MIJIN KARUWA

Chapter 10

by @pinkyjay


BOOK ONE


PAGE 1️⃣9️⃣▶️2️⃣0️⃣



tare suka fito parlo yana riƙe da hannunta suka wace wurin cin abinci da kansa ya zuba mata komai kana ya haɗa tea ya fara sha, Samra ce ta sauko, parlon wani mugun kallo take aikawa Anita kamar ta kasheta haka take ji, wurin cin abincin ta ƙarasa, pilet ta dauka ta zuba abinda take so, kana ta juya da gangan ta buge kujerar da Anita take,


zaune ta kai cup ɗin tea bakinta ya goce tare da zube mata a jiki, wata ƴar ƙaramar ƙara ta saki, tare da janyo Samra da ƙarfi ta kefe ƙasa cike da masifa Anita ta ce "Ke mahaukaciyar ina ce duk hanyar dake wurin nan batayi miki ba sai wurin da nike, shine saboda sharri zaki nemi ƙona ni, to wallahi ki shiga hankalinki." 

Samra kuwa da kanta ya bugu da step ɗin wurin cikin zafin rai ta miƙa tsaye, ta ware hannu zata kaiwa Anita mari cikin zafin Nama ta goce, tare da riƙa mata hannu, ta ce "Kan Uba ni zakiyi ƙoƙarin duka to wallahi na wuce ki, mahaukaciyar banza kawai." Samra ta ce "Kutumar Uba ni kike kira Mahaukaciya ko da yake ba laifinki bane,


rashin tarbiyya ne da baki samu ba sai yawon karuwanci, kawai kika ajiye." "Hhhhhhh naji banda tarbiyya ke banda biyar Malamai me uwar taki ta koya miki, wacce ko lalurar mijinta bata iya ɗauka har zaki nuna min ke wata ce to ni nafi ƙarfinki wallahi na wuceki nesa ba kusa sai ki tambayesa nida ke wacece karuwa wacece cikakkiyar Mace." 


Samra ta ce "Ke Uwar yawa zakiyiwa sharri ko da yake wannan sakaren da ya ajiyeki shine ya janyo mata duk kalar zagin da kikeyi mata." Tas tas! Anita ta wanke Samra da mari "Ke jaka jahila Mijin nawa ne sakare Uwarki ce sakara da bata koya miki yadda ake girmama miji ba, kuma wallahi idan kika koma zagina sai jikinki ya tsami." 

Kallon Aroon tayi dake zaune yana kallonsa hankalinsa kwance ta ce "Beb muje ciki ko." Ta shi ya yi kana ya riƙa hannun Anita suka bar Samra nan tsaye dafe da fuska, "Wshi Allah na!." Anita ta faɗa tare da yi baya kamar zata faɗi da sauri Aroon ya taro ta, "Lafiya." Ya faɗa cikin sigar shagwaɓa ta ce "bazan iya tafiya bane ƙasana ciyo yake yi sosai."


ɗaukar ta ya yi chak suka shige ciki wani ihu Samra ta saka tare fara fasa kayan dake parlon, tana kuka tana zagin Anita da Aroon,  ganin ɓatawa kanta lokaci takeyi tashi tayi zuwa bedroom ɗinta, wanka tayi kana ta ɗauko key ɗin motarta ta fita, zuwa gida, 


Aroon kuwa kaya ya sauyawa Anita kana ya ce zai fita sai ya dawo har waje ta rakasa ya ce masu aiki su kwashe kayan da Samra ta fasa a fitar da su waje za'a kawo sabbi, Company ya wuce saboda ya san Samra taje gida 

be jima da fita ba su Rumana suka zo Anita ta basu labarin abinda ya faru, ai kuwa suka shiga dariya Aliya ta ce "Ai kamata ya yi ki ajiyeta ƙasa kiyi mata mugun duka." Anita tace "Ai bana jin daɗi ne, wallahi sai da Dr Joy ta ɗinka ni da yau ta gane ta takalo tsuliyar dodo." Nihal ta ce "Wai su Any Baby anji maza kenan yanzu ke tantance 


aure da rashin aure." Rumana ta ce "Allah dai ya yi Aroon zai fasa yarinya yanzu sai ki dage sosai da shan ƴaƴan itatuwa don gamsar da Ogah zuwa jibi zan haɗo miki wasu shegun kaya kici uwar sabada." Anita tace "Ke bana so kiga wahalar da nasha kuwa suma fa nayi." Aliya ta ce "Yo ai dole haka ta kasance daren farko, 


gaki gwanar shan zuma kina tsalki da ruwan miski saiki ƙara dagewa sosai kwana biyu sabawa zakiyi wallahi Bura akwai dad'i." Suka fashe da dariya, 


