ƘADDARARMU CE TA ZO A HAKA

ƘADDARARMU CE....13

by @nusybee143

🫰 ƘADDARAR MU CE....👌
(Ta zo a haka)


✍️ Nusy bee
❤️* young talented writers association YOTA* ❤️ 

Page 13



Take Star boy ya ɗaga waya ya kira Meena, bugu biyu ta ɗaga

"Hello!"ta amsa

Ajiye wayar ya yi a kusa da Faisal ya saka ta a speaker ya ce"Are you with me Meena?"

Meena ta ɗan yatsina fuska ta ce"yes!any problem?"

Ba tare da tunanin komai ba ya ce"kan batun kawar taki ne, so nake komai ya zama ready,for me na samu na shawo kan abokina"

Meena ta gyara kwanciyarta ta ce "baku da matsala,na shirya komai tuntuni,kun zo kanon ne?"

Star boy ya ce"no muna Abuja,amma yau zamu taso,don Allah bana son a samu matsala"

Meena ta ja numfashi ta ce"to shikenan,sai kun zo, kuɗina fa?"

"Yanzu ki duba account ɗinki,na tura miki advance,bayan komai ya cika zan tura miki ciko"

Meena ta girgiza kai tana faɗin "no!duka nake so,idan baka tura min ba wallahi ba zan bayar da haɗin kai ba,ku yi komai da kanku"

Tsaki Star boy ya yi ya ce"na ji,bari na tura miki "ya kashe wayarshi yana jan tsaki"

A take ya tura cikon 2m ɗin da za su Turawa Meena making 5m,babu shakkar komai ta kira ta gaya masa ta gani,aiki zai kammala 

Faisal dai yana zaune yana jin komai,ya ɗan tsorata duk da shaiɗan da ya yi tasiri a ranshi,don Aneesa bata da aminiya irin Meena,amma Meena ta rufe idanu saboda kuɗi ta yi mata haka?





SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 

Ajiye wayarta ta yi a kusa da ita tana kallon hoton da yake kan wallpaper ɗin wayar,ita da Anee ne ranar da suka yi graduation na kammala NECO exam, murmushi ta yi sosai tana kallon hoton,dukkansu sun yi kyau sosai,sun yi murmushin da ke nuna tsantsar farin cikin su na kammala secondary school 

A bayyane ta furta "tsawon rayuwata babu wani abu da na tsana,ya sako ni gaba ya hana ni rawar gaban hantsi irinki ANEESA!

Na tsane ki,a kowanne lokaci kowane minti kowanne second ƙara tsanarki nake yi!!

A matsayinki na ƴar talaka me ya kai ki competition da ni har ki rinƙa yin nasara a kaina?

Ni Faisal ya cancanta ya so,amma ya ƙare da son ƴar talaka irinki!

Ni na cancanta na zama abar kwatance a ajinmu amma kowa maganarki yake yi

Duk lokacin da za'a yi school competition ke ce a gaba, ni ko zance na ba'a yi,ko batun class ɗinmu aka yi ke kike zuwa ran mutane?

Wacece ke?me aka yi aka yi ki? wallahi na tsane ki Meena!!"

"Aunty Meena me kike cewa ne?"da sauri ta waiga tana kallon ƙanwarta Samha da ke tsaye bakin ƙofar ɗakinta fuskarta a haɗe,cikin in ina ta ce"malama...g..g..get out please!am I your mate?"

Samha ta yatsina fuska ta ce"whatever!amma aunty Meena you have to wake up! ƙawarki bata yi miki komai ba,ta girmama ki,ta girmama iyayenki,ta mutunta ƴan'uwanki,ta riƙe ki da zuciya ɗaya,ta ƙaunace ki don Allah,kar ki ci amanarta ko ki yaudare ta Please "

"Kin san wacece Aneesa ma da kika zo kina yi min wannan maganar Samha?"a cewar Meena cikin ɓacin rai 

Samha ta gyara tsayuwa ta ce"Aneesa ƙawarki ce,mai kirki, mai sanin ya kamata,kar ki bari shaiɗan ya ingiza ki zuwa ga turbar dana sani,kar ki yaudare ta ki cuce ta,samun ƙawa mai halinta sai an tona aunty Meena "

Meena ta ɗan ja fasali kafin ta ce"hakane kuma,ma gode da tunatarwa, Allah ya tsare mu sharrin shaiɗan "Samha tana murmushi ta dafa kafaɗarta ta ce"Ameen aunty Meena,dama Mamie ke kiranki"Meena ta ce"to gani nan zuwa"Samha ta yi waje Meena ta raka ta da wata muguwar harara





