ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

ƘADDARARMU CE....7

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)

✍️ Nusy bee 
❤️*Young talented writers association YOTA*❤️ 


My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143



*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,*👇
***, 
***

Page 7


"Okay Ummina!bye!"daga haka ya sauke wayar yana ƙarewa mutanen da ke kai kawo a beach ɗin kallo a tsanake

Wata kyakkyawar baturiya ce da ke sanye da bikini ta ƙaraso kusa da shi tana murmushi take faɗin

"Hye handsome!"daga idanunshi ya yi ta cikin baƙin glasses ɗin da ya rufe idanunshi yana ƙare mata kallo kafin ya ɗauke kanshi gefe,ya mayar da kanshi jikin kujerar da yake zaune ya jinginar da kanshi ba tare da ya sake bin ta da kallon banza ba ma

A ƙalla ya kai kusan awa guda kafin wata baturiya ta zo ta same shi,yana ganinta ya ɗan daidaita zamanshi yana kallonta ta cikin glasses ba tare da ya saki fuskarshi ba ballantana har ya yi mata magana,ita kam babu alamun damuwa ta ƙarasa kusa da shi ta rungume shi tana faɗin "hye my love, I'm missing you so much"

Kallonta ya yi fuska a ɗaure ya ce"what is this Abigail?

Why do you keep me waiting?just like that?"

Murmushi ta yi ta kwanta a jikinshi ta na faɗin "I'm sorry baby!now,can we go?"

Bai yi musu na ya miƙe tsaye tana jikinshi 

Da kamar mintuna goma sha biyar ya kammala shirinshi cikin wasu tsadaddun designer riga da wando da takalmi,ya gyara zaman p-cap ɗin da ke kanshi da baƙin glasses ɗinshi,suka shige tsadaddiyar motarshi ya tayar suka bar wajen 

Tun a hanya wayarshi take ta ƙara,bai samu ya ɗaga ba sai da isa gidanshi,cikin fusata ya ɗaga yana faɗin "Najma which kind of stupidity is this ne?"

"Big bruh!yaya ALIYU fa is on his way,daga yau zuwa koyaushe zai iya sauka a ƙasar nan"

"What?ya aka yi kika sani?"

"Jiya na ji su Abby suna maganar,and tunda na ji Abby yana maganar definitely zai dawo ne"

Shiru ya yi na ƴan mintuna kafin ya ce"to yanzu menene abin yi Najma?"

"Kai ma dawowa za kayi, don't let him to win over you,ya kamata a wannan karon ka yi abinda zai burge Abba,is not proper abinda kake yi kai ma"

Ya sauke numfashi ya ce"okay! I'm on my way,Ina waccan matashiyar tsuntsuwar?"

Najma ta taɓe baki kamar yana gabanta ta ce"uwar isa da gadara tana nan,last week ma ta dawo daga Estonia,wai ta je wajen dangin mamanta"shima taɓe baki ya yi ya ce"time will tell,I promise you sai na ga ƙarshen izzarta"

Najma ta ce"I'm hoping that Yaya"

Ya ce"okay yanzu dai sai na taho,in sha Allah within some hours za mu taso,zan zo na yi maganin duk wani tsagera,don ita Ummi abinda aka ga damar yi mata ake yi mata,ni ba zan iya zuba idanu hakan ya rinƙa faruwa ba"

Najma cikin takaici ta ce"Nima ba so nake ba yaya,amma ai ita ce take janyowa,a cewarta wai bata son hayaniya da neman fitina"ya yi ɗan murmushi ya ce "shiyasa wannan karon ba da hayaniya ba,a nutse za mu yi maganin duk wani abu da ke damunmu, gidanmu ne babu wanda ya isa ya hana mu mallakar shi,dukiyarmu ce ko kowa ya ƙi,mu haɗa kai don ganin bayan kowa,ina waccan uwar rashin zuciyar?"

