ƘADDARARMU CE....11
by @nusybee143
🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)
✍️ Nusy bee
*❤️ Young talented writers association YOTA ❤️*
My TikTok account 👇
***
My Instagram account 👇
***
My arewa pen link 👇
https://arewapen.com/u/nusybee143
Page 11
Tsayawa ya yi kawai yana kallon Hayat kamar bai gane abinda yake faɗa ba, Hayat kam kallonshi yake yi cike da tausayinshi,kamar wanda aka zarewa laka kuma sai ya juya akalarshi izuwa part ɗin Abby
Da sallama ya shiga rantsatstsen parlourn,Abby ya amsa ciki ciki,kallo ɗaya ya yi musu shi da Ummi ya yi kasada kanshi,ya kutsa kai cikin parlourn ya samu waje ya zauna yana faɗin
"You are welcome Abby!"
"No ka riƙe welcome ɗinka da duk wata gaisuwarka,nima na san ban yi deserving dinta ba tunda na haifi yara irin ku, waɗanda sam....."
"Haba Abby haba Abby!!! menene hakan don Allah?yanzu fisabilillahi ya dace ka zo kana irin wannan kalmomin ga ɗanka wanda mu mun shaida yana yi maka biyayya?ƙanwarshi ce ta yi laifi,kuma shine ya warware matsalar,amma ji faɗan da kake yi masa kamar shi ya yi maka laifi,kuma ko itama da ta yi ai bai cancanci ka yi mata wannan faɗan ba
Haba Abby,ya kamata ka san cewa Aliyu ɗanka ne,kuma yana buƙatar soyayyarka,ko da ace shine ya yi maka laifi kamata ya yi ku yi magana da juna ku fahimci juna,ba wai ka zauna kana masa faɗa ba, ballantana ma abinda ba laifinshi ba,haba don Allah "ta yi shiru tana huci,ranta a ɓace
Kallonta kawai Abby yake yi batare ya ce uffan ba har ta kai aya,a nutse ya sauke numfashi ya ce "kin gama?"
"Eh na gama,ya kamata ka rinƙa sasassautawa yaron da bai yi maka komai ba,da wanne zai ji don Allah?duk ka bi ka tsamgwame shi kamar ba jininka ba"
Abby ya numfasa yana kallonta ya ce"Rumaisa! I'm tired of how you are treating my child!
Gaba ɗaya kin lalata shi kin sangarta shi,ya lalace,shine shaye shaye,neman mata,duk wani fasadi da shegantaka yana yi,amma ke kin killace naki ɗan kin bashi tarbiyya,kina yi masa faɗa, saboda me?
Saboda ba ke kika haife shi ba ko me??"
Kuka sosai Ummi ta fashe da shi,cikin kukan take faɗin"amma baka yi min adalci ba Alhaji,baka kyauta min ba,ka zalunce ni da har kake tunanin zan nuna bambanci tsakanin Rayyan da Aliyu,amma shikenan,na gode da munana zato,idan kana son ka ce yara na su koma gidan uban su babu laifi,ka yi ƙoƙari ma a haka,amma idan ka shigo da wata maganar baka yi min adalci ba,Allah shaida tunda mahaifiyar yaran nan ta bar duniya nake jansu a jiki bana son ganin damuwarsu,dama ba wai don ka yaba na yi ba,tunda wanda na yi don shi ya gani kuma ya yaba ai shikenan "ta miƙe fuuu tana goge hawayenta ta yi waje
Kan Ashraf yana ƙasa,wani irin suya zuciyarshi take yi masa,yana ƙaunar Ummi yana girmama ta,ta yi masa abinda ko mahaifiyarshi iyaka kenan,ta kyautata musu sosai,don haka cikin sanyin murya ya kalli Abby ya ce
"Abby I'm sorry please, Ummi uwa ce,ta kyautata mana a rayuwa,ta zamar mana bango majingina,ba zata taɓa cutar da ɗayanmu ba,ita ɗin masoyiyarmu ce,the last thing abinda zata yi shine cutar damu, I'm so sorry Abby"
"Okay ashe ka san da haka ko?ka san da haka ka mannewa wannan butulun yaron,wanda ya tozarta mu ya tozarta alkhairinmu a gare shi?ya tsallake ya koma gefe yake koya maka munanan ɗabi'u ko?wanda ka nunawa duniya ya fi mu daraja da ƙima a wajenka ko?
