KOMAI YAYI FARKO...

1

by @rahmakabir13

*KOMAI YAYI FARKO...*
Book 1.

Na

©®Rahma Kabir MrsMG.

Page 1.

Sarac Stars R Pen...✍️

*Labari ne da wani ɓangare ya faru da gaske, wani sashi kuma na kirkireshi da kaina dan ƙawata labarin, dan haka sai da na samu sahalewar rubuta shi daga mai labarin kafin na fara, wataƙila yayi iri ɗaya da labarinki ko wata 'yar uwarki to arashi ne, fatana in isar da saƙo da faɗakarwa a cikin nishaɗi.*

*Gargaɗi*
_Ban yarda a juya mini labari ba ko ayi afmani da wani ɓangare na labarin, ko a ɗaura min shi a wata kafa ta media ba tare da izini na ba, sannan ina gargaɗi ga masu cire sunana a cikin labarina su saka nasu tare da sakinsa a shafinsu, a bar mini sunana tare da barin rubutuna a yadda yake, da fatan za a kiyaye_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM* 

*****

FARIDA.

Aure mai saka natsuwa da farin ciki ya kuma danƙa kambun 'yanci ga duk wata 'ya mace a hannunta wacce ta samu kanta a ɗakin mijinta. Kamar dai ni Farida dana samu wannan matsayin na zama cikakkiyar matar aure mai tsumayen zama uwa tagari. Tsaye nake a falona ina ƙare masa kallo duba da irin tarin dukiyar da aka narka mini, Umar ya kama mana ɗaki ciki da falo manya da bayi a uwar ɗaka sai kitchen a falo, ko'ina cike yake da kaya kasantuwar ni ce 'ya ta fari a gurin iyayena kuma mahaifina yana da rufin asiri dai-dai gwargwado dan za a iya saka shi a jerin masu wadata a cikin unguwarmu, an nuna mini gata domin duk wanda yayi ƙatari da kayan da aka yi mini a ɗakina sai ya tabbatar da an narka dukiya, saboda komai da ake buƙata na jin daɗin rayuwa an siya an saka. Fannin katako ma Italian bed aka siya mini wanda a lokacin shi ake yayi kuma sai gidan wane da wane, ga wardrobe babba mai ƙofa huɗu, sai kuma kujeru royal manya waɗanda suka ji form sosai, zannuwan gadona ma a ciki akwai ɗan Saudi da mamanmu ta saka aka kawo mata da kuma wani daga Dubai. Ɓangaren kitchen kuwa nan ne aka ƙare bajinta domin standing gas aka siya mini, ga water heater wanda sai ɗai-ɗaikun amare ne suke samunsa, rice cooker, kuloli set biyar, kofunan tangaran na gayu da plates masu matukar tsada, ga oven da sauran kayan amfani kala-kala, sannan gudunmawar da aka bawa Mamanmu na kaya sai da aka tattara su gabaɗaya aka kawo mini saboda kawai ɗan mai kuɗi na aura, kuma gashi dama Umar ya zuba mini kayan akwati masu kyau da tsada sosai, ga su da yawa dan akwati set ne yayi sai da aka cika su taf har da extra ɗin wata jaka da aka zuba wasu kayan a ciki, shiyasa ma iyayena suka zage damtse wajen nuna nasu bajintar dan fitar da ni kunya, aka yi mini gyaran abinci mai yawa, haka suma dangin ango an kai musu gyarar da ake kaiwa gidan iyayen miji na al'ada. 

Fannin gyaran jiki kuwa gurin Mami 'yar Shuwa naje ta yi mini, saboda Mamanmu musamman ta bayar da kuɗi domin wannan, ga maganin mata da ta haɗa mini nasha kala-kala har sai da na shiga tsoron kar su yi mini yawa su min illa. A lokacin bikin kuma, Mami yar Shuwa ita ce ta yi mini lalle da gyaran kai da kitso na fito fes ina sheƙin amarci kuma da yake ni fara ce sosai ga tsayi ba ni da ƙiba ga kuma ƙarancin shekaru, shiyasa kyauna ya ƙara fitowa sosai, sannan Alhamdulillah duk da rashin jikina Allah ya wadata ni da dukiyar Fulani wanda yana ɗaya daga cikin abunda yaja hankalin Umar ya ƙosa ayi aurenmu, dan tunda aka tsaida rana yake yi mini wasu maganganu da suke saka ni jin kunyarsa har nake ganin kamar ko Jikina yake so ganin ya kasa danne maitarsa, wani lokacin in muna waya da ya fara sakin layi nake kashewa da sauri ina jin zuciya ta tana tsinkewa da baƙon yanayi, duk abunda ban sani ba dangane da soyayya ko na aure to Umar shi ne ya fara fayyace mini sirrin komai, shiyasa zuciyata ta shiga kokwanto ko so da Manufa yake yi mini tare da fargabar zuwan ranar da zan kasance a gidansa. 

