BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 33

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

033

Da sallama a bisa laɓɓanta ta shigo gidan sai dai cak ta tsaya zuciyarta na wani irin buguwa sakamakon aman da ta ga Ammunta na kwararawa a inda suke wanke-wanke. Da sauri ta nufi wurin hankali a tashe tana faɗin

''Ammuna baki da lafiya ne ki...'' maganarta ta katse ganin ɗan jini-jini a cikin aman,waro lulu eyes ɗinta ta yi waje,take hankalinta ya sake tashi.

''Ammu jini! Wayyo Allahana! Ammuna aman jini kike!" Ta faɗa cikin sigar kuka. Sai da Mairi ta gama aman sannan ta ɗan ɗago tana sakar mata murmushin ƙarfin hali tare da girgiza mata kai alamar kar ta yi kuka. Murya a can ƙasan maƙoshi ta ce

''Ɗebo mini ruwa na wanke bakina''

Jinjina mata kai ta yi ta ruga ɗaki da gudu ta ɗibo ruwa a ƙaton kofi ta kawo mata,ko samun damar ajiye jakarta bata yi ba. Kurkure bakinta ta yi ta wanke fuskarta sannan ta miƙe,wani irin jiri take ji kamar za ta faɗi ƙasa, a hankali ta taka zuwa ɗaƙin, HAFIZA kuma ta tsaftace wurin. Bayan ta kammala ta shigo falon ta sameta kwance saman doguwar kujera idanunta a lumshe kamar mai bacci. Jiki a sanyaye HAFIZA ta ajiye jakar makarantar ta tako zuwa kujerar ta durƙusa. Jin motsin mutum a kusa da ita ya sakata ɗan buɗe idanunta a raunace, HAFIZA ta yi ƙuri tana kallon fuskar Ammunta cike da tausayi. Murmushi Mairi ta sakar mata,madadin ta mayar mata ta martanin murmushin sai ta ce

''Ammuna kullum cikin rashin lafiya kike amma baki son su Ammu Jamila da Yaa Jalil su sani. Ni dai sai na kira na faɗa musu'' ta yi maganar tana share hawayen da suka fara zubo mata a saman kunci.

''Waya ce miki kullum ne ba ni da lafiya Auta. Kawai don kin ga na yi amai da jini shikenan za ki tayar da hankali. Ni dai lafiyata lau babu abin da yake damuna kin ji HAFIZATA. '' ta yi maganar tana share mata hawayen fuskarta. Tabbas ta san bata da lafiya,amma ɓoye mata shi ne mafita a gareta,bata son ta tayar da hankali yaranta da na 'yar'uwarta. Kusan wata shida kenan da  fara rashin lafiyarta,yau ta tashi cikin ƙoshin lafiya,gobe kuma ta tashi da zazzaɓi, ga ciwon ƙirji musamman saitin zuciyarta kusan duk dare sai ta yi fama. Yau kwana uku kenan da ta fara aman jini,na yau kuma ya tayar da hankalinta ganin aman da yawa,ga ƙirjinta da yake mata wani irin raɗaɗi wanda bata saba ji ba,ita dai ba za ta kira hakan da ulcer ba tun da bata cika wasa da cin abinci ba. Mairi ta lula tunani bata ankara ba ta ji HAFIZA na waya da alamu da Jamila take wayar. Da sauri ta yi yunƙurin miƙewa sai kuma ta kasa saboda wani irin azazzaben ciwo ta ji ƙirjinta yana yi tamkar zuciyarta za ta tarwatse. Babu yadda ta iya sai ta zuba mata idanu don ko maganar ta kasa yi. HAFIZA ta natsu cikin siriryar muryarta tana faɗa ma Ammu Jamila halin da Ammunta ke ciki a waya. A nutse take sanar mata duk abin da yake faruwa da Ammunta har da yadda kullum take riƙe ƙirjinta. Sosai hankalin Jamila ya yi mugun tashi,a take ta ce mata gata nan zuwa,sai ta katse kiran. Mairi kam sai kallon HAFIZA take cike da mamaki saboda bata taɓa tunanin tana lura da duk motsinta ba,ashe har kukan ta take duk dare idan ta tuno da mijinta tana sane. Hawayen gefan idanunta ta share tana sake lumshe idanu,hannunta ɗaya a saitin zuciyarta. HAFIZA bayan ta yanke kiran, ta lalubo lambar Jalil ta kira,a bugun farko ya ɗauka tare da faɗin

