ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

KADDARARMU ce....6

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)

✍️Nusy bee
❤️*Young talented writers association YOTA*❤️ 



My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143


*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL*👇
***, 
***

Page 6



Faisal ya yi murmushi mai sauti ya ce "all is well sweetheart,I hope kema lafiya kike"Aneesa ta yi ɗan murmushi ta ce"lafiya nake,yanzu dai ka ce na zuba idanu zuwa next week?"

"Exactly my dear!a ranar za ki ga Faisal ɗinki,Nima zan ga my Aneesa "ta yi murmushin jin daɗi,suka cigaba da hira cike da farin ciki 

Sun kwashi wasu mintuna, hankalin Aneesa ya kwanta sosai, aƙalla ta samu nutsuwa tunda ta ji masoyin nata ya na lafiya,sun yi hira cike da farin ciki da soyayyar juna kafin su yi sallama

Ta kai mintuna biyar a zaune a ɗakinta tana tufka da warwara kafin ta miƙe ta koma ɗakin Ammi,da sallama ta shiga, Ammi da take zaune gefen gado ta amsa da sallama tana ƙare mata kallo,gefen gadon itama ta zauna tana faɗin "Ammi wai me yake faruwa ne?meyasa yanzu Abba bai cika son ya kira mu a waya ba?"

Ajiyar zuciya Ammi ta yi ta ce "Nima abin nan ya na matuƙar damu na wallahi,yanzu gaba ɗaya abbanku bai cika damuwa damu ba,tunda ya koma,wajen watanni biyu kenan"

Kallonta Aneesa kawai take yi har ta gama magana,kafin a hankali ta ce"to yanzu menene mafita Ammi?meyasa Abba yake haka?"

A ƙule ammi ta ce"shekarun mu ashirin kenan da aure tsakani na da abbanku,amma bai taɓa yi min haka ba sai yanzu don ya auri wannan matar,to gaskiya dole na ɗauki mataki,don an ce haka suke da baƙin asiri,ba sa barin mutum da matarshi ma,mune muka yi sa'a "Aneesa ta ɗauke kanta daga kallon Ammi da ke ta kumfar baki sannan ta ce

"A ina kika san ta kika san halinta?"

Kai tsaye Ammi ta ce"ƴar unuguwarsu ce ta sanar da ni halinta,ta san su ta san family ɗinta sosai"Aneesa ta ɗan girgiza kai ta ce

"To yanzu wanne mataki za ki ɗauka?"

Ba tare da tunanin komai ba Ammi ta ce"malamai magada annabawa xan haɗa ta da su su yi min roƙo,da izinin Allah sai dai na ga bayanta na dai ta ga nawa ba,don yadda na auri abbanku tun bamu san kanmu ba in sha Allahu sai dai ɗaya ya binne ɗaya"

"To yanzu ke Ammi baza ki iya roƙon Allan da kanki ba sai kin saka wani?"da sauri Ammi ta kalle ta kafin ta ce

"Manyan malamai ne ba wani ba,suna da ƙarfin yawu,da wuya su yi addu'a ki ga abu bai daidaita ba"Aneesa ta ɗan girgiza kai cike da takaici,ta ɗauki wayarta ta fice daga ɗakin 




ASOKORO,ABUJA, NIGERIA 

Zaune take a gaban madubi tana gyara dogon brown ɗin gashinta,daga ita sai bathrobe,a lokacin da wani zai ganta ba zai yi tsammanin ta iya wani harafi ɗaya na Hausa ba,ta kai a ƙalla mintuna talatin tana gyara gashin nata, kafin ta kammala,ta sanya wasu fararen riga da wando hoodie,ta saki gashinta baya,babu batun ɗankwali,sannan ta janyo wayarta da take ta ringing tun ɗazu tana kallon sunan wanda yake kiran nata a wulaƙance 

Tsaki ta ja ta mayar da wayar ma'ajiyarta,sannan ta zura slippers ɗinta ta fice daga ɗakin nata ta nufi downstairs 

A main parlour ɗin gidan ta ci birki tana kallon waɗanda suke zaune kamar bata saba ganinsu ba, Ummi ce,wato mahaifiyarsu,sai Najwa,hira suke yi sosai,suna ganinta Ummul Ummi ta saki murmushi sosai tana faɗin "Welcome daughter!har na ce lafiya?na saka Najwa ta kira min ke a waya kuma tana ta kira ba ki ɗaga ba, I hope all is well!"