Najma ta kyaɓe baki ta ce"tana nan tana fama,ƴar wahala, baka ga yadda take wahala akan wannan shegiyar zabiyar ba amma bata gani,ta yi ta yarfa ta tana wulaƙanta ta,kuma a ce za'a gaya mata gaskiya ya zama tashin hankali,kuma ga Ummi sai ta yi ta goya mata baya "tsaki ya yi yana faɗin 

"Wahalalliya,ai sai ta yi,Kinga sai mun yi waya,ina da wajen zuwa"suka yi sallama ya kashe wayar 

Ajiye wayar ya yi idanunshi yana kallon jikin bango,ya yi wani murmushin gefen baki,a fili yake faɗin"ALIYU MAZAN FAMA!wannan karon kaine zaka yi fama,amma tabbas haɗa hanya da RAYYAN ba zai taɓa zame maka alkhairi ba,za ka ga uƙuba ganin idanunka,wannan alƙawarina ne!!!"



QUEBEC CITY, MONTREAL, CANADA 

Cikin nutsuwar shi yake ƙarasa shirinshi cikin wasu riga da wando designer,ya dora rigar sanyi akan kayan,ya sanya baƙin spec ya rufe blue eyes ɗin shi,yana shirin fita ya ji motsin mutum yana shigowa

Ɗaga kai ya yi yana kallon Saif da ya shigo fuskarshi babu rahama, dakatawa ya yi da abinda yake yi yana bin shi da kallo,kallo ɗaya Saif ya yi masa ya ɗauke kai ya wuce bedroom ɗin shi na gidan 

Yana nan tsaye yana jiran fitowar Saif sai gashi ya fito hannunshi riƙe da waya yana daddannawa,ya ɗauke kai ya nufi ƙofar parlourn zai fita,a zafafe Ashraf ya janyo rigarshi yana kallonshi a fusace, kallon sama da ƙasa Saif ya yi masa yana faɗin "ya akayi?"

Ashraf ya ja tsaki a fusace,dama akwai shi da zafin rai,cikin fushi ya ce "dude what's wrong with you ne wai? menene haka don Allah?sai wani share ni kake yi kana yi min wulaƙanci,tun shekaranjiya nake yi maka magana ta Whatsapp kake manna min hauka,wai kanka ɗaya kuwa?"

"Take off your hand from me please!"Saif ya bashi amsa calmly ya na watsa masa wani kallo 

Cikin hargagi Ashraf ya ce"ba zan ɗauke ba,malam just give me my answer,or else everything can happen!"bai rufe baki ba Saif ya buge hannunshi ya juya ya nufi ƙofa a zafafe, Ashraf ya bi shi da kallo, Saif yana daf da fita Ashraf ya furta

"Saifudeen wannan ita ce amanar da kake iƙirarin za ka riƙe?a hakan?"

Cak Saif ya tsaya jikinshi yana yin sanyi,bai yi magana ba ya juyo ya tako har inda Ashraf ke tsaye,blue eyes ɗinshi sun chanja kama saboda tsananin ɓacin ran da yake ciki

A duniya bai damu da duk wanda zai juya masa baya ba,duk wanda yake jin haushinshi baya damuwa da sabgarshi,bata shafe shi ba,fushin saif shi kaɗai ne fushi mai ma'ana a wajenshi,fushin Saif ne kaɗai fushin da yake ji a ranshi,ko Abby ne ya yi fushi dashi baya damuwa,amma idan Saif ya yi fushi da shi gaba ɗaya rayuwar ƙunci take yi masa

"I'm here Man! what's your problem?"calmly Saif ya faɗa yana kallonshi fuskarshi har yanzu a ɗaure, hannayenshi zube a aljihunshi 

Kallonshi kawai Ashraf yake yi na ƴan seconds kafin ya ce"what's your problem dude? tukunna ma,me na yi maka?"

