ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

ƘADDARARMU CE....12

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)

✍️ Nusy bee 
❤️*Young talented writers association YOTA*❤️



My TikTok account 👇


***



My Instagram account 👇

***


My arewa pen link 👇


https://arewapen.com/u/nusybee143


Page 12


"To mai zai hana zuwa nan da ranar Sunday,nan da kwana uku kenan,akwai wani hatsabibin boka,sai mu je wajenshi?"a cewar Ruky tana gyara zaman ɗan fingilin mayafinta akan kafaɗarta 

Maimuna ta ɗan ja fasali ta ce"to shikenan, Allah ya kai mu,amma tabbas sai Fareeda ta ci ubanta, ba'a yaudara ta a zauna lafiya"

A nan Ruky ta kai yamma,sun tsara yadda za su yi komai, Maimuna ta sallame ta da wasu manyan kuɗaɗe, Ruky ta ji sanyi sosai,cike da farin ciki ta yi ta mata godiya 

Tana zuwa bakin gate ta fashe da dariya tana faɗin "kayya!kin tafka kuskure Hajiya!daga ke har Fareedan kar nake kallon ku"ta wuce titi ta tsari taxi ta tafi gida ranta fes 




SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 


Yau su Aneesa suka kammala jarrabawar WAEC,farin ciki sosai fal ransu,kamar yadda suka saba tare suka taho yanzu ita da Meena 

Meena ta kalle ta tana murmushi ta ce "Anee wai ya kuke ciki ke da guy ɗinki ne?ko kema ya raina miki wayo kin yi masa checking out kamar yadda na yi wa Sabir?"

Juya idanu Aneesa ta yi ta ce"muna tare da my Faisal har mutuwa har gida ta aljanna,mai raba ni da shi sai Allah "

Meena tana murmushi ta ce"kin yi sa'a Anee,ya kamata zuwa yanzu a san dashi a gidanku,kin ga maganar aure ya dace ya shigo tsakaninku saboda zuwa yanzu na san kin fahimci juna ko?"

"Yeah mun fahimci juna,tabbas maganarki,don yanzu haka ma ya ce zai sanar da iyayenshi,nima dawowar Abba nake jira na gaya masa zuwan su,in sha Allah nan da ɗan lokaci Aneesa zata zama ta Faisal"ta ƙarashe tana fari da idanunta 

Meena tana murmushi ta ce"all the best aminiyata, Allah ya sa mu a danshinku,tabbas soyayya gaskiya ce, musamman ma idan ka dace da masoyin gaskiya kamar Faisal "

Aneesa tana murmushi ta ce"shiyasa nake yi miki fatan kema Allah ya azurtaki da nagartacce kuma mai ƙaunar ki kamar Faisal,rayuwar soyayya akwai daɗi, musamman idan kika haɗu da miji na gari "

Meena ta ce"hakane,amma ya ɓangaren danginshi? Allah ya sa suma suna sonki?"

Shiru Aneesa ta ɗan yi kafin ta ce"I can't tell,ni dai abu ɗaya zan iya ɗorarwa game da ƴan'uwanshi,they are always minding their own business,abu idan bai shafe su ba babu ruwansu da shi"

Meena ta girgiza kai ta ce"ba ki san masu kuɗin nan ba kawai,ki sake sabon karatu akan su,suna da wulaƙanci da ɗabi'ar ƙwarya ta bi ƙwarya,kin ga idan haka ne za su iya ba ku cikas"

Gaban Aneesa ya faɗi,cikin sanyin jiki ta kalli Meena ta ce"sam ban yi wannan tunanin ba Meena,amma idan suka raba mu bana jin sun kyautawa soyayyarmu"

Meena ta yi ɗan murmushi ta ce"sai kun dage kam,amma irin waɗannan masu hannu da shunin akwai wulaƙanci da raina mutane"Aneesa ta sauke ajiyar zuciya tana faɗin "to Allah ya yi mana maganinsu"

Meena ta ce"Ameen dai"

Satinsu biyu da gama WAEC Faisal ya kira ta da albishir ɗin manyan shi suna zuwa sati mai zuwa,farin ciki babu irin wanda bata yi ba,ta yi murna sosai,ta sanar da Ammi,sannan ta sanar da Abba da yanzu sukan yi waya jefi jefi

