BAHAGON TUNANI BOOK 1,2&3

Chapter 40

by @narrnarhhbukar00

The Amazing Pen ✍️.......

BAHAGON TUNANI

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم

040

Kallon ƙasa da sama maman 'yar gayu ta ma Jamila sannan ta ce

''Ina abun yake a nan! A ɗaura kashi ko a ɓata igiya! Ni ban ga abin kai kasuwa a nan ba! Yau za ki gane shayi ruwa ne! Za ki tabbatar da kin shigo bariki, domin dambe a wurinmu ba komai ba ne!"

Ɗankwalin kanta ta ciree ta yi ɗaurin ƙugu. Dariya ma abin ya ba Jamila,kalmashe hannu ta yi tana mata kallon mahaukaciya.

"Wai ke baiwar Allah ki fito fili ki bayyana me ke tafe da ke! Har yanzu ban fahimci yaranki ba''

''Au ma baki fahimci yarena ba! To bari ki gani a aikace''

Ta daka uban tsalle za ta cacimi wuyan Jamila,sai dai kash! Ta makara, kafin hannunta ya sauka a kafadun Jamila ta mata kamun kazar kuku,duk yadda ta so ƙwace hannunta ta kasa. Ram! Jamila ta matsesu tana murɗa jijiyan hannunta,take Maman 'yar gayu ta saki ƙara tana faɗin

''Shegiya sake mini hannu... Wayyo Allah!" Ta furta da iya ƙarfinta saboda yadda ta ji Jamila ta murɗe mata hannu ɗaya kuma taƙi saki. Ji take kamar hannun zai ɓalle.

''Wayyo Allah! Ki sake mini hannu!''

''Ba kin ce za ki nuna mini halin bariki ba! To bismillah! Hala ƙawar taki bata sanar miki wace ce ni ba'' ta yi maganar tana sake murɗa hannun da iya ƙarfinta,ji kake ya ba da sautin ƙas! Razananniyar ƙasa ta saki tana kiran Sahura ta kawo mata ɗauki. Sahura da ke leƙensu ta windon falon ita da Ɗayyaba ta ce

''Ai na faɗa miki maman 'yar gayu, karki ja ta da faɗa ta miki lahani irin nawa"

''Wayyo Allah! Dan Muhammadu ɗan Abdullahi ki yi haƙuri. Hannuna ya karye! Zai cire hannuna! Wayyo wayyo''

''Sai na lillisaki ta yadda gobe ba za ki yi gigin shiga faɗan da ba naki ba'' Jamila ta faɗa tana wurgi da ita kamar kayan wanki. Ta bigi bango ta zame a ƙasa Tim! Bata gama dawowa daidai ba ta ji saukan maruka a kumatunta hagu da dama. Ɗif ta yi kamar ɗaukewan ruwan sama sakamakon marin ya shigeta sosai. Take ta fashe da kuka tana faɗin

''Don girman Allah ki yi haƙuri! Ban za ci haka kike ba! Na roƙeka da Ubangijin talikai ki yi haƙuri! Allah ya jiƙan yayarta ya mata rahama! Na ci darajarta ki yi haƙuri '' kuka sosai take har da majina tana tsiyaya,duk yadda take jan majinar bata hana fitowanta ba. Tabbas idan bata yi wasa ba a banza za sha duka. Mikewa Jamila ta yi tana watsa mata harara ta ce

'''Kin haɗa ni Allah,sa'ilinan kin zci darajar fiyayyen halitta da kuma yayata. Gobe ki kara shiga sharu ba shanu ki gani idan za ki fita.'' tana faɗin haka ta wucewarta ɗaki wurin HAFIZA. Da kyar maman 'yar gayu ta iya miƙewa,makullin da ta saka a aljihun wandonta ta cire da hannun da ba ya mata ciwo ta buɗe ƙofar. Kamar jira suke ta buɗe ƙofar suka shigo da sauri.

''Ba na faɗa miki karki nemeta da faɗa ba. Kina zaman zamanki lafiya kin jawo ma kanki jalli joga. Tun da na ga ta ma yaya Sahura dukan mutuwa na sallama mata'' Ɗayyaba ta fada tana komawa wurin da ta tashi.

''Sannu maman 'yar gayu! Bata ji miki ciwo ba dai ko?"

Ɗago da Jajayen idanunta ta yi tana hararta ta ce

''Ke baki ji ƙarar karyewan hannuna ba! Daga nan asibiti na nufa a duba hannuna!"

''Bari na karaki asibitin''

''Tom''

Da kyar ta saka hijabin saboda yadda hannun yake mata zugi,har yanzu bata daina jin zafi a kumatunta ba. Sahura ta shiga ɗaki ta sauya hijabi ta fito suka fice.

