba茩i,ta wanke gashinta,ta zo gida ta fara 茩o茩arin nema masa abinda zata tarye shi da shi
Meena aminiyarta ta kira,ita ce ta bata shawarar su yi masa girki mai kyau sannan su ha蓷a masa da snacks,haka kuwa aka yi,suka shiga kitchen suka fara girke girken tarar babban ba茩o Faisal,Meena sai tsokanar Aneesa takeyi masoyan asali other half zai zo, Aneesa tana ramawa itama
Wajen 茩arfe hu蓷u na yamma Aneesa ta gama komai tsaf,ta yi wanka ta shirya cikin wani tsadadden material da aka yi mata 蓷inkin doguwar riga,gashinta da ya sha gyara ta 蓷aure shi da wani madaidaicin ribbon ta na蓷e shi ta yi wa kanta simple make up, Meena ta taya ta da 蓷aurin 蓷ankwali,sannan ta wuce gida,duk da magiyar da Aneesa take yi mata,tana bata uzurin za su fita ne ita da mamiensu
Wajen 茩arfe hu蓷u da rabi Aneesa ta fara kiran wayar Faisal don ta ji yaushe zai 茩araso,amma a kashe,abin ya bata mamaki,sai dai bata sake gwada kiran ba,ta ajiye wayar tana ta mamakin dalilin Faisal na kashe waya,amma sai ta yi masa uzurin ko yana cikin jirgi ne,tuna hakan ya sa ta ji zuciyarta ta sake,ta sauke ajiyar zuciya
MAITAMA,ABUJA, NIGERIA
Kwance yake akan makeken gadonshi daga shi sai singlet da shotneaker ya lumshe idanunshi, jikinshi sai kyarma yake yi,da alamu yana cikin tsakanin 蓳acin rai, lokaci guda ya bu蓷e idanunshi,a matu茩ar fusace ya zauna sosai, maganganun mommanshi suna dawo masa kai kamar yanzu ta fa蓷a masa
"Are you out of your sense Faisal?ni kake kallo kana gaya min cewa wai ka samu matar aure?oh ko don freedom da muke baka ne Shiyasa kake jin zaka iya shige boundaries 蓷inka?
Kwata kwata nawa kake Faisal? dududu yanzu kake 24 years fa,yayanka Mu'ayyad ko maganar mace baya yi shi da yake 28 years ma gani yake ya yi 茩an茩anta da soyayya,shi kanshi Musaddeeq ba yanzu ake maganar zai yi auren ba ma?ya kai ga yi?sai kai rasa kunya?so stay away from that childishness, otherwise ranka ya fi nawa 蓳aci"cikin marairaice murya ya sake fa蓷in"don Allah momma kar ki ce a'a, I love her,I can't do without her, please kar ki raba mu momma,she is my everything "wani takaici ya tsaya a 茩ahon zuciyar Hajiya Haleema,ta yi 茩o茩arin danne bacin ranta ta ce"Ni ban hana ka aure ba,as per as yarinyar ta cika qualities 蓷in da nake so,but trust me son,ba zaka yi aure yanzu ba,idan zaka jira ka 茩ara girma to,bana son musu get out of my side!!"
Cikin marairaicewa ya langwa蓳ar da kai ya ce"to Please Momma,kin yarda yau kawai na je na ganta,na yi booking flight,kuma na sanar da ita,don Allah kar ta ga kamar bani da al茩awari ne "Momma ta ajiye coffee mug 蓷in da take sipping coffee 蓷in ciki a hankali ta watsa masa wani mugun kallo,ya yi saurin yin 茩asa da kanshi,ya sani mommanshi tana matukar sonshi da kulawa dashi a matsayin shi na autan maza,kuma yana daga cikin wa蓷anda ta fi sha茩uwa da su a cikin 拼a拼anta,amma hakan ba ya hana idan ya yi abu sa蓳anin ra'ayinta ta raba hanya da shi,ko ta tsawatar masa,yana matu茩ar shakkarta,don haka yanzun ma sum sum ya wuce 蓷akinshi zuciyarshi cike da damuwa
Tun wajen 茩arfe sha biyu na rana yake kwance bayan ya kashe wayarshi,ba don komai ba sai don 茩unci da ba茩in cikin da yake ciki,bai samu zarafin tashi ba sai yanzu da Mu'izza ta yi knocking 茩ofar
A fusace ya kalli direction 蓷in 茩ofar ya ce"who is that?"
"It's me bruh Faisal!you have a guest"ta fa蓷a daga waje
Ya ja wani dogon tsaki ya ce"let him in"
Mintuna ka蓷an sai ga amininshi Star boy ya shigo,asalin sunanshi Julaibib,amma saboda yadda yake acting like Wizkid suke kiran shi da star boy tun suna secondary school
"Ya dai friend! I hope all is well,me kake yi har yanzu?muna can muna jiranka zamu buga match kana nan a kwance?"
Faisal ya yun茩ura ya zauna batare da ya kalli star boy ba,sai sauke numfashi yake yi a hankali cikin 蓳acin rai, star boy ya sake matsawa kusa dashi,cikin kwantar da murya ya ce "menene yake faruwa ne friend?feel free ka gaya min,in sha Allah zan samo maka solution"
Faisal ya yatsina fuska,cikin 蓳acin rai ya ce"Momma mana,so take ta raba ni da love 蓷ina,wai ban dace da aure ba at my age,this and that"
Star boy ya Dan zaro idanu sannan ya kwashe da dariya yana fa蓷in "like seriously! which lucky lady is this,ko dai sweet baby 蓷inka?"Faisal yana kallonshi ya ce"Yes!ka san na gaya maka sai na aure ta, I love her, and I can do anything for her sake"
Girgiza kai star boy ya yi,a nutse ya kalli Faisal ya fara magana cikin kwantar da murya
"No man!kar ka yi jayayya da Momma, You know that she loves what you love,so relax,ka yi masters 蓷inka,itama kafin nan yarinyar ta sake zama educative, I'm telling you you won't regret it,zata shigo gidan nan a mutunce,You know yadda gidanku yake,so let her ta samu abinda zata zama mai daraja, kaima zuwa lokacin ka sake zama a responsible man,try it and see "
Kallon tsaf Faisal yake yi masa har ya gama tsari kafin ya ce"so now,are you advising me na bar ta sai na zama responsible man this and that?"
"No!ba haka nake nufi ba,ina nufin maganar auren ka ajiye ta,but you can continue dating her,there is nothing "
Faisal ya girgiza kai ya ce"to Momma ta hana ni kai mata ziyara yau,bayan kuma na sanar da ita "
Shiru Star boy ya yi na some seconds,kafin ya ce"to why not ka sake fixing date idan ya so sai ka je ka ganta?"
"Ka manta Momma ta hana ni zuwa?"Faisal ya fa蓷a yana harararshi
Star boy ya ce"ai ba gaya mata zaka yi ba,just tell her something like,ka je birthday ne or something else haka"
#Nusy_bee
***