LIKITAN RUHI

SHIDA

by @zeeeyybawa

LIKITAN RUHI

Na

ZAYNAB BAWA

AREWABOOK@Zeeeyybawa

SHAFI NA SHIDA  

  Gabaki ɗaya baccin danayi bai wuce na ƴan wasu mintuna da bazasu gaza talatin ba amma cikin ikon Allah na samu nutsuwa sosai. shigowar regina ce ta tasheni daga baccin, a hankali na tashi zaune sannan na ɗauki gilashina na saka na kalleta wacce itama kallon nawa takeyi har wannan lokaci a cikin zuciyarta mamaki takeyi yanda na zama likita kuma na samu ɗaukaka a wannan ƙananun shekarun nawa duk iya lissafinta da yanda nayi sauri wajan gama wannan karatu lissafin yakasa zuwa mata adai-dai, Ajiyar zuciyar dana sauƙe ne ya sanyata dawowa daga cikin tunanin data shige cikin shifa wacce take tattare da ladabi tafara isarmin da saƙon director akan ana jirana domin gudanar da ƴar ƙaramar lacture akan aikin da zamu shiga. Kai na gyaɗa haɗeda miƙewa na ɗauki file da Director yabani, gaba tayi ina biye da ita a baya cikin nutsuwa muke tafiya ina duba file ɗin, Regina tanada nutsuwa samm batada hayaniya shiyasa tamu zata iya zuwa ɗaya kuma da alamu ta lura ni bawai mai son hayaniya bace shiyasa take bina a yanda nake, kafin muje hall ɗin da za'a gudanar da lacture ɗin na duba duk wani abunda nakeson gani a cikin wannan file ɗin daff zamu shiga cikin hall ɗin na rufe sannan na miƙawa Regina.

Nasan zakuyi mamakin yanda a ƙanƙanin lokaci na nazarci abunda ya kamata ace na nazarta a makonni koh? Toh ba abun mamaki bane domin hakan yana ɗaya daga cikin baiwar da Allah ubangiji yayi min kuma hakan ya kasance sirrin zuwa matakin da nake a ƙananun shekaru na. Batare da Regina ta amshi File ɗinba tace.

"Dr zaki iya buƙatar file ɗin a ciki ya kamata ki shiga dashi" sai da na kalleta sannan nayi wani tunani a takaice nace da ita.

"Okay Thank you" ina faɗin haka saina shige ciki, Manya-manyan likitocine a cikin madaidaicin hall ɗin da bazai dauki sama da mutane ashirin ba, ciki harda wannan professor Ɗalhatu wanda na taɓa assisting a kano mukayi aiki, cikin ladabi na gaidasu suka amsa sannan na nemi waje na zauna Prof Ɗalhatu har a fuskarsa ta nuna yaji daɗin kasancewata a wajan. Gabaki ɗaya mu takwas ne a wajan. Kuma duka wajan ni kaɗaice resident doctor (trainee doctor) a ciki. gabaki ɗayansu manya-manyan likitoci ne wanda ake ji dasu a wannan ƙasar tare da likitocin wasu ƙasashen wato fararen fata suma zasu bada tasu gudumawar a aikin da za'a gudanar, sauran likitocin wanda basu san da zuwana ba sunyi mamakin ganina a wajan domin aikin da za'a gudanar Babban aikine da har yanzu ƙasashe da yawa basu samu damar fara yinsa ba. saboda girmansa ko de-dai da assisting dinsa ba kananun likitoci bane sukeyi sannan aikine da ba kowacce kasa bace suka samu damar fara gudanar dashi komu anan wannan karon shine na uku da za'ayi anyi kwara biyu successful wannan na ukunma muna fatan ya zama hakan. Da yawansu daga cikin likitocin fuskarsu ta nuna rashin jin daɗin ganina a cikin wajan sai dai basu furta hakanba. Wani Babban professor na cikin asibitin babban cardiologist na asubitin shine wanda yyi bayani dallah-dallah akan aikin sannan bayan ya gama, masu tambaya suka fara tambayoyi akan conditions na patient ɗin da basu gane ba. Surgery ne da zai daukemu tsawon awanni shiyasa ake buƙatar kowa ya fahimci yanda aikin zai tafi duk da akwai alamun likitocin sun kwana biyu suna shiryawa aikin sannan sunyi nazari akansa yadda ya kamata saboda akwai yiwuwar canja likitan da zaina jagoranta duk bayan 1hour hakan yana nufin ta'iya yiwuwa likitoci guda huɗu zuwa biyar ne zasu ja ragamar aikin. Kusan kowa a cikin wajan yyi tambaya akan abunda bai ganeba amma banda ni hakan yasa Prof da yayi mana lacture ɗin ya kalleni yana tambayata ko inada tambaya kasancewar gabaki daya cikin wajan nice ƙaramar likita kuma nice kawai wacce ban tofa akan surgery ɗinba a tunaninsu kuma nice wacce ya kamata nafi kowa yin tambaya saboda fage ne wanda ya wuce mataki na, hankalin mutanen wajan gabaki ɗaya ya dawo kaina saboda tambayar da prof yayi mun, cikin nutsuwa da kamewa na sanar masa banida tambaya, mamaki sosai ya cika mutanen wajan da abunda na faɗa, prof dake gaban board yana bayani ya jijjiga kai sannan ya miƙomin white board maker dake hannunsa yace.