"In dai za ka cigaba da kula matan banza kana abinda ka ga dama don ka ga babu idan su Abby zan fita batunka, I'm telling you this "ya ƙarasa idanunshi ƙyar a kan Ashraf yana karantar yanayinshi

Ajiyar zuciya Ashraf ya ɗan sauke yana ɗauke kanshi,kamar wanda aka yiwa dole ya sake kallon Saif da yake kallonshi,cikin sanyin murya ya ce 

"I'm leaving Canada for Nigeria first thing tomorrow morning "

"I hope all is well "Saif ya tambaya ya na sassauta muryarshi,tausayin abokin nashi yana mamaye masa zuciya 

Dan girgiza kai yayi,a hankali ya ce"I don't really know,Abby dai ya kira yana son ganina urgently,so I must leave "

Saif ya dafa kafaɗarshi yana faɗin"okay!safe trip dude! Allah ya tsare,all is well,I hope wannan karon komai zai wuce tsakaninka da Abby "

Tuni fuskar shi ta sake ɗaurewa,ya ɗauke kanshi batare da ya sake magana ba, Saif kallonshi yake cikin jin takaici, Ashraf bai sake magana ba ya juya ya nufi bedroom ɗin shi, Saif ya bishi da kallo kanshi yana sake ɗaurewa 



MAITAMA,ABUJA, NIGERIA 

"Zaitun me ya hana ki fita aiki yau ne?"

Wadda aka kira da Zaitun, matashiyar mace ce,wadda za ta iya kai wa 33-35 years, kyakkyawa ce sosai,ƴar gayu kuma ƴar hutu,ta ɗago kai tana ɗan yatsina fuska ta kalli Momma da ke yi mata wannan tambayar,kamar wadda aka yiwa dole ta ce

"Bana jin fitar ne yau, I hope all is well"Momma ta ja ajiyar zuciya ta samu waje kusa da Zaitun tana zauna tana kallonta

"Momma I hope all is well"ta faɗa tana kallonta 

Ɗan girgiza kai Momma ta yi tana faɗin "Faisal mana, imagine this boy ya damu wai aure zai yi,da farko na yi tsammanin maganar ta mutu ashe shi a wajenshi bata mutu ba,shine jiya ya zo ya na roƙona wai na barshi ya yi aure,ba zai iya jurewa ba, imagine!!!"

Zaitun ta zare medicated glasses ɗin idanunta,ta sauke numfashi tana kallon Momma ta ce"yarinta ke damun Faisal,amma ban ga dalilin da zai saka ki saka damuwa akan shi ba,talk with him,he is your son,and I'm sure yana jin maganarki,this time kar ki ce za ki tsananta masa, I'm sure he will understand what you mean, faɗa I think will not work at this point,so please take it easy Momma,da siyasa ake lallaɓa yaro"Momma ta jinjina kai cike da gamsuwa,don ta ji daɗin magana da Zaitun sosai

Da daddare Faisal yana zaune a babban parlournta yana kallon football match,amma gaba ɗaya hankalinshi baya kan match ɗin,hankalinshi yana kan Aneesa da ta yi masa message ta Whatsapp tana tambayarshi yaushe zai zo da ya ce zai zo next week?ya kasa bata amsa so yake dai Momma ta amince tukunna 

Momma ce ta fito daga ɗakinta tana kallonshi,yana kwance yana kallo amma hankalinshi baya kanta,a tausashe ta ƙaraso kusa da shi ta zauna tana kallonshi,ya ɗago yana kallonta,cikin sanyin murya ya ce

"Good evening mum!"

Murmushi ta yi tana kallonshi,ta kalle shi cikin kulawa tana faɗin "Weldon son!hutawa ake yi?"shima murmushin ya yi ba tare da ya ce komai ba,ta samu waje kusa dashi ta zauna tana kallonshi cikin kulawa

Ganin kamar da magana a bakinta ya sa ya mayar da hankali sosai gare ta,yana faɗin "any problem Momma?"

"No son!dama wata magana zamu yi game da wannan maganar da muka fara sweetheart"

Shiru ya ɗan yi yana kallonta,ba don bai gane abinda take nufi ba,sai don bashi da abinda zai faɗa,ta sake fuskantar shi sosai,cikin kwantar da murya ta fara magana 

"Dama batun yarinyar da kake so a nema maka aurenta ne,a ina take?"

Tuni fara'a ta mamaye masa fuska,cikin fara'a ya amsa "Kano unguwar sabuwar gandu take, Momma za ku je ne?za ku tambayar min aurenta?"

Momma ta ɗan yi sigh ta ƙara mayar da hankalinta ga Faisal,cikin kwantar da murya ta ce

"Yeah!zamu nema maka aurenta,but answer my questions first,ta gama karatunta ne?"

Ɗan yatsina fuska Faisal ya yi sannan ya ce"no Momma,asalima she is about to write her SSCE exams,da na ce why not ta yi karatun a gidana kawai?"

Momma ta girgiza kai tana faɗin"that's not proper son,da hakan why not mu tambayar maka aurenta idan ya so tana gama karatun sai ka aure ta?"

Shiru Faisal ya yi na ƴan daƙiƙu kafin ya jinjina kai a sanyaye,sam ba haka ya so ba,ya so a yi aurenshi shi da Aneesarshi nan da watanni shida ma,amma hakan ma ya yi masa,don haka cikin sanyin murya ya ce

"Yes Momma,ni dai Please help me kar na rasa sweetheart Momma please"Momma ta dafa kafaɗarshi tana murmushi ta ce"don't bother son, I promise I will always be there for you sweetheart "rungume ta Faisal ya yi,yana murmushi yana faɗin"I love you so much Momma "itama rungume shi ta yi tana murmushi 

Wajen ƙarfe tara na dare Faisal ya fito sanye da farar shirt da wando 3 quarter baƙi, hannunshi riƙe da tsadaddiyar wayarshi yana dannawa star boy kira,babu daɗewa ya ɗaga wayar

"My G yane? what's up?"a cewar Star boy 

Ɗan yatsina fuska Faisal ya yi,kamar wanda aka yiwa dole ya ce"wher are you Julaibib?"

Star boy ya gyara zamanshi sosai a cikin motarshi,don ya sani duk lokacin da Faisal ya kira real name ɗinshi wata magana mai muhimmanci zai yi masa

"I'm off to club, I'm on my way,any problem?"yatsina fuska Faisal ya yi ya ce"ka biyo mu tafi tare"yana kai wa nan ya kashe wayarshi,sannan ya samu waje ya zauna yana danna wayarshi 

Mintuna kaɗan sai ga Star boy ya shigo gidan da motarshi,bai ɗaga kai ba har sai da Star boy ya ƙaraso kusa da shi ya samu waje ya zauna yana kallonshi,cikin classy tune ɗins shi ya ce

"What's up my G?any problem"

Sauke ajiyar zuciya Faisal ya yi,ya ajiye wayarshi a gefe ya ɗago sosai yana kallon Star boy,a hankali ya fara magana 

"I can't wait for the time you advised me Julaibib,ba zan zuba idanun ina kallon Aneesa ba,ba abin mamaki bane a samu wani ya yi min shigar sauri ni ina nan ina jiran lokacin da su Momma za su ji cewa na cancanta na yi aure"

Shiru Star boy ya yi yana kallon Faisal da shima yake kallonshi,a hankali Star boy ya ce

"To yanzu ya kake son a yi?me ka yanke game da maganar?kar dai ka yi abinda zaka fusata su Momma,ka san dai daga ita har Daddy kaifi ɗaya ne"

"Yeah you are right!

Shiyasa na sanar da ita,yanzu ta yanke zasu tambayar min aurenta,idan ta kammala karatunta kuma sai a yi aurenmu, I love that girl with all my heart dude"



#Nusy_bee