To na kusa yafe masa kai, idan ya so sai ya zama uban naka gaba ɗaya"
Da sauri ya girgiza kai yana faɗin "I'm sorry Abby,ba zata kai ga haka ba,in dai Saif ne wallahi na bar shi,na fita batunshi "
Tsaki Abby ya yi ya ce"baka isa na yarda da kai ba har sai ka zauna a Nigeria,na gaji da gantalin ƙasashen da kake yi kana ja min magana ka ɓata min suna,kano nake so ka koma ka kular min da asibitina,na gaji da barinshi a hannun bare,bayan ga ka nan, abinda ka karanta kenan"
Kan Ashraf a ƙasa ya ce"to Abby,in sha Allah "
Abby ya ja numfashi ya ce"I'm done,you can leave "ya sake rissinawa ya ce"na bar ka lafiya Abby "Abby bai sake magana ba ya miƙe jiki a mace ya fice daga part ɗin ya nufi na Ummi
Da sallama ya shiga yana kallon Ummi da ke zaune ta jinginar da kanta da kujera,da alamu abinda Abby ya yi mata ya dake ta sosai, Abby bai dace ya yi mata haka,ko babu komai ta raine su tamkar mahaifiyarsu tsawon shekaru,ta kula da su sosai,bata taɓa bambanta su da yaranta na cikinta ba
Gabanta ya zube,kanshi a ƙasa cikin raunananniyar murya ya fara magana
"Ban san da wacce kalma zan yi amfani wajen ba ki haƙuri ba Ummi,ko babu komai ke uwa ce a gare ni,abin yana yi min ciwo a ce wai saboda ni za'a zarge ki akan aikata ba daidai ba,kowa ya yi nagari kanshi,amma tabbas Ummi kin cika uwa ta gari,ina roƙon ki da kiyi haƙuri,kiyi afuwa sannan ki manta baya
Ko da Daddy ya ce kin bambanta mu mun san ba ki bambanta ba,don haka ina roƙonki Ummi,ke ɗin alfaharinmu ce,cigabanmu,kuma farin cikin mu
Ki taimaka ki cigaba a yadda kika fara,mu masu biyayya ne a gare ki"ya ƙarasa magana yana ɗago raunanan idanunshi ya kalle ta
Murmushi sosai Ummi ta yi baƙin cikin zuciyarta yana wankewa,tana murmushi sosai ta ce"har abada ku ɗin ƴaƴana ne Aliyu,you are mine and you will remain mine ko me mahaifinku zai ce kuwa
Abu ɗaya nake rokonka Aliyu,ka ji tsoron mahaliccinka,ka gyara halayenka,ka ja mutuncinka da na mahaifinka, Aliyu ko ba don Daddy ba ka daina wasu abubuwan,sam bai dace da kai ba,an sha yiwa mahaifinku shaguɓe da habaici akan halayenka, mahaifinku ya ƙauracewa siyasa saboda kai, menene ya sa kake haka don Allah?
Why please Aliyu??"
Shiru Ashraf ya yi yana sauraren nasihar matar mahaifin nashi,ji yake da yana da hali da ya chanja kanshi,amma a hakan ma zai yi ƙoƙarin ganin ya gyara
A hankali ya ce"in sha Allah Ummi,don Allah ki rinƙa saka ni a addu'a "ɗan murmushi ta yi ta ce"bana fashin saka ka a addu'a son,na sani Allah ya amsa min, is just matter of time,amma sai ka bani haɗin kai, Allah ya albarkaci rayuwarka "Ashraf ya yi murmushi ya miƙe yana faɗin"na bar ki lafiya mum"ya fice daga parlourn jiki a sanyaye
A parlour ya samu Hayat,da hannu ya yi masa inkiya,babu musu Hayat ya miƙe suka fice daga parlourn zuwa part ɗin Ashraf ɗin
A can Ashraf ya zube kan kujera ya dafe kai, Hayat cikin tausayawa yana kallonshi ya ce"why Ashraf?a ina matsalar take ne?ya kuka yi da Abby ne?ya kuka yi da Maleeka?"
Zazzafan huci ya furzar,cikin karayar zuciya yana ɗauke kai ya ce"everything is annoying Hayat,Abby ya ce sai dai na rabu da Saif,ina ƙaunar shi sosai,ina son komai da ya dangance shi,he is my blood,kuma shima abin tausayi ne,na kasa gane dalilin da ya Abby ya kafa min sharaɗin rabuwa dashi"ya dafe kai yana sauke huci mai zafi
Hayat ya ƙaraso kusa da shi ya zauna daf da shi,ya dafa shi,cikin sanyin murya ya ce "all is well friend!
But ya kamata ka san ya kamata zuwa yanzu,yes Saif ɗan'uwanka ne,amma tarayyarka da shi ba zata haifar maka ɗa mai ido ba,yana pushing ɗinka kana aikata a abubuwa marasa kyau,yana saka ka kana yin abubuwan da ba su dace ba, menene manufar hakan for God sake?"
Girgiza kai Ashraf ya yi, kan shi a ƙasa ya ce"kar ka zamo ɗaya daga cikin masu munanawa Saif zato,shi ɗin mutumin kirki ne wanda....."
"I will never agree with you Aliyu,idan mutumin kirki ne menene dalilin da,zai saka ya bijirewa Ummi da ta raine shi tun bayan rasuwar mahaifinku?
Idan mutumin kirki ne menene dalilin da zai saka ya tsallake ku ya tafi wata uwa duniyar yana rayuwa shi kaɗai?
Idan mutumin kirki ne menene dalilin da yasa duk lokacin da kuka tare baya hana ka mummunan aikinka?sai dai ya barka kayi ta aikata abinda ka ga dama?
Say something that I will understand Aliyu,an ji ɗan'uwanka ne ta ɓangaren mahaifiya,amma mara amfani, wanda ƴan'uwantakar ku bai amfana maka komai ba,mai rushe kyakkyawan ginin da wannan baiwar Allah mai tarin nagarta ta yi,tabbas ya ci amanar zumunci weather like it or not "
"Na ji,a bar maganar "a cewar Ashraf
"Baza'a barta ba sai na samu confirmation na cewa zaka zaɓi iyayanka akanshi,idan ba haka ba I'm telling you Nima zan fita batunka "
Ashraf ya dafe kai ya ce"na ji,na fita batunshi,are you happy now?"murmushi Hayat ya yi,ya sani tunda Ashraf ya ce ya bar batunshi to ya bari ɗin,don shi kaifi ɗaya ne
Sun ɗan juma suna hira, Hayat yana ta ƙarfafa masa gwiwa da ba shi shawarwari,har ya samu Ashraf ya ɗan rage damuwa,kafin ya yi masa sallama ya tafi
DODAN BARRACK, IKOYI, LAGOS STATE, NIGERIA
Yau kwana uku kenan da Maimuna ta yiwa Aneesa ture,sai zuba idanu take yi ta ji nada news amma bata ji komai ba,tabbas ranta ya ɓaci sosai,don abu ɗaya ya zo ranta, shine Fareeda yaudararta ta yi
Ba tare da tunanin komai ba ta kira a fusace, lokacin Fareeda ta koma Kaduna,asalima tana gidan saurayinta da ya kama musu,a lokacin ma tana kwance a jikinshi bayan sun gama sheƙe ayarsu
Tana ganin numbern Maimuna ta yi wani murmushi,ta kalli farkon nata wanda ya kasance babban mutum ne wanda aƙalla ya doshi shekaru sittin,ta ce"bari na ɗaga wannan kiran, wataƙila ya zo da ƙaruwa ko da raguwa,koma dai yaya ne bana yarda na faɗi"
Murmushi ya yi yana faɗin "an gaida kaska raɓi mai jini"ta kashe masa ido ta daga sabon kiran da yake shigowa
Kafin ta yi magana ta fara jin saukar hayaniyar Maimuna a dodon kunnenta
"Daƙiƙiya!jahila!! tsinanniyar karuwa!!!ni za ki yaudara?ni za ki cuta?ni za ki mayar sakarya?