"Tunda ance kina iya ganin abu ta yanda mu bama gani ta'iya yiwuwa akwai abunda kika fahimta game da lamarin wanda mu bamu fahimta ba ko zakiyi mana ƙarin haske akai?" Babu wani abu dana fahimta fiye da abunda ya aka tattauna a wajan sannan banga patients ba tayaya za'ace nayi bayani fiye da abunda yake rubuce a cikin file ɗinsa. Magana nake ƙoƙarin yi domin tabbatar masa da babu wani abu dana fahimta fiye da wanda aka faɗi a wajan amma Prof Ɗalhatu dake kallona yyi saurin girgiza mun kai, ƙasa nayi da kaina sannan na sauƙe ajiyar zuciya a hankali na miƙe cikin nutsuwa na isa gareshi haɗeda amsar white board  maker dake hannunsa, ko ɗar-ɗar banji a raina ba na isa gaban board ɗin na tsaya domin ni ko tsoro bani dashi inada wata irin dakekkiyar zuciya ce wacce abu guda kawai take tsoro kamar yanda na faɗa muku a baya. Duk da tana cike da rauni amma bata tattare da gazawa zuciya ce mai ɗauke da nauyin son cimma burinta, na tabbata da cewa har indai ina son samun  cikar buri toh tabbas sai na zama dakekkiya maras tsoron duk wani abun firgici domin abunda nake tunkara a gabana abune babba da duhunsa yafi na dare mai cike da hatsari da muninsa yakai matuƙa, duk da sanin girman lamarin da nake tunkara baisa naji zuciyata ta gaza ba a shirye nake, nayi ɗammara domun tunkararsa gaba da gaba koda kuwa a sanadiyyar hakan zanyi nunfashina na ƙarshe. Ajiyar zuciya na sake saukewa.  batare da nayi clearing board ɗin ba na shiga bayani game da abunda na fahimta. Umarni yabani akan nayi clearing board saboda nayi bayani da kyau. Kamar yanda ya umurta nayi cikin nutsuwa nacigaba da bayani da kuma hanyar da za'a gudanar da aikin. Banyi bayani sama da abunda yayi ba sannan kuma bai gaza nasa bayanin ba, bayan na kammala na koma na zauna. Da yawan mutanen wajan basuga wani abu na musamman a tattare dani da har za'a ɗaukakani harhaka ba, Bayan an kammala tattaunawar ne muka fice domin shirin shiga surgery ɗin. sai da na canja kayana zuwa na surgery naje nayi Scrubbing sannna kai tsaye na wuce ɗakin theatre ɗin.