SARDAUNA CRESCENT, NASSARAWA GRA, KANO STATE 

A ƴan kwanakin nan tunda ya dawo Kano sam baya jin daɗin komai, Ummi da Hayat kaɗai yake waya da su,suma lokaci zuwa lokaci,banda su biyun babu mai neman shi ko a waya,ciki har da Saif da ko bai ɗaga wayarshi ba yana jin sanyi idan ya kira shi 

Yanzun ma yana kwance a parlour akan doguwar kujera yana kallon hotunan da suka yi da Saif ɗin cikin matuƙar farin ciki da walwala a Quebec da yake yawan kai masa ziyara,gaba ɗaya duniyar ji yake ta daina yi masa daɗi,ji yake dama ya mutu kawai ya huta

Ƙarar intercom ɗin da ya ji ne ya sa ya tashi da sauri,ya san wataƙila saƙon da ya aika a kawo masa ne

Ai kuwa ya yi sa'a, wanda ya aika ya kawo masa giya ne,ya yi saurin amsa ya koma parlourn,ya fara bulbulawa cikinshi batare da jiran komai ba

Sai da ya yi mankas sannan ya baje a parlourn ya fara barci

Yanzu rayuwarshi kenan,babu abokin hira sai giya da taba,in dai ba wajen aikinshi ba to yana gida yana kwankwaɗar giya,ko yana bulbulawa cikinshi hayakin taba

Bai tashi ba sai bayan la'asar sosai,da ƙyar ya iya tashi ya yi wanka,ya yi alwala ya yi sallar maghriba da isha'i sannan ya shirya ya fice daga gidan ya nufi club 

Bai dawo gida ba sai wajen ƙarfe shida na safiya,don da ya je can bayan ya gama masha'arshi ya yi overdose na ƙwayoyi da yake ganin za su kore masa damuwa,ya yi kwanciyarshi ya yi ya bacci har zuwa bayan sallar asuba,ya tashi ya yi tahowarshi gida

A gida ya samu ya yi wanka ya yi Sallah, lokacin ma takwas ta kusa,ya samu ya karya,bai fita daga gidan ba sai bayan ƙarfe takwas

Yana offce bakin aikinshi wayarshi ta yi ƙara,sai da gabanshi ya faɗi ganin sunan Abby,ya daure ya ɗaga da sallama 

Ko amsa sallamar Abby bai yi ba ya ce"sannu da aiki Aliyu,wato kai dai karfi da yaji sai ka ɓata min suna ko?na gode!

Amma ka sani zan fita sabgarka na bar ka ka aikata abinda ka ga dama, dama haka kake so ko?"

Kamar zai duƙa yake faɗin I'm sorry! I'm very sorry Abby,in sha Allahu zan koma yadda kake so,ka yi min aikin gafara Please"

"Okay!idan kana son na yafe maka ina buƙatar ganinka nan da next week,kuma nan da zuwa ranar da za ka dawo na sake jin ka aikata wani abu tabbas za ka gane kurenka "bai jira amsarshi ba ya kashe wayarshi 

Ajiye wayar Ashraf ya yi cikin ɓacin rai yana furzar da zazzafan huci,daidai lokacin da wata nurse ta shigo tana faɗin 

"Sir is time!"a fusace ya kalle ta,sai wani rangwaɗa take yi tana kashe murya,a fusace ya ce"get out of my side malama!"yadda ya daka mata tsawa ya sa ta fice da ɗan gudu gudu tana zazzare idanu 

Tsaki ya ja mai ƙarfi ya miƙe ya fice daga office ɗin,kai tsaye ya faɗa motarshi ya nufi gida

Saboda tension ɗin da yake kanshi ya buge wani mai daidaita da yake gabanshi bai kula ba,da sauri mai adaidaitan ya yayi parking a gefen titi ya fito yana duba ɓarnar da aka yi masa 

A fusace Ashraf ya fito yana kallon matashin mai adadaita sahun,cikin fusata Ashraf ya ce"hey Young Man!baka kula ne?yanzu da ka ja min wata matsalar da?sai ku yi ta shiga hanyar mutane don ku samu kafar ɓata mana suna!"