A can ɗakin, Jamila ta iske HAFIZA kwance gefenta ta ajiye drawing book. Za ta zauna ta ji muryar HAFIZA

''Ammu har kin kammala damben?"

'yar dariya Jamila ta yi tana ƙarashe zama a kusa da ita.

''Oh kin mayar da ni 'yar dambe ko HAFIZA''

Murmushi HAFIZA ta yi

''Ai Ammu na leƙo na ga kin murɗa hannunta sai na dawo na kwanta. Gwara da kika koya mata hankali. Na ji daɗi sosai Ammu"

''Har kin san mugunta ko HAFIZA. Allah ya shiryeki''

''Ameen Ammu'' ta fada tana murmushi.

Waya Jamila ta ɗauka ta shiga latsawa, HAFIZA kuma ta gyara kwancinyarta tana lumshe ido alamun bacci yana son ɗaukarta.

A can asibiti,an duba hannun maman 'yar gayu sannan aka bata maganin rage zugi da kumbari sai suka fito,kowa ya bi hanyar gidansa. A hanya maman 'yar gayu ta ayyana ita da ƙara zuwa gidan Sahura sai bayan tafiyan Jamila. Bata yi tunanin Jamila na da mugun ƙarfi kamar namiji ba,har ma take tunanin ta fi wani namijin. Gida Sahura ta koma,uwar ɗakanta ta wuce ta cire hijabin ta zauna a gefan gadon. Uban tagumi ta rafka tana kallon wuri ɗaya. Lokaci guda tunanin Gwaggwonta ya ziyarci zuciyarta,ko sun dace oho! Za ta yi farinciki mara misaltuwa idan sun yi nasara. Tana tsaka da karanta wasikar jaki wayarta ta hau ringing. Kallon wayar ta yi ta ja tsaki har ta yanke bata ɗaga ba. Aka kuma kiran,a hasale ta ɗauka za ta kashe kiran idanunta suka yi arba da lambar ƙasar waje. Babu abin da ya faɗo ranta sai Gwaggwonta. Da sauri ta ɗauki kiran ta yi sallama. A can Gwaggwon Bugaje ta ce

''Uwata ce nice. Ina gadon asibiti yanzu''

Ras kirjinta ya buga. Bata san lokacin da ta miƙe daga zaunan ba tana ware idanuwanta waje.

''Gadon asibiti Gwaggwo! Kar dai ki ce mini hatsari kika yi''

A can Gwaggwon Bugaje ta ce

''Na sha wuya a hamadar boka Ataka sosai Uwata, idona ɗaya ya tsiyaye a cikin hamadar. Ƙiris ya rage su hallakani.''

Nan da nan jikin Sahura ya dauki tsuma saboda tsananin tashin hankalin da ta shiga.

''Wayyo ni Sahura! Gwaggwo ki dawo na kaiki asibitin ido a Kaduna. Kai amma Allah ya tsine ma wannan bokan...''

''A'a uwata ki daina tsine mishi taimakonmu ya yi fa...''

Ƙit aka yanke kiran,sake mayar da kiran Sahura ta yi sai aka ce kuɗinta ya yi ƙasa da wannan kiran. Tsaki mai tsayi ta ja. Kai kawo ta fara yi a ɗakin. Bata san lokacin da hawaye suka fara kwaranya daga idanuwanta ba. Shikenan yanzu alkalamin rubutunta ya ƙone ba ma bushewa ba. Yanzu kenan ba za ta sake mallakar Dauda Imamu ba! Kai! Ina da sake! Ai ba boka Ataka kadai ne ya iya aiki ba,da kanta za ta nemarwa kanta mafita tunda Gwaggwo ta yi iya koƙarinta,yanzu ne lokacin da ya dace ta farka ta kuma yi tsayi irin na daka. Komawa ta yi ta zauna,kuka ya taso mata tun daga ƙasan ranta,bata cuci kanta ba ta shiga rairawa ba tare da ta share hawayen ba. Ba komai ta tuno ba sai sabon wulaƙancin da Dauda Imamu ya ɓullo mata,da nuna ikon da yake a kanta da yaranta yana matuƙar ci mata tuwo a ƙwarya. Ta ci kuka sosai sannan ta shiga bayi ta wanke fuskarta ta wuce falon ta zauna,bata bari Ɗayyaba ta fahimci yanayinta ba. Ko mintuna biyar ba su cika da zamanta a falon ba Aunty Saudah ta shigo ciki. Kasuwa ta je siyayyan kayan abincin da babu a store. Ajiye kayan ta yi a kicin sai ta dawo falon ta zauna tana latsa watarta...✍️

^^^^^^^^^^^^^^

PHC Aouata,Bégajé yakin Zinder,ƙasar Nijar

Hannu Sajida ta saka ta amshe wayar daga kunnen Gwaggwon Bugaje ta katse kiran tana faɗin