To wallahi ahir ɗinki,wato na ce ki kawo min magani shine za ki cuce ni ki ci kuɗi na ko?"
Ganin abin na Maimuna ya fara yawa cikin ɗaga murya ta ce"relax malama!bana son hayaniya,bana son tsawa!na yi miki aikinki yadda ya dace amma ni ba yaudara ta kika yi ba?kin biya ni yadda ya dace ne?to ga albishir kyauta,na je har gida na tona miki asiri a wajen matar da kike rainawa hankali,idan kin isa kuma ki cigaba da cutarta mu gani ko za ki iya "ƙit ta yanke wayarta ta saka a Flight mode,sannan ta sake rungumo kwarton nata
Murmushi ya yi yana shafa ƙirjinta yana faɗin "ja'ira!kina wuta ina bin ki da fetur,in dai shaiɗanci ne na yarda da ke ta wannan fannin"Fareeda ta yi dariya tana sake maƙalƙale shi,suka faɗa kan gadon suna cigaba da baɗalarsu
🌟✨
A ɓangaren Maimuna kam kanta ne ya shiga juyawa,me Fareeda take nufi?tana nufin ta tona mata asiri?to sai me idan ta tona mata?ai dai ta mallake mai gidan kankat ai shikenan,to amma me take nufi?ta daina yi mata aiki ne?idan ta daina yi mata aiki to wa ta kama?ita da ba wani sanin malamai da bokaye hatsabibai ta yi kamar Fareeda ba?me ta yi wa Fareeda da zata yi mata haka a lokacin da take tsananin buƙatarta?ta ja tsaki,sai yanzu ta ji nadamar rashin zuwa wajen bokaye da malaman tsibbun da kanta da bata yi take tura Fareeda, da tana zuwa da kanta da komai bai lalace mata ba
Zama ta yi yaraf akan kujera tana ture ɗan kwallon kanta,gaba ɗaya duniyar ji take yi ta yi mata zafi,babu abinda take tunani sai mafita, daidai lokacin ta ji sallama
Da hanzari ta ɗago ba tare da ta amsa sallamar ba tana kallon wadda ta shigo, Ruky ce,sha riga da skirt da suka kama ta tsam, mayafinta a ajiye a gefen kafaɗarta,ta saki kitson attachment ɗinta har bayanta
Da yake mafita Maimuna take nema sai ta saki fuskarta,tana faɗin "sannu da zuwa Hajiya Ruky,shigo"Ruky ta shiga tana ɗan murmushi ta samu waje ta zauna
Suka gaisa, Maimuna ta kawo mata abinci,bata yiwa kanta mugunta ba ta buɗe ciki ta ci ta ƙoshi, Maimuna ta dube ta tana faɗin
"Wai ƙawarki lafiya kuwa?na ji ta shiru kwana biyu"
Ruky ta ɗan gyara zama tana kallonta ta ce"dama abinda ya kawo ni kenan,ki yi haƙuri ki fitar da Fareeda daga tsarinki,dama tuntuni na ga alamu tana jin haushin cigabanki,bini bini ta kawo sukarki,don ma bana bata fuska,last week dai ta ce min wai ba zata sake yi miki aiki ba, saboda kin hana ta kuɗi"
Tsaki mai ƙarfi Maimuna ta ja tana faɗin "wawiya! ai kanta ta cuta,to alhamdulillahi dai da ba ita kaɗai ta san hanyar wajen malaman tsubbu ba"Ruky ta ce"ko ni tsaf zan yi miki wannan aikin idan kina so"
Maimuna ta yi ɗan murmushi tana faɗin "godiya nake sister!
Akwai aikin da na ce wannan matsiyaciyar ta yi min na wata ƴar mijinta,shegiya ashe bata yi ba,don Allah za ki raka ni wajen wani bokan wanda zai yi min aikin?"
Murmushi sosai Ruky ta yi,duk da bata ji daɗi ba,ta so a sakar mata aiki kamar yadda aka sakarwa Fareeda,amma idan ta san wata ai bata san wata ba, don haka ta ce"baki da matsala uwar ɗaki, yaushe kika shirya?"
Maimuna ta ce"ko gobe ma a shirye nake wallahi"
#Nusy_bee
***