Abba ya tabbatar mata da zai dawo nan da kwana uku, don ya samu a shirya komai yadda ya kamata a tarbi baƙin 





PUNTA CARRETAS, MONTEVIDEO, URUGUAY 

Tsaye yake a jingine a jikin bango,waya ce a hannunshi yana daddannawa,mintuna kaɗan ya kara a kunnenshi gami da lumshe idanunshi,kallo ɗaya za'a yiwa fuskarshi a ga alamun damuwa da suka bayyana a fuskar shi,wadda hakan take da alaƙa da wanda yake yunƙurin kira 

Kira na uku kenan ana yi masa rejecting,a jikinshi yake jin babu lafiya,don ya sani Ashraf baya iya ɗaukar lokaci bai kira shi ba ballantana ya har shi ya kira shi ya danna masa busy,dole ya je Nigeria don ganin me yake faruwa?amma shi kam ya san da lauje cikin naɗi na wannan shariyar da Ashraf yake yi masa

Ji ya yi an dafa shi,ya waigo a hankali yana kallonta, murmushi ta yi tana kallonshi cike da kulawa tana faɗin "ya dai namijin duniya?any problem?"

Murmushi ya yi yana lumshe idanunshi,ta ƙaraso gabanshi ta zauna tana kallonshi,ya buɗe blue eyes ɗin shi yana kallonta,cikin sanyin murya ya ce 

"Gaba ɗaya ina cikin damuwar halin da Ashraf yake ciki ne,baya ɗaga min kira baya amsa saƙona,na san halin da yake ciki,na san damuwarshi,ina tsoron kar ya sake shiga wadda tafi ta baya"gyara zama ta yi sosai tana kwantowa jikinshi,cikin sanyin murya ta ce "akwai Allah dear, tabbas duk wanda ya dogara ga Allah zai kawo masa ɗauki 

Mu saka Ashraf a addu'a, Allah yana sane da mu kuma yana sane dashi"

Ajiyar zuciya Saif ya yi sannan ya ce"I was thinking ko mu je Nigeria zuwa next month?"ɗan murmushi ta yi ta ce"hakan yana da kyau,nima ka ga sai na je na ga iyayena"Saif ya dungure mata kai yana faɗin"sannu uwar son kai,kawai ki ce mu je ki aiwatar da buƙatarki"dariya ta yi ta ce "seriously na yi kewar su Mamana ne,rabo na da Nigeria fa kana gani tun haihuwar Hibban,amma idan ka ce a'a I will obey the law Sir"ya yi dariya sosai,itama ta yi dariya,ya ce"to ki shirya mu je,amma sai mun fara branching Abuja mun ga halin da Aliyu yake ciki"ta yi murmushi ta ce "babu matsala mai gidan Arwa "

Bayan kwana biyu suka shirya don tafiya Nigeria,ko a jirgi gaba ɗaya jikin Saif a sanyaye yake,don yana tsoron kar ya kasance abinda yake gudu ne ya faru, idan haka ta kasance to fa bashi da sauran hope akan Ashraf 

Da fargaba suka tare taxi zuwa asokoro, Najma tana zaune a parlour tana kallo sai ga su Saif da sallama

A hargitse ta ɗago tana kallonsu, musamman Saif da ya ɗaure fuska tamau yana kallonta,ta miƙe tsaye tana ƙare musu kallo da shi da Arwa da ke tsaye a bayanshi tana rungume da Hibban da yake bacci tana kallonta 

Tsaki Najma ta yi ta tsartar da yawu sannan ta wuce parlourn Ummi, Ummi na zaune tana shirya kaya a cupboard sai ganin Najma ta yi ya faɗo ko sallama babu


Sai da ta firgita,ta ɗan bi ta da kallo tana faɗin "lafiyarki kuwa? menene haka?"

"Ummi wannan matsiyacin,shine shi da karuwarshi"a firgice Ummi ta miƙe tana faɗin "wanene?wa kike magana a kai Najma?

Najma ta ce"Saif, wallahi shine da shi da wata matsiyaciyar mata"Ummi bata gama sauraren Najma ba ta yi waje da sauri gabanta na faɗuwa 

A parlour ta samu Saif ya zauna,itama Arwa ta zauna a gefen shi,amma gaba ɗaya a tsorace take,ya amshi Hibban daga hannunta ya cigaba da ƙoƙarin kiran layin Ashraf 

Hawaye suka cika idanun Ummi suka zubo kan fuskarta,tana kallon Saif ta ce"bawan Allah me ya kawo ka kuma?