''Karki ƙarar mini da kati gaskiya! Yin waya da 'yan ƙasarku akwai cin kuɗi sosai''

Gwaggwon Bugaje kamar ta yi kuka,hakura ta yi ta gyara zama ta fara cin abincin da Sajida ta zuba mata a plate. Bata ci abincin kirki ba saboda rashin ɗanɗanon da babu a bakinta,sai ruwa ta sha ta sake kwanciya tana lumshe ido ɗaya. Suna zaune wata nurse ta shigo ɗakin tana sallama. Dukkaninsu suka amsa mata. Ta cire drip ɗin sannan ta tambaya ya take ji a jikinta. Da sauƙi sosai ta ce saboda so take su sallameta ta koma Nijeriya. Rubutu ta yi a wata tarkada sannan ta ce

''Za mu baki sallama yau tun da kin ji sauƙi. Dole ki je asibitin ido a dubaki kar ya shafi dayan. Allah ya ƙara sauƙi''

''Ameen'' suka amsa ta bar ɗakin.

Da yamma aka sallameta. Suna isa gida ta fara shirin tafiya. Sajida ta so ta bari ta ƙara jin sauƙi,amma fafur ta ki yarda,burinta kawai ta ganta a Nijeriya. Za ta jima ba su ganta a Nijar ba. Nan Sajida ta shiga tsokanarta da cewan boka ya koya mata hankali,bata kula ba ta ci gaba da shirinta. Washegari ta assusuba yaron Sajida ya rakata tasha ta hau mota....✍️

^^^^^^^^^^^^^^^

Barikin sojojin sama jihar Kaduna Nijeriya

A daren ranar Jamila ta tara su Yasir a gidan Momy ta yi musu nasiha da kuma ƙaunar junansu,ta nuna musu su riƙe sirrinsu kar su zama masu fallasa sirrinsu musamman ga kishiyar uwarsu. Sai da ta biya gidan maman Jawaheer suka yi sallama sannan suka dawo gidan. Washegari da sassafe Yasir da Jalil suka rakata tasha ta hau mota. Bayan sun dawo daga rakiya Jalil ya ɗauki HAFIZA suka tafi gidan momynsa a can ta yini sai dare ya dawo da ita. Sabon gado da katifa ta iske a ɗakinsu har da wata 'yar drawer ƙarama inda za ta dinga saka litattafanta a ciki. HAFIZA ta yi farinciki sosai,a gefa guda Nu'aymah da sauran 'yanta haushinta ne ya mamayesu,gani suke saboda yafi sonta shi ya sa ya siya mata gadon zamani ba na karfe ba. Bata ma san suna yi ba. Bayan Isha'i da Dauda Imamu ya dawo ta fito falon ta zauna,bayan ya ci abinci ya mata ja a cikin Alkur'ani. Kasancewar tun lokacin da suka dawo daga Gusau Dauda Imamu ya hana kallo da daddare, sai dai da rana ko weekends. Ya umurci kowa ya maimaita abin da aka koya masa a daren madadin kallon. Ba don ransu ya so ba suka haƙura da kallon. Dauda Imamu ya yaba karfin haddar HAFIZA sosai,ya mata wasu tambayoyi a litattafan islamiyya,nan ma babu laifi sai suka yi sallama ta wuce daki ta kwanta.

Sai kusan 12:13am na dare Hamid ya dawo gidan. Dauda Imamu bai san Hamida baya daki ba. Jin karar bugun ƙofa ya tayar da hankalinsa,mamaki yake waye kuma da daddare haka. Jallabiya ya saka sannan ya fito falon.

''Wane ne?" Ya tambaya kafin ya ƙaraso wurin ƙofar.

''Ni ne Baba!" ya faɗa da wata iriyar murya irin ta 'yan ƙwaya.

''Hamid! Daman baka cikin ɗaki na kulle ƙofar?"

''Eh Baba'' ya ba shi amsa.

Bude ƙofar ya yi ya shigo ciki. Take hancinsa ya shaƙi warin wiwi. Da sauri Dauda Imamu ya dubi Hamid ya ce

''Daga gidan uban wa kake a daren nan"

Kafin ya ba shi amsa Sahura da ke bayansa ta ce

''Haba baban Hamid wace kalar tambaya kake masa haka kamar baka yarda da ɗanka ba!"

Juyawa ya yi ya harareta sannan ya ce

''Ban gane ban yarda da shi ba! Yana ɗana ban da ikon na tambayi daga ina ya fito ba! Ke baki ji warin da yake yi ba! Ki duba agogo ƙarfe sha biyu har ta gota yana waje. Wani yaron arziki ne zai kai wannan lokacin baya gidan iyayensa. Ko tara bata yi ba Yasir ya shigo gidan nan. Karki sake saka mini baki idan ina magana da yarana!"