Na sauke gwauron numfashi akan tunawa da na yi da wani bigire na kafin aurenmu. Haka na gama duba ɗakin lungu da saƙo ina jinjina kai wai komai na ciki mallakina ne, hatta toilet sai da na duba shi da aka ƙawata shi da mirrow wanda jikinsa akwai wajen aje sabulu da brush da mayukan wanke gashi, ga bangon yaji tiles tun daga sama har ƙasa mai kalar fari, shiyasa yake da haske mai ɗaukar ido kamar haƙori, kuma da yake ni ɗin uwar tsafta ce shiyasa tsawon mako biyu da muka yi a gidan yana nan kamar yadda muka same shi, dan kullum sai na wanke shi. Dana gama da toilet ɗin na rufo ƙofar ina sakin guntun murmushi duk da zuciyata a takure take domin duk wannan tarin gata da aka yi mini sam auren bai dame ni ba, hasalima bana jin farin ciki ko murnar kasancewata a cikin gidan, saboda tunda biki ya ƙarato babu kyakkyawar jituwa a tsakanina da Umar, bama waya sosai shiyasa bana jin irin ɗokin nan na 'yan mata da suke yi in zasu yi aure su ji sun ƙosa a kaisu, dalilin da yasa ko gayyata banyi sosai ba dan Umar ya dakusar min farin ciki da ɗokin auren. Saboda A ranar ɗaurin aurenmu ma ban ga ango ba, dan bai bai samu zuwa gidanmu ba, irin hotunan nan da ake yi na tahiri ango ya zo da abokai ayi mana to ban samu wannan ba, kuma abun mamaki anan kusa da gidanmu aka ɗaura aurenmu a wani masallacin juma'a, sai wani sashi na zuciya ta ya shiga gaya mini ko wani uzuri ne ya riƙe shi da ya sa bai zo ba, amma kuma ga yadda na sani ga sabbin ango suna ɗokin ganin amarya dan haka suke aje duk uzurinsu su zo dan ganin juna, shiyasa har cikin raina ban ji daɗin abunda Umar yayi mini ba, amma dole na kawar da damuwar kar mutane su fahimci halin dana ke ciki, haka nasha hotuna da ƙawaye da 'yan uwana. Zuwa dare kuma 'yan ɗaukar amarya suka zo tare da abincin biko mai yawa, abu dai na girma da arziki, ko motocin da suka kawo na ɗaukar amarya a tarihin unguwarmu tunda ake bukukuwa ba a taɓa kawo matoci masu yawan na bikina ba, saboda akwai waɗanda suka tafi empty saboda an gama kwashe mutane masu zuwa, komai dai dangin ango da abokansa sun suna babu ƙaranta a ciki.

