ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

KADDARARMU CE....8

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)

✍️ Nusy bee 
*❤️ Young talented writers association YOTA ❤️*


My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143


*TALLA!TALLA!!TALLA!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,*👇
***, 
***


Page 8


Star boy ya sauke numfashi ya ce"I wish you all the best dude,ni kaina zan yi fatan ka samu yarinyar nan,ko don irin son da kake yi mata,ko na ce kuke yi wa juna "murmushi kawai Faisal ya yi, zuciyarshi fes

Star boy ya miƙe tsaye yana faɗin"to dude,yanzu dai, I'm on my way to club now,can we go?"babu musu Faisal ya miƙe,suka nufi motar star boy,suna sake jaddada zancen da hanyar da za su bi don ganin Momma bata basu matsala ba





SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 


Yau su Aneesa suka fara SSCE,kowannsu zuciyarshi cike da fatan sa'a, musamman irinsu Aneesa da Meena waɗanda su already sun zana JAMB kuma sun yi nasara, Meena microbiology take son karanta, Aneesa kuma Basic nursing,duk da har yanzu tana cikin ƴar damuwa saboda a yanzu ba su cika waya da baba ba,asalima idan ta kira bata cika samunshi ba

A ɓangaren Faisal kam sai son barka, don soyayyarsu suke zubawa sosai,don sai abinda ya yi gaba ma

Yau ma bayan sun fito daga exam hall zama suka yi a inda suke zama su huta su sha hira su biyar ne,ita, Meena,sai wasu ƙawayensu su uku,hira suke yi sosai cikin farin ciki kan yadda jarrabawar ta yi musu daɗi sosai,kira ya shigo wayar Aneesa 

Tashi ta yi daga cikinsu ta koma can gefe,ganin sunan mai kiran ya sa murmushi ya ƙwace mata,a hankali ta ɗaga wayar batare da ta ce komai ba,ta nemi waje ta zauna ta jiginar da kanta da bango

Murmushi sosai Faisal ya yi ya ce"I hope my lady is doing well"

Ɗan murmushi ta yi tana faɗin "I'm okay, what about you my heart?"

Shafa kanshi ya yi yana faɗin "everything is okay, guess what my queen"

Ɗan lumshe idanunta ta yi ta buɗe su tana murmushi,ƙasa ƙasa ta ce"You know I'm not a good guesser, just tell me my One"

Shima murmushin ya yi yana faɗin "Ina Kano tun safe fa, I'm coming in few hours time"

Bata san sanda ta miƙe tsaye ba tana dafe baki,farin cikinta ya ƙi ɓoyuwa,da ƙyar ta iya faɗin "seriously mine?I.... I....."sai kuma ta kama ƴar dariya, Faisal ma dariyar yake yi, tana murmushi ta ce

"I can't wait, Weldon my guy, Allah ya kawo ka lafiya, I miss you so much"Faisal ma murmushi yake yi,suka cigaba da hira cike da shauƙin soyayya 

Bayan maghriba Faisal ya iso gidansu Aneesa,a parlourn Abba ta sauke shi, lokacin Ammi bata nan,ta tafi night duty da take da shi 

Yau ma Meena ce ta taya ta girki da sauran aikace aikace,ta shirya parlourn ya yi matuƙar kyau,bata juma da idar da sallar maghriba ba Faisal ya iso, Al'amin ne ya sauke shi a babban parlourn bayan ya gaishe shi cikin girmamawa 

Ta kai kusan mintuna goma tana yunƙurin ɗora ɗankwalin tsadaddiyar atamfarta,idan ta yi ta ga bai yi ba sai ta warware ta sake, daga ƙarshe dai ta haƙura ganin tana ɓata masa lokaci 

Da sallama ta shiga tangamemen parlourn Abba, Faisal ya ɗago da fara'a yana kallonta,ya sake faɗaɗa murmushinshi yana faɗin "You are welcome my girl"

Zama ta yi,suka gaisa,sai ƙare mata kallo yake yi yana murmushi,ta yi kyau sosai

Ba su wani daɗe suna hira ba ta zuba masa abubuwan ciye ciye da ta shirya masa,kusan tare suka ci abincin suna cike da shauƙin soyayya 

Sun ɗan taɓa hira,anan yake yi mata albishir da zuwan family ɗinshi nema masa aure,farin ciki fal ranta, shima dai zuciyarshi cike da farin ciki,don maganar gaskiya shima yana matuƙar ƙaunar Aneesa 

Bai tafi ba sai wajen ƙarfe tara na dare,ita ta rako shi har bakin motarshi,ya kwaso kayan da ya siya mata,daga na kwalliya zuwa na ci ya ba ta yana murmushi yana faɗin 

"This is for my Lady,then sai yaushe?"