Kallo ɗaya mai adaidaitan ya yi masa ya ɗauke kai yana cigaba da duba ɓarnar da ya yi masa,amma a kallo ɗaya za'a gane yadda ranshi ya yi matuƙar ɓaci 

Tsaki mai ƙarfi Ashraf ya ja,ya ce sai ka ba ni account numbernka na saka maka abinda za ka gyara,yadda next time matsiyata irinku za su ji daɗin cigaba da yin abinda suka ga dama a titi kamar na ubansu

A fusace matashin ya kalle shi ya ce"bana buƙata yallaɓai,kuma bi ba matsiyaci bane,ina da arziƙin da zan iya magance matsala ta ba sai masu ƙaryar dukiyar haram irinku sun shiga ba"

Maganar ta sake fusata Ashraf,ya ɗaga hannu da nufin sauke masa mari amma ya ji an riƙe hannun na shi

Da mamaki ya waiga yana kallon mai wannan ƙarfin halin, matashiyar budurwa ce wadda ko Najma ta girme mata, ballantana Maleeka,sai watsa masa wani mugun kallo take yi fuskarta a ɗaure

Da mamaki yake kallonta,ta yarfar da hannunshi cikin iska,ta kalli tsakiyar idanunshi ta fara magana 

"You are mistaken ɗan ƙaruna,babu matsiyaci sai wanda bai san darajar al'umma ba,wanda bashi da tarbiyya bashi da mutunci da mutunta ɗan adam!

Talauci na hauka bane, jarrabawa ne, shima mai kuɗin da Allah ya rufa masa asiri jarrabawa ne a gare shi,so idan mutum yana da hankali ba zai taɓa wulaƙanci kan ni'imar da bai isa ya yiwa kanshi ba

Menene laifinshi? saboda ya hau titi ɗaya da kai,to ai na ga hanyar ba ta ubanka ba ce,ta Allah ce, idan kuma ta ubanka ce ka ce masa ya naɗe abarshi mu tafi a ta Allah 

Ka cigaba da wulakanta mutane son ranka, lokacin ka ne,amma watan watarana ko kuɗi aka ba ka akace ka yi hakan ba za kayi ba, mtseeeewwwwww!malam mu je raina yana sake ɓaci"ta faɗa adaidaitan,mai adaidaitan ya ja suka bar Ashraf sake da baki yana bin su da kallo, mutanen da suka fara taruwa suka fara yin nasu waje 

A adaidaitan Aneesa sai sauke numfashi take yi zuciyarta tana ta tafasa,bata yi aune ba sai ta ji hawaye sun ɓalle mata,babu abinda yake ƙona mata rai kamar yadda ake ƙasƙantar da talaka 

Yanzu dai ƙiri ƙiri zancen aurenta ya zama tarihi saboda su talakawa ne,ta share hawayenta tana jin mai napep ɗin yana yi mata godiyar abinda ta yi masa,da yi mata ƙarin bayanin wulaƙancin da suke fuskanta amma sai dai ta yi murmushi bata tankawa

Wayarta ce ta yi ƙara,ta ɗauko ta duba,ganin sunan Meena ya sa ta ɗaga kiran

"Bestie kina ina ne?"a cewar Meena 

Anee ta sauke ajiyar zuciya ta ce"kan hanya,na ɗan je kasuwa na siyo wasu kayayyaki ne,any problem?"

"Please za ki samu shigowa yau ɗin nan?"a cewar Meena 

Ɗan dafe kai Anee tayi ta ce"kin san yau Ammi tana da night duty,so dole ni zan yiwa yara girki,don haka sai dai ki jira ni zuwa bayan maghriba,idan na gama zan zo in sha Allah"

Farin ciki fal zuciyar Meena ta ce"to Allah ya kawo ki lafiya,sai kin zo"Anee ta ajiye wayar tana dafe ƙirjinta,haka kawai take jin gabanta na faɗuwa 




 JABI,ABUJA, NIGERIA 


Kallonshi ya mayar kanta sosai,ɗauke kanta ta yi tana yin abinda ta saba,wato danna waya,cikin taushin murya ya ce"Maleeka ba kiji abinda ya samu ɗan'uwanki bane?menene dalilin da ya sa sam baya cikin lissafinki?a kullum nunawa duniya baki da alaƙa da shi kike bayan babu wanda kuke da alaƙa a kaf faɗin duniyarnan sama da shi?"

Murmushi ta yi kawai, wanda ita kaɗai ta san ma'anarshi,ta ajiye wayar tana kallonshi ta ce"yaya Saifudeen kenan!