''Assalamu Alaikum Ammunata! kin yi kewata hala''

''Yaa Jalil ni ce'' ta faɗa a sanyaye

''Ohhh! Auta ce! Ya kike? Ina Ammuna''

''Yaa Jalil bata da lafiya har aman jini ta yi yau''

Take zuciyar Jalil ta yi wata iriyar halbawa,kamar tana kallonsa ya zaro manyan idanunsa da suke iri daya da na Mairi. Cike ta tashin hankali ya ce

''Aman jini HAFIZA! Da gaske kike?"

Cike da ƙosawa don ta gaji da maganar ta ce

''Eh!''

''Ok! Zuwa gobe za mu zo in shaa Allah! Bata wayar na mata sannu''

Ba tare da ta ce komai ba ta kara mata wayar a kunne tana faɗin

''Yaa Jalil ne''

Jinjina kai Mairi ta yi a hankali ta ce

''Ɗana''

''Na'am Ammuna! Ya jikin naki! Ashe baki da lafiya amma baki sanar mana ba! Har aman jiki kike HAFIZA ta ce''

Ɗan murmushin ƙarfin hali ta yi, a raunace ta ce

''Wasa fa take muku,ni lafiyata lau karku tayar da hankulanku''

A can Jalil ya girgiza kai don bai yarda da maganarta ba,daga jin muryarta ya fahimci bata da lafiya,tana so dai karsu tayar da hankulansu ne. Cike da damuwa ya ce

''Ammu muryarki kaɗai ta tabbatar mini baki cikin ƙoshin lafiya,zuwa gobe za ki ganmu in shaa Allah. Allah ya baki lafiya ya sa kaffara ne kin ji Ammunata''

A hankali ta furta ''Ameen'' daga haka ya katse kiran.  HAFIZA ta kira Yasir sai dai bai ɗauka ba saboda yana lectures. Ɗaki ta nufa ta sauya kayanta zuwa na gida sannan ta wuce kitchen,bata iske komai ba hakan ya tabbatar mata Ammu bata yi girki ba, garri ta jiƙa da suga da saka madara ta zuba gyararriyar gyaɗa a ciki sannan ta rufo kicin ɗin ta dawo falon kusa da Ammu ta zauna sai ta fara sha. A can ta dubi Mairi

''Ammu kin ci abincin rana kuwa"  ta yi magana tana dubanta

Jinjina mata kai ta yi. Ɗan turo mitsitsin bakinta ta yi gaba a shagwaɓe ta ce

''Ni dai ban yarda ba Ammu, ba kin yi amai ba! Kuma kin ce idan mutum ya yi amai dole sai ya ci abinci''

''Ai ni babba ce HAFIZA! Ba sai na ci abinci ba idan na yi amai!"

''Um-um Sai kin sha garin nan. Tashi Ammu" ta yi maganar tana zama a gefan kujerarta. Ɗan dafe kanta ta yi saboda yadda yake sara mata,ta san darun HAFIZA, tun da ta ce sai ta sha garin idan bata sha koda cokali ɗaya ba ne ta dinga damunta kenan. A hankali ta zauna, HAFIZA ta ɗibo cikakken cokali ta kai bakinta.

''Ni kuwa Auta ina zan kai garin nan,rage mini ya yi yawa''

Noƙe kafaɗarta ta yi ta ce

''A'a ai kin fi ni ƙaton baki''

Ɗan Murmusawa Mairi ta yi sannan ta buɗe bakinta ta saka mata garin,duk yadda ta so ta doje da shan garin HAFIZA ta ƙi,tare suka shanye sannan ta kai kofin kicin ta ɗibo  ruwa a kofi ta kawo mata. Kasancewar yau Alhamis ranar hadda sai kawai ta fasa zuwa tun da Ammunta bata jin daɗi. Lokacin sallar Asr ya yi suka yi sallar a tare sai HAFIZA ta nufi kicin ɗin ta hura wutar gawayi,suna da miyar tumatur sai kawai ta ɗora musu farar shinkafa.Babu laifi Hafiza ta ɗan iya girki duk da ba sakar mata ragamar girkin Mairi take ba amma irin jollof ɗin taliya, shinkafa duk da ɗan iya. A ɓangaren aikin gida wannan ta iya sosai,tun daga gyaran ɗaki, wanke-wanke da dai sauransu...✍️

^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

Keke napep ɗaya Aunty Saudah ta ɗauka kasancewar Gwaggwon Bugaje ta zo da kaya sosai,bayan sun sauka ta biya kuɗin sannan ita da Autar mamarta suka kama jakar zuwa flat ɗin Gwaggwon Bugaje na biye da su. Zuwa yanzu ta ƙara tsufa,fatar jikinta ta fara yaushi,har ta gashin giranta furfura ne. Sanye take cikin riga da zani irin ɗinkin tsofaffi ta yafa mayafi. Bayan sun shigo Sahura da ke kicin ta fito fuskarta ɗauke da sihirtaccen murmushi ganin uwarta mai maganin damuwarta.

''Gwaggota ta kaina sannunku da zuwa! Kun sha hanya''

''Yawwa! Ai Mun sha hanya kuwa,don ma da asussuba muka taso, da ba mu iso yanzu ba''

''Gaskiya dai! Ga ruwa ku jiƙa maƙoshinku. Ɗayyaba auta ya yaran? Shi ne baki zo da ko ɗaya ba'' ta yi maganar tana sakar mata murmushi. Ɗan murmushin yaƙe Ɗayyaba ta yi ba tare da ta ce komai ba. Gwaggwon Bugaje ce ta ce

''Ai mijin ya saketa har saki uku Uwata''

Waro idanu ta yi waje tana faɗin

''Don Allah Gwaggo! Garin ya haka! Ba tana da mallaka ba! Aunty Saudah zubo musu abinci" Ta yi maganar tana zama kusa da Gwaggwon Bugaje. Cike da takaici Gwaggwon Bugaje ta ce

''Hmmm! In ji mai ciwon baki! Ai shegiyar uwarsa ce hatsabibiya ta warware mallakar sannan ta saka shi ya yi mata saki har uku irin yadda uwar tsohon mijinki ta yi miki. Abin ban haushin ta hana ta ɗauki yaran''

''Lallai wannan matar ta ciko uwar wuta, wato har da yaran ta tattara saboda samun gindin zama. Baki koma wurin boka Ataka ba ne?"

''Aikin gama ya gama ai,saki uku fa! Miye amfanin zuwana. Shi ya sa na zo da ita nan ta zauna da ke,idan ta samu miji ko a cikin sojoji ne ta yi auranta a nan''

''Hakan kuwa ya yi Gwaggo. Kin ga idan ta samu babban soja mun warke''

''Da kuwa na yi farin ciki har da taka rawa'' ta yi maganar tana dariya. 'yar dariya suka yi su ma. Abincin da Aunty Saudah ta kawo musu suka fara ci suna ɗan taɓa hira jefi-jefi. A nan Sahura take sanar mata Aunty Saudah ta samu miji kuma mai kuɗin gaske. Farinciki sosai Gwaggwon Bugaje ta yi. Bayan sun kammala cin abincin ta yagar musu naman kazar da gorar fanta ɗaya ta tsiyaya musu a kofi ta miƙa musu baki har kunne suka amsa suna godiya. Ɗayyaba kyakkyawar mace ce wacce ba za ta haura shekara talatin da biyu ba,yaranta biyar ne duk maza tana aure a cikin Sakkwaton kusa da unguwarsu Gwaggwon Bugaje,kusan halinsu ɗaya da Sahura sai dai ta ɗan ɗara Sahura a tausayi. Mahaifiyar mijin ba a zaune take ba,ita ma kamar su Gwaggwon Bugaje ce,tana bin malamai da bokaye don biya ma yaranta maza ta mata buƙata,shi ya sa mallakar Ɗayyaba bata wani jima ba wanda daga ƙarshe ya saketa kuma ya amshe yaran.

Su Sahura na tsaka da hira Nu'aymah,Maryam da Amina suka shigo flat ɗin. Babu shiri suka yo kan Gwaggwon Bugaje da gudu suka rungumeta suna mata oyoyo musamman Nu'aymah da suka fi shiri. Ko cire kayan makarantar ba su yi ba suka soma cin abinci,suna tsaka da ci Halima da tawagar ƙawayenta suka ma gidan tsinke. Cike da girmamawa suka gaishe da 'yan ɗakin. Halima ta dubi Gwaggwon Bugaje,suna haɗa ido ta ƙyafta mata tare da faɗin

''Yawwa Gwaggwon Bugaje gwara da Allah ya sa kina nan. Na ce ma ƙawayena lokacin da kika je aikin hajji kin yi hoto da maman Sudais kuma hoton yana a wayar Aunty Saudah,shi ne ba su yarda ba suka ce sai na kawo su sun gani da idanunsu''

Buɗar bakin Gwaggwon Bugaje ta ce

''Yo har sai sun ga hoton! To bari ku ji 'yan mata ni nan da kuke gani ba maman Sudais kaɗai ba har da maman sarkin Makkah na yi hoto da ita''

''Ikon Allah! Ashe Halima ba karya take ba'' cewar Haulat.

''A'a gaskiya ta faɗa muku,ai muna da dangi masu kuɗi sosai a Saudiyya'' cewar Sahura.

Halima kamar an tsomata cikin aljanna tsabar farinciki,ko babu komai sun wanketa a gaban ƙawayenta. Ɗari bisa ɗari ƙawayenta suka yarda,suka musu sallama Halima ta rakasu. Bayan ta dawo ta daka tsalle tana faɗin

''Yes! Asirina ya rufu! I'm now saved, Gwaggwon Bugaje kin iya barikanci''

Murmusawa Gwaggwon Bugaje ta yi sannan ta ce

''Ai tun da kika ƙyafta mini ido na fahimci inda kika dosa,ko babu komai mun kankaro mini mutunci a idonsu sannan za su yarda mu ba talakawa ba ne''

''Wannan haka yake Gwaggo,shi ya sa ni ma saka baki'' cewar Sahura

''Ni kuwa ina yaran kishiyarki ne ban ga gilmawansu ba''

Ɗan tsuke fuska Sahura ta yi sannan ta ce

''Hamida na san tana gidan maman Jawaheer,Yasir kuma ya tafi boko. Shegen cikinsu yana gidan officer ''

''Ya yi kam! Ni ba...'' maganarta ta katse sakamakon shigowan Hamid hannunsa riƙe da ƙaton MP3 yana jin waƙar Nairi Marley ta TESIMOLE sanye yake cikin ƙananun kaya ya zazzago da wandonshi ƙasa a ta baya  kaɗan. Gashin kansa a murmurɗe kamar na dada. Babu sallama ya faɗo falon kamar an jefoshi yana bin waƙar.

''Mijina kana sha'aninki!''

''Yeah tsohuwa mai ran ƙarfe! How far ya tsufan! Na ga sai ƙara kyau kike 'yar tsohuwa mene ne sirrin''

Daƙuwa Sahura ta yi masa da cewa

''Kai Hamid ka kiyaye ni! Me ya sa ka raina mini uwa har haka. Ya maka kyau''

''Bashshi Uwata, idan bai tsokane ni ba wa zai tsokana.''

''Haka ne kam''

Wani shafin hira suka buɗe,Hamid kuma ya wuce kicin ya sako abinci ya fito falon ya fara ci yana ɗan bin waƙar. Hamida ta shigo falon bakinta ɗauke da sallama. Babu wanda ya amsa mata sai ma harar da kowa yake aika mata a kaikaice, bata damu da hakan ba ta juya za ta nufi ɗakinsu Gwaggwon Bugaje ta tsaka mata tsawa tana faɗin...✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen✍️

***