MIJIN KARUWA

Chapter 7

by @pinkyjay


BOOK ONE

PAGE 1️⃣3️⃣▶️1️⃣4️⃣

Rumana ce ta shigo kitchen ɗin tace "Ani meke damunki ne wani abin ne ya faru.?" Ta ce "Besty wai Aroon ya fasa aurena saboda ya ce na fito ya na ƙofar gida na ce bazanzo ba." Rumana ta ce "Kai Besty faɗamin gaskiya dai iya abinda ya faru kenan.?" Shiru Anita tayi Rumana ta ce "Na gaya miki Besty ki ajiye wannan zafin kan naki 

da rashin mutunci idan kunyi aure da Matarsa zaki fafata duk abinda ya yi miki karki yarda ki walaƙanta shi a gabanta ko zakiyi mai wani abu ki bari sai Yana bedroom ɗinki amma idan ita tayi miki kici uwar shegiya yanzu abinda ya kamata ki kirasa ki bashi haƙuri."

"Na bashi haƙuri fa.?" "Eh mana ko bazakiyi ba kefa Anita kinada matsala wallahi yanzu duk abinda na faɗa miki be shiga kunnen ki ba to idan bazaki iya ba ai shikenan ke kikayi asara." Rumana na gama faɗar haka ta bar kitchen ɗin Anita ta biyo bayanta da gudu tana faɗin "Kiyi haƙuri Besty zan kirasa yanzu." 


Wayar ta ɗauka kana ta danna mai kira kusan sau uku bayan ɗagawa sai a na huɗu ya ɗaga batare da yace mata komai ba, cikin sanyin murya tace "I'm sorry my dear raina ne a ɓace Mamanka ce tazo ita da ƙawarta suka yi muna rashin mutunci, yanzu haka sunje ɗauko muna ƴan sanda." Lumfashi ya sauke! 

Kana ya ce "Okey." Ya kashe wayar Anita ta ce "Besty kiji fa abinda ya ce wai Okey ya kashe wayar ɗan rainin hankali." Rumana ta ce "Kega fa sai keyi haƙuri, be fiye magana bane, a hankali zaki saba da halinsa, wata ƙila ki sauya shi ya rinƙa magana yadda ya kamata." "To naji yanzu dai muje gidan cin abinci, yunwa nikeji bazan iya girki ba."

Rumana tace "babu gidan abincin da suka isa buɗewa Bara na shiga kitchen ɗin." Aroon kuwa jin Hajiya Nafisa taje gidan abin ya bashi mamaki,  beyi tsammanin haka daga gareta ba, saboda haka kiran Alex ya koma yi ya sanar da shi, abinda ke faruwa Alex yace "Aroon kana da ƙarfin iko a ƙasar nan saboda haka 

ka kira  shugaban ƴan sanda ya turo jami'an tsaro, su yi gadin gidan duk wanda ya zo su kama shi."  "Okey Bara na kira." Ya kashe wayar Anita kuwa Alex ta kira ya ce "Yanzu nike ƙoƙarin kiranki, Aroon zai turo jami'an tsaro zasuyi gadin gidan duk wanda ya zo kamashi zasuyi." 

Anita ta ce "Ya haƙura kenan.?" Alex ya ce "Bansaniba." "Haba Alex miye haka wallahi na bashi haƙuri." "To ke kyautawa kanki sai anjima." Ya kashe wayar,  

Hajiya Nafisa kuwa ƴan daba sukayo haya mota ɗaya suka dawo Unguwar, zuwansu ya yi daidai da isowar jami'an tsaro, aikuwa kafin kace me sun chafke su gaba ɗaya sun zuba a mota, harsu Hajiya Nafisa aka wuce Office dasu Aroon aka kira suka sanar da shi, ya ce a tsare su 


kar a sake kowa, Hajiya Nafisa ta ce "Uban waye ya baku damar kamani har ku ajiyeni cikin wannan ƙazamin wurin kun san ni matar waye.?" Babu wanda ya tanka mata tayi ta masifa da zage zage tana son kiran Daddyn Aroon amma tana jin shakkar gayamai abinda ta aikata, 


Aroon ta kira, amma yaƙi ɗagawa, ƙarshe kashe wayarsa ya yi, dole ta kira Daddy buga ɗaya ya ɗauka , ta sanar da shi, tana Office ɗin ƴan sanda, ya ce "Me ya kaiki Ofishin ƴan sanda Nafisa.?" Kaga fa wasu ƴan iskan yara ne sukayiwa min rashin kunya nida Ƙawata Mairo shine muka ɗauko yaran da zasu koya musu hankali shine ƴan sanda suka kama mu."