Karɓa ta yi tana murmushi tare da faɗin "jazakallahu Khairan sweetheart! let's chat later"ya yi murmushi ya shiga motarshi yana faɗin "sai mun yi waya, I love you so much dear"

"Love you more,bye!"ya ɗaga mata hannu ya faɗa motarshi ya bar bakin gate ɗin gidansu 

Da murmushi ta koma gida,a ɗakinta ta ajiye ledar da ya bata ta kwanta akan gadonta ta lumshe idanunta tana murmushi,she can't wait for the day da zata zama mallakin Faisal,a lokacin da zata zamo matarshi,ita kaɗai ta san me ta tanada a zaman aurensu,dole sai soyayyarsu ta zamo abin kwatance a wajen ma'aurata da dama,za su yi soyayya sosai,za su haifi yaran da za su kula da abinsu tare,a take a wajen ta tsara har sunan yaransu,sai kuma ta rufe idanu da tafukan hannayenta tana dariya, zuciyarta cike farin ciki 

Washegari Faisal bai koma Abuja ba sai da ya sake zuwa suka yi sallama,sannan suka gaisa da Ammi, Ammi ta yaba da tarbiyyar yaron sosai,ya yi mata sallama, Aneesa ta raka shi har bakin gate,yau ma kamar jiya ya siyo mata kayan kwalliya da na ƙwalam,har da wata kyakkyawar teddy bear da ta tafi da iymanin Aneesa 

Daga nan ya yi mata sallama,suka rabu cike da shauƙi da kewar juna 




NNAMDI AZIKWE AIRPORT, ABUJA, NIGERIA 

Cikin nutsuwarshi da yanayinshi na rashin son hayaniya yake saukowa matattakalar jirgin, hannunshi riƙe da ɗan ƙaramin trolley ɗinshi,a nutse yake ƙarewa airport ɗin kallo kamar bai taɓa ganinta ba,daga ƙasan zuciyarshi kuwa kewar ƙasarshi yake ji tana ratsa ko'ina na jikinshi,a hankali ya kai hannu ya gyara zaman baƙin glasses ɗin da suka rufe blue eyes ɗinshi 

A reception ya fara kalle kallen ta inda zai gano su Ummi,muryar wanda ya ji ya dakatar dashi 

"Dr Ashraf!yau kaine a ƙasar tamu kenan,ashe dai ba banza ba jikina ya bani kawai na baro Lagos na dawo"

A hankali Ashraf ya mayar da hankali kan matashin saurayin da yake magana,dogo ne baƙi,amma ba can ba, kyakkyawa ne,kuma da alamu, hutu da gayu sun yiwa fatarshi yawa saboda yadda ta yi luf luf da ita,ɗan murmushi Ashraf ya yi,yana faɗin "HAYAT kenan,kai dai baka rabo da wasa, let's go,duk da mun yi waya da su Ummi sun ce min suna zuwa,but I didn't see any of them"

Hayat ya ja hannunshi suka fice daga reception ɗin,shima hannunshi riƙe da nashi trolley ɗin yana faɗin"let's go malam, maybe ma suna waje,ko wani uzurin ya riƙe su"

Ai kuwa suna fita suka gamu da Ummi da Mimi,da mugun gudu Mimi ta ƙaraso ta ɗafe Ashraf tana faɗin"yaya! I miss you so much yaya, shine baka zuwa kana gani na, and I asked you to go with me but you refused "

Murmushi Ashraf ya yi yana faɗin"to parrot, can't you greet Yaya Hayat?"

Da sauri ta mayar da hankalinta ga Hayat da yake kallonta yana murmushi, yarinyar tana burge shi, akwai wayo sosai,gashi bata da raini,ta ƙarasa kusa da shi ta kama hannunshi tana faɗin 

"Welcome yaya Hayat!we missed you too "shima yana murmushi ya amsa mata da faɗin"Weldon mamanmu, I missed you too mamanmu "murmushi kawai take yi,suka ja hannunta suka nufi inda Ummi take tsaye tana murmushi 

Da fara'a ta amsa musu gaisuwa,ta kalli Hayat tana murmushi ta ce "Yanzu dai abokin naka ya dawo,na san za'a waiwayi gidanmu ko?"