Me ka zo yi?ko ka zo ka ƙarasa abinda ka fara?"

A nutse Saif ya ɗago ya kalle ta, fuskarshi babu alamun damuwa ya ce"na zo ne don na ga ɗan'uwana, I just want to confirm he is okay"

"To za ka iya tafiya don Allah, lafiya ƙalau yake,jibi jibin nan ma zai tafi Kano ya kula da Asibitin da mahaifinshi ya bashi"

Saif ya ɗan yamutsa fuska yana kallon wayarshi da Ashraf ya katse,ya ɗaga idanu yana kallon Ummi da ke ta share hawaye,ya ce"ina buƙatar ganin shi yanzu,idan da hali ina son magana da ɗan'uwana!"

"Ka je ka nemi ɗan'uwanka malam!amma matsiyaci mugu kuma munafuki bai isa ya zama ɗan'uwan wani a gidan nan ba,don haka get out Malam!"

A nutse Saif ya ɗaga kai yana kallon Rayyan da ke yi masa wannan maganar yana nuna masa bakin ƙofa,ya kalli Arwa da ta ƙanƙame shi,ya sa hannu ya tallabe ta sosai,ya mayar da hankali ga Rayyan sosai ya ce

"Malam ɗan ƴar uwata nake son gani,bana son AGOLA ya sake saka min baki"

Kalmar ta hargitsa Ummi da Rayyan,har ma da Najma da ke tsaye tana kallonsu,kafin wani ya yi magana muryar Abby ta ratsa dodon kunnensu 

"Kafin Rayyan ya zo gidan nan a matsayin agola ina ganin kamar ka riga shi ko?

To don haka ina ganin kamar kanka kake yiwa gori,kuma ka fice min daga gida,ko a hanya bana buƙatar ƙara ganinka,idan ka kuskura na sake ganin mummunar fuskarka kuwa ina mai tabbatar maka da sai na ɗaure ka, matsiyaci,daƙiƙi,butulu!!!"

Murmushi sosai Saif ya yi ya ɗauke kanshi daga kallon Abby ya ce

"Alhaji Mustapha,Barka da warhaka,ina fatan kana lafiya 

I'm sorry ba hayaniya ta kawo ni ko gori ba,ka riƙe ni tun ina yaro ka yi ƙoƙari, Allah ya biya ka, amma yanzu ɗan'uwana na zo gani,kuma tabbas sai na ganshi "

Sosai Abby ya fusata,batare da ɓata lokaci ba ya ɗauke Saif da mari yana faɗin"ba kaji abinda aka faɗa maka bane?ba zaka ganshi ba,tunda ɗana ne, idan kana da zuciya ka fita daga sabgar shi,idan ba haka ba wallahi sai na wulaƙanta ka,wawa kawai,butulu!!!"

Murmushi sosai Saif ya yi yana shafa kunci shi,da idanu ya bi Ashraf da ya leƙo parlourn,suna haɗa idanu ya yi maza ya juya ya bar wajen,ya sake ɗagowa,a nutse ya kalli Abby ya ce"ba yau kaɗai ba,ko gobe,ko nan da shekaru biyu,ko shekaru goma, a'a za ka cigaba da riƙe matsayinka na uba a gare ni tsawon numfashi na,zan cigaba da baka girma ko don albarkacin matarka HAMDA 

Idan har zan iya ɗaukan mataki akan mahaifin da ya tsuguna ya haife ni tabbas zan ɗauki mataki akanka "

"To dama kana da mahaifi ne?ba tsintacciyar mage bace? wadda bata mage?wa ya sani ma ko shege ne babu asali?"

