LIKITAN RUHI

BIYAR

by @zeeeyybawa

LIKITAN RUHI

Na

ZAYNAB BAWA

AREWABOOK@Zeeeyybawa

SHAFI NA  BIYAR

A hankali na tashi saida na jawo gilashina na saka sannan na buɗe ƙofar na dawo ciki bayan na bata umarnin shigowa. Komawa nayi na zauna akan kujera ta shugo, cike da girmamawa ta gaidani ɗaga ido nayi na kalleta a ƙalla zata bani shekara 5-6 koma sama da haka amma tana gaisheni cike da ƙam-ƙam dakai kamar mai shirin rusuna min. kawar dakaina nayi gefe sannan na bata umarnin zama da mamaki take kallona domin ba haka suka saba gani a wajan manyansu ba ace ta zauna a kujera ɗaya dani ba. A haka dai ta zauna sannan ta fara sanar dani abunda zatana taimakin dashi gyaɗa kaina nayi kawai ita kuma tacigaba da mun bayani tana mun wani irin kallo da yake nuna irin she's amaze da kallona a yanzu. Tsayarda bayanin da takea mun tayi, tana kallona baki a buɗe, jin ta tsaya ta magana ne ya sanyani kallonta da sauri ta dawo cikin hayyacinta tana faɗin.

"I'm sorry maa na shiga cikin mamaki ne ban taɓa tunanin ganinki ido da ido ba a koda yaushe ina kallon interviews da akeyi dake ina fata ace na haɗu dake kuma gashi naganki you're very young dan a ido ma yarintarki tafi nunawa" kawar da kaina gefe nayi sannan nace.

"Menene sunanki?"

"Regina maa, sunana Regina" Kai na jijjiga sannan na miƙe ina duban agogon wayata goma ta ɗan gota nace.

"Zamu iya farawa?" da sauri ta miƙe har a lokacin fuskarta tana ɗauke da murmushi tace.

"Yes maa muje" tare muka fita da ita duk wani wajan daya kamata na sani sai da regina ta nuna mun sannan muka dawo office lokacin 1pm ta wuce missed calls nagani da yawa a wayata harda na Miemie. Miemie nafara kira a waya ko ince ita kaɗai zan iya kira a cikin missed calls duk da kuwa harda na Abbuna,

   Nasan abunda Miemie zata tambaya bazau wuce fitan sasaafen da nayi ba. Kamar yanda nayi zato hakanne ta tambaya. Na shaida mata akwai aikin da zanyi ne ya sanyani fita sassafe kuma banaso na tashesu shiyasa. Abbu kuma na tura masa message akan ina aiki sauran missed calls ɗin kuma duka na sharesu. A office nayi sallar azahar sannan Regina ta shigo mun da File na wasu daga cikin patients daya kamata na gansu gobe na duddduba sai bayan la'asar  na gama nazari akansu. Natshi nayi sallar la'asar sannan na fita zuwa wajan motata wasu daga cikin snacks da yogurt dana siya na ɗauko a ledarsu na fito dasu zuwa office. A office nayi lunch da Cup ramyeon dana siya da safe a super market. Zan iya cewa Cup ramyeon itace rabin abincin da nakeci a gabaki daya rayuwata kusan koda yaushe ita nakeci sai snacks da sauran abubuwan leda.

Tun la'asar nagama duk wani abunda zanyi harna sallami regina amma ni ina office anan nayi isha'i sai da 8pm ta wuce sannna na tashi domin komawa gida, yawanci likitocin sun tattashi nima kai tsaye motata na shiga na nufi gida kafin na isa gida 9pm ta kusa lokacin har Abba ya dawo,  dake ban samu kowa a palour ba ɗaki na wuce nayi wanka sannan na fito na nemi Miemie muka wuce wajan Abba tare cike da tausayawa Abba yake faɗin.

"Amma Ameerah aikin nan baiyi miki yawa ba ace kin fita tun sassafe sai 9 zaki tashi" Girgiza kai nayi nace.

"Abba baiyi ba inaga saboda zuwan fari ne ta iya yiwuwa lokaci yana tafiya aikin yana sauki ne"

"Allah yasa" Abba yace. Ummi kuma cewa tayi akan na dinga zama ina breakfast a gida amma na gwada mata hakan bazai yiwu ba saboda aikina da sassafe ne ta nuna damuwarta amma na gwada mata babu wata damuwa bazan rasa abunda can dinga yin karin kumallo dashi ba, nayi tunanin Abba zaiyi faɗa akan tafiya da nayi ni kaɗai batare da najira yaya Bilal kamar yanda yace ba amma sai naga baiyiba. Na lura shima Abba kamar Abbuna yake sam basason yimun faɗa akan wani abun da nayi ba dai-dai ba barinma Abbu da sam baya mun faɗa, na alaƙanta hakan da wani tsauni dana taka a rayuwa tun da ƙarancin shekaruna shiyasa suke taka tsan-tsan da duk wani abunda zai taɓani a cikin zuri'armu akwai wanda suka taka matakai da yawa wanda yafi nawa sai dai ba kamar ni ba domin ni na kasance ta daban, da ƙananun shekaruna na cimma abunda a duniya mutane ƴan ƙalilan ne suka iya cimmashi.  Na ɗan zauna a wajansu shida Ummi na ƴan mintuna sannan na fito wajan miemie, sai surutu Miemie takeyi tana tsara mana yanda auran Anty samha zai kasance anan take shaidamin ashe wanda Anty samha zata aura gidansu suma a layin yake, Nidai sauraronta kawai nakeyi kuma wasa gaske hirarta tana ɗebemin kewa ba kamar yanda nayi tunanin surutunta zai iya takurani ba.

A shekarun baya kafin rayuwa ta sakani a cikin duhu kaff cikin danginmu babu wacce nake so da ƙauna kamar Miemie a duk lokacin da akace za'aje kaduna toh na dinga kuka kenan har sai antaho dani koda kuwa tafiyar kwana ɗaya ce  saboda ita, itama hakanne a wajanta batada wacce ta shaƙu kuma take ƙauna a kaff danginmu kamar ni duk da kuwa akwai tazarar nisa a tsakanin wuraren da muke rayuwa, sannan familynmu Babban family ne mai ɗauke da mutane masu yawa.

    Yau ma kamar jiya sai da dare yaraba sosai sannan Miemie tayi mun sallama ta wuce. Yau ma dai duk ƙoƙarin na ganin nayi bacci abun ya faskara, inaso na samu salama a ruhi na na samu sassauci a zuciyata na samu saukin lamarin da yake damuna shine dalilin zuwana Zaria, amma abunda na baro a bauchi suna hunting ɗina sun kasa barina na samu sassauci, Hmm koda yake bazanyi gaggawar yanke hukunci ba  ta iya yiwuwa anan gaba zan saba ta'iya yiwuwa zuwa wani lokaci na samu nutsuwar da zan iya rintsawa akan gadona kamar kowa ina fatan hakan. Ana cewa dare mahutar bawa amma a nawa wajan rana ce mahutata a cikin rana nake samun sasssauci a ruhina da zarar dare ya shigo kamar yanda duhu ya mamaye ko'ina haka ruhina yake mamayewa da duhu.

_______

   Da Sassafe kaamr yanda ta kasance jiya na fice zuwa asibiti amma yau ban sayi komai ba saboda snacks da drinks dana siya a jiya suna da yawan da zasu ɗauki tsawon lokaci basu ƙare ba. Na isa asibitin yawanci ma'aikatan asibitin basu iso ba kai tsaye na wuce office ɗina. Ko'ina tsaff-tsaff kamar yanda na barshi, ajiye bag ɗina nayi a agefe na kwanta cikin ƙanƙanin lokaci bacci ya ɗaukeni. Yau dai ba kamar jiya ba regina tayi kokarin zuwa da wuri ƙarfe tara naji shigowarta office ɗin. Buɗe idona nayi sannan na dauki gilashina dake gefena na saka na zauna regina ta gaidani cikin ladabi kamar jiya yauma ban amsata ba, ganin ta girme mini sosai. Naga almaun jikinta yyi sanyi sai dai ban damu dana kula hakanma kai tsaye ta shaidamin zan fara ganin patients da misalin ƙarfe goma na safe.

  Ƙarfe goma bata cika ba na samu kira daga wajan director akan yana son ganina, babu ɓata lokaci na tafi zuwa office ɗinsa. Babu kowa a office din sai shi kadai na shiga bakina dauke da sallama na gaisheshi cike da nustuwa da kamewa ya amsa yana mai nuna min wajen da zan zauna, zama nayi haɗe da yin shiru ina sauraron abunda zaice. File ya turo gabana batare da yabari na ɗauki file ɗin ba yafara faɗin.

"Sorry Dr Khadija Ajiya kinzo asibiti batare da wata gagarumar tarɓa ba kamar yanda muka samu karramawar samun likita kamarki a wannan asibiti ya kamata ace da zuwanki mun haɗa miki welcome party domin karramaki da tarɓanki amma your grandfather Prof- Ajiya ya shaidamin baki son hayaniya so shiyasa bamuyi hakan ba and gashi daga zuwanki mun samu babban aiki da zamu gudanar a yau kuma muna buƙatarki a ciki akwai majnyacinmu da muke dashi anan asbitin wanda yake buƙatar Heart transplant, heart ɗinsa ta kai end-stage failure yayi exhausting duk wani treatment option. last option ɗin shine muyi implantation na wata zuciyar, cikin ikon Allah mun samu healthy heart da za'ayi replacing da tasa due to condition da yake ciki dole ne za'ayi masa aikin cikin gaggawa yanzu haka akwai Dr da yakai matsayin professor daga kano da yake hanya zuwa 11am zai iya isowa 12am zamu shiga surgery in sha Allah" sai da yagama bayani sannan na kalleshi cikin yanayin nutsuwa nace.

"Har yanzu banyi specializing a kowane fanni ba and I'm not a cardiologist wannan kuma surgery ne da ba kasafai aka cika yinsa a wannan ƙasar ba nikuma ƙaramar likita ce bana tunanin akwai taimakon da zan iya badawa wanda mutanen da suke wajan bazasuyi sama da hakan ba" Girgiza kai yayi sannan yace.

"A'a Dr khadija ina biye da duk wasu surgery da kika bada gudumawa a ciki tun ba yanzu ba inada masaniya akan komai, ko last successful heart transplant da akayi a kano kina cikin surgery ɗin kuma kin bada gudumawa, so anan ma ina buƙatar gudunawarki" ni ba yarinyace mai son musu ba hakan yasa kawai na gyaɗa masa kai amma wannan surgery da yake faɗin anyi a kano dani saboda nice wacce nake duba wannan patient ɗin nafi sanin condition ɗinsa fiye da kowa shiyasa koda akayi referring zuwa kano da za'ayi wannan aikin na kasance a kusa domin bada taimakona. Amma wannan fa bansan komai akan patients ɗin da condition ɗinsa ba. Muryarsa ce ta katseni da faɗin.

"Zan saka ayi canceling duk appointments da kike dasu da patients na yau saboda zamu dauki 4-5hour  a cikin  OR (operation room) depending on the complications sai abunda muka buɗe muka gani" Kai kawai na gyaɗa masa na ɗauki file ɗin na wuce office tun kafin na isa ya sanarwa regina akan babu patients da zan gani, a lokacin aka canja musu Doctor da zasu gani a wannan rana. Nikuma ina shiga office maimakon na buɗe file ɗin kawai sain aajiye na kwanta domin a halin yanzu bbu abunda nake buƙata kamar baccin duk da kuwa ina iya tsawon kwanaki ba tare da na runtsa ba a duk lokacin da zamu shiga surgery toh ina buƙatar nutsuwa a ruhi da kuma gangar jiki sune Babban makamina ga samun nasara.

#ZEE ALABURA

#LIKITAN-RUHI

#SOYAYYA

#ƘADDARA..