Murmushi kawai Hayat yake yi kanshi a ƙasa, Ashraf ya kama hannun Mimi ya yi gaba, Hayat ya biyo bayanshi, ita ma Ummi ta biyo bayansu 

Ashraf ne ya ja motar,kai tsaye asokoro ya nufa,duk yadda Hayat ya so ya bar shi ya nufi gidansu da ke Wuse zone 2, Ummi ce ta fara masa faɗa "Hayatu dole fa ka je ka ci abinci ka huce gajiya, abinda gidan namu ma ba ganinka ake yi ba sai idan Aliyu yana nan?tunda kai dai ba son zumunci gare ka ba"murmushi Hayat ya ɗan yi yana faɗin"a yi haƙuri Ummi,ayyuka ne suke hana mu rawar gaban hantsi,gashi idan Ashraf baya nan ayyuka yawa suke yi min"

Ummi ta ce"mhm! faɗi wani abin dai Hayatu,amma ba wannan ba"

Dukkansu dariya suka yi,har Mimi, Ummi da ya riga su fita daga motar kai tsaye sashenta ta nufa, Mimi ta bi bayanta,su kuma suka nufi sashen Ashraf da ke cikin gidan

Bayan hour guda sun gama shiryawa a cikin kaya marasa nauyi,suna zaune a parlourn Ashraf, Hayat ya ɗaure fuska ganin Ashraf ya fito da kwalin cigarrete yana ƙoƙarin kunnawa, batare da tunani biyu ba ya fizge kwalin yana harararshi 

Yatsina fuska Ashraf ya yi ya ɗauke kai, Hayat cikin ɓacin rai ya fara faɗin 

"Ban san menene matsalarka ba wallahi,wai me kake ji a wannan abin ne?kai kenan ka yi ta bankawa cikinka hayaƙi don tsabar rashin sanin ciwon kai?to ko Rayyan da yake bawa mutane ciwon kai a baya a yanzu na ga ya daina,sai kai da muke yiwa kallon mutumin kirki"

Yatsina fuska Ashraf ya sake yi,kafin ya ce"Ni ba mutumin kirki bane,idan ma kallon da kuke yi min kenan you better stop, I'm not that type,and I will never be like that"

Kallonshi kawai Hayat yake yi ranshi yana ƙara ɓaci, ya kai mintuna biyu cikakku kafin ya yi magana ranshi a ɓace 

"Is not your fault Aliyu!wannan ashawon da aka taimaka aka mayar mutum a gidan nan shine yake causing komai,wato yadda ya bijire yake so laima ka bijire saboda.....

"Enough please Hayat! let's change the topic please!"ya faɗa a ɗan fusace 

Taɓe baki Hayat ya yi,ranshi yana suya,bai kalli Ashraf ba ya miƙe yana faɗin "let's go mu sake gaida Ummi"shima Ashraf ya miƙe batare da ya kalle shi ba,suka jera suka fice daga part ɗin suka nufi main building na gidan 

Da sallama suka shiga part ɗin Ummi, Lateefa da dawowarta kenan daga saloon ta ɗago da sauri tana kallon guy ɗin nata da ya sake zama Cool handsome guy

Da sauri ta miƙe tsaye, bakinta ya ƙi rufuwa saboda tsananin farin cikin da take ciki,sanye take da dogon wando da ya kama ta baƙi,sai riga sky blue,kanta yane da wani siririn mayafi wanda ya tsaya mata a kafaɗa, gashinta baƙi siɗik da ya sha gyara an sake shi ya samu masauki zuwa gadon bayanta 

Da gudu ta nufi inda Ashraf yake tsaye shi da Hayat,bata yi wata wata ba ta ɗage shi tana murna,ya ɗan haɗe rai yana sauke ta daga jikinshi, bata wani damu ba,ta maƙalƙale shi tana ta murmushi,cikin muryar shagwaɓa ta fara faɗin 