Wayata ce da tayi ƙara yasa na fito falo da sauri na duba, sai naga saƙon MTN ne da suka saba yiwa mutane, na zauna a Cushing ina lumshe ido da tuno irin azabar da Umar ya bani a darenmu na farko, domin a ranar da aka kawo ni a daren ango ya yi buɗar kai, kuma a wannan ranar ban tsallake ba sai da ya sha mai na, kuma Alhamdulillahi ya sameni a cikakkiyar budurwa duk da ba wata soyayya daya gudanar dan ƙara armashin abun, babu tura ɗan saƙo ko ɗan aike kamar yadda malamai suke magana akai, haka ya haiƙe mini ya biya buƙatarsa dan gusar da ƙishin ruwan daya jima yana dakonsa tun tasowar samartakansa, kuma haka ya cigaba da biya mini wannan Karatun ba tare da nuna kulawarsa akan ina samun gamsuwa ko akasinsa ba, shi dai ya sauke nashi buƙatar, wanda hakan ya saka mini tsoro da tunanin auren ma ba daɗi gare shi ba da nake ganin wasu matan suna ɗokinsa da surutun kullun mijinsu kaza-kaza, ko da yake ina da labarin an ce jin daɗin abun sai mace ta haihu tukuna, wata ma sai tayi haihuwa biyu zuwa uku, shiyasa na ke ganin kamar na yanke hukunci cikin sauri, amma bari naga zuwan lokacin da zan haihu ƙila zan tantance bambancin, sai dai nan take naji sarewa da jin karaya a zuciyata akan zan jure har zuwa lokacin kuwa.? domin ni azaba nake sha ba kuma ya sarara mini dan sai yaje mini sau biyu ko sau uku a dare, wani lokacin har kuka nake yi ina matsar kwallar wahala, idan komai ya lafa ne nake gasa jikina a ruwan ɗumi kafin na samu natsuwa. Gashi har yau sati biyu da kwana biyu da aka yi bikinmu lamarin bai sauya zani ba, Umar sai sake ɗaurani yake yi akan sabbin halayyarsa da ban sani ba, dan shi kaɗai yaci amarcinsa dan ni azaba ya gana mini a wannan kwanakin, sai da ya tabbatar da ya mayar da ni cikkikiyar mace na shiga sahun manya. Babban sauƙin dana samu shi ne daya fara fita aiki, duk da ba ni da masaniyar haƙiƙanin aikinsa amma dai ya sanar da babanmu aiki yake yi a wani asibiti sannan bai gama ƙarƙare karatunsa na Dgree a nan KASU ba. Gashi yau haka yayi mini sallama ya fita ba tare da ya bani kuɗin cefane ba, domin akwai abinci da komai amma babu kayan miyan da zan sarrafa hatsin, ko karyawa bai yi ba haka nima ban karya ba ga ba kuɗi a hannuna kuma babu kayan tea domin wanda ya siya sun ƙare, shiyasa na soma tunanin me zan dafa naci.? Tun ba aje ko ina ba na soma ganin tafiyar namu da gargada. Bazan manta ba a kwana biyu da aurensu ya amshe mini wayata Android Infinix hot 8 duk da shi ne ya siya mini lokacin ina gidanmu kuma sabuwa ce a kwalinta ya bani bata jima sosai bama, sai ya ce mini zai yi amfani da ita dan yanzu ba shi da waya, ya bani ƙaramar Tecno mai Torchlight an naɗeta da robali na saka Sim ɗina, a lokacin ban damu ba dan dama shi ne ya bani wayar, kuma dan ya amsa ba wani abu bane, sannan nasan duk bayan biki akwai rashin kuɗi da yake samun ango saboda ya gama ƙarar da kuɗinsa kan shagalin biki, nasan zai bani wata wayar nan gaba in ya samu buɗi. Duk da da farko abun yaso ya bani mamaki dan nasan mahaifinsa yana da kuɗi ban yi zaton haka daga Umar ba, sai dai wani ɓangare na zuciyata ya bani amsa akan duk kuɗin babansu ba zai sa ya ɗauki ɗawainiyarmu ba dan shima yana da hidimar sauran yaransa balle shi Umar da aka yi masa auren gata, tamkar ya sallame shi ne ya bashi damar jan ragamar rayuwarsa. Babansu babba ne a gommati dan ya riƙe muƙamin special Adviser na gomnan da ya sauka, kuma a yanzu lecturer ne a nan KASU, shiyasa a gidansa ake cima mai kyau, dan ko tuwo za a dafa to miyar da kaza a ciki, domin ranar dana fara zuwa gidansu da ya kai ni da yamma irin wannan dabgen naci, shiyasa na soma tunanin irin rayuwar gidansu zan samu a gidan Umar, sai dai da alama tafiyarmu da bambanci, dan ba a yi nisa ba na fara banbance tsanani aya da tsakuwa. To na rame nayi haske ko cikar ɗaki da amare ke yi ban yi ba, sai ma rama dana ƙara yi sosai saboda yawan buƙatarsa da yake zuwa mini da shi, ga jikina bana samun wadattacen kayan marmari ko abinci mai gida jiki da zai ƙara mini kuzari, rabona da kaza ko nama tun daren aurenmu na farko, ga rashin wadataccen bacci da daddare, kuma idan gari ya waye bana samun yin baccin saboda baƙi da suke zuwa, shiyasa na fige na ƙara ƙanƙancewa, dama ba shekaru ne sani ba dan ban wuce shekara sha takwas ba, shekara ɗaya kenan da na kammala secondary na fara zuwa NCE dake nan makarantar sakandire dake unguwar gomna road, kuma cikin Ikon Allah ba jimawa da fara karatun na samu wata makaranta private nan kusa da unguwarmu tudun Wada na soma zuwa ina koyarwa, suna biyana dubu takwas duk wata, kuma da albashina mamanmu ta shiga a dashe dubu biyar duk wata, dubu ukun kuma ina riƙewa saboda transport da kuma ɗan siyan katin waya, wani lokacin ma ban fiye kashe kuɗin ba saboda ban saba ba dan ba ni da wayewa da ilimin zamantakewar rayuwa ko sanin wasu abubuwa da zan gyara kaina, dan babu shaƙuwa sosai a tsakanin da Mamanmu, bata zama dani ta nuna mini abubuwan da zan samu na waye da sanin rayuwa, Shiyasa ko a ranar da za a kawo ni gidan Umar ko irin faɗan nan da iyaye ke yiwa 'yarsu in za ta tafi gidan miji iyayena basu yi mini ba, basu yi mini nasiha ba, babansu ma tun bayan ɗaurin aure ban sake saka shi a idona ba har aka kai ni gidan mijina, haka itama mamansu koda innarta ta kai ni gabanta akan tayi mini faɗa, sai cewa tayi ita me zata ce.? Kawai su wuce da ni, sai ta bimu da addu'ar zaman lafiya, ƙarshe sai dai 'yan uwa babanmu ne da suka zo daga ƙauye suka yi mini nasiha kafin aka wuce da ni. Dan haka ko da Umar ya fara yi mini bitar kalmar haƙuri, kamar yadda iyaye suke faɗa zaman aure haƙuri ne, yasa na ƙara shiga natsuwata dan na karanci asalin halinsa akan yadda zan ci maganin zama da shi, to ga shi ba a je ko ina ba ya fara nuna mini rashin kulawa, baya ririta ni irin yadda sabbin angwaye ke yiwa Amarensu kamar dai yadda muka saba gani a zahiri ko a film da labaren hikaya, babu wata doguwar hira a tsakaninmu dan in ya fita tun safe baya dawowa sai dare, kuma da ya dawo abinci zai ci sai kuma maganar a kwanta bacci ya tara mini gajiya.

