MIJIN KARUWA

Chapter 4

by @pinkyjay

💅 *MIJIN KARUWA* 💅
(*Love and romantic story 💋)

Story and Writer Bey 
*PINKY DARLING MRS JAY*
Gimbiyar Jajirtattu Writer's

PAGE 7️⃣▶️8️⃣


Alex ne yace "Anita ga Aroon shine wanda na gaya miki, zamu zo tare." Murmushin ta ƙaƙalo kana tace "Sannunku da zuwa Bara na kawo muku ruwa." Ta shige kitchen Aroon ya rakata da idanu, saboda ganin kwancin nononta kawai  ya tayar mai da sha'awa, da ƙyar ya buɗe baki kamar anyi mai dole kana yace "Alex anya wannan yarinyar zata iya ɗaukata kuwa?


tayi yarinta dayawa baza ta wuce 17-18 year's ba fa." Alex yace "Ina mai tabbatar ma zata baka mamaki baka san yara sunfi wasu manyan mata jarumta ba fagen sha'ani?." Aroon yace "Uhmm." bai koma magana ba, lokacin Anita ta fito ɗauke da tire, kayan abinci da lemu, ta dire gabansu, 


kana ta zauna Alex ya tura mata saƙo a waya tana dubawa wani murmushi tayi kana ya je kan kujerar da Aroon yake zaune itama ta zauna gefensa har jikinsu na gugur juna, pilet ta janyo tana zuba jalop ɗin taliya da mango juice, gilas cup, spoon ta saka tare da ɗibo abincin tana kallon Aroon tace "Bisimillah my dear!." 


tana kai cokalin gab da bakinsa idanu ya zuba mata yadda tayi mai kamar wani yaronta kamar tasan abinda yake tunani kenan tace "Kaga fa ka buɗe baki kawai kaci abinci Alex ya gayamin duk abinda kake buƙata, so naga kamar ba iya wancen kake buƙata ba har da wannan kulawa kana buƙata,


saboda haka buɗe min bakinka kawai." Tafa tana ɗora cokalin a bakinsa, Alex dake kallonsu, yace "Haba Aroon ka buɗe baki mana." Haka ta rinƙa ciyar da shi, bai kula ba yaci abincin sosai, ta bashi mango juice ya sha kana ta goge mai baki, Alex kuwa na gefe ya cika cikinsa fam yace "Anita ki saka min raguwar abincin a kula gobe zan mayar miki, 


wallahi nayi missing ɗin girkinki sosai." Rausayar da kai tayi kana tace ka shiga kitchen ka zuba, kayan abincin ta kwashe kana ta dawo jikin Aroon ta zauna tare da kwantar da ƙirjinta kan nashi, tace "Baby tun zuwanku bakayi magana ba lafiya.?"  Ta faɗa, cikin yanayin shagwaɓa, sai da tsikar jinkinsa ta tashi, 

shafa fuskarsa ya yi kana yace "Am ba komai zan tafi sai munyi magana." Ya faɗa tare da janyeta jikinsa, tace "Okey." Bedroom ɗinta ta shiga wani kwalin turare ne ta ɗauko mai data siyo a Dubai a kuɗin Najeriya dubu ɗari uku ne kuɗinsa, ta saka cikin wata ƙaramar jaka mai masifar kyau, ta fito har sun fita parlon, 


saida ya shiga Mota kana ta bashi jakar tace "Ga wannan ƴar ƙaramar kyauta na gode sosai Allah ya tsare." Tana gama faɗar haka ta juya tare karkaɗa mai ɗuwawunta, rufe idanunsa ya yi da sauri, yana ɗora kansa a sitiyarin mota, Anita kuwa tana komawa ta kira Rumana ta da wasu ƙawayenta tace duk abinda sukeyi suzo gidanta yanzu,


Aroon kuwa da ƙyar ya ƙarasa gida a hanya ya sauke Alex, a parlo ya samu Samra, tana sana'ar dannar waya, tana ganinsa da jaka ta biyu bayansa tana kiran "Aroon menen wannan ni ka siyowa.?" Tana ƙoƙarin karɓar jakar ya buge mata hannu, ya shige bedroom ɗinsa, tare da saka key, kwanciya ya yi kan bed idanunsa, na ƙara hasko mai bearst ɗin Anita da ɗuwawanta, ga shep ɗin hips ɗinta, 


Anita kuwa kayan ta shiga buɗewa tana dubawa, sai ga ƙawayenta Aliya da Rumana da Nihal, Aliya tace "Anita wannan kayan fa na waye.?" Rumana tace "Ikon Allah!." Nihal tace "Wannan tambayar fa ai kusan wannan kayan nata ne bana kowa ba." Anita tace "Kai ƙawata kanki naja wallahi, bari na baku labari."

nan ta sanar dasu abinda ke faruwa, Rumana tace ina "Ina fatar ke yarda da auren saboda wallahi na jima inason naga ranar da Aroon zai ƙara aure, sai gashi abin ya kwana gidan sauƙi." Anita tace " Besty dama kesan Aroon ne.?" Tace " Sosai kuwa Anty Jannat yaso ya aure amma matar babansa, ta hana saboda son abin duniya shine ta haɗa shi da ƴarta, Samra,  da yarinyar tazo gidan ubanta yarasu,


baya iya jayayya Hajiya Nafisa saboda ta mallake sa ta cosa mai ƙiyayyar mahaifiyarsa, Samra nada masifar kishi, ko kaɗan bata yarda wata ƴa mace ta kusance Mijinta ba, ko masu aikin gidan maza ne ba mata, saboda kishi, duk yacce zan gayamiki labarin Samra da Mamanta Hajiya Nafisa bazaki gane ba, sai ke zauna da su, makirai ne na bugawa a jarida, 


saboda haka ya zama dole ki zage damtsi, Anita ki aje komai gefe ki samu soyayyar Aroon dole sai ke aje komai gefe kiyi iya ƙoƙarinki, ki sace zuciyar Aroon zamuyi iya ƙoƙarin zamu taimaka miki Anita please ki ajiye komai dan Allah." Shiru tayi kana tace "Naji zanyi tunani." Kafin ta ɗibarwa kowa kayan 


su Nihal kuwa gidansu suka wuce saboda shirin fita zuwa party, Rumana Alhajinta yazo ɗaukarta tacewa Anita sai sun haɗu gurin party, tun fitarsu kwanciya tayi kan kujera, ta lola duniyar tunani, itafa tana tsoron masu biyar Malamai, amma ba komai zata aure Aroon, saita koyawa Samra da Ummanta hankali, 


Samra kuwa mamaki ne ya kamata yau ita Aroon zaiyiwa haka, lallai da sake Ummanta ta kira tana ɗagawa tace "Hello Mommy wallahi gaba ɗaya Aroon ya sauwa kwana biyun nan." Nan ta kwashe ƙarya da gaskiya ta gaya mata, Mommyn tace "Haba Samra ai tun ranar da ya fara yimiki iskanci ya kamata ki sanar dani, 


amma karki damu gobe zanje gurin malam, ya duba muna abinda ke faruwa." Tace"Yauwa Mommy shi yasa nike masifar sonki." Kana ta kashe wayar, Hajiya Nafisa kuwa Aroon ta kira tana son ganinsa, yace bayan sallar isha zai zo, daga masallaci, ya wuce gidansu dake rijiyar lemo, da sallama ya shiga babban parlon gidan, 


Writer Bey PINKY DARLING