Saif ya kalli Rayyan da ke wannan maganar a nutse sannan ya ce"kar ka sake yi min shishshigi a maganata,ba da kai nake magana ba,da uwarka da mijinta nakeyi so ka kama min baki"ya kalli Arwa da ke ta kuka a tsorace ya ce tashi mu tafi"ta miƙe kamar wadda aka tsikara tana sake ƙanƙame Hibban da ya sake mayar mata dashi,suka nufi bakin ƙofa 

Yana daf da fita ya juyo yana kallon Ummi cike da tsana ya ce"Hajiya Rumaisa!yanzu kin yi farin ciki?ko da saura?"bai saurari amsarta ba ya juya ya fice zuciyarshi shi kaɗai ya san me yake ji a cikinta 

A harabar gidan ya samu Ashraf a zaune,yana gano su ya yi azamar tashi ya shige part ɗinshi, Saif ya bishi da kallo kafin ya girgiza kanshi kawai

Arwa ta yi hanzarin riƙe masa hannu tana faɗin "dear gudunka yake yi fa,ka gani baya son ganinka, Saif ya yi murmushi mai ciwo yana faɗin"good for him "daga haka bai sake bata damar magana ba ya ja hannunta suka faɗa mota,ya tayar suka bar harabar gidan 



SABUWAR GANDU,KANO STATE, NIGERIA 

Tsawon watanni uku kenan yanzu, abubuwa sun chanja sosai ga Aneesa tunda aka yi rigima kan batun aurenta da Faisal, don ƙiri ƙiri Mu'ayyad yayan Faisal da ya zo binciken wacece ita ya kushe komai nasu,a cewarshi ba cancantarsu bane haɗa jini da talakawa irin su Aneesa, daga Aneesa har Faisal sai da suka yi ɗan ƙaramin hauka,ita Aneesa ma sai da ta yi kwanciyar asibiti, amma Ammi ta sake tabbatar mata da tunda danginshi suka ce basa sonta ko Allah ya yi ta aure shi ba zata taɓa samun girmamawa da mutuntawa daga wajen danginshi ba 

Sau tari tana kiran Faisal ta yi ta rusa masa kuka,hakan ba ƙaramin karya masa zuciya yake yi ba,shima yana shan tashin hankali saboda rashin batun auren nan 

Yau tana zaune tana duba wani English novel, karatun takeyi amma sam hankalinta ba a jikinta yake ba,kiran Faisal ya shigo wayarta 

Jikinta har karkarwa yake yi, ta yi maza ta ɗaga,daga can ɓangaren Faisal ya ce

"Love! I miss you so much!"

Hawaye suka zubo mata,cikin raunin murya ta ce"I miss you more hubby,yanzu mantawa kake yi dani"

Ɗan murmushi mai sauti ya yi yana faɗin "Ni?na manta da ke?har gaba da abada

Ni ba wannan ba,na zo mana da dabara ne kawai"da zumuɗi a muryarta take faɗin "wacce dabara ce please?"

Kai tsaye Faisal ya ce"zamu gudu mu yi aurenmu"

Gaban Aneesa ya faɗi,cikin in ina ta fara girgiza kai tana faɗin "a....a.... a'a,kawai.....ka ga.....um...don Allah mu bi zaɓin iyayenmu,ina son iyayena,komai runtsi ba zan iya bijire musu ba"

"To shikenan!"abinda Faisal ya iya faɗa kenan a fusace,gani yake ai kawai ba wani sonshi take yi ba, shiyasa bata damu ba ganin za'a raba su

Star boy da ke gefenshi,wanda ya ji komai ya kalle shi ya ce 

"Akwai mafita ɗaya dude"

Kallonshi kawai Faisal ya yi, Kafin cikin sanyin murya ya ce 

"Mecece mafitar?"

Kai tsaye star boy ya ce"raping ɗinta zaka yi!"

A firgice Faisal yana zaro idanu ya ce"raping?are you listening to yourself kuwa?baka san ita ce mace da nake so ba,baka san bata da na biyu a rayuwata ba?"

Star boy yana kallonshi ya ce"of course yes! raping ɗinta ne kawai mafita because hakan zai saka dole Dada da Momma su rufe maganar ta hanyar aura maka ita,ka ga shikenan ka samu muradin ranka cikin sauƙi "shiru Faisal ya yi yana kallon Star boy yana nazari, Star boy yana kallonshi ya ce"think twice my G, that's only the best solution "

Faisal ya sauke ajiyar zuciya ya ce"to ta yaya zamu aiwatar da hakan?"Star boy ya yi murmushi ya ce"ka bar komai a hannu na,kai dai kawai ka zama cikin shirin zama ango"Faisal ya yi ƴar dariya cikin jin alfahrin samun aboki kamar Julaibib Star boy 




To pa!da alamu Aneesa tana shirin faɗawa mugun hannu😭

#Nusy_bee