ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

KADDARARMU CE....5

by @nusybee143

🫰ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)

✍️Nusy bee 
❤️*Young talented writers association YOTA*❤️ 



My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143


*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,*👇
***, 
***

Page 5


Faisal ya sauke ajiyar zuciya ya ce "to shikenan,Man let's go kawai,gaba ɗaya gidan ma ya ishe ni"Star boy ya yi ƴar dariya, Faisal ya sanya jersey ɗinshi suka fice daga gidan 



QUEBEC CITY, MONTREAL, CANADA 


Ranshi a ɗan ɓace yake kallon Ashraf da ya shigo cikin parlourn hannunshi riƙe da cigarrete ya na busawa, Ashraf ya kalle shi ya watsar, daidai lokacin Rachel ta fito da gudunta ta ɗane shi,ya rungume ta shima,cikin murmushi ta ke yi masa raɗar cewa she missed him so much,ya wuce da ita zuwa ɗakinshi yana murmushi 

"Ji mana!"kakkausar muryar Saif ta katse su, Ashraf ya juya yana kallon Saif fuskarshi a ɗaure

Saif ya miƙe daga inda yake zaune,ya ƙarasa gabansu, fuskarshi a ɗaure yake kallonshi,cikin harshen Hausa ya fara magana 

"Ashraf kana ganin daidai kake aikatawa don ka ga babu idanun Abby?wacce riba ce a cikin shaye shaye da neman mata da ka dilmiyar da kanka a ciki da hankalin ka da ilmin ka?me ya shiga kanka ne Ashraf?idan kana buƙatar aure ka yiwa Abby magana,na san ba zai ƙi ba,don Allah Ashraf ka dawo cikin hayyacinka,na rasa wacce riba kaka ci da zina da neman mata "

Shiru Ashraf ya yi yana zuba masa blue eyes ɗin shi har ya gama bayani,batare da ya ce komai ba ya kewaye shi ya ja hannun Rachel suka nufi ɗakinshi,cikin wani irin ɓacin rai Saif ya ce"Ashraf ina yi maka magana amma ka kewaye ni ka wuce ko?to shikenan,in sha Allah ba zan sake yi maka magana ba,ka yi abinda ka ga dama"shi dai Ashraf bai tsinka ba ya ja hannun Rachel da take ta bin su da kallo don ba jin abinda Saif ɗin yake cewa takeyi ba,suka shige ɗakin nashi 

Takaici da baƙin ciki ne ya sanya Saif barin gidan,a ranar ya wuce Cuba inda zai gabatar da wani aiki, lokacin da Ashraf da Rachel suka fito sam Ashraf bai ji daɗin rashin ganin shi ba, shine ya kai Rachel har gidanta sannan ya dawo yana zuba idanun neman ta inda Saif zai shigo gidan 

Ganin har wajen sha ɗaya na dare babu shi babu alamun shi ya sa cikin sanyin jiki ya shirya ya fice zuwa club da ya saba zuwa,akwai haɗaɗɗun babes ɗinshi da suke haɗuwa a can 

Yana driving yana tunani, shekarun baya shi mutum ne wanda ya tsani dukkan kayan laifi,yana tsananin ƙyanƙyamin zina da kayan shaye shaye,amma a yanzu ji yake idan bai sha ba,ko bai tara da mace ba zai iya samun matsala,a da ya kan tuna saboda waɗannan mugayen ɗabiun basa haɗa inuwa ɗaya da RAYYAN,amma a yanzu ya san ko tantama baya yi ya fi Rayyan shaye shaye,ya fi shi neman mata,amma shi yana yi da taka tsantsan ne don kar Abby ya gano shi,ba kamar Rayyan ba da yake abinda ya ga dama ko a gaban abbyn ne ballantana Ammi,amma ya kasa gane dalilin da ya sa ko sunanshi Abby baya son ji,ko fara'a yake yi da ƴan'uwanshi yana ganinshi fara'ar zata ɓace ɓat,abin yana matuƙar damunshi 