"I miss you so much love, I miss you badly,ka manta ni ko?ka manta akwai mai dakon dawowarka ko?wadda dukkan numfashinka soyayyarka ke bayyana a cikinta? kai ne komai nawa, please kar ka sake nisa da ni, I love you more and more my other half"

A kaikaice yake kallonta tana ta surutanta,tana gamawa ya zame hannunshi daga nata,ya bi bayan Hayat da ya tsallake ya yi gaba ya bar su a wajen,kai tsaye suka nufi ainihin parlourn Ummi 

Sun gaisa sosai,sai tsokanar Hayat Ummi take yi, Mimi tana ta damunsu da surutanta na yarinta,sai da Ummi ta gaji ta kora ta daga ɗakin,ta fice tana kumbure kumbure, Hayat ya bi ta da kallo yana murmushi,kafin ya ce

"Ummi da alamu fa ana shiga haƙƙin auta,bai kamata don babban da ya zo ba a yi abandoning auta"

Ummu ta girgiza kai tana murmushi ta ce"da tsohuwar zuma ake magani,kafin na san auta babban ɗa na na fara sani,don haka bar ni da shiriritar wannan ja'irar yarinyar"

Sun ɗan juma suna hira kafin su fito parlourn farko, Lateefa ce ke ta Safa da Marwa tana jiran fitowarsu,suna fitowa cikin zaƙin muryarta take faɗin 

"Yawwa yaya,ga abinci na kai muku,bari na yi serving ɗinku"Ashraf bai yi magana ba ya nufi dinning area ɗin,don dama yunwa yake ji,kuma sam baya wasa da cikinshi 

"Babu gaisuwa ne Madam? Ya ji muryar Hayat"ɗaga kai ya ɗan yi yana kallon Najma da ta ɗan taɓe baki tana cigaba da danna wayarta, tabbacin bata da lokacin tankawa kowa a cikinsu,ya ɗauke kai yana kallon agogon hannunshi,tuni Lateefa ta yi nisa a serving ɗin shi

Hayat tsaki ya yi ya ce"ke a gidan nan kin fi kowa raini da rashin mutunci,wani abu ne zai same ki idan kin gaishe mu?ko kuma raini ne ya sa bakya kallon kan kowa da gashi sai wanda kika so?to wannan bai dace ba,ya kamata ki rinƙa sanin me ya kamata, girmama babba abune mai kyau,idan kika ce kowa raina shi za ki yi......."jan bakinshi ya yi yana kallonta ranshi a ɗan ɓace,don earpod ta saka ta toshe kunnawanta, ba tare da ɓata lokaci ba kuma ya fara bin waƙar da ta kunna ba tare da ta kalli inda yake a tsaye ba ma

Tsaki ya yi ya wuce dinning area ɗin inda Ashraf ke zaune yana jinsu,amma ko ɗaga kai ya kalle su bai yi ba,don yana daga cikin ɗabi'unshi sanannu shine baya shiga abinda babu ruwanshi, musamman abu irin wannan 

Kujera Hayat ya ja ya zauna yana jan tsaki, kallonshi kawai Ashraf ya yi batare da ya ce masa uffan ba,sai cin abincinshi yake yi a nutse 

Hayat ya kalli Lateefa da ta ja gefe ta tsaya tana harɗe hannayenta tana kallonsu,yana ɗan murmushi ya ce"Madam saura ni,ba kiyi serving ɗina ba"

Juya kyawawan ƙwayar idanunta ta yi,wanda hakan ya tilasta masa ɗauke kanshi gefe,da ƴar muryar shagwaɓa ta ce

"Mijina kawai na ga zan iya serving,serve yourself kawai Malam"

Ɗan murmushi ya yi ya fara serving kanshi yana faɗin 

"Ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu ko?ki bari mu fara kai ki before ki zama tashi"

Lateefa ta ɗan ɗaure fuska batare da ta ce komai ba

Rai a ɗan ɓace Hayat ya kalli Ashraf ya ce"wannan ƙanwar taku Najma ya kamata ku rinƙa nuna mata hanya,sam albasa bata yi halin ruwa ba wallahi 

Cikin nutsuwarshi ya cigaba da cin abincinshi,muryarshi a nutse ya ce

"Wacece ƙanwar tawa?"

Hayat ya sake fusata ya ce"Najma or what do you call her? seriously she is very arrogant"

Ashraf ya cigaba da cin abincinshi,kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya ce"good for her!"






#Nusy_bee