ƊAKIN TIYATAR

A hankali na shiga ɗakin theatre ɗin da aka riga aka kwantar da marar lafiya. Anesthesiologists suna tsaye akan aikinsu, suna sa ido kan duk wani canji da zai iya faruwa kafin a fara babban aikin. Na tsaya daga gefe ina kallon patient ɗin sosai, zuciyata na ƙoƙarin gane bambancin da nake gani yanzu a zahiri da wanda yake rubuce a cikin files ɗinsa. Abin da na hango akwai tazarar bambamci da wanda na’urori suka nuna,  Har manyan likutocin suka shigo bance komai ba kuma banda niyyar cewar duk da zuciyata tana son aikata hakan, bana son furta komai donin abin da na gani kafin a fara aiki ba lallai ne ya zama abinda mutane zasu yarda da shi kai tsaye ba.

Shiru na yi, ina mai lura da yadda sauran likitoci ke shirye-shiryen su. suka soma aiki cikin natsuwa, kowa na yin nasa fannin da cikakken ƙwarewa. A hankali, suka fara buɗe thoracic cavity domin isa ga zuciyar, an fara da incision a ƙirjin marar lafiya, a hankali kuma cikin kulawa domin kada a cutar da wasu tsokoki masu muhimmanci.

  Ana buɗewa, cardiopulmonary bypass machine ya fara aiki, wato na’urar da ke ɗaukar nauyin zuciya da huhu a yayin da zuciya take hutawa. Wannan na’ura tana bada damar yin aikin zuciya ba tare da patient ya rasa numfashi ko jini mai muhimmanci ba. muna  saka ido akan duk wani canji da zai iya faruwa,

A lokacin da suka gama buɗe ƙirjin maras lafiyan, Prof Ɗalhatu ya tsaya cak, ya kalli sauran likitoci sannan ya furta cikin yana yin dan firgici:

“The inflammation is worse than what I saw in the echo test.”   shine abunda ya fada bayan abunda idonsa ya gani, Na sauke ajiyar zuciya na san hakan tun kafin a buɗe. naso in sanar dashi kafin a fara, amma bana son bayyana sirrina da yake ɓoye. Abin da mutane suka sani a tattare dani a yanzu ya isa. Bana buƙatar wata ɗaukaka data wuce wannan shiyasa na kyale su gani da idonsu idan sun buɗe. Nasan da cewa rashin sanarwar tawa bazai zama matsala ba domun munsan da cewa akwai abunda na'ura bata iya ɗauka, mu likitoci a duk lokacin da zamuyi aiki munsan da cewa ba lallai  bane abunda test ya nuna shine exact abunda zamu gani idan munzo aiki ba a koda yaushe muna shiga aiki da shirin sai abunda muka buɗe muka gani."

  

  

A hankali muka fara cire zuciyar da take da matsala, aka maye gurbin ta da wata zuciyar mai lafiya. sannan aka hada manyan jijiyoyi anastomoses da coronary arteries da kyau cike da kulawa. Duk wani bleeding ko abunda zai bamu matsalamun saka ido akai, patient din yana samun kula cikin ƙwarewa.

  Alokacin da zuciyar da muka musanya tafara bugu jini yafara gudana yadda ya kamata, gabaki daya likitocin wajan idanuwan su ya nuna fara’a da masu hamdala ga ubangiji, kusan dun likitocin dake wajan murmushi suke da masu dariya amma banda ni wanda sam fara’a bata ciki a tsarina a yanzu, amma dai bazan iya cewa banji dadin ganin zuciyar da muka dasa tana aiki yanda ya kamata ba. Mun cigaba da aiki tare da kokarin kawar da duk wata matsala da zata iya tasowa.

 

#ZEE ALABURA

#LIKITAN-RUHI

#SOYAYYA

#ƘADDARA.....