A kaikaice ta ɗan kalli sashen Najwa da take ta aika mata kallon banza,don sam Najwa bata tolerating wulaƙanci da rainin Maleeka, ita ma Maleekan ɗauke kai ta yi, maimakon ta bawa Ummi amsa sai cewa ta yi

"Ummi ina Lateefa da Mimi?"

Cikin sakin fuska Ummi ta amsa"Lateefa ta tafi wani birthday ɗin ƙawarta, Mimi kuma ta na study room,kin san ta da maitar karatu"Maleeka ta ɗan taɓe baki kaɗan, lokaci guda kuma ta nemi waje ta zauna tana mayar da hankalinta ga kallon TV ɗin da ke parlourn,su kuma suka cigaba da hirarsu 

Mintuna kaɗan sai ga sallamar Lateefa,suka amsa mata,ta yi matuƙar kyau cikin red riga da jan wando,sai wata ƴar riga da ta ɗora itama fara,farar fuskar nan an yi mata light make up,ta sha kitso da jan attachment da ya sauka har gadon bayanta,sai ɗan siririn mayafi da aka ɗan ɗora akan attachment ɗin aka yi crossing 

Kai tsaye wajen da Maleeka ke hakimce ta nufa bayan ta gaida Ummi,tana zuwa ta zauna tana kallonta ta na murmushi,kafin ta ce

"Ƙawata Ameera ta ce a gaishe ki"

"Ina amsawa"Maleeka ta faɗa ba tare da ta kalli Lateefa ba

Sam Lateefa bata damu ba,don ta saba da halin Maleeka,cikin fara'a ta sake faɗin"ta so ki zo fa,amma babu damuwa, wataran na san za ki je ko?"

Maleeka ba ta bata amsa ba,sai ɗaure fuska da ta yi, alamun ta gaji da magana, murmushi sosai Lateefa ta yi,bata gajiya da yiwa Maleeka hira,ranta sam baya ɓaci muddin tana tare da Maleeka ko me za ta yi mata,ta na jin daɗin ta yi abu don ta burge ta ta ga ta burge ta ɗin,don Maleeka tana tuna mata da wanda ta mallakawa soyayyarta kuma ruhinta,duk da abinda ke tsakaninsu

Muryar Ummi ce ta katse mata hanzari,ta yi saurin waigawa tana kallon Ummi da ke faɗin 

"Don kamar yadda abbynku ya gaya min ba zai wuce cikin satin nan ba in sha Allah"

"Yeeeeee!don Allah Ummi? yayana zai dawo? wallahi dama I'm missing him soooo much! wayyo daɗi!!!"dukkansu suka kalli Mimi da ke fitowa daga study room tana wannan shirmen,har da tsalle da rawa

Lateefa da Najwa suka kama yi mata dariya,Ummi tana murmushi ta ce"sannu auta,ke kam auta akwai shirme,ai sai ki yi masa adduar dawowa lafiya ko?sai nake ga kamar ta fi wannan shirmen da kike yi"tuni Mimi ta nutsu tana ta murmushi,farin ciki fal ranta babban yayanta masoyinta zai dawo 

Da idanu ilahirin mazauna parlourn suka bi Maleeka da kallo,wadda ta kusa isa matattakalar ƙarshe na sashenta,fuskarta babu alamun wani abu na damuwa ko farin ciki,a maimakon haka ma zaman gashin kanta da ya sauko zuwa kafaɗarta take gyarawa tana takunta cike da isa da izza 

Babu wanda ya yi gigin yi mata magana ko tambayarta ba'asi,don tsarin Maleeka ba'a tambayarta ba'asi ko a tsara mata yadda zata yi,yadda take ji da kanta ba zai bata damar sauraren wani da sunan son jin ba'asi ko neman chanjin rayuwa ba, kazalika babu mai ce mata don me ballantana bari 

Da daddare suna zaune dukkansu a dinning area suna cin abincin dare,sai surutu Mimi take yi cikin farin ciki tana sanar da Abby zuwan babban yaya

Murmushi Abby ya yi cikin takaici ya ce"ya ga dama kenan,to Allah ya kawo shi lafiya,amma wannan karon zan ɗauki tsatstsauran mataki akan shi, because for sure na gaji da halinshi,this time zan nuna masa ni na haife shi ba shi ya haife ni ba, wannan karon sai ya gaya min wanene mahaifinshi tsakanin ni da wannan ɗan iskan yaron"

Tuni fara'ar fuskar Ummi ta ɓace,ta ce"kai!wai menene matsalar yayansu ne?har yanzu yana tare da wannan yaron?muna gini yana rushewa?amma Abby ya kamata ka rinƙa bincike before ka yanke hukunci,kar ka je ka yi masa rashin adalci,na san baya jin magana,amma kuma I'm wondering idan laifin wancan yaron ne"

"Believe me, laifin shi ne cigaba da mu'amala da wancan yaron,amma na san ba laifinshi bane abubuwan da yake yi, I will talk to him in sha Allah,don Allah ka rage kyararshi don bashi da wani uba da ya wuce kai "Abby bai sake magana ba ballantana ya kalli Mimi da ke ta ɓata rai jin ana aibataata sweet yayanta 

Babu wanda ya kula da tashin Maleeka ta nufi sama tana danna waya,sai Najwa da ta bi ta da kallo,kafin cikin sanyin jiki ta girgiza kai,ta kalli Abby ta ce

"Abby I can't get what Maleeka is doing anytime ana batun big bruh,sai kawai mu ga ta tashi ta nufi sama,is she okay?"

"Don't mind her!"ita ce amsar da Abby ya bata ba tare da ya damu ba,sai ma abincinshi da ya cigaba da ci suna ɗan taɓa hira da Ummi 




DODAN BARRACK, IKOYI, LAGOS STATE, NIGERIA 

A wulaƙance take kallon magungunan da Fareeda ta kawo mata,kafin ta taɓe baki tana ɗaga su ɗaya bayan ɗaya tana ƙare musu kallo,tana kuma sauraren bayanin da Fareeda da ƙawarta Ruky suke yi mata akan maganin 

"Wannan wanda muka karɓo a wajen bokanmu na kwara ne,wancan wajen wani muka je a Bayelsa,wancan dunƙulen kuma na wajen bokanmu na Enugu ne, magungunan akwai kaifi,amma akwai sharaɗi"

Sai da Maimuna ta gama wulaƙanci kafin ta ce"menene sharaɗin?"

Wannan karon Ruky ce ta amsa"ya ce wai idan ana amfani da maganin nan,na Bayelsa,wai ba'a wankan tsarki,dole za ki daina Sallah, sannan kuma za ki yanka zakaru guda biyar ta baya ki binne,babbar matsalar ma ita ce sai dai ki yi da kanki"

Ga mamakinsu sai suka ji ta ce"babu matsala,yanzu a samo min zakarun,zan yi duk yadda ake so"

Fareeda ta jinjina abin a ranta kafin ta ce"yawwa!sai batun sakaryar kishiyarki,kin san ta yarda da duk abinda na faɗa mata?jiya ma ta tura min da 20k wai na kai malami ya yi mata addu'a"ta ƙarashe tana dariya 

Maimuna ta yi wani miskilin murmushi ta ce"ku bi ta a haka,sai ta san ni ba sa'ar yin ta bace ba,sai ta gane kurenta"Fareeda tana murmushi ta ce"na san za ki iya ai, Allah ya ja da ran uwar ɗakina"Maimuna bata yi magana ba sai wayarta da ta janyo,a ƴan mintuna wayar Fareeda ta yi ƙara,ta yi saurin dubawa tana fara'a,amma fara'ar ta ɗan ragu bayan ta ga abinda Maimuna ta tura mata,cikin murmushin yaƙe ta ce

"Na ga saƙo uwar ɗakina,godiya dubu"Maimuna ta gyara zaman ɗankwalin kanta tana faɗin "yawwa!"

Fareeda ta kalli Ruky da ta ɗauke kai tana danna wayarta,ta dake ta sake kallon Maimuna ta ce"uwar ɗakina za ki yi min ciko ko?"

Wani kallon banza Maimuna ta yi mata tana faɗin "cikon me?kin taɓa ganin an bi ni bashi?"

Fareeda ta yi yaƙe tana girgiza kai,ta ce"a'a,kawai dai na ga 50k kika yi min alƙawari ne, shiyasa na tuna miki,na san baya saɓa alƙawari "ta ƙarashe tana ƴar dariya 

Maimuna ta kalle ta ta watsar,ta ce"to ki cika da dubu ashirin da kika karɓa"Fareeda kamar ta kurma ihu don takaici,don tuni ta yi budget da kuɗin,wani malolo ya tsaya mata a maƙoshi,da ƙyar ta dake tana yaƙe ta ce

"To uwar ɗakina godiya nake,yanzu dai bari mu tafi, saboda gobe asubanci zan yi zuwa Kaduna "Maimuna ta taɓe baki tana kallonta sheƙeƙe ta ce"hala wajen wani kwarton za'a je ko?"

Fareeda ta yi dariyar dole ta ce"uwar ɗakina zama waje ɗaya tsautsayi inji kifi,dole mu motsa"ta mike tsaye tana faɗin"yanzu dai zamu ɗauki hanya,sai mun yi waya"Ruky ma ta miƙe tsaye, Maimuna ta kalle su ta ɗauke kai tana faɗin"to a sauka lafiya"babu wadda ta sake magana suka fito daga cikin gidan

A bakin gate Ruky ta kalli Fareeda ta ranta yake a matuƙar ɓace,ta ce"Madam a nan fa zamu rabu,amma Banga alamun za ki bani haƙƙina ba,me kike nufi ne?"

Rai a ɓace Fareeda ta kalle ta tana faɗin "cewa na yi ba zan ba ki bane?don Allah bana son hayyata"ta ja tsaki kafin ta cigaba da mita

"Kina ganin wulaƙancin da wannan tsinanniyar matar ta yi min amma kina batun kuɗi saboda ba ki da tausayi"

Ruky ta gyara tsayuwa tana faɗin "ke dai saka min haƙƙina,sai mu yi magana daga baya"babu musu Fareeda ta ciro wayarta,cikin ɓacin rai tayi wa Ruky transfer na 10k,bayan Ruky ta ga alert ta ɗago kai a wulaƙance tana ƙarewa Fareeda da ta ɗauke kanta kallo,tana yatsina fuska ta ce

"Hajiya ban wani gane 10k ba,ta mece ce?"

Fareeda ta ɗan daidaita fuskarta tana yin ƙasa da murya,cikin kwantar da murya ta ce"ki yi haƙuri da wannan,yanzu dai Kaduna zan tafi gobe in Allah ya kai mu,kin ga bani da wasu isassun kuɗi,wannan matsiyaciyar ta yaudare ni kan batun kuɗin nan,ba don haka ba da komai normal,kin san na tambaye ta kuɗin da zan damfari kishiyarta na wanene ta ce nawa ne,ashe wai abinda za tayi kenan, shegiya fasiƙa "

Ƙiris ya rage Ruky ta fashe da dariya amma ta danne,ta ce"gaskiya dai bata kyauta ba,amma yanzu ta sha ki a banza kenan?babu wani mataki da za ki ɗauka?"

Wani kallo Fareeda ta yiwa Ruky ta ce"ashe kin manta wacece Fareeda, wallahi bata isa ta ci banza ba,jira nake sai ta gama yi min komai,ta share min hanya a gidan major,ta fitar min da kishiyar tata,ni kuma zan shiga gidan itama na fitar da ita,na nuna mata na fi ta iya bariki "Ruky ta yi ƴar dariya tana yiwa Fareeda alamar jinjina da hannu, Fareeda tana murmushi ta tari taxi ta shiga tana ɗagawa Ruky hannu, ita ma Ruky ɗaga mata nata hannun ta yi har ta ƙule

Tana ƙulewa Ruky ta yi murmushi tana faɗin"duk ku gama haukanku,amma za ki sha mamaki tabbas, lokacin da kika fitar da Maimuna kina shirin shiga ki miƙe Kafa na yi gefe da ke"daga nan ta tari taxi don zuwa hotel ɗin da customer ɗinta ke jiranta 




MIAMI BEACH, FLORIDA,USA

Kyakkyawan matashi ne sosai,wankan tarwaɗa, mai murɗaɗɗen jiki,daga shi sai shotneaker da baƙin glasses,waya ce a kare a kunnenshi,yana magana ƙasa ƙasa,da alamu bashi da son hayaniya 

"Why sweetheart?is there any problem bayan wannan?na gaya miki ba zan samu damar dawowa ba sai nan da ten days because akwai ayyukan da nake son na gama ne, but trust me sweetheart Ina gamawa zan dawo"ya ɗan yi shiru alamun saurare

Ɗan murmushi ya ɗan yi,cikin nutsuwar tashi ya ce"yeah I'm aware,kema kin san ina sane,and I know what I'm doing,so just relax, everything is moving smoothly "



#Nusy_bee
***