Chapter 8
by @pinkyjay
BOOK ONE
PAGE1️⃣5️⃣▶️1️⃣6️⃣
Rumana ta kira su Nihal ta sanar dasu gobe ne ɗauren Aure saboda haka su fito da wuri a gayama sauran ƙawaye, saboda ayi walima da yamma, ai kuwa haka akayi dama suna da group, Aliya ta sanar nan fa suka fara shirye-shiryen abinda za'a yi goben,
Anita ta ce "Besty nifa kamar a mafalki nike ganin wannan lamari." Dariya Rumana tayi kana ta ce "Ai haka abubuwa ke zuwa fatanmu Allah ya sa gidan zamanki ne har abada, Allah ya sa aurenku ya zama alkhayri ga juna."
Ƙarfi sha ɗaya na dare Aroon ya kira Anita Alex zaizo ya kawo mata kayan da zatayi amfani dasu gobe saboda akwai dinner ƙarfe tara na dare, Rumana tace "Kai amma gaskiya an mamaye mu dole ma mu fita tunda safe muje kantin Hajiya Mamu mu siye kayan da zamu saka wurin dinner."
Anita tace "Tana siyar da ɗin kakkun kaya ne.?" "Eh mana har na anko." Data ta kunna ta shiga group ta sanar da su kowa ya fito da kuɗi washegari, ranar sukaje shagon dama su uku ne manyan ƙawayen Anita suka siye wani blue ɗin matiriyal da net fari, sauran ƙawayensu suka siye farin yaɗi da blue ɗin net,
suka wuce kasuwa wurin soyayyar kayan walima, sai 12 suka dawo Aliya ta kira me kwalliya tazo aka fara yima Anita said an gab da tasowa masallaci aka kammala Alex ya kawo mata dogayen riguna kala biyu, da gorldig, da ash ko wace da takalmi da jaka da sarƙa, ash ɗin riga ta saka aka kafa mata ɗauri mai kyau irin na amare,
kana su Rumana suka fara shiryawa, Alex ne ya kira Aliya ya ce mata an ɗaura auren Anita da Aroon suna hanya gasu nan zuwa ƙarfe uku suka iso gidan aka fito da Anita zuwa mota zasuje gidan hutwar Aroon ayi musu hotona, tare da me kwalliya akaje da Rumana,
idan ku ka yadda Aroon ya sha ado kamar wannan ne aurensa na fari, ya yi kyau kamar ka sace sa ka gudu, suna isa aka fara ɗaukar su video da hotona, sai wani murmushi suke zubawa kamar irin Masoyan nan da suka jima suna soyayya, sunyi hotona sunfi kala ashirin kana aka mayar da Anita gida,
Rumana tayi magana da mai Camera ya tura mata wasu hotona guda biyu nasu Aroon ta wuce da su wurin buga jakunkuna, a aka haɗa komai kana ta dawo gida
lokacin ƙarfe huɗu na yamma, wanka Anita ta sakeyi ta saka wata Black ɗin lafaya kana aka fara shirye-shiryen walima ƙarfe huɗu da rabi Malamar da suka gayyta tazo ba laifi an taru sosai, anyi walima lafiya, an rabawa jama'a kayan biki ga manyan jakunkuna da akayi masu ɗauke da hoton Anita da Aroon,
Ɓangaren Samra kuwa, gida ta koma ta saka Hajiya Nafisa a gaba tana kuka dole sai Aroon ya fasa auren Anita, babu kalar lallashin da batayi mata ba amma a banza dole ta ɗauke ta a Mota suka nufe gidan Hajiya Mairo ta kaisu gidan Malam nan fa ya shiga zane zane kan ƙasa ya jima yana abu ɗaya har gumi yake haɗawa,
kana ya ɗago fuskarsa ya ce "Gaskiya akwai matsala babba wannan auren babu makawa har an ɗaura shi to amma nayi wani bincike, wanda ya rikitar dani ban taɓa ganin irin abinda na gani a wannan lamari ba amma akwai mafita guda ɗaya zan bata maganin da zatayi amfani da shi, na kwana uku daga lokacin zai juyawa yarinya baya,
da ita da babu duk ɗaya sai abinda ku kace shi zaiyi amma sharaɗin wannan aikin kar ki kuskura cewa ya sake Yarinyar, wani ƙullin magani ya ɗauko ya bata kana ya ce " ki rinƙa turarasa sau uku a rana har na kwana uku ki tabbatar da shi da ita sun shaƙe wannan turare." Karɓa tayi sukayi godiya kana Hajiya Nafisa ta ajiye mai rafar kuɗi suka fito,
