MIJIN KARUWA

Chapter 5

by @pinkyjay

💅 *MIJIN KARUWA* 💅
(*Love and romantic story* 💋)
Story and Writer Bey 
*PINKY DARLING MRS JAY*
*Gimbiyar Jajirtattu Writer's*

PAGE 9️⃣▶️1️⃣0️⃣

Gaba ɗaya mutanen gidan suna paroln, Alhaji Abdullahi da Hajiya Nafisa, sai ƴaƴanta guda biyu Zubaida da Husna, bayan ya gaida su kana yaran suka gaida Aroon shiru paroln ya yi kafin Abba yace "Babana kamar da magana a bakinka.?" Sosa kansa kana yace "Eh Abba muje ciki." Hajiya Nafisa tace "Wane irin kuje ciki ke Zubaida ku tashi 


zuwa ɗakinku magana zasuyi." Ba musu yaran suka tashi, kana Abba yace "ina jinka Babana meke faruwa ne.?" Gyra zama ya yi kana yace "Abba aure zanyi inaso ka sanar dasu Uncel Bashir." Abba yace "Aure! fa kace Babana gaba ɗaya yashe akayi aurnka da Samra yanzu kazo da zancen aure." 


Hajiya Nafisa kuwa ba ƙaramar kaɗuwa tayi ba da jin zancen auren Aroon yace "Abba wannan fa itace wacce nikeso mun jima muna soyayya nida ita, lokacin da natafi London shine ina dawowa ka ɗaura min aure da samra, banyima gardama ba na amince yanzu meya sa kai bazaka yimin abinda nikeso ba.?" 


Aroon ya faɗa yana kwantar da murya, tausayin ɗansa ne ya kama Abba yace "Shikenan Babana in sha Allah gobe zan sanar dasu, sai aje a nemo ma aurenta!." Hajiya Nafisa tace "Haba Abban Zubaida yanzu bayansa zaka bi ya ƙara aure me Samra tayi masa gidan duniya? Ya rasa abinda zai saka mata da shi, sai kishiya."


Abba yace "Hajiya Nafisa namji da mijin mace huɗu ne Allah ya halitta mai auren mace fiye da ɗaya har zuwa huɗu, yadda mukayiwa Aroon ba Kowane ɗa mai biyayya zai yarda ayi mai haka ba, a tunanina kema zaki goya mai baya, ya aure wacce yakeso." Hajiya Nafisa tace "Haka ne Allah ya sanya alkhayri." 

Abba yace "Amin ko kefa." Kana yace Babana ƴar gidan waye.?" Aroon yace "Abba marainiya ce, bata da Iyaye, duk sun rasu sanadiyar gobara, kuma gaba ɗaya iyayenta ba ƴan ƙasar nan bane, wannan dalili ne ya sa naƙara son auren ta." Ɗari-bisa ɗari Abba ya yarda da maganar Aroon yace "Yanzu tana ina ne." Aroon yace "Tana Unguwa uku, 

a chan na siya mata gida ta zauna tare da dattijowa dake tayata zama." Abba yace "ma sha Allah gaskiya ina alfahari da kai Babana kana da hankali sosai da sanin ya kamata, saboda haka, gobe Hajiya Nafisa kuje a ɗauko ta ta zauna gidan nan sati mai zuwa sai a ɗaura aure."  Aroon yace "A'a Daddy kawai a ɗaura auren banda gobe,


saboda tafiya zanyi zuwa Ingila." Abba yace "To Babana yadda kake so haka za'ayi, Hajiya ba sai keje ba, zan tura miki miliyan ɗari biyar ki haɗa mata kayan lefe na gani na faɗa, kai kuma Babana sai ka baiwa Samra kuɗi itama ta siye abinda take buƙata." "Okey Abba na gode." Kana ya kalle Hajiya Nafisa yace "Mommy gani." Tace "No maganar ta wuce ka tafi kawai."


ta faɗa tare da barin paroln, Abba ma yace "Babana sai da safe karka damu da sauyawarta dole taji ba daɗi zakayiwa ƴar cikinta kishiya kasan mata haka suke in sha Allah zuwa gobe zata dawo dai-dai." Da wannan Aroon ya samu ƙarfin guywa, ya wuce gidansa Alex ya kira yana ɗagawa yake sanar da shi yadda sukayi da Abba,


Alex yace "Aroon waye ya baka wannan labarin.?" Aroon yace "Na rasa abinda zan gayama Abba ne kasan halina ban iya ƙarya ba wallahi wannan ne karona na farko." Alex yace "Wallahi Aroon ba ƙarya ka faɗawa Abba ba, da gaske abinda ya faru da Anita kenan." "Ya salam!." Aroon ya furta yace "Yanzu kana nufin bata da kowa a ƙasar nan.?" 

Alex yace "sosai kuwa batasan asalin ƙasarsu ba, wuta ta cinye komai." Aroon yace "Shikenan sai munyi magana."

Hajiya Nafisa kuwa Samra ta kira, tana ɗagawa tace "Ya dai Mommy ya zo gidan ya ku kayi da shi.?" Mommyn tace "Samra zama bai kamani ba Aroon aure zai ƙara satin nan yanzu haka yana parol shi da Abbansa ya goya mai baya, saboda haka karki yarda ya samu damarki Samra ki tayar mai da hankali ya kasa samun natsuwa,

zuwa gobe zanje nida Hajiya Mairo, gurin binciken ko wacece zai aura." Samra da taji maganar auren Aroon kamar saukar arado tsaye take gaban mirror saida ta kai zaune zuciyarta na dukan uku-uku tace "Aure fa Mommy lallai Aroon ya cika butulu amma zan gasa mai gyaɗa a hannu." Mommyn tace "yauwa Ƴata haka nikeso, sai munyi magana." Ta datse kiran, 

 Ya kashe wayar  Samra ce ta shigo, ɗakinsa riƙe da ƙugu kallonta ya yi kana ya kawar da kansa, "Aroon ashe maciyi amana ne kawai wato ni zakayiwa kishiya  wallahi wallahi kaji na ranste da Allah duk macen da ta shigo gidan nan saina nakasa ta,


saina gidan nan ya zame mata bala'i da masifa, wallahi Aroon saikayi nadamar zuwanka duniya duk baka janye maganar auren nan banda cin amana yanzu shi ne Abba ya goya ma baya kaje kayi aure, saboda ni ba ƴarsa bace ai da Husna za'ayiwa kishiya na tabbatar sai inda ƙarfinsa ya ƙare, kai kuma butulu miye Mahaifiyata batayi ma, ba,


itace tayi ma komai har ka girma me ya hana sakarar uwarka ta.....Tas! Tas! Kakeji har sau uku, Aroon ya kife ta da muruka sai da ta ga wasu taurari sun gifta ma ta, wani jiri na kwasar ta, cikin ɓaci rai yace "Samira wallahi idan ki ka kuskura koma ambatar mahaifiyata saina zubar miki da haƙura banza kawai wacce batasan ciyon kanta ba."


duk da marin ya shige ta ta tsorata sosai da yanayinsa amma bakinta bai mutu ba, sai cewa tayi "Idan ka iya ka aika ni lahira, kuma wallahi bala'i da masifa yanzu ka fara ganinsu a gidan nan." Da gudu ta bar ɗakin ta san idan ta tsaya komai zai iya faruwa, 


Writer Bey PINKY DARLING MRS J