"Ai kunci riba nidai bazan zo ba zankira DSP ." Ya kashe wayar DSP ya kira nan yake sanar da shi, Ƴallabai Aroon ne ya bada izinin a kama su  babu yadda za'ayi a sake su dole sai Aroon ya sani Daddy ya kira wayar Aroon bata shiga Alex ya kira bugu ɗaya ya ɗauka bayan sun gaisa Daddy ya ce "Aliyu ina Aroon yake.?" 

"Alex ya ce "Gaba ɗaya yau bamu haɗu ba." Daddy ya ce "duk inda yake ka nemo min shi yanzu ina nemansa." Alex ya ce "Angama Daddy." Kallon Aroon ya yi dake kwance kan kujera, ya ce "Inaga fa Mommy ta kira Daddy kasan baza'a iya sakinsu ba dole sai da yardar ka, Daddy ya ce duk inda kake na nemo ka yana son ganinka." 

Aroon ya ce "Kaga babu inda zanje." "Haba Aroon Daddy ne fa kayi haƙuri dan Allah kaje saboda duk abinda su Mommy sukayi ai bashi ya turata ba." Da ƙyar Aroon ya yarda suka wuce gida wurin Daddy Yana paroln sa Daddy ya ce "Babana ya akayi ka saka aka kama Mommyn ku." Aroon ya ce "Daddy nifa ban san Mommy bace,


Anita ta kirani wasu mata sunzo sun zageta har sunyi barazanar ɗauko mata ƴan sanda shine na kira jami'an tsaro na ce duk wanda ya dawo gidan su kama shi." "To yanzu ka kira a sake su ta dawo gida  nan Aroon ya kira aka sake Hajiya Nafisa da Mairo 


Aroon ya ce "Daddy inaso gobe a ɗaura min aure da Anita."  Daddy ya ce "Ayi haka Babana.?" "Eh Daddy zanyi magana da ita." Daddy ya ce "Okey To Allah ya kaimu zan sanar da Babanka guda." To Daddy maganar lefen nan a barta kawai zan kai mata kayan da zatayi amfani dasu zuwa jibi sai muje tare ta na siya mata duk abinda takeso."


"To shikenan Allah ya yima albarka." Ya ce Amin suna fita gidan Unguwar su Anita suka nufa, Alex ya kirata a waya suna ƙofar gida, da sauri ta fito gudun kartayi laifi gaidasu tayi Alex ne kawai ya amsa Aroon kuwa sai haɗe fuska ya yi, ganin yadda ta fito daga ita sai wando iya guywa da riga sai ɗan ƙaramin mayafin abaya data rufe kanta da shi, 


Alex ya ce dama munzo sanar dake ne gobe idan an gama sallar jumu'a za'a ɗaura aurenku keda Aroon kuma gobe zaki tare." Da sauri ta kallesa kana tace "Haba Alex ya zakayi min haka babu abinda na shirya fa." Sai lokacin Aroon ya yi magana "Dama ai ba dole saike shirya ba don ba shirinki nike buƙata ba, yanzu kije ki sauya kaya,

Ki fito na ajeki wurin gyaran jiki." Ganin babu alamar wasa akan fuskarsa ta koma ciki ta sanar da Rumana suka shirya kana suka fito, wani babban shagon gyaran jiki na Hauwa Maiduguri ya kaisu komai anayi a shagon gyaran jiki kitso da lalle na amare. da kayan mata duk wani abu da ya danganci gyaran jiki na mata anayi a wurin,


Mai shagon ya yi magana da ita yace ayi ma ta duk abinda ya dace zaije ya dawo a nan ya barsu kana ya wuce gidansa, Samra bata gidan Companynsa na kayan ɗaki ya kira, suka zo aka kwashe komai aka zuba sabbin kayan ɗaki da parlo, har Kitchen biyu ne ya buɗe ɗaya aka zuba mai kayan kitchen su gas aka jona komai,

aka sauya labulayen gidan gaba ɗaya Kowane part da kalar kayan da aka zuba mai, koda akayi sallar la'asar an kammala komai Alex ya je gidan Anita ya kwaso kayanta gaba ɗaya aka saka mata a part ɗinta kana Aroon ya rufe da key wanka ya yi kana ya shirya cikin wani lallausan yadi read  colour ya yi masifar kyau, 


ya fito, suka fita shida Alex,  sai bayan sallar magrib suka je ɗaukar Anita gaba ɗaya Aroon bai ganeta saboda tayi masifar kyau da haɗuwa har wani sheƙi fatar jikinta keyi, kamar wacce tayi wata ɗaya ana gyarawa, nan. Aroon ya biya kuɗin da aka kashe mata suka wuce gida, 


Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY