Chapter 36
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
036
Cike da tabbatarwa likitan ya ce
''Yadda kika jin malama! Abin da binciken ya bayyana kenan. Sai kuma Echocardiography hoton zuciya,mun gano zuciyarta ta kumbura sannan aikin zuciyar ya ragu sosai. Ejection fraction ya yi ƙasa zuwa 30% wanda hakan yake nuni da chronic heart failure. Hakan ya nuna ta jima tana fama da ciwon. Sai gwajin ƙarshe da muka yi, chest x-ray wato hoton kirji,mun gano zuciyarta ta faɗaɗa,sannan tana da matsalar Pulmonary edems jini ko ruwa sun taru a hunhunta wanda shi ne yake jawo mata aman jiki. Daga ƙarshe mun gano tana fama da chronic heart failure wanda ya tafi zuwa mataki mai matuƙar haɗarin gaske wato stress-induced cardiomyopathy "
Shiru ya ratsa ɗakin,baka jin motsin komai sai shessheƙar kukan Jamila. Damuwa,ƙunci,fargaba da tsoro sun mamaye duniyarta. Ashe yayarta ta jima da ciwon zuciya amma bata taɓa faɗa ba,me ya sa ta kasa fahimtar yanayinta da shirun da take yawan yi ita kaɗai a duk zuwan da take gidan. Me ya sa Yayarta ta ɓoye mata damuwarta har yanzu da ya zama wata babbar matsalar da Ubangiji kaɗai ne ke iya maganceta. Wani sabon kukan ta saki mai sauti. Cike da matsananciyar damuwa Kawu Rabi'u ya dubi likitan ya ce
''Yanzu likita wani taimako za ku iya mata ta samu lafiya har ta tashi a dugaduginta? ''
Ɗan Murmusawa likitan ya yi sannan ya ce
''Za mu yi iya ƙoƙarinmu amma komai yana hannun Ubangiji,muna saka ran in shaa Allah za ta samu lafiya amma za a ɗan jima. Sannan dole ku kuji duk wani abu da zai ɗaga mata hankali,ko barinta shiru. Duk abin da kuka san zai sakata farinciki don Allah ku yi iya ƙoƙarinku don ganin ta samu wannan farincikin,domin ta hakan kaɗai ne zai taimaka zuciyarta ta tsallake wannan matakin mai haɗarin da take ciki a yanzu''
''To likita in shaa Allah za mu yi ƙoƙarin haka.''
''Yawwa! Za ku iya tambayarta kuji me take so,ku kuma idan ta sanar muku sai ku yi ƙoƙarin yi mata abun don faranta ranta. Sannan ku ci gaba da yi mata addu'a,Allah ya bata lafiya ya sa kaffara ne"
''Ameen ya Hayyu ya Qayyum! In shaa Allah za mu yi ƙoƙarin haka mun gode likita'' Kawu Rabi'u ya faɗa yana miƙewa. Jamila ta miƙe tana kuka suka bar ofis ɗin. Tafiya take kamar wacce ƙwai ya fashe mata a ciki,jinta take kamar an zare mata lakkar jiki,duka kuzarinta ya gushe sai tarin gajiyar da bata san afkuwarta ba. Suna gab da shiga ɗakin Kawu Rabi'u ya hangi Jalil riƙe da hannun HAFIZA ta je tarbosu a wajen asibitin,wani ɗan saurayi a gefansa,Hamida da Yasir a bayansu suna tahowa inda sukee. Da sauri Jamila ta hawayenta don bata son ɗaga musu haankali,Jalil ya ga lokacin da ta share hawayen,haka kurum zuciyarsa ta halba. Suna isowa wurin suka gaishe da su tare da ƙarasawa cikin ɗakin. A nan ma suka gaisa da mutanan ɗakin. Kawu Rabi'u ya dubi Yasir ya ce
''Ya ban ga kun zo da mahaifunku ba? Ko ba tafiyarku ɗaya ba ne?"
Shiru Yasir ya yi don bai san amsar da zai ba shi ba, Jalil ne ya yi ƙarfin halin cewa
''Matar shi ta hana shi zuwa Kaka''
''Ta hana shi zuwa! Bata san mahaifiyarku bata da lafiya ba ne?" Ya tambaya.
''Ta sani kaka,don yau ma da ƙyar ta barsu Yasir zuwa nan. Da yake ina wurin mahaifin abokina,jiya da Ammu Jamila ta kira ni cikin dare take sanar mini jikin Ammu ya motsa suna asibiti sai da asuba muka zo gidan Abba kiransu Yasir daman tun daren jiya na sanar musu su shirya. Ta so hanasu zuwa har ta kira Abba daga masallaci a kan ya dakatar da ni,har take cewa idan na nuna taurin kai za ta saka shi ya tsine mini''
Take ɗakin ya kaure da salati da sallalami tsabar yadda maganarsa ta daki zuciyarsu. Jamila kuwa ta kafe Jalil da ido tana sauraronsa. Zuciyarta na wani irin tafarfasa da ƙwaɗayin haɗuwa da Sahura,wata zazazzafar ƙiyayyarta na ƙara naso a cikin zuciyarta. Jalil ya ci gaba da cewa
''Kaka kamar mun sani ni da ɗan uwana Muhsin muka haɗa mata plan a kan idan taƙi yarda mu tafi da su Yasir sai mu yi kiran ƙarya. Daman akwai wata babbar soja da take matuƙar jin tsoranta. Ganin taƙi yarda sai na ce Muhsin ya kira mini lambar madam Ngozi, kafin na kai ga kara wayar a kunne ta ce mu wuce''
''Kai amma wannan matar ba za ta gama da duniya lafiya ba! Wannan wani irin rashin imani ne haka!'' cewar ɗan uwan mahaifinsu Jamila fuskarsa shimfiɗe da maɗaukakin mamaki,don bai da labarin abubuwan da Mairi take fuskanta a gidan auranta.
''Saka mini lambar mahaifinku na kirashi yanzu,wannan ai zancen banza ne! Har mace za ta hanashi zuwa duba uwar 'ya'yansa!'' Kawu Rabi'u ya faɗa a hasale yana miƙa masa ƙaramar wayarsa mai botira. Amsa Jalil ya yi ya saka mishi lambar sannan ya kira ya saka a hands free ya miƙa mishi. Kowa a ɗakin yana jin ƙarar wayar,har ta kusa tsinkewa sannan aka ɗaga kiran. Madadin su ji muryar Dauda Imamu sai suka ji muryar mace ta ɗauka kiran.
''Mai wayar ba ya kusa ne?" Kawu Rabi'u ya tambaya. A can Sahura ta ce
''Ya barta ta yi caji ne a gida. Ni ce matarsa Sahura uwar gida kuma amarya! Za ka iya sanar mini saƙon idan ya zo na faɗa masa!" Ta faɗa cike da tutiya da gadara. Ba Kawu Rabi'u kaɗai ba kusan kowa na ɗakin sai da ya yi mamakin furucinta idan ka cira su Jalil da suka san abin da ya fi ma haka za ta iya faɗa.
''Baki da labarin Mairi abokiyar zamanki bata da lafiya tana kwance a gadon asibiti?" Ya jefo mata tambaya. A can Sahura ta taɓa baki har da jan siririn tsaki ta ce
''Eh! Ina sane! Sai aka yi yaaa!"
Jinjina kai Kawu Rabi'u ya yi jin ƙarfin halin Sahura da rashin kunyarta,lallai matar nan ta yi nisa bata jin kira.
''Yanzu fisabilillah kin yi wa abokiyar zamanki adalci? In kece a halin da take ciki ya za ki ji idan ta hana mijinki zuwa wurinki?''
''Kai dalla malam ja can gefe! Ka daina ma saka ni a matsayinta domin ruwa ba sa'ar gwando ba ne! Na hana shi zuwan sai mene ne! Ko kana da ja ne!"
Girgiza kai Kawu Rabi'u ya yi kamar tana ganinsa ya ce
''Tabbas ba ni da ja amma Ubangiji na kallonki, shi zai yi hisabi a tsakaninku tun a nan duniya ba sai an je lahira ba da yardar Allah'' yana kai ƙarshe ya katse kiran. Idanunsa sun ɗan sirka tsabar ɓacin rai.
''Kai amma matar nan ta yi nisa wallahi! Tana alama tana da ƙaranci addini,domin mai ba za ta ɓata aikata abin da ta aikata ba saboda son zuciyarta!" cewar mijin Jamila cike da mamaki,bai taɓa tunanin rashin imanin Sahura ya kai har haka ba,duk yadda Jamila take misalta mishi halayyarta bai yi tunanin ta kai haka ba. Jamila tamkar an ƙara linka tsanar Sahura a cikin zuciyarta ne,ji take ina ma tana kusa da ita su goge raini,ta nuna mata Mairi na da 'yar'uwar da za ta tare mata faɗa da share hawayenta. Saɗiku ma ya yi matuƙar mamakin furucin Sahura duk da bai santa ba har zuwa yanzu,amma jin kalamanta ya tabbatar masa da bata da imani,take tausayin Dauda Imamu ya ɗarsu a zuciyarsa,ko ba a fada masa ba,ya san asiri ne ke ɗawainiya da shi. Dubu talatin ya ciro ya miƙa ma Jamila yana faɗin.
''Ga shi a ƙara kuɗin asibiti, kafin a sallameta in shaa Allah zan ƙaro wasu kuɗin. Allah ya bata lafiya ya sa kaffara ne. Ni zan koma kasuwa'' ya yi maganar yana nufar ƙofa. Matarsa ta mika ma Jamila ledar kayan marmarin da suka siya a hanya sannan suka bar ɗakin. Kawu da sauran mutanen Mada suka fara haramar tafiya duk da har yanzu bata tashi daga baccin ba,sai dai suna iya ganin tafiyar numfashinta da taimakon na'ura. Kuɗi mai yawa suka ba Jamila tare da alƙawarin dawowa nan da kwana biyu su sake dubata sannan idan akwai abin da suke buƙata na kuɗi za su iya sanar musu,godiya sosai Jamila ta musu sannan suka wuce. Ya rage daga Jamila sai yaran, HAFIZA na kusa da Jalil,shiru ɗakin ya ɗauka. Jamila can ta ce
''Yasir ya kamata ku je gida ku watsa ruwa ga key,idan ya so bayan kun dawo sai na je na yi mana girki'' ta yi maganar tana mika mishi key. Amsa ya yi ya miƙe sauran ma suka miƙe daga saman doguwar kujerar da suke zaune.
''Ammu Jamila bari na yi girkin ki huta abinki'' cewar Hamida. Ɗan murmushi Jamila ta yi sai ta ce
''To shikenan. Na ga shigowanku kenan garin akwai gajiya,amma tun da kina son yi babu matsala. HAFIZA '' ta kira sunanta. Ɗan dagowa HAFIZA ta yi ta furta ''Na'am Ammu''
''Ku je tare da Hamida ki nuna mata kayan abincinku,kin fi ni sanin komai na gidan''
''To '' ta faɗa tana miƙewa suka fita tare. Su biyu aka bari a ɗakin wanda zuwa lokacin an fara kiran sallar azahar. Miƙewa Jamila ta yi zuwa bayin ɗakin ta ɗauro alwala sannan ta kabbarta sallah...✍️
^^^^^^^^^^^^^^
Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya
Jin mutumin da ya kiran wayar ya katse kiran sai ta saki malalacin murmushi, ta san kalamanta sun shaƙar da shi sosai,mayar da wayar ta yi caji sannan ta dawo falon ta zauna kusa da Gwaggwon Bugaje. Ɗan kallonta Gwaggwon Bugaje ta yi sai ta ci gaba da kallon.
''Gwaggwo kin san wani rainin hankali da aka mini yanzu kuwa?" Sahura ta faɗa. Juyowa Gwaggwon Bugaje ta yi tana fuskantar ta ce
''Ina kuwa zan sani uwata,ɗanɗana mini a baki na ji garɗinsa''
''Hmmm wani ne ya kira baban Hamid wai ban san Mairi bata ta lafiya ba ne?"
''Ke kuma wace amsa kika ba shi''
Ɗan taɓe baki Sahura ta ɗan yi sannan ta ce
''Ce mai na yi na san da rashin lafiyarta,kuma na hana shi zuwa,ya yi duk abin da zai yi''
''Da kyau! Kin ba shi amsa daidai da tambayarsa. gobe ya...'' kasa ƙarasa maganar ta yi jin sautin waƙa Hamid na rerawa yana shigowa cikin tsakiyar falon.
''Personally! Persona! Personally! Ahhhh! Personally! Intentionally! I no go lie! The thing wey dey ma mind!..."
Shiru suka yi suna kallon yadda yake tiƙar rawa,Sahura sai murmusawa take tana ƙara alfahari da ɗanta,yayin da Gwaggwon Bugaje ta cika ta batse da fushi,saboda su a garinsu mai irin wannan kade-kaden ta waƙe-waƙen ɗan iska suka ɗaukeshi.
''Mene ne kake haka Hamid kamar kirista!" Gwaggwon Bugaje ta faɗa cike da jin haushi. Bata amsa ya yi da '' Bitar zazzafar waƙar da aka saki kwanan nan,gobe za mu yi gasar rawa a night club,duk wanda ya ci gasar za a bashi dubu hamshin''
Kafin Gwaggwon Bugaje ta ce wani abu Sahura ta rangaɗa guɗa har da girgiza kafaɗa saboda jin daɗi ta ce
''Da kyau Hamidina! Yaro ɗan ƙwalisa kai ne babbansu kuma autansu! Wannan gasa dole ka cita don kana kewaye da albarkata!har dubu hamshin! Kuɗi tsugugu haka!"
''Yeah momcy! " Ya yi maganar yana lankwasa hannu irin yadda macheal Jackson yake,shi ala dole ɗan rawa.
''Allah ya ƙaro dubban nasarori Hamidina ɗan albarka. Na san wata...''
''Kai amma Sahura baki da tunani da sanin ya kamata'' rai ɓace Gwaggwon Bugaje ta faɗa tana kallonta. Wangale baki Sahura ta yi tana mata kallon uku saura kwata ta ce
''Ban gane ban da lissafi da tunani ba gwaggwo?" Ta yi maganar cike da rashin kunya.
''Yanzu goyen bayan shirmen Hamid kike? Wannan ai rashin kunya ne! 'yan iska suke irin waɗannan waƙoƙin musamman masu shaye-shaye''
Tsam! Sahura ta miƙe tana mata wani irin ƙasƙantaccen kallo ta ce
''Bakinki sai dai ya sari ɗanyen kashi Gwaggwo! Ni za ki kalla ki ce ɗana yana da jiɓi da kalar masu shaye-shaye. Ba zan ga wannan ba in shaa maka Allahu!''
''Allah ya huci zuciyarki Uwata'' ta faɗa cike da sanyin murya.
''Ya wuce.'' Sahura ta faɗa tana sassauta muryarta.
''Momcy! granny bata waye ba ne shi ya sa ta faɗi haka'' ya faɗa cikin rawa. Ɗan murmushi Sahura ta yi sannan ta ce
''Manta da ita sharrin tsufa ne''
Harar wasa Gwaggwon Bugaje ta mata tana murmushi. Fita Hamid ya yi bayan ya maƙala air phone a kunnansa,mayar da hankalinsu suka yi ga TVn. Yaran duk sun tafi makaranta,Aunty Saudah da Ɗayyaba sun tafi kasuwa cefane...✍️
^^^^^^^^^^^^^^^^
Yariman Bakura specialist hospital
Ƙarfe 8:12pm na dare
A Hankali ta fara buɗe idanunta da suka mata nauyi,tun tana ganin ɗakin dishi-dishi har idanunta suka buɗe tsaf! Mamaki ya cikata tsintar kanta cikin wani ɗaki da bata san ina ba ne. Wani abu ta ji ya rufe hancinta da bakinta,ta yunkura za ta tashi muryar HAFIZA ta sauka a kofofin kunnuwanta.
''Laaah! Ammuna kin tashi! Ya jiki?" Ta yi maganar tana zuwa inda take tare ta kama hannun da ba a saka drip ba,jinjina mata kai ta yi tana lumshe ido. Kafin ƙyatawa da bismillah sauran 'yan ɗakin suka ma gadon rumfa,amon muryoyinsu na sauka a masarrafar jinta,yayin da idanuwanta suka mata tozali da su. Sanyi ta ji a ranta ganin ahalinta na kewa da ita,sai dai har yanzu akwai giɓi ɗaya a cikin zuciyarta. Kullum da tunaninsa take kwana kuma take tashi, kunnuwanta suna kwaɗayin sake jin muryarsa, idanuwanta na mararinsa tozali da shi,haka gangar jikinta na kewar duminsa. Wai yaushe za ta yi arba da sanyin idaniyar ne? Bata burin da ya wuce ta ga mijinta,uban 'ya'yanta koda kuwa zai zo mata a kumurcin zakin da zai iya illatata. Ta lula duniyar tunani wata nurse ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Bayan ta gaishe da Jamila ta duba drip ɗin sannan ta cire mata oxygen ta ajiye gefe sa'ilin nan ta bar ɗakin. Duk da an cire mata abun shakar lumfashin amma har yanzu bakinta na mata ɗan nauyi. Momy ta kira wayar Jalil sun gaisa da Jamila,haka Maman Jawaheer ta kira Yasir sun gaisata Jamila tare da tambayar mai jiki. Sun dan jima a ɗakin daga bisani mazan suka wuce can gida aka bar Jamila da su HAFIZA. Nurses sun so hana kwanansu Hamida a ɗakin, da ƙyar Jamila ta shawo kansu suka yarda. Hamida da HAFIZA suka kwanta a gado dayan da yake ɗakin,Jamila ta kwanta da doguwar kujerar ɗakin.
^^^^^^^^^^^^^^
Bayan kwana biyu
Jikin Mairi ya yi sauƙi ba kamar ranar farko ba,tana magana amma ba mai tsayi ba,abinci ma tana ci shi amma kaɗan. Ɗakin bai rabo da masu dubiya musamman 'yan'uwansu na Mada, Kawu ya sake dawowa dubata, kishiyar Jamila da mijinta tare da wasu maƙotanta sun zo duba Mairi. Suna samun alkhairai sosai wurin masu dubiyan. Officer Kabir ma ya kira sun gaisa da Mairi,Momy da maman Jawaheer suna ƙokarin kira. Dauda Imamu ne shiru har yanzu bai kira ba,balle suka uwar gayya Sahura. Zaune HAFIZA take a saman gadon Mairi tana bata labarin da malaminsu kwanaki ya ba su a islamiyya, cikin natsuwa ba tare da hargowa ba take bata labarin, murmushi mai bar fuskar Mairi ba har ta kammala labarin. A can ƙasan maƙoshinta ta ce
''Allah ya albarkaci rayuwarki HAFIZA da sauran 'yan'uwanki''
''Ameen Ammuna'' ta faɗa cike da murna. Jamila da Hamida dake gefansu suka murmusa.
''Ammu ni ma zan baki labarin makarantarmu''
''Ina sauraro Hamida'' ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi. Hamida ta gyara zama za ta fara magana su Muhsin suka shigo ɗakin laɓbansu ɗauke da sallama sun dawo daga sallar magrib. A tare suka amsa har da Mairi, murmushi ya kasa ɓoyuwa a fuskarta.
''Ammu wannan murmushi haka '' Jalil ya faɗa yana ƙarasowa inda take.
''Ai tun ɗazu Yaya take murmushi'' cewsr Jamila.
''Allah Sarki Ammuna kinata samun sauƙi'' cewar Yasir yana matsowa kusa da su. Muhsin da ke gefen Hamida ya ce
''Ya jiki Ammu''
''Jiki ya warware. Alhamdulillah'' ta faɗa tana bin shi da murmushi. Ɗan gyara mata kwanciya Jamila ta yi ta bata abinci,cokali huɗu ta ma tuwan ta sha ruwa. Duban Jalil ta yi ta ce
''Jalil kira mini Abbanku na ji muryarsa koda zai zama na ƙarshe ne a rayuwata...''
''Haba yaya wace kalar mummunan fata kike ma kanki! Don Allah ki bar wannan maganar! Kina saka zuciyata tsinkewa''
''Ni ma dai Ammu" cewar Jalil
Murmushi Mairi ta yi har haƙoranta na bayyana. A hankali ta ce
''Yanzu laifi ne don na ce a kira mini Abbansu mu gaisa!"
''Jalil kira shi Don Allah '' Jamila ta faɗa tana sake bin yayarta da kallon tausayi. Ringing take amma har ta katse ba a ɗaga ba. Sake kiran wayan ya yi har ta kusa yankewa aka ɗaga.
A can barikin Dauda Imamu na kusa da Sahura ne ya sa bai ɗauki kiran tun farko ba,da aka sake kira na biyu ya miƙe har zai fita Sahura ta dawo dashi tare da ba shi umarnin ya ɗauki kiran sannan ya saka a hand free ta ji. Jikinsa na rawa ya ɗaga kiran tare da sakawa a hand free ya yi sallama.
A hands free Jalil ya saka wayar sannan ya matsa kusa da Mairi.
''Assalamu Alaikum Abba ''
A can Dauda Imamu da jikinsa ke tsuma ya amsa da ''Wa Alaikumussalam Jalil. Ya mai jikin''
''Da sauƙi sosai Abba. Daman tana son ku gaisa ne''
A can Dauda Imamu ya ce
''To bata mu....'' Caraf Sahura ta karɓe wayan ta karata a kunne.
''Ba za su gaisa ba! Na san kina jina Mairi! Ya kika ga salon! Ba na faɗa miki karan batta da ni babu daɗi ba! Ni da kaina na hana shi zuwa kuma na hana shi kiranki! Idan kin tashi ki haɗiyi zuciya amma keda ganin Dauda Imamu sai a lahira,a lahirar ma ina gefansa..."
''Ke Sahura! Ya isheki haka! Wai ke wace kalar ƙidahur jahilar mata ce mara hankali da tunani kamar ana kaɗaki da ruwan hanji!'' Jamila ta faɗa a tsawace bayan ta amshe wayar daga hannun Jalil. Kalaman Sahura sun daki zuciyar Mairi sosai,nan da nan hawaye suka shiga gangaro mata a bisa kunci, HAFIZA da ke gefen ta saka hannu ta share mata,ita ma hawayen take. Hamida,Yasir da Muhsin kalaman Sahura sun saka su kuka musamman Hamida da take da saurin kuka. Jalil idanunsa ne suka kaɗa zuwa ja,ƙamas suke babu alamun kuma amma zuciyarsa na tafarfasa da ƙara jin zafin Sahura. A gefe guda ran Sahura ya yi matukar ɓaci da jin kalaman Jamila,nan suka shiga afkawa junansu zagi ta uwa ta uba. Mairi ta kunnuwanta suka gashi ta jin kalaman ta rushe da matsanancin kuka.
''Don Allah Jamila ki kyaleta! Ta shanye shi idan ruwa ne! Na mene ne wannan jarabar haka! Ta je da shi na bar mata har abada! Ai Allah ba azzalumin bawansa ba ne! Wallahi wallahi wallah ba zan taɓa yafe miki ba Sahura! Sai kin yi nadamar cutar da ni,yarana da mijina da kika yi! Allah sai ya saka mun! Ki jira karshenki! Allah ya isa!"
A can Sahura ta kwashe da dariyar ƙeta,Dauda Imamu na gefe yana hawayen baƙinciki,yarasa wace kalar ƙaddara ce haka, wannan ce daman ƙaddararsa! Rabon da ya yi kuka har ya manta,amma yau yana ji yana gani an katange shi da abar ƙaunarsa,wacce bayan iyayensa bai da tamkarta. Muryar Sahura ta farautoshi daga duniyar tunani.
''Ai na sha tabara na sha yasin Mairi! Ko Allah ya isa biliyan gashin tunkiya za ki mini ba zai dameni domin na yi nasara gwaggwaba a kanki.''
Mairi da har yanzu kukan take ta ce
''Allah na nan! Na barki da mai Sama Sahura! Na barki da.....'' wani irin tari mai ƙarfi ya sarketa. Babu shiri Jamila ta yi wurgi da wayar tana matsowa kusa da ita a rikice.
''Yaya sannu! Don Allah karki tafi ki barmu!" Take ta fashe da matsanancin kuka tana jijjigata. Aman jini Mairi ta fara guda-guda wanda hakan ya ƙara gigita su,har Jalil da ke da dakakkiyar zuciya ya fashe da matsanancin kuka. Kuka HAFIZA take kamar karanta zai fita tana goge jinin da ke zuba a jikin Mairi da hannunta. Sai fadi take ''Shifakillah ya Ammuna! Ammu kar ki mutu ki bar ni! Zan bi ki Ammu! Ammu idan na girma zan gina asibiti na kaiki na yi miki magani ciki! Ammu muna ƙaunarki! Ammuuuu'' a rikice take kiran sunanta saboda yadda take aman tana kakari,idanunta duk sun firfito. Muhsin ne ya yi saurin barin ɗakin da gudu ya je kiran Doctor. Da ƙarfi Mairi ta tamƙi hannun Yasir, Jalil da Hamida suka riƙe hannun da ta riƙe Yasir,ɗaya hannun ta riƙo hannun Jamila,da ƙyar take iya magana wanda kaɗan yake fita.
''Jamila ga! Ga! Yaranaaa! Na yafema Da! Dau! Dauda! Duniya da lahira! Ki riƙe mini suuu!"
Cikin kuka Jamila ta ce
''Yaya don Allah ki bar faɗin mutuwa! Za ki tashi da yardar Allah! In dai Sahura ce sai na yi miki maganinta da hannuna! Sai na illata rayuwarta da duk wani makusancinta! Ke kadai kika rage mini a faɗin duniyar nan"
Murmushi mai ciwo Mairi ta yi numfashinta na fita da ƙyar ta ce
''Barta da da..... dduniya...La'ilahaaaa haaaaa!! Ilallahhhh! Mu! Muhammadu.......'' Ɗif ta yi kamar daukewar ruwan sama,daidai Muhsin na shigows tare da likita da nurses uku. Cak! Jamila ta tsaya, taƙi sakin hannuwanta har likitan ya ƙaraso wurin. Dakyar aka ɓanbareta daga rikon da ta yi musu. Take Jamila ta saki gigitacciyar ƙara tana zubewa a a ƙasa warwas!. Wani sabon kuka ya cika ɗakin jin likita na sanar da mutuwarta. Duk yadda suka so cire HAFIZA daga rungumar da ta ma Mairi nurses ɗin suka kasa,kuka take tamkar ranta zai fita,sai ambaton sunan Ammu take a gigice kamar zautatta,Yasir bajewa a ƙasa ya yi yana gurshiƙeƙen kuka tamkar yaron goye. Jalil ne mai dan karfin hali a cikinsu. Addu'o'in neman dacewa ya shiga kwarara mata yana kuka. Nurses biyu suka taimaka aka kwantar da Jamila a saman dayan gadon tare da bata taimakon gaggawa. Da kyar likitar ya fitar da su HAFIZA daga ɗakin. Bayan an lulluɓe Mairi da farin yadi. A daren su Jalil suka kira duk wanda yake da alhakin sanin mutuwarta. Koda Yasir ya gwada kiran Abbansu ya ji wayar a kashe. A daren mijin Jamila,kishiyarta,Kawu Rabi'u, Mamman da uwar gidan Kawu Rabi'u suka zo asibitin. Sun yi kuka sosai, kowa sai faɗin kyawawan halayanta yake,hakurinta,tausayinta da kawaicinta wanda samun tamkarta sai an tona.
Washegari aka ba su gawarta suka zo unguwarsu aka sallaceta,a nan ma Kawu Rabi'u kafin a wuce da ita ya sake kiransa. Sahura ce ta ɗaga kiran,bai jira cewarta ba ya sanar mata da rasuwar Mairi sannan ya katse kiran. Mairi ta samu rakiyar mutane masu ɗumbin yawa wanda wasu ba ba a sansu ba,kowa sai shaidar arziki yake mata da yi mata fatan dacewa in shaa Allah. Bayan an kaita sai aka zauna amsar gaisuwa. A cikin gida 'yan'uwa da Abokan arziki suna zaune ana alhini. Jamila tun da ta farfaɗo ba um ba um-um sai kallon jama'a. A ranar Momy,Raihana,Maman Jawaheer da Jawaheer suka iso Zamfara. Aka ci gaba da zaman makokin da su.
^^^^^^^^^^^^^^^
Washegari
Ƙarfe 1:50pm na rana
A daidai wannan lokacin Sahura ta saka ƙarfarta a cikin gidan,makota a gefe zaune a saman tabarma. Sanye take cikin doguwar riga ta yafa gyala kamar ba matar malam ba, Gwaggwon Bugaje,Ɗayyaba,da yaranyta suna bayanta, Hamid da Dauda Imamu sun tsaya a wajen amsar gaisuwa a waje. HAFIZA ta fito kenan daga ɗaki za ta je ɗauro alwala kamar ance ta kalli ƙofar waje, idanunta suka sarƙafe da na Sahura. Rassss! Ƙirjin Sahura ya yi mugun bugawa. Take ta ji idanunta sun ɗau raɗaɗi da zugi kamar an watsa musu barkono,haka bakinta ta ji kamar ana cizge hakoranta da ƙarfi da yaji. Wani irin abu ta ji mai matuƙar ƙarfi ya fita daga bakinta,duhu ya mamaye ganinta,kamar walƙiya ta ji abubuwa sun fita daga idanuwanta. Sai kuma ta ji ta koma normal kamar babu abin da ya sameta. HAFIZAN dai ta sake arba da ita ta kafeta da manyan idanunta kamar na uwarta. Duk yadda take ganin kyawun Nu'aymah,sai ta ga ai wannan sha kundum ce a komai. Take wata zazzafar tsanarta ta kewaye lungu da saƙon zuciyarta. ''Da alama wannan ce HAFIZA d" ta furta a ranta tana ƙarasowa cikin gidan. A gefan HAFIZA kallon tsana take wurga ma matar haka kurum duk da bata san wacece ita ba,duba da yadda ta yi shigar ya baƙanta ranta,ta zo gidan rasuwa da gyale. Siririn tsaki ta za sannan ta wuce bayi.
Mutanen tsakar gida suka gaisa sannan suka ƙarasa ciki. Cike da iyayi ta yi sallama tana shigowa cikin ɗakin su Gwaggwon Bugaje na biye da ita. Saman kujera ta zauna tare da Gwaggwon Bugaje,yaran da Ɗayyaba suka fito waje saboda ɗakin ya yi kaɗan. Tun da Sahua ta shigo ɗakin Jamila ta kafeta da mayatattun idanuwanta da suka kumbura tare da sauya kala zuwa ja kamar jan gauta. Take wata zazzafar ƙiyayyarta ta taso mata tun daga ƙasan zuciyarta. Tsam! Ta miƙe ba tare da ta ce da kowa komai ta wuce uwar ɗaka. Bata daɗe ba ta fito sanye cikin riga da wando,sosai kowa ya yi mamakinta don tun lokacin da aka yi mutuwar da hijabi take zaune. Sahura sai ciccin magani take tana harare-harare. Kai tsaye Jamila ta nufi ƙofar falon ta saka makulli ta rufe ɗakin tare da saka key ɗin a aljihun wandonta.
''Jamila lafiyanki kuwa'' Uwar gidan Kawu Rabi'u ta faɗa cike da mamaki. Duban Sahura Jamila ta yi da fuskarta ta nuna alamun tsorata ta ce
''Yau kin shigo hannun zakanyyar da ta shekara goma tana farautar namun daji amma ta gaza samu sai a yau! Kin tafka babban kuskuren shiga gonar Jamila! Yau baki da mai ceton ki Sahura''
Wani irin kukan kura...✍️
Tsokaci
Kamar yadda na sanar muku a farko,hybrid fiction ne,ma'ana akwai real life story da ƙirƙira. Ɓangaren Sahura ya faru a duniyarmu ta zahiri,sannan ita wacce take da kishiyar ta jima da rasuwa,ita muguwar kishiyar yanzu take girbar abin da ta shuka. Sannan akwai babban al'amari da zai afku bayan rasuwar Mairi,wanda idan tana raye ba zai faru ba. Ku biyoni a sannu,i assure you ba za ku yi da na sanin karanta labarin nan ba. Yanzu tauraruwarmu HAFIZA za ta shigo cikin labarin ka'in da na'in. Stay tuned with the Amazing pen✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen
***