Shiru Sahura ta yi tana kallonsa. Juyowa kan Hamid ya y da ke layi. Take ya ɗaga hannunsa sama ya sauke a kumatunsa ji kake Tasssss! Babu shiri Hamid ya riƙe kumatunta saboda azazzaben zafin da ya ziyarci shi. Tamkar a kumatun Sahura ya yi marin,yadda ta tallabo su da hannu biyu ka ce itan ce aka mara. Sosai zuciyarta ta sosu,idan kana son ganin ɓacin ranta mararan,ka ma yaranta faɗa ko ka taba lafiyar jikinsu. A nan za ta ajiye kawaici a gefe ta ma wankin babban garbo duk kusancinku.

''Dan ubanki daga ina kake! "

Cikin rawar murya Hamid ya ce

''Gidan abokina"

''Shi abokin naka ba shi da iyaye ne?"

Girgiza kai ya yi. A tsawace Dauda Imamu ya ce

''Baka da baki ne?"

''Yana da su Baba amma ba sa nan"

''Ok'' ya faɗa yana jinjina kai.

''Warin me naji kana yi''

Inda-inda ya fara yi wanda yake nuna tsantsar rashin gaskiyarsa a fili. Tsawa ya daka masa yana zare masa ido

''Wallahi! Tallahi! Summa billahi! Idan baka sanar mini warin me kake ba za ka sha mamakina! Da hannuna zan danƙaka hannun sojoji su hukunta mini kai. Ni ba uban banza ba ne! Ina matsayin limamin masallacin juma'a kuma shugaban karantar islamiyya na bariki bakiɗaya za a samu ɗana da shaye-shaye! Ko ba warin wiwi na ji kake yi ba...."

''Haba baban Yasir! Wannan ai ƙazafi kake shirin yi ma ɗana! Yarona kaɗai ka saka ma ido! Wa ya san abin da su Jalil suke aikawa a bayan fage! Ni abin da ba zan lamunta kenan gaskiya! Ka bar dana ya sarara ya huta! Lokacinsa ne! ''

Shiru Dauda Imamu ya yi yana binta da kallon mamaki,ya ma rasa abin faɗa. Can kuma ya ce

''Lallai Sahura ni kike fada ma lokacinsa ne! Dududu shekarar Hamid nawa ne da zai fara shaye-shaye!"

''Nifa dana ba ya shan komai,hancinka ne bai shaƙi daidai ba!''

''Allah ya kai mu gobe lafiya za ka sha mamakina" ya fada yana komawa ɗaki. Kulle kofar Sahura ta yi tana jan Hamid kicin. Cikin ƙasa da murya ta ce

''Hamid da gaske ne abin da mahaifinka ya faɗa a kanka?"

''A'a Momcy bana san komai wallahi''

Murmusawa ta yi tana jin sanyi a ranta ta ce

''Yawwa ɗan albarka wuce ka kwanta,ba zan bari mahaifinka ya hukunta ba. In shaa maka Allahu''

Ɗan ɗago da rinannun idanunsa ya yi yana sakar mata murmushi irin na jin daɗi ya ce

''Momcy ina gab da samun aikin''

Waro ido ta yi waje tana fadin

''Don Allah! Wani irin aiki ne ɗana?!"

''Sana'ar Yahoo abokina zai koya mini,idan na iya sa yai siyan mini babbar yawa na fara nawa''

''Kai na ji dadi sosai da wannan aikin. Ai daga jin sunan aikin akwai samun kuɗi sosai''

''Miliyoyan kuɗi ake samu momcy,amma karki sanar ma Baba''

''Shikenan ni Sahurar Gwaggwon Bugaje na warke! Ina zan bari ya sani ɗana! Na dade da sanin ɗan baƙin ciki ne. Yanzu dai ka je ka kwanta zuwa gobe sai mu yi maganar da kyau"

Daga haka kowa ya wuce ɗakinsa. Har ta yi nisa a bacci ta ji ƙarar wayarta. Daukar wayar ta yi cike da mamaki,ganin lambar Gwaggwota a saman screen din wayar ya saka saurin ɗaga kiran tana mikewa daga kwancen.

''Gwaggwo lafiya kika kirani cikin daren nan''

A can Gwaggwon Bugaje ta ce

''Ina wajen gate ɗin barikinku ne. Sojojin sun tsare ni wai sai na kira wanda zan je wurinsa ya zo da kansa ya ɗauke ni''

''To Gwaggwo yanzu nan zan zo'' ta fada tana katse wayar. Da sauri ta miƙe ta fara shiri. Tsam Dauda Imamu ya tashi daga kwancen fuskarsa a murtuke ya ce....✍️

Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️

***