Samra kuwa tana shiga gida bedroom ɗin Hajiya Nafisa ta wuce zaune ta sameta, rungumeta tayi kana ta fashe da kuka tana gaya mata ƙarya da gaskiya wai Aroon marinta ya yi, akan Anita ta zageta ta rama, ai kuwa Mommy ta kira Hajiya Mairo, 

suka haɗu a hanya gidan Aroon suka wuce  da manyan itace zasuyiwa Anita dukan tsiya,  da shigarsu gidan kai tsaye part ɗin Anita suka shiga kayan paroln suka fara fasawa, ƙarar da suka ji ne Rumana ta fito, da gudu ta koma bedroom ta saka key, ta ce "Any Kira Aroon ga Nafisa da Samra nan suna fasa kayan dake parlon ki,


da manyan itace suka shigo." Aliya tace "Kutumar uban nan wallahi babu wanda za'a kira ai ina da saurayi ɗan daba kusa ga Unguwar nan gidansu yake." Kiransa tayi ta sanar da shi, ya ce yanzu ya dawo gida gashi nan zuwa shi da abokansa ta ƙofar baya Anita ta fita ta buɗe musu Get, suka shiga da manyan itace suma kai tsaye paroln suka shiga, 



suka rufe su Hajiya Nafisa da suka ta ko ina sai lokacin su Nihal suka fito, suma suka fara jibagar su Hajiya Mairo party ɗin Samra suka shiga duk abinda ke wannan part sai da suka fasa shi har bedroom ɗinta sai da suka lalata komai, kana suka fito, Hajiya Mairo kuwa da ƙyar ta gudu zuwa waje, anyi musu,


jina jina, kana Saurayin Aliya da jama'arsa suka bar gidan kamar kayan wanki haka su Nihal suka janyo su Samra waje tsakiyar paroln ƙasa suka ajiye su ko motsin kirki basu iyawa, masu aikin gidan na part ɗinsu Babu wanda ya san abinda ke faruwa, Kitchen Anita ta shiga tayi bilandin ɗin tarugu, da gishiri, ta fito, 


ta rinƙa zubawa su Samra shi a jiki sai ihun azaba sukeyi, kana suka koma ciki, paroln suka gyara komai abinda ya fashe suka fitar da shi waje, kana suka dawo paroln ƙasa  suna hira, Alex ne ya Kira Anita ya ce "Amarya ke sha daɗi." Anita ta ce "Alex kasha wahala ya akayi.?" "Au haka zaki cemin, to ya yi, gani bakin Get a buɗe min."


rimout ta danna Get ɗin gidan ya buɗe Alex ya shigo, a ƙofar shigowa paroln ya ga Hajiya Mairo kwance sai mayar da lumfashi takeyi, ciki ya shiga nan ya tarar da su Samra kwance, kamar jajkai, kallon su Aliya ya yi kana ya ce "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! meke faruwa ne.?" Rumana ta gaya mai abinda ya faru, 


da sauri ya kira Aroon ya sanar da shi ya zo gida yanzu akwai matsala kusan minti goma sha 11 saiga Aroon ya shigo da kallo ya ke binsu kafin ya ce "Alex me ya samesu mota ce ta kaɗesu.?" Alex ya ce "Ba wata mota faɗa ne sukayi da su Aliya shine sukayi musu dukan tsiya." 