Ikon Allah ne kawai ya kai shi club ɗin da ya saba zuwa,babban club ne sosai da yake tara ƴaƴan manya, waɗanda suka ci suka tada kai, waɗanda babu mai ce musu bari, abinda suka ga dama shi suke yi,daga can gefe ya hango abokinshi Edward da sauran mutanensu a zaune kowa da abinsha a hannunshi,kai tsaye ya nufi can

Yana isa David da ya fi kusa dashi ya bashi hannu yana faɗin "Master!I hope all is well"Ashraf ya zauna ba tare da ya ce komai ba,idanunshi akan Rachel da tunda ta ganshi take ta murmushi,da hannu ya yi mata alamar ta taho,babu musu ta zo ta haye masa jiki tana shafa masa ƙirji tana murmushi,a hankali kuma ta ɗago da alcoholic drink ɗin dake riƙe a hannunta ta ɗora masa a baki,babu musu ya amsa ya fara sha

Ashraf bai koma gida ba sai washegari wajen ƙarfe takwas na safe,don tunda suka gama watsewarsu yake baccin overdose na ƙwayoyin da ya yi,bai farka ba sai wajen ƙarfe takwas da rabi,bai wani jira komai ba ya tsallake Rachel ya shiga mota ya ja ya nufi gida 

Ya na shiga ya ga Saifudeen ya fito,ko kallonshi bai yi ba ya nufi inda motarshi take, Ashraf ya yi murmushi ya shige cikin gidanshi,ya san in dai Saif ne fushin ɗan lokaci ne zai sauko da kanshi 

Sai da ya fara yin wanka ya shirya sannan ya rama sallar asuba da bai samu ya yi ba,ya ɗauki briefcase ɗinshi da labcoat ya nufi fita daga cikin gidan

Ya na ƙoƙarin rufe ƙofar main entrance ɗin wayarshi ta yi ƙara,ya zaro wayar ya na kallon numbern da ke yawo akan screen ɗin gabanshi na faɗuwa "ABBY!"ya san me kiran Abby yake nufi,Abby baya taɓa kiranshi sai idan matsala ta faru,ko ya yi laifi,hakan bai hana shi dakewa ya ɗaga kiran ba ya na rissinawa kamar yana gaban abbyn 

Abby bai amsa masa gaisuwar ba,sai ma umarnin da ya bashi a kausashe "duk abinda kake yi ka bari ka dawo gida,na baka nan da one week,bana son wani excuse or something else,Ina fatan bazakayi abinda ka saba ba this time"ya na kaiwa nan ya kashe kiran ba tare da ya saurari abinda Ashraf ke ƙoƙarin cewa ba 

Ashraf ya bi wayar da kallo bayan Abby ya kashe,bayan wasu ƴan seconds ya ɗan ja ƙaramin tsaki a ƙasan maƙoshinshi ya fice daga cikin gidan, zuciyarshi cike da fargabar abinda ya faru wannan karon,don dai ya san wannan kiran na Abby babu lafiya 



SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 

Aneesa ce kwance a ɗakinta,kallo ɗaya za'a yi mata a ga tashin hankali da damuwa akan fuskarta,kuma hakan baya rasa nasaba da rashin zuwan masoyinta Faisal,da kuma rashin samunshi a waya,sai sauke ajiyar zuciya take yi ita kaɗai, lokaci guda hawaye suka ciko idanunta,ta tashi zaune tana amsa sallamar Ammi da ta dawo daga aiki yanzu 

Fitowa ta yi tsakar gida tana yi mata sannu da dawowa,daga sama har ƙasa Ammi take ƙare mata kallo,kafin ta ce

"Lafiya dai ko?"

Aneesa ta kawar da kai tana goge hawayen idanunta,Ammi ta kalle ta sosai da mamaki tana faɗin"kuka kuma?kukan me kike yi?"

Aneesa ta girgiza kai batare da ta ce uffan ba,Ammi ta taɓe baki ta nufi ɗakinta batare da ta sake kallonta ba,itama Aneesa ta juya ta koma ɗakinta zuciyarta a cunkushe 

Tana nan zaune ta ji Ammi ta ƙwala mata kira, ba tare da ta amsa ba ta miƙe ta nufi ɗakin Ammi,da sallama ta shiga, Ammi ta watso mata wata uwar harara ta ce"bakinki baya amsa kira ne?ko don kin mayar da ni ƴar iska shi yasa zan rinƙa kiranki amma kina ji na ki kasa amsawa?"cikin sanyin murya fuskarta babu walwala ta ce"ki yi haƙuri"Ammi ta ja tsaki ta na cigaba da gyara kayan Hafeez 

Sai da ta gama ta kalle ta,har yanzu tana tsaye jikin bango fuskarta babu walwala,ta ce"me aka yi miki?"

Girgiza kai ta yi,cikin raunin murya kanta a ƙasa ta ce"Faisal ne ban san a wanne halin yake ciki ba,na kira wayarshi a kashe"

Sakin baki Ammi ta yi,kafin cikin mamaki ta ce"shine dalilin da ya sa kike kuka?"

Aneesa ta ɗan juyar da kanta gefe ta ce"I'm just wondering idan lafiya yake,don baya saɓa min alƙawari,tunda ya ce zai zo I'm very sure zai zo,sai dai wani abin ya tare shi,wanda nake fatan Allah ya sa ba wata matsalar bace "Ammi ta ce"to Allah ya kyauta

Kun yi waya da abbanku kuwa?"Aneesa ta ɗago ta kalli Ammi ta ce"eh mun yi waya da shi,da wata matsala ne?"

Ammi ta girgiza kai ta ce"to kira min shi"babu musu Aneesa ta kira number ɗin Abba da ta yi saving da "my pride"ta miƙawa Ammi ita kuma ta fice daga ɗakin zuwa nata

Ammi ta ja ajiyar zuciya ganin Aneesa ta fita,seconds kaɗan wayar Abba ta shiga 

Duk ringing ɗin da wayar take yi da bugun zuciyar Ammi take tafiya,kusan seconds goma tana ringing kafin Abba ya ɗaga 

Cikin sanyin murya ta amsa sallamar shi kafin ta ɗora da faɗin "Barka da yamma yallaɓai"

Idan ba kunnenta bane yake gizo sai ta ji kamar ɗan ƙaramin tsaki ya ja,tunda ya koma bakin aikinshi ta daina gane kanshi,ya ɓullo mata da wasu kalar dabi'u waɗanda a can baya ma baya yi mata su,jiyo shi ta yi yana faɗin "yawwa!da wani abu ne?"

Ammi ta haɗiye ta wani abu mai ɗaci ta ce "babu,kawai dai ɗazu na kira ka da na ji shiru,baka ɗaga bane,shine na kira don na ji ko lafiya"

"Lafiya!"abinda ya ce kenan ya fara ƙoƙarin kashe wayar 

"Abban Aneesa wai lafiya? menene dalilin da ya sa ka daina kira na ne?idan na kira da layi na baka ɗagawa,ko wani laifin na yi maka ne?"

"A'isha!wai menene matsalarki ne? menene dalilin da ya sa bakya son zaman lafiya ne don Allah?yanzu idan kika kira ni me za ki gaya min? me kike buƙata? menene ban yi miki ba? gaskiya ki bar ni na yi aikina cikin kwanciyar hankali, bana son fitina,ai ban ce ma manta da ke ba,idan ina buƙatar jin lafiyarku zan kira ki,ba sai kin kira ni ki dame ni ba"bai bata damar magana ba ta ji ɗif ya kashe wayarshi 

Mutuwar zaune ta yi tana kallon wayar hannunta, tsawon zamanta da Ahmad wannan ne karo na farko da ya rufe ta da faɗa don kawai ta tambaye shi ya lafiyarshi?iya zamanta da mijinta komai ta yi masa na gwaninta yaba mata yake yi ko da ace bai yi masa ba,ta goge guntuwar ƙwallar da ta tarar mata a idanu,ta janyo wayarta tana kallon mai kiranta 

Wannan baiwar Allan ce,wadda take gaya mata duk abinda ake ciki tsakanin Major Ahmad da amaryarshi,bata yi wani jinkiri ba ta ɗaga kiran da sallama

Daga ɓangaren Fareeda ta amsa,suka gaida a mutunce kamar yadda suka saba,kafin Fareeda,wadda ta ambaci kanta da maman Islam ta ce

"Ya haƙurin rayuwa kuma? Allah ya ƙara haƙuri ya ba ki juriya,abin sai addu'a kawai"gaban A'isha ta faɗi,amma ta daure ta ce

"Ameen, wallahi abin babu daɗi,yanzun nan ma na kira shi yana ta yi min wasu maganganu marasa daɗi, waɗanda bai taɓa yi min makamantansu bay tunda muka yi aure wallahi,na kasa gane me hakan ke nufi"

Fareeda ta yi murmushi,amma sai ta langwaɓar da kai cikin yanayin tausayi ta na faɗin "wallahi fa dama an ce ba haka suke barin maza idan suka aure su ba,a hakan ma kin yi sa'a da ba'a raba ku ba,don su ƴan gidansu haka suke,ba sa zama da kishiya,ke kin yi dace ma da ta zauna da ke"

A'isha ta sauke numfashi cikin damuwa, daidai nan Aneesa ta shigo ɗakin don ganin ko Ammi ta gama wayar,sai ta ga wayar a gefen gado,ita kuma tana waya da tata wayar,ta sanya hannu ta ɗauki wayarta Ammi ta ce

"Gaskiya dai na ga alamu, wallahi yanzu har zullumin kiranshi nakeyi saboda tunda ya koma ban sake jin kalma mai daɗi daga gare shi ba"

Fareeda ta ce"sai fa kin nemawa kanki mafita,don rayuwarnan bata yiyuwa haka"

Aneesa ta ɗago sosai tana kallon Ammi don jin amsar da zata bawa matar da ta kira da munafuka,sai ta ji Ammi ta ce"to menene mafitar?"

"Dole ki nemi taimakon malamai magada annabawa,su tashi miki tsaye kan buzu,komai sai ya zama tarihi"shiru Ammi ta yi tana juya zancen, Aneesa ta miƙe tsaye sosai da mamaki tana kallon Ammi,zuwa can Ammi ta ce"to yanzu ya kike ganin za'a yi?"

Zan yi miki magana da shi malamin,idan mun gama magana sai na tuntuɓe ki,amma babu daɗi mace da gidan aurenta a zo a raba ta da shi"maman Aneesa ta ce"to na gode maman Islam,sai na ji ki"suka yi sallama 

"Ammi wacce magana na ji kuna yi ne?"a cewar Aneesa fuskarta a ɗan ɗaure 

Kallonta Ammi ta yi fuskarta babu yabo babu fallasa ta ce"ba abu bane da ya shafe ki"

Aneesa ta sauke numfashi ba tare da ta sake magana ba ta ɗauki wayarta ta juya ta fice daga ɗakin,a ranta tana fargabar kar mahaifiyarta ta jefa kanta kogin nadama

Ta na shiga ɗakinta wayarta ta ɗauki ruri,da sauri ta ɗaga ganin sunan da ta sakawa Faisal,ta na ɗagawa hawaye ya fara yi mata zarya,ta toshe bakinta tana jan numfashi 

"My angel!are you?kina ji na?kina tare da ni?"ta lumshe idanu,aƙalla dai ta samu nutsuwa tunda ta ji lafiya yake,cikin sanyin murya ta ce

"Faisal!are you?why?why Faisal?where have you been? what's the problem?I know my husband well,baya breaking promise,then for now what's the problem?"

Sauke numfashi Faisal ya yi ya ce"some issues muka samu,but for now everything is okay,in sha Allah zuwa next week zan shigo Kano"Aneesa ta ja ajiyar zuciya ta ce"Allah ya nuna mana sweetheart,i hope all is well?"




#Nusy_bee
***