KADDARARMU CE....9
by @nusybee143
🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)
✍️Nusy bee
*❤️ Young talented writers association YOTA ❤️*
My TikTok account 👇
***
My Instagram account 👇
***
My arewa pen link 👇
https://arewapen.com/u/nusybee143
*TALLA!TALLA!!TALLA!!!*
*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.
*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL,👇*
***,
***
Page 9
Wani mugun kallo Hayat ya yiwa Ashraf da ko kallon banza bai yi masa ba,ya ja tsaki ya fara cin abincinshi zuciyarshi duk babu daɗi,shi dai Ashraf har yanzu hankalinshi na kan wayarshi da yake ta faman dannawa,ita dai Lateefa bata saka musu baki ba,kallonsu kawai take yi,sai ta kalli Najma da har yanzu babu alamun ta san da zamansu a kan fuskarta
Sun kai a ƙalla rabin awa suna cin abincin,daga baya ma hirar ayyukansu suka fara yi,still Lateefa tana tsaye tana kallonsu,babu wanda ta sake yiwa magana,haka zalika babu wanda ya yi mata magana,sai da suka gama za su tafi ta tafi da sauri ta ɗan rungume Ashraf tana murmushi ta ce
"To sweetheart Allah ya tsare min kai, I'm gonna miss you my other half"bai tanka mata ba,kamar yadda bai bata haɗin kai a abinda take yi ba,shi dai Hayat ya harɗe hannayenshi a ƙirji yana kallon wannan yarinyar da ya kira da ballagaza marar tarbiyya,don shi a ganinshi mace mai mutunci ba zata rinƙa rungumar namiji irin haka rondomly ba, musamman ma wanda bai damu da ita ba irin Aliyu Ashraf
Ashraf ne ya fara yin gaba shima Hayat ya bi bayan shi,kai tsaye suka nufi parking lot, motar Ashraf suka faɗa suka fice suka bar gidan
Ashraf bai dawo ba sai wajen ƙarfe goma da rabi na dare,don bayan ya sauke Hayat a gida,duk da yadda Hayat ya rinƙa yi masa magiyar ya tafi gida kar ya tsaya wani wajen amma Ashraf bai ji ba, don sai da ya siya kwalaben giyarshi da cigarrete ɗinshi sannan ya nufi gida
Kai tsaye bayan ya isa kayanshi ya ɗiba zuwa part ɗin shi,yana shiga banɗaki ya faɗa ya yi wanka,bayan wasu mintuna ya fito sanye da bathrobe ya fara murza mai a jikinshi
Cak ya tsaya da murza man yana kallon hoton da ya yi appearing a katafaren madubin ɗakin nashi, tsurawa hoton idanu ya yi rauni yana bayyana akan fuskarshi,a hankali ya yi ƙasa da kanshi,wani irin sanyi yana mamaye jikinshi,ya sake ɗaga kai ya kalli hoton matar da ke bayyane a tangamemen madubi shi,kamar mai ciwon wuya sai kuma ya waiga yana kallon hoton, lokaci ɗaya kuma ya miƙe ya nufi inda hoton yake yana kallonshi tamkar yau ya fara ganinshi,hawaye suka fara kwanciya a kwarmin idanun nashi
"Mum!"ya furta a hankali tamkar wadda aka yiwa dole"I lost, I lost everything with me, you are my everything, meyasa za ki tafi ki barni a lokacin da nake matuƙar buƙatarki?
Mum kin san bani da kowa a duniya sai ke,ke ce farin ciki na,ke ce walwala ta,ke ce maganin kuka na, Allah ya yi miki rahama, Khairan in sha Allah mum!"ya yi saurin goge ƙwallar idanunshi ya cigaba da shirinshi na bacci
Washegari wajen ƙarfe goma ya shigo part ɗin Ammi,jiya bai yi bacci ba sai da ya samu ya kwankwaɗi barasarshi, yanzun kuma bai fito ba sai da ya tabbatar mayen ya sake shi,ya yi wanka ya shirya cikin ƙananun kaya ya nufo parlourn Ummi
Kusan karo suka ɗan ci,da sauri ya ja baya yana kallonshi,kallon kallo suka yiwa juna kafin kowa ya ɗauke kai, Ashraf ya shige cikin parlourn,shi kuma Rayyan ya fice yana jan tsaki
Yana shiga gabanshi ya buga sakamakon ganin Maleeka a zaune tana danne danne a system ɗinta,daga ita sai riga fara da wando three quarter pink colour,kanta babu ɗankwali sai brown gashinta da ya sha gyara da ta sake shi bayanta
Sam sam babu niyyar amsa sallamar da ya yi a tare da Maleeka, Najma da ke gefe tana kallonsu ta taɓe baki tana dauke kai,bata san meyasa ba ta tsani waɗannan mutane biyun,ko da yake ta sani,hakan baya rasa nasaba da alaƙar da ke tsakaninsu da Ummi da kuma yadda Ummi ta girmama su da babban matsayi,ita kuwa Maleeka bata ɗago ko da wasa ta kalli komai na parlourn ba,don babu abinda yayi mata,kuma babu wanda ya yi mata
Ɗauke kanshi ya yi,kai tsaye ya nufi main parlour ɗin Ummi,a can ya samu mimi,ta taho da gudu ta ɗane shi tana faɗin
"Good morning big brother!"