Hmmmm Hawayen daya cika mini ido shi ne yasa na gimtse wannan tunanin na shanye su basu zubo ba dan yayi wuri ace na fara zubar masa da hawaye, bana son yawan tunanin amma da alama ya fara zame mini jiki duba da ba ni da abokin hira, ba babbar wayar da zan hau social media na rage lokaci, sai dai na fita ƙofar ɗaki na zauna nasha iska, domin wayata ma da kanta ɗaukewa take yi saboda tsabar tasha hannu da yawa, dan wani lokacin sai na dauƙo zan duba ko an kirani sai na ganta a kashe, da farko na ɗauka matsalar chargy ne amma sai daga bisani na gane wayar ce ke da matsala, haka dai na ke haƙuri da riƙe ta ina maneji har zuwa lokacin da Umar zai sauya mini wata.

*****

Washe gari Ranar Monday. Da sassafe na gama shirina tsaf dan zuwa makarantar da nake koyarwa na boko, da yake mun yi yarjejeniya da Umar zan cigaba da zuwa makaranta da aikina, kuma duk ya amince mini. Dama makarantar sun bani hutun sati uku ne, sati ɗaya kafin aurena sai sati biyu bayan aure, dan haka yau Monday ya kama ranar da zan koma bakin aiki, na karya da sauran shinkafar dana dafa jiya mai da yaji na haɗa da ruwan lipton da sugar, sai na zauna zaman jiran Umar ya dawo saboda ya fita kuma yace na jira shi. Shiyasa yana shigowa na miƙe na gama haɗa duk abun buƙatata a cikin jaka, na dauƙo wayata kenan, sai na duba ko na samu miscall amma abun mamaki sai na ga wayar kamar ba Simcard babu wannan sandar service ɗin, Sai nake ce masa.

Laaa kaga wayata kamar babu Sim, ko network ne matsalar ban gane ba.

OK ai ni ne na cire Sim ɗin.

Ya ƙare maganar cikin gimtse fuska, na kwaɓe fuska malamar zanyi kuka.

Ayya Faruk ban san zaka cire ba ai da ka faɗa mini na yi copying number ɗin mutane na masu muhimmanci a takarda, dan bana so na rasa numbobin ƙawayena.

Na ƙare maganar ina dubansa cikin rashin jin daɗi, sai ya sauke numfashi yace cikin ɗaure fuska .

Ai jiya da daddare bayan kinyi bacci wani ya kira ki, bama mutum ɗaya ba samari sun kai su uku, kuma idan kika ji irin kalaman da suke faɗa na soyayya abun sai ya baki mamaki. Amm Farida dama baki faɗa musu zaki yi aure ba?

Haba Umar wani irin magana ne kake yi haka.? idan wasa kake yi mini ka dai na.

Na ƙare maganar ina ɗan turo baki alamar na ji haushi, dan gaskiya ba ƙaramin ɗaure mini kai yayi ba da mamakin maganar.

*Tafiyar yanzu muka fara, zamu ji wani irin rayuwar aure ke gudana a tsakanin Farida da Umar, karku manta labarin gaske ne*