ita da Hajiya Mairo sai miyagun shawara suke baiwa Samra, akan yadda zata juya Aroon ta walaƙanta Anita, har suka iso gida,
Ƙarfe takwas aka fara shirye-shiryen zuwa dinner, golden ɗin dogowar riga ta saka aka kafa mata ɗauri mai kyau, ta saka takalmi masu masifar tsini, da sarƙar zinari, ba'ayi minti goma ba Wasu arnayen Motoci suka zo ɗaukar Anita, farar Mota Anita ta shiga Aroon na ciki ya sha wankan gizna, fara, anyi mai aikin zare Golden,
hular kansa ma haka, da takalmi, haka motaci suka nufe babban hall da aka ƙawata shi domin dinner, motacin na isa masu Camera suka fito aka fara ɗaukar su hotona da video,wani security ne ya fito ya budema Aroon mota ya ya jima kafin ya fito kana ya miƙawa Anita hannu ta fito, ƙafrta ta zame ta faɗa ƙirjin Aroon ya saka hannu ya zageye ƙugunta suna kallon juna nan fa wuri yta kauri da Ihu da tafi,
masu wayoyi na ƙara ɗaukarsu hoto, saƙale da hannun juna suka shiga wurin taron, Dj ya sake musu waƙar Ali jita ko rana da wata suna da haske gimbiyata saike soyayyar mu har abada Ilove You baby Sarauniya Baby har suka isa wurin zamansu aka fara rabawa mutane abinci da kayan lashe lashe, daga nan aka buƙace ango da amarya su fito fili, aka saka musu waƙar Ali jita, nan fa mayan abokan Aroon suka fito, dana Anita suka fara zuba masu kuɗi
Wani gaye me suna Maleek dala ya rinƙa karawa su Aroon Rumana ita da su Nihal dala suke zuwabawa Anita, dai dai lokacin Samra ta iso ita da su Husna da Hajiya Nafisa, Dj kuwa da MC sunga kuɗi sai kirari suke zuwabawa Aroon don shi rufin India ya fitar ya na liƙawa Anita, itama ta na kara mai,
kafin MC ya buƙace su koma su zauna Samra kuwa kamar ta haɗiye zuciya ta mutu idanunta sun ciko da hawaye ta ce "Haba Mommy dama Kesan wannan yarinyar ta fini komai amma bakiyi gaggawar zuwa wurin Malam ba sai yau dana matsa miki, jifa kiga yadda yake rawar ƙafa a kanta ko lokacin da akayi bikinmu ba'ayi hidima irin wannan ba,
gaskiya Aroon ya cuceni ta fashe da kuka tare da barin wurin ta shige mota, Hanya Nafisa tabi bayanta tana kiran su Husna suzo su tafi gida amma sukace babu inda zasuje, MC sukayiwa magana kannen ango suna buƙatar Amrya ta fito fili, ita da ango, ai kuwa MC ya kira su suka fito,
su Husna suka fito fili aka saka musu kiɗa suka rinƙa yiwa su Aroon karin daloli shinma Aroon da Anita suka shiga karawa su Husna abin ya burge kowa kafin ƙarfe 11 na dare taron ya watse, bayan su Rumana sun raka Amarya ɗakinta, suka wuce gida, sai lokacin wani kuka mai cin rai ya zowa Anita,
yau tayi aure babu Uwa ba Uba ba dangi ko ɗaya sai ƙawaye, data gaji da kuka wanka tayi ta buɗe wadroub ta ɗauko kayan bacci ta saka, gefen gado ta zauna, tayi shiru, tana tunani, Aroon ne ya turo ƙofar ya shigo, part ɗin Samra ya shiga amma ta rufe ya yi bugawa taƙi buɗewa, dole ya dawo, ledar ya ajeye kana ya ce "Je kiyi alwala."
Batace komai ba ta shiga bathroom tayi kana ta saka dogon hijab har ƙasa, ya jasu sallah kamar yadda addini ya tanadar haka sukayi da kansa ya ɗauko pilet ya zuba Naman kazar a ciki kana zuba madara mai sanyi cikin cup, kallonta ya yi kana ya ce "Zo ki ci abinci, yarinya." Kau da kanta tayi kana ta ce "Na ƙoshi." "Okey."
Madarar kawai ya sha kana. saka naman a firij, ya kashe hasken ɗakin, ya zo ya kwanta tare da janyota jikinsa, kwacewa tayi ya ce "Kega wallahi ƙara ma ki tsaya hakan zaifi miki." shiru tayi mai
Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY