Chapter 6
by @pinkyjay
BOOK ONE
PAGE 1️⃣1️⃣▶️1️⃣2️⃣
Aroon kuwa kwanciya ya yi kan bed wato Mommy ta sanar da ita aure zai ƙara shine takeyi mai wannan rashin mutunci,har tana kiransa da butulu, miye ya yi mata da har zata kirasa da butulu amma ba komai duk tsiyar da zatayi a gidan bazai koma shiga sabgarta ba, sai Anita ta shigo gidan zai koya mata hankali, saboda ta rainasa sosai kamar ba Mijinta ba,
amma a haka take tunanin hana sa ƙara aure wannan ai bata isa ba, washegari da safe wanka ya yi kana ya shirya cikin ƙananan kaya, ya fita, abin mamaki parlo ya samu Samra zaune wacce bata tashi bacci sai zuwa 12:00 Pm hanyar fita ya nufa tace "Allah ya haɗa ka da bala'i da masifa Aroon kai da wannan shigiya shaiɗaniyar yarinya da zaka aura."
bai juyo ya kalleta ba ya fita, kai tsaye motarsa ya shiga gidansu ya wuce ya samu Abba ya sanar da shi abinda Samra tayi mai da zai fito haƙuri Abba ya bashi kana yace zai kirata ya yi mata faɗa kana yace "Abba Mommy na ciki.?" Yace "A'a ta fita tun ƙarfe 7:00 na safe har yanzu bata dawo ba, na kira wayarta bata ɗauka ba."
Aroon yace "shikenan Abba ni zan fita gurin Anita zanje mu ƙarasa magana naji ko akwai abinda take buƙata." Abba yace "Allah ya tsare ya kai ka lafiya ka gaidar min da ƴata kafin mu haɗu." Kana Aroon ya wuce
ɓangaren Mommy kuwa ita da ƙawarta suka fita zuwa binciken inda Anita take da ƙyar suka samu gidan Anita, a bakin Get sukayi parking ɗin motarsu kana suka shiga norking ɗin get lokacin Anita na zaune parlo ta na azkar, ƙawarta Rumana na kwance kan kujera tana video call da Alhajin ta,
suka fara jin ana norking ɗin gida Anita ta ce "Besty duba ki ga waye yake buga muna gida tun da safe haka." "Okey." Kawai ta ce kana ta fita da ga ita sai rigar bacci, iya cinya ƙofar Get ɗin ta buɗe su Hajiya Nafisa ta gani tsaye kallonsa tayi kana ta ce "A'a daga ina wa kuke nema.?" Hajiya Mairo ta ce "Kece Anita.?" Rumana ta ce "Eh ni ce ya akayi ne.?"
Hajiya Nafisa ta ce "Zuwa mukayi muyi miki kashe di akan aurenki da Aroon don wallahi idan kika yi kuskuren aurensa sai na lahira ya fiki jin daɗi ke banda ma lalacewa me ya gani a jikinki wanda Samra bata da shi.?" Mairo ta ce "Gane min hanya dai Ƙawata, yarinya karuwa mai zaman kanta wacce ko asali bata da shi."
Anita kuwa jin shiru Rumana bata dawo ta sanya hijab ta fito, daidai lokacin da "Rumana ta buɗe baki ta ce "Ke Hajiya Nafisa ki shiga hankalinki wallahi ku na saka ayi muku dukan mutuwa a unguwar nan ke banda ƴarki lalatacciya ce ai da Aroon bazai zo neman Aure ba saboda haka wannan barazanar bata shiga ba kuma wallahi aure anyi an gama."
Anita data ƙaraso ta ce "Bestyna lafiya suwaye.?" Rumana ta ce "Sakarar Matar Uban Aroon ce ko ince surukarsa data shaƙa mai auren jakar ƴarta wacce batasan darajar aure ba barazana tazo yi ma mutane ta ɗauka kowa shasha ne irinta." Hajiya Mairo ta ce "Ke marar kunya uwarki ce shasha." Tas ka keji, Rumana ta ɗauke Hajiya Mairo da mari,
ta ce "Ke ƙaramar karuwa me biyar mazan waje da aurenta har ke isa ki zagar min Uwa na kyale ki wallahi idan ki ka sake wannan kuskure sai na kifar da ke a wurin nan." Hajiya Nafisa ta ce "Wallahi kun jawa kanku bala'i da masifa don yau hannun ƴan sanda zaku kwana." Wata dariya Anita ta yi kana ta ce "To Tsohowar banza mai yawun taya ƴarta kishi,
idan ke isa mu kwana ƙiyama ba hannun ƴan sanda ba idan bakuyi wasa ba kune zaku kwana hannun su ba mu ba, jahilai kawai." Suka shige cikin gida tare da turo ƙofar get da ƙarfi, har ya buge fuskar, Hajiya Nafisa ta dafe goshi ta ce "Mairo muje mu ɗauko wa yaran nan ƴan sanda kawai."
Mairo ta ce "Ina mu ɗauko musu yan daba kawai su lahanta shego zanga yadda za'ayi auren." Nafisa ta ce "Ke kawo shawara muje." Suka shiga Mota suka bar unguwar, ko mintuna goma basu yi ba sai ga Motar Aroon ta shiga unguwar bakin Get ya tsaya kana ya kira wayar Anita, har ta katse bata ɗaga,
haushi abin ya bashi, ya koma kiranta sai lokacin ta ɗauka cikin zafin rai ya ce "Wane irin iskanci ne ina kiran wayarki baki ɗauka.?" Anita kuwa ranta ne ya ɓaci ta ce "Iskancin da ka koya min." "Ke ni kike gayama magana wallahi sainayi maganinki zaki shigo hannuna ne gani ƙofar gida ina jiranki."
"Bazan fito ba." "Okey." Kawai Aroon ya faɗa ya bar Unguwar zuciyarsa na tafarfasa, Alex ya kira bugu ɗaya ya ɗauka "Alex ka sanar da wannan ƴar iskar yarinya na fasa auren." Alex ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un"Aroon me ya yi zafi haka.?" Nan ya gayamai abinda Anita tayi mai Alex ya ce "Kayi haƙuri Aroon yanzu zata kiraka ta baka haƙuri,
kasan yarinya ce fa ba wani wayo ne da ita ba." Tsaki Aroon ya yi kana ya kashe wayar, kiranta Alex ya yi ta ɗauka ya ce "Anita yanzu abinda kika aikata keyi dai dai kenan Mijin da zaki aura ne fa, amma kike gaya mai magana haka zakiyi idan kunyi aure Kesan darajar Miji da aure kuwa? idan baki koye haƙuri da shi sai yaushe zaki koya,
Aroon nada masifar zuciya amma yana da sauƙin kai, sai idan baka zauna da shi ba, wannan aure fa da zakuyi saboda ya samu kwanciyar hankali ne yaji daɗin aure ba wai don ki rinƙa tayar mai da hankali ba kina gaya mai magana yadda kikaga dama Aroon ba sha shanci yazo yi dake ba, da zaki wulaƙanta shi,
gashi yanzu har ya hasala ya ce na sanar da ke ya fasa auren! sai inga ta yadda burinki zai cika." Alex ya kashe wayar ya san yanzu ya birkita mata lilsafi, Anita kuwa tsaye take kitchen, sai da ta kai zaune zuciyarta na dukan uku uku, yanzu ɗan wannan abin da ya faru shine har ya fasa aurenta a fali ta furta na shiga uku yanzu ya zanyi.?"
Writer Bey PINKY DARLING M