Sau tari rayuwa kai kaɗai tana da daɗi more especially if you are sorrounded by wrong people,kowa cikinsu ya zame maka abin ƙyama,to live alone and peacefully will be best and better for you,don haka na zaɓi hakan,rayuwa ni kaɗai ta fiye min komai

Na rayu da ciwo da baƙin ciki na tsawon shekaru,wanda ba kowa bane sila sai wanda kake yiwa kallon ɗan'uwana,wanda ni kuma har abada a yanzu na gwammaci na rayu bani da kowa da na nuna shi a matsayin ɗan'uwana 

Bana son na cigaba da jin ciwon shi,gwara mu nisanci juna,don ko darajar iyayenmu aƙalla ya samu ya ci mana,don haka Please yaya Saif a bar wannan maganar"Arwa da ta ƙaraso ta ajiye mata abinci ta kalle ta cikin tausasawa tana faɗin"a bi komai a sannu Maleeka!komai ya yi farko yana da ƙarshe"Maleeka ta tari numfashinta da faɗin"banda ƙiyayyar da nake yiwa yaya Ashraf aunty!"kallonta Arwa ta yi na ƴan seconds,yadda take magana da yanayinta ya nuna tsananin ɓacin ran da take ciki,sai dai har yau ta ƙi ta gayawa kowa abinda yayan nata yayi mata 

Duk yadda Saif da Arwa suka so cooling Maleeka hakan ya ci tura ƙarshe ma kuka ta saka cikin tsananin jin ciwon abinda take ji

Ƙarshe da ƙyar suka lallashe ta,sun ɗan juma suna hira kafin ta yi musu sallama ta tafi gida 

Bayan ta tafi Arwa ta kalli mijin nata,cikin karayar zuciya ta ce"dear me hakan ke nufi?wannan anya Maleeka da na sani ce?"murmushi mai ciwo ya yi ya ce "ita ce of course,kawai dai akwai wani abu da yake tafiya ba daidai ba,sai kin saka min su a addu'a, don wannan da alamu shiri na musamman ne aka yi don tarwatsa kan yaran Mum"hawaye suka zubowa Arwa ta ce"ko ma waye ya Allah na tashi ba, Allah yana sane da su, Allah ya kawo musu ɗauki,ana zaluntar bayin Allan nan"Saif bai sake magana ba ya cigaba da abinda yake yi ranshi yana zafi 




SABUWAR GANDU, KANO STATE, NIGERIA 


Kasancewar Aneesa ta dawo gida rai babu daɗi bata sami ta ɗora girkin da wuri ba ma,bata gama ba sai daf da isha'i,ta samu su Sauban suna kallo,ta tambaye su

"Sauban ina Al'amin?"ya kalle ta ya ce"yana masallaci,suna karatu yau"

Aneesa ta ce"okay zan je gidansu Meena yanzu,zan rufe ƙofa,idan Al'amin ya dawo ya buga gida ku faɗa masa ya biyo ni gidansu Meena ya karɓi makulli,sai na dawo"suka yi mata fatan dawowa lafiya,ta sanya hijabinta ta fice daga gidan 

Tana shiga gidansu Meena ta ganta a zaune a parlour cike da farin ciki tana faɗin "Mrs Faisal in sha Allah,ya garin? Aneesa ta yi murmushin yaƙe kawai, Meena tana murmushi ta ce"kaya aka kawo,na zaɓar miki wasu, bari ki gansu"har zata tafi Aneesa ta riƙo ta tana faɗin"kin san bani da kuɗi,kar ki haɗa min gwarama,kin san bana son damuwa"ta ja tsaki ta ce"rainin hankali!to siya miki na yi,ina zuwa"ta yi azamar ficewa daga parlourn 

Ɗakinta ta shiga,ta kira numbern yaran Faisal ya gaya musu su shiri, kowanne lokaci daga yanzu zata iya fitowa don tana gidansu,sannan ta koma parlour bayan ta ɗebi kayan

Sun ɗan juma suna hira kafin Anee ta ɗebi kayanta ta yiwa Meena sallama tana godiya,ita kanta Anee ta yi mamakin fara'ar Meena,ko da ta tambaye ta cewa ta yi babu komai kawai yanayin garin ne yake mata daɗi 

Yaron su Faisal mai suna Charles ne ya fara hango matashiyar budurwa ta fito daga gidan da akayi masa kwatance, Allah ya ba shi sa'a bai ga mutane ba,dama area ɗin su Meena Sam babu mutane,yana kallonta har ta zo ta saitin motarsu, ya matso kusa da ita kamar zai yi mata magana,tana waigawa don bashi attention ya yi hanzarin shaƙa mata Cocaine,kafin ta san me take yi ya ja ta zuwa mota ,ya rufe, abokinshi da suke tare ya ja motar da gudu suka bar wajen




Tirƙashi🤔




*This is the end of free pages,ga duk mai buƙatar wannan littafin don jin yaya wannan cukurkuɗaɗɗen lamarin zai warware ya biya paid group,#500 ne kacal, VIP group kuma 1k ne,ga number ta nan a ƙasa ga wanda zai yi min magana*



#Nusy_bee
***