"Morning sweetheart!yau ina school na ganki a gida?"
Baya ta ɗan ja tana ƴar dariya ta ce "yaya hutun second term fa muka yi,ko ka manta ne?"
Ɗan zaro idanu ya yi ya ɗan dafe kai ya ce"oh shit!kin san ni da mantuwa fa"Mimi ta yi ƴar dariya,ya ƙarasa inda Ummi ke zaune tana kallonsu tana murmushi zuciyarta cike da ƙaunar yaran nata
Zama ya yi a kan kujera ya gaida Ummi,ta amsa cikin fara'a,ta tambaye shi lafiyarshi,ya amsa mata komai ƙalau
Sun ɗan taɓa hira sosai,cikin hikima da dabara irin ta uwa ta yi ta masa nasiha da jan hankali,shi dai shiru kawai ya yi jikinshi yana sanyi,gaba ɗaya baya jin daɗin ɓatawa duk wanda ya kasance masoyinshi,he wish zai iya chanja rayuwarshi,da bai cigaba da ɓata ran mutanen da ke kusa da shi ba
Sun ɗan juma suna hira kafin ya miƙe cikin sanyin jiki ya fice zuwa main parlour inda Maleeka da Najma suke zaune, kowacce da abinda take yi
Kallo ɗaya ya yiwa sashen da Maleeka take ya ɗauke kanshi, Najma kam bai nuna ya san Allah ya yi tsiron halittarta a wajen ba,ita ce ma ta bishi da wani mugun kallo fuska a gatsine,kafin ta tsartar da yawu tana jan tsaki
Wayarshi ce a hannunshi yana danne danne, Rayyan ne ya shigo parlourn fuskarshi a sake, Najma ma ta saki fuska tana kallonshi,cikin sakin fuska ta ce
"Good morning bruh!how was your night?"
Wani miskilin murmushi ya yi yana kallon sashen da Ashraf yake, tamkar bai ma san da zaman Maleeka ba,ya ce
"Good morning big brother, Mr Aliyu Haidar"
Batare da Ashraf ya kalle shi ba ya yi nodding kan shi, Rayyan ya mayar da kallonshi ga Najma ya ce"I hope kin gaida babban yaya"Najma ta kyaɓe baki tana juya idanu ta ce"ni kuma?ka san idan mutum ya isa ai ba gaisuwar kowa yake amsawa ba"
Rayyan ya zauna yana cafe maganarta da faɗin"kazalika idan mutum ya isa ba kowa yake gaidawa ba"
Najma ta kwashe da dariya tana kallon sashen da Maleeka take zaune,wadda har zuwa yanzu babu wanda ya ishe ta kallo a parlourn,ta ce"kuma ka san shi girman kai ga mace ai ba ado bane,abu ne wanda yake abin kunyar bayyanawa, ga mace wadda bata cika mace ba,ko mun rako mata ita ce take ganin girman kai a matsayin ado"
Rayyan ya yi ƴar dariya yana girgiza kai yana faɗin "kuma a ƙare girman kan a auri wanda aka gama wulaƙantawa ba"
Najma ta saka dariya,ta sake kallon sashen da Maleeka take tana harararta,a gidan babu wadda ta tsana sama da Maleeka, saboda girman kai da gadararta da suka yi yawa,abin haushin ma shine Ummi bata ishe ta kallo na indai ba ita bace ta gaishe ta,bata yiwa kowa magana sai wanda ya yi mata da girmamawa,shima sai ta ga dama zata amsa, Najma ta miƙe rai a ɗan ɓace ta nufi fita daga parlourn,amma kafin ta fice sai da ta taka ƙafar Maleeka da ke zaune tana wasa da dogon gashinta tana ta danne danne a laptop
Ko nuna alamun ta san Najma ta wuce bata yi ba,sai dai ta daina danna laptop ɗin ta janyo waya ta fara dainawa,bayan ɗan lokaci ta ajiye wayar ta cigaba da abinda take yi
Rayyan waya ya kama amsawa yana ta shaƙiyancin shi yadda ya saba,shi kam Ashraf ji yayi ma gidan ya ishe shi,ya miƙe ya fice don tafiya gidansu Hayat da kusan ya fi jin daɗin rayuwa a can fiye da gidan mahaifinshi
Daidai bakin gate yana ƙoƙarin fita da mota ya ga motar ƴan sanda na ƙoƙarin shigowa, ɗan bin su ya yi da kallo,a ranshi yana gulmar su kuma waɗannan me ya kawo su,bai tsaya ba dai,ya ja mota ya bar gidan a guje
MAITAMA, ABUJA, NIGERIA
"Well Haleema!why wani lokacin idan yara suna abu sai ki yi ta biye musu?ina Faisal ina aure don Allah?in dai ba ɗauko magana ba for sure kema kin san Faisal bai kai aure ba ko?"
Hajiya Haleema(Momma)ta ja ajiyar zuciya ta sauke,cikin kwantar da murya ta fara yiwa mijin nata bayani
"I'm sorry dear!kaina ne ya kulle gaba ɗaya wallahi, I understood that he loves that girl wholeheartedly, and....."
"Who is she? I mean the girl,ƴar wanene ita a ƙasar nan?"
Mum ta sauke numfashi ta ce"I can't tell,but in sha Allah zan bincika"
"Noooo Haleema,what do you mean?are you telling me kina barin yarona yana mingling da yaran da bai dace ya kula ba? wannan shine adalci kenan?"
Momma ta ɗan langwaɓar da kai tana faɗin"ayi min afuwa Dada,ka san yaran zamani ka haife su baka haifi halinsu ba,banda haka kaima ka san babu yadda za'a yi Faisal ya yi soyayya at his age,yayyenshi ma ba su yi aure ba sai shi saboda neman rigima irin na yaran zamani?for God sake fa!
Amma in sha Allah zan kawo ƙarshen abin,don na yi masa alƙawari cewa xan shige masa gaba a maganar neman auren,amma ba za'a yi auren ba sai yarinyar ta gama makaranta,tunda ya tabbatar min da cewa yarinyar is about to finish her secondary school "
Alhaji Nazir ya zuba mata idanu kafin ya ce"kuma dai,kai yara da shiririta suke,just yarinya secondary holder har ta san wai ta yi saurayi?"
Maganar ta bawa Momma dariya,Dada ya ce"seriously fa Haleema, yarinya kamarta suppose to focus on her SSCE,amma sai su saka ɗa namiji a ransu,sai abu ya kwaɓe a zo ana ya akayi ya aka yi,amma babu masu babban laifi kamar iyayenta "
"No Dada, don't blame her parents,ɗan yau ka haife shi ne baka haifi halinshi ba,banda haka shi Faisal da ya fara yayibo ta haka muka saka shi?"Dada ya ce"kuma haka ne fa, Allah ya sa yarinyar nan ma bata dace da tsarinmu ba,don in dai haka ya faru dole ya rabu da ita "professor Haleema ta ɗauke kanta tana faɗin"Ameen Alhaji"
DODAN BARRACK, IKOYI, LAGOS STATE, NIGERIA
"To ni zan fita ko?"
Ɗaga kai Maimuna ta yi yana kallon Major Ahmad da ya kammala shiryawa cikin wani tsadadden suit da suka amshe shi sosai,a hankali ta ɗauke kai ba tare da ta sake magana ba,shima bai damu ba ya ɗauki briefcase ɗinshi ya nufi ficewa daga ɗakin
"Ji mana!"ya ji muryarta a zafafe,tsayawa ya yi ya waigo yana kallonta,a hargitse ta miƙe ta iso har daf dashi ta ce
"Ina za ka tafi kake nufi?"
"Na gaya miki Abuja zan tafi,akwai aiki mai muhimmanci da zamu yi, flight ɗinmu ma by 4:00pm ne,gashi kuma 3 ta kusa,bana son makara don Allah,stop creating issues Maimuna "
Tana huci ta ce"amma kuma wa za ka barwa Ni?ka kawo ni gari sannan kuma kana maganar za ka tafi wani wajen ka yi aiki,wai me kake nufi ne?"
Ganin da gaske so take ta ɓata masa lokaci sai ya kwantar da murya ya ce"don Allah kar ki damu,ba zan wuce nan da kwana uku ba,in sha Allah ko zan wuce zan tura miki kuɗin jirgi ki dawo kusa da ni, You know I can't do without you "ɗan murmushi ta yi,a zahiri dalilin kalmomin da ya yi amfani da su ne,amma a baɗini ta ji daɗin batun kuɗin nan,don ta san zai turo ninkin wanda za ta buƙata
Ita ta raka shi har bakin gate,ya faɗa mota driver ɗinshi ya ja suka bar barrack ɗin,ta dawo cikin gida zuciyarta cike da farin ciki,don zata fara aiwatar da mugun aikinta a nutse
Magungunan da su Fareeda suka kawo mata ta ɗauko ta fara aiwatar da mugun nufinta,a yanzu tsanar da take ji ta Aneesa bata jin koda kwatankwacinta akan A'isha mahaifiyarta, don A'isha ma sai yanzu ta fuskanci ba wani wayo ne da ita,amma kiran da Aneesa ta yi mata jiya da maganganun da ta yi mata cikin hikima ya tabbatar mata da ta gane ita ta saka Fareeda ke rainawa mahaifiyarta hankali,kuma ta yi mata kashedi cikin hikima da dabara,sannan ta sake nuna mata a bayyane cewa ta san asiri ta yiwa mahaifinta,amma su kam babu abinda zata iya yi musu, shiyasa yau ta ɗauko magungunan da ta saka a yi mata don ganin bayan Aneesa ta gani tsakanin su biyun waye mai nasara?
To pa!tsakaninsu wa kuke ganin zata yi nasara??
#Nusy_bee
***