"To ai sunci riba ni na zata wani abu ne daban." Alex ya ce "Yanzu dai muje a kaisu Hospital, a duba su." Aroon ya ce "Wallahi babu inda zanje ai bani na saka su saboda haka yadda suka kwaso ƙafa suka shigo to su tashi su tafi inda suka fito." Ya na gama faɗar haka ya juya zuwa part ɗinsa 

Kwanciyarsa ya yi, Alex ya kwashe su zuwa Hospital ɗin Aroon aka yi musu duk abinda ya kamata kana ya sauke Mommy gida itama Hajiya Mairo ya sauketa gida kana ya wuce da Samra yana ajeta ya wuce abinsa ko da Samra ta shiga parlon gidan ba kowa, da ƙyar ta haura sama, ta shige bedroom ɗinta, fuskarta duk ta kumbure da dukan da tasha


tashi tayi ta buɗe jakarta ƙullin maganin da Malam ya bata ta ɗauko kana ta fito zuwa kitchen, ta saka turaren a kasko ta fito sai da ta turare parlon gaba ɗaya kana ta haura sama nan ma ta turare sa, ta shige bedroom ɗinta

bata jima da shiga ba su Rumana suka fito zasu wuce gida Anita ta rakosu har bakin Get, Aliya ta ce "Wai bakuji wani warin turare ba da muka fito har kaina sarawa yakeyi.?" Rumana tace "Ni mura nikeyi banji komai ba." Nihal ta ce nima dai haka babu abinda naji." Anita ta ce "gaskiya naji warin turaren maybe kuma wani abu ne da ban ."


Rumana ta ce "To Allah ya kyauta sai na dawo." suka shiga motarsu Anita ta koma ciki har wani jiri takeji a hanya ta haɗu da Aroon ya fito, Abba ya kirasa sai faɗa yakeyi mai Hajiya Nafisa ta gayamai ƙarya da gaskiya wai sunje ganin Anita shine ta saka ƙawayenta sukayi musu dukan tsiya ita da Samra, 


Aroon kuwa ransa in ya yi dubu to ya ɓaci, wai yaushe Mommy ta iya ƙarya ne? babu wanda ya yi ma ɗan uwansa magana ya fita, ita kuma ta shige part ɗinta, lokacin ƙarfe biyar na yamma, Aroon bai dawo gidan ba sai bayan sallar isha'i, lokacin Samra ta koma turare parlon gaba ɗaya har bedroom ɗinsa ta shiga ta saka turaren 


Anita kuwa ciyon kaine ya dameta da ƙyar tayi sallar magrib da isha'i, kana tayi wanka ta gasa jikinta, kayan bacci kawai ta saka kana ta kwanta, ga yunwa takeji amma bazata iya fita ba saboda warin turaren, da ke tashi a paroln ƙasa, wani bacci mai nauyi ya yi awon gaba da ita,  

Aroon kuwa bedroom ɗinsa ya wuce wanka ya yi kana shirya cikin kayan bacci ya kwanta , yana so yaje wurin Anita amma duk jikinsa ya yi sanyi baya jin zai iya tafiya, a haka har bacci ya ɗauke sa, Anita kuwa bacci take sam bata sakawa ranta Aroon zai shigo ba,


Washegari tun da asuba Samra ta koma turare gidan gaba ɗaya koda Aroon ya fito sallar asuba sai tari yake yi har ya bar parlon, Anita kuwa gaba ɗaya bata fito ba sai ƙarfe goma na safe  bata samu kowa ba a paroln ta haɗa abinda zata ci ta koma part ɗinta, 

Hajiya Nafisa kuwa bata haƙura da abinda su Rumana sukayi mata ba saboda haka Unguwa su ta nema koda ta samu gidansu Rumana Mahaifiyarta ce kawai a gidan ta saka ƴan sanda suka tafi da ita, lokacin Rumana ta fita, bata dawo ba sai yamma, maƙociyarsu ce ta sanar da ita Ƴan sanda sun tafi da Ummanta, 


bincike ta soma yi da yake tasan wasu manya har ta gano Office ɗin aka kai Ummnata Alhaji Khamis ta kira suka tafi tare sai da aka kira Hajiya Nafisa bata  zo aka bada belin Umman Rumana suka dawo, gida ko da Hajiya Nafisa ta kira suka sanar da ita anyi belin matar data saka aka kama ,


Gidan ta koma tayi sa'a Rumana da Nihal na gidan tana gaya mata abinda ya faru, "Nihal ta ce "Anya ba Hajiya Nafisa ɓace tayi miki wannan iskanci.?" Rumana tace "bana tunanin itace na tambaye Umma ta ce "Ita bazata iya gane ta ba." Saiga Hajiyar Nafisa ta faɗo cikin gidan Ummnata Rumana ta ce 
Writer Bey PINKY DARLING MRS JAY