ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

ƘADDARARMU CE....10

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)

✍️ Nusy bee 
❤️*Young talented writers association YOTA*❤️ 



My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143



*TALLA!TALLA!!TALLA!!!*

*SHIN RAMA CE MATSALARKI? BUSHEWAR JIKI KO KUMA MATSALAR SANYI? TO ALBISHIRINKI, NA ZO MUKU DA INGANTACCIYAR SABAYA DA AKA SARRAFATA DA NATURAL GRAINS, HERBS DA KUMA SPICES, WADDA ZA TA INGANTA LAFIYAR JIKINKU, TA CIKO DA JIKI, SAMAR DA RUWAN NONO GYARAN BREAST, TA KUMA YI MUKU MAGANIN SANYI DA MA SAURAN GYARAN JIKI NA MATA, DUK A KAN KUƊI ƘALILAN. SABAYARMU BA MA SANYA ƘWAYA A CIKINTA, DA TSIRRAI KAWAI MUKE SAMAR DA ITA. SANNAN AKWAI MAGANIN SANYI GA MASU FAMA DA MATSALAR INFECTION KOMAI DAƊEWARSA. AKWAI COMPLETE SET NA GYARAN BREAST, SPECIAL PACKAGE, KU NA IYA TUBTUƁA TA KAI TSAYE KU TUNTUƁE NI AYSHERCOOL TA LAMBOBIN WAYATA ****.


*WELCOME TO MARYAMA'S COLLECTION,DEALERS OF ALL KIND OF BABY AND ADULT WEARS AND KITCHEN UTENSILS, FOR MORE INFORMATION, CONTACT US VIA WHATSAPP OR PHONE CALL, 👇*
***, 
***

Page 10

Misalin ƙarfe biyu na dare Maimuna tana zaune a ɗaki,daga ita sai wani jan ƙyalle da ta ɗaura a jikinta,daga ƙirji zuwa gwiwa,kanta babu ɗan kwali,sai wani jan ƙyalle da ta ɗaura a goshinta, hannunta riƙe da wata kalar ƙwarya wadda bata da kyan gani,wasu irin halittu ne a cikin ƙwaryar masu ban tsoro,amma sam ko tsoro bata ji,a hankali ta fara karanta wasu siddabaru,take wani baƙin hayaƙi ya mamaye ɗakin,ya yi duɗum,ta runtse idanunta tana ƙwala kiran 

"ANEESA! ANEESA!! ANEESA!!!"bayan wani lokaci hayaƙin ya washe ya ɓace ɓat tare da halittun cikin ƙwaryar nan

Miƙewa tsaye ta yi tana ɗan murmushi,a hankali ta furta "uwarki bata zame min tarnaƙi ba,ke ba ki kai wannan matakin ba"daga haka ta fice zuwa ainihin ɗakinta





SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 


A matuƙar firgice Aneesa ta farka daga nannauyan baccin da take yi gabanta yana faɗuwa,ta kama waige-waige sakamakon wani motsi da take ji a ɗakin, take jikinta ya kama karkarwa,ta yi saurin janyo hularta ta rufe gashinta da yake bayyane, daidai lokacin ta ji an kece da dariya,ta fara karanto dukkan addu'ar da ta zo bakinta a bayyane,a hankali ta fara jin nutsuwa ta fara shigarta, hayaniyar da take ji da ɗan giftwar halittun duka suka ɓace ɓat tamkar ɗaukewar ruwan sama 

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke,cikin mutuwar jiki ta zuro ƙafafunta daga kan gadon,har yanzu jikinta na rawa,kai tsaye ta nufi banɗakinta ta yi alwala ta dawo ɗakin ta ɗauki darduma ta fara sallah

Ba ta kwanta ba sai bayan da ta idar da sallar asuba ta yi azkar,bayan ta kwanta ɗin ma bacci ya ƙauracewa idanunta,gaba ɗaya mamaki ne ya mamaye ta,dama gidan nasu da aljanu ne? ko dai jiya suka zo?kai ko dai tana da aljanu ne itama?

Juyi ta yi akan gadonta,ita dai iyakar saninta bata san tana da wasu aljanu ba,amma bata sani ba ko jiyan ta samu,dole ma ta sake dage dantse da addu'o'in neman kariya,don yadda take ji da labarin masu aljanu ta san suna shan wahala,dole ta yi riga-kafi wanda aka ce ya fi magani

Da ƙyar ta samu bacci ya ɗauke ta,da ta yi bacci ma sai da ta yi mafarki,don sosai ta saka abin a ranta,don Aneesa akwai ta da saka abu a rai

Ranar bata da exam,yini ta yi tana tuna abinda ya faru,gashi ta kasa gayawa kowa,ciki har da Ammi da ta dawo daga aiki wajen ƙarfe tara na safe,a lokacin su Al'amin gaba ɗaya suna makaranta 

Da yamma tana zaune a ɗakinta ta ji an yi sallama,ranar Ammi bata da night duty,tana zaune a parlournta yana yankewa Hafiz farce,ta amsa,matar ta shigo tana sake gaida Ammi fuska a sake

Ƙwalawa Aneesa kira Ammi ta yi, Aneesa ta fito tana gyara zaman hularta da ta cire saboda kwanciyar da ta yi, Ammi ta ce"kawowa baƙuwa ruwa"

A ɗan kaikaice ta kalli baƙuwar da take kallonta tana murmushi,haka kawai ta ji bata yarda da baƙuwar ba,ta wuce kitchen ta ɗebo ruwa da lemo a fridge ɗin kitchen ta zubo su akan tray ta nufo Parlourn 

Tana gaida baƙuwar tana ɗan satar kallonta, baƙuwar ta amsa da matukar fara'a,ta miƙe tana taɓe baki,don ita baƙuwar ma kama take yi mata da karuwai, saboda yanayinta,tsabar bleaching har wani kore kore take yi,ga gaban kanta duk ya cinye saboda attaching 

Maimakon ta koma ɗakinta kamar yadda take zaune ɗazu sai ta nemi waje ta yi zamanta a tsakar gida inda zata iya jin abinda Ammi da baƙuwar suke tattaunawa 

Ji ta yi baƙuwar tana faɗin "maman Aneesa ya gida?ya yara kuma?"

Ammi ta ce"alhamdulillahi kowa lafiya,ya hanya?"

Baƙuwa ta ce"hanya alhamdulillahi mun shawo ta"

"Mamie ta ce"to madalla,sai dai ban gane ki ba"ta ƙarashe tana ɗan murmushi 

Murmushi matar ta yi itama sannan ta gyara zama ta ce"ba ki sanni ba dama

Sunana Salma ne,na kasance mazauniyar barikin da mijinki yake zaune yana aiki,nima mijina soja ne

Dama zuwa na yi ma gaya miki ki yi hankali da matar mijinki,ko na ce kishiyarki"

Gaban Ammi ya buga dam!amma ta dake ta ce"wani abin ne ya faru?"

Jinjina kai matar ta yi ta ce"of course yes!

Suna auren namijin da ke da mamora ne su tatike shi bayan sun raba shi da kowa nashi,su ɗaiɗaita masa iyalai suma su kama gabansu,ko haihuwa ba sa yarda su yi

Ke taki bayan wannan ta haɗa da makirci saboda ganin yadda mijinki yake sonki,da farko ta saka wata ƙawarta ta kira ki a waya wai ta zuga ki har ki tayar da rikici tsakaninku ke da mijinki,ganin haƙarta ta gaza cimma ruwa sai kuma ta saka wannan ƙawartata ta rinƙa amsar kuɗinki da sunan za'a je wajen malamai ayi miki roƙo,wannan karon aka yi dace kika bayar 

Dama zuwa na yi na ankarar da ke tarkonsu,don ko jiya ta yiwa babbar ƴarki ture,amma kuma bata yi nasara ba"

Da sauri Aneesa ta dafe ƙirjinta jin wai abinda ya same ta ture ne daga matar mahaifinta,da sauri ta fara ambaton sunan Allah a ranta,mamaki da tsoro ya mamaye mata zuciya,ta miƙe jiki a sanyaye ta bar wajen ta koma ɗakinta 

Bata san yadda wannan baiwar Allah suka ƙare da Ammi ba,ita dai Ammi ta kira ta bayan ta ji matar tana yi mata sallama, daga baya ta ji tafiyarta,ta miƙe cikin sanyin jiki ta nufi parlourn Ammi 

Kallo ɗaya ta yiwa Ammi ta ga yadda jikinta ya yi wani irin sanyi,ta ɗauke kanta cike da tausayin Ammin,cikin jimami Ammi ta ce

"Aneesa dole fa mu ƙara dagewa da addu'a,kin ji ashe wai matar abbanku bata daina bibiyarmu da sharri ba?"

Waje Aneesa ta samu ta zauna kanta a ƙasa,cikin sanyin murya ta ce"shiyasa na ce kar ki yarda da maganar matar nan Ammi,amma ba ki yarda da ni ba,Ni na gane ba mutuniyar kirki ba ce,wannan ma da ta zo bana jin shima zuwan ba wani ɗin plan aka shirya ba

Idan mutum ya ce baya sonka to har abada baya sonka, hanyar ganin bayanka kawai yake nema "

Shiru Ammi ta yi kawai tana juya lamarin a ranta, Aneesa ta ce"addu'a kawai da neman tsarin Allah shine maganin komai,shi zamu cigaba,da ikon Allah babu wani azzalumi da ya isa ya yi nasara a rayuwarmu"cikin sanyin murya Ammi ta ce"to Allah gamu gare ka, Allah ka iya mana da iyawarka "Aneesa ta amsa da"Ameen Ammi "





ASOKORO, ABUJA, NIGERIA 


Da ƙarfi yake danna horn ɗin motarshi,da gudu mai gadi ya wangale tangamemen gate ɗin, ba tare da ɓata lokaci ba ya danna hancin motar,kai tsaye ya nufi ƙaton parking space na gidan,ko gama daidaita parking bai yi ba ya fito ya nufi cikin gidan,gaba ɗaya hankalinshi baya jikinshi,tunda Ummi ta kira shi ya rasa nutsuwarshi, musamman yadda take kuka ya san ba lafiya ba

Yana shiga main parlour ya bi kowa da kallo, Najma ce tsaye tana kuka,two female police sun buga mata ankwa,ga Ummi tana share hawaye, Mimi tana maƙale a jikinta tana nata kukan,ga Rayyan daga gefe a tsaye,da alamu lamarin ya tsorata shi,ga kuma Abby da bai san sanda ya dawo ƙasar ba,yana tsaye yana aiko masa da wani mugun kallo 

Parlourn ya shiga yana sake binsu da kallo jikinshi yana ɗan rawa,a fusace Rayyan ya zo ya shaƙe shi yana aika masa da wani mugun kallo,a fusace yake faɗin "Allah wadaran rashin tarbiyya da rashin ganin girman manya irin naku kai da wawiyar ƙanwarka,rashin mutunci kowa ya iya,sai dai muna ɗaga ƙafa ne kawai saboda darajar manya,kai da alamu baka san darajar naka manyan ba,ko na ce baku sani ba,to wallahi kuna daf da ƙure ni,don ba'a haifi wani ko wasu wawaye da suka isa su wulaƙanta min uwa da yan'uwa in zuba musu idanu ba,bullshit!!!"

Idanu kawai Ashraf ya zuba masa har ya gama kumfar bakinshi,a hankali ya furta"take your hand off my shirt Rayyan!"

Da tsawa Rayyan ya ce"ba zan ɗauke ba, matsiyaci mara tarbiyya,wawa kawai butulu,ina ce mahaifiyar taku da ta rasu kuke ta walagigi tamu mahaifiyar ce ta janyo ku ta rungume,amma ji wulaƙancin da kuke saka mata dashi saboda baku da iymani "

Muryar Ummi ta tari numfashinshi,da tsawa ta furta"Rayyan! menene haka?dalla malam sake shi,bana son shashanci,ko shine ya yi maka laifi?"

Rayyan ya saki wuyan rigar Ashraf ya ja baya zuciyarshi tana suya,cikin ɓacin rai ya ce"Ummi da shi da ƴar uwar tashi bakinsu ɗaya ai,ba shine yake zuga ta tana abinda ta ga dama...."

"Bana son shirme Rayyan,kai Aliyu,ka yiwa Maleeka magana,wai ɗazu sun samu saɓani da ƴar'uwarta Najma sai ta saka aka zo har gida a kamata,mun yi mata magana ta yi mana banza ta shige ɗakinta,hatta abbynku da ya dawo yanzu babu yadda bai yi mata ba amma tayi mana banza,don haka don Allah kayi mata magana ko zata haƙura,sai mu zauna mu yi magana a tsanake,a sulhunta abin, family issue kuma mai ya shigo da maganar ƴan sanda kuma?"

Fuskarshi a ɗaure ya yiwa ƴan sandan izinin fita daga parlourn,babu musu suka fita daga parlourn,bai yiwa kowa magana ba ya wuce sashen Maleeka da ke ɓangare dabam a parlourn 

Da sallama ya shiga har bedroom ɗinta,inda take zaune a gefen tsadadden gadonta tana danna laptop ɗinta,daga ita sai wando iya gwiwa da farar T-shirt,kanta babu ɗankwali,sai brown ɗin gashinta da ya sauka har gadon bayanta,blue eyes ɗinta yana kan computer ɗinta 

Ƙare mata kallo ya yi a seconds,kafin ya fara magana a ɗan zafafe

"Ke wai mene ne matsalarki ne?ya za ki saka a kama ƴar'uwarki da take matsayin ƙanwa a gare ki? meyasa kike abu tamkar mara hankali ne?You chose your lifestyle,babu wanda ya ce miki uffan,so ki yi kalar rayuwar da kike so and leave other people alone please,idan kika ce za ki cigaba da shirme wallahi sai kin yi regretting "yana kai wa nan ya juya da nufin ficewa daga ɗakin 

Kamar daga sama ya ji ta ce"ji mana!"

Tsayawa ya yi ya juya yana kallonta da mamaki,rabon da ya ji muryarta da sunan tana yi masa magana zai iya cewa shekaru biyar kenan zuwa shida,amma dai ya ɓoye mamakinshi yana kallonta 

Takowa ta yi har gabanshi tana jefa masa kallo cikin tsananin tsana,shima kallonta kawai yake yi,cikin isa da gadara da ya zame mata jiki ta nuna shi da yatsa tana faɗin 

"Daga rana irinta yau,anan wajen na shata maka layi da rayuwata,kai da dukkan abinda ya shafi rayuwata,na tsane ka,na tsane ka,ina fatan ka nisance ni ka fita daga rayuwata kamar yadda na fita daga taka 

Babu wata kalma da nake tunani zata yi amfani don ta wanke ka a idanuna,na tsane ka tsanar da ban taɓa yiwa wani ba, wallahi da za'a bani dama na kashe wani rai da kai zan kashe,don haka ka fita daga rayuwata fita ta har abada,don idan ina ganinka zuciyata bazata huta ba,yanzu ka fice min daga nan kafin kaima na saka a kama ka,don ka ji ka sake ji na fi ganin waccan da na saka aka kama da mutunci akan ka"

Ba yau ya saba jin waɗannan kalaman daga bakin Maleeka ba,har ma da waɗanda suka fi su zafi da muni,tun yana jin zafi har ya daina,ya taɓe baki ya juya don ya fice daga parlourn, issues ɗin da ke kanshi ma sun ishe shi,bashi da lokacin ajiye wani issue na Maleeka 

"Ka cigaba da abinda kake yi, Allah yana madakata,baya son zalunci kuma baya son azzalumi,kuma har abada jinin NAINA yana wuyanka,ko ba daɗe ko ba juma sai ka biya bashi,na ci mata zarafi da kuma na kashe ta da ka yi"a hargitse ya waiga yana kallonta,tana gama magana ta ɗauke kanta don ta cigaba da danna laptop ɗinta,ganin ba zata iya cigaba da danna laptop ɗin ba ta miƙe ta shige banɗakin da ke jikin ɗakinta,kuka mai ƙarfi yana ƙwace mata,sosai take jin ciwon da ke zuciyarta yana motsawa saboda tuna Naina da ta yi,ta rushe da kuka sosai tana rufe banɗakin ta kife kanta tana kuka sosai

Ji take inama zata iya kankare alaƙar da ke tsakanin ta da Ashraf,ina ma zata iya kashe Ashraf don ɗaukar matakin abinda ya yiwa aminiyarta,ina ma inama?kuka take yi sosai, tsohon mikin da ke zuciyarta yana taso mata 

Ashraf kam da tsananin mamaki a ranshi ya fice daga part ɗin ya sauka ƙasa a main parlour 

Da kallo ya bi Hayat da ke zaune a parlourn,a nutse Hayat yake ƙarewa fuskarshi kallo ganin tashin hankali da ruɗani akan fuskarshi,bai yiwa Hayat magana ba ya nufi fita daga part ɗin, Hayat ya ɗan ɗaga murya yana faɗin "dude Abby fa na jiranka"






#Nusy_bee