Chapter 41
The Amazing Pen ✍️.......
BAHAGON TUNANI
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيم
041
Tsam Dauda Imamu ya tashi daga kwancen fuskarsa a murtuke ya ce
''Da izinin wa za ki je ɗaukota a cikin daren nan? Me kuma ta zo yi?"
Cak ta dakata daga shirin da take ta juyo. Wannan Daudan da ke gabanta ba wanda take juyashi ba ne a shekarun baya,gwara ta lallaɓa shi har zuwa lokacin da kambun ikonta zai dawo hannunta.
''Baban Hamid Gwaggwo ce fa! Ta yi Hatsari idonta daya ya tsiyaye a Nijar wurin duba 'yar'uwarta da take rashin lafiya'' cike da sanyin murya ta yi maganar fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa.
''Allah Sarki! Ai ban sani ba! Mu je na rakaki,ido ɗaya ya tsiyaye? Ko dai rauni ta ji a idon?" Ya furta da sanyin murya mai nuna tsananin tausayawa.
''Da gaske nake faɗa maka Baban Hamid! Shi ya sa na ce ta wuto ta nan mu je eye center a dubata'' ta fada tana ci gaba da shirin. Jallabiya ya mayar ya ɗauki hula ya saka.
''Hakan da kika yi kin yi tunani mai kyau'' ya faɗa yana yin gaba.
Biyosa a baya ta yi bayan ta sanya hijabi,ɗakin mazan ya je ya tashi Yasir. Umurtarsa ya yi idan sun fita ya kullo ƙofar, sannan ya zauna a falon idan sun dawo ya zo ya buɗe musu. Bayan sun fita ya kulle ƙofar. A jere suke tafiyar har suka iso inda sojoji ke gadi kusa da asibiti. Da yake kusan sojojin wurin sun sanshi,taimakonsu ya nema a kan sirikarsa ce a wajen gate ta zo daga Nijar idonta ɗaya ya tsiyaye silar accident da ya faru da ita a garin. Tausayin Dauda Imamu ya kama sojojin,wani daga cikinsu ya ce ba sai sun je ba,bari ya kunna mashin ɗinsa ya ɗaukota. Godiya sosai ya sama sai aka basu benci suka zauna. Sun zauna da kusan mintuna ashirin,suka hangi sojan ya dawo da Gwaggwon Bugaje a bayansa. A wurin da suke zaune ya faka mashin ɗin ta sauka. Sai faman zare idonta ɗaya take tana bin wurin da kallo ciki har da sojojin da suke tare da su.
''Sannu Mama. Allah ya ƙara sauƙi'' wani daga cikin sojojin ya faɗa.
''Ameen Ameen yarona''
Sauran sojojin ma suka mata sannu da jiki.
''Gwaggwo ashe hatsari kika yi a Nijar?" Dauda Imamu ya tambaya
Kallon Sahura ta yi daidai ta dubeta,take ta ƙyafta mata ido alamun ta amsa. Fahimtar abin da Sahura take nufi sai ta ce
''Wallahi kuwa!" Ta tsaya a haka don bata san me Sahura ta faɗa masa ba,gudun kar ta saki layi ya fahimci wani abu.
''Allah ya kiyaye na gaba,zuwa gobe sai ku je asibiti a duba idon''
''To Dauda''
Shiru ya biyo baya,babu wanda ya sake magana a cikinsu har suka iso flat ɗin. Babu mai gilmawa a ɓangaren sai su. Suna isa bakin kofar Dauda Imamu ya ƙwanƙwasa sau biyu ya jira. Yasir da ke saman kujera bacci ya fara fizgarsa ya ji bugun ƙofar,sai ya miƙe ya buɗe,bayan sun shigo ciki ya kulle ƙofar. Ido suka haɗa da Gwaggwon Bugaje amma ya yi mursisi ya wucewarsa ɗakinsu ba tare da ya gaidata ba,wanda idan da da ne har rissinawa yake yana gaisheta. Ran Gwaggwon Bugaje ya sosu sosai,danne fushinta ta yi ta zauna a kujerar falon tana cire mayafinta. Sahura ta shiga kicin ta tsamo sauran ɗan wanken da suka rage ta zuba mai da yaji ta kawo mata haɗe da ruwa. Dauda Imamu bai tsaya a falon ba ya wuce ɗaki,duba agogon ɗakin ya yi,ƙarfe 2:30am,ɗauko Al'qur'ani mai tsarki ya yi daga mazauninsa,ya shimfiɗa daddduma ya ajiye Al'qur'anin a gefe sannan ya wuce bayi dauro alwala. Bayan ya fito ya zauna a saman daddumar ya shiga raira karatun Alqur'ani cike da natsuwar jiki da na ruhi. A falon bayan Gwaggwon Bugaje ta kammala cin ɗan wanken duk da bata ƙoshi ba,sai ta gyara kwanciyarta a saman doguwar kujerar ta kwanta. Sahura ta kwashe kwanukan ta kai cikin sannan ta mata sallama ta wuce ɗaki. Tun daga ɗan lungun da zai sadata da uwar ɗakansu ta ji sautin muryarsa yana karatun Alqur'ani. Take annurin fuskarta ya yi ɓatan dabo,ƙunci da baƙinciki suka mamaye zuciyarta. Wannan karatun Alqur'anin da sallar daren da yake a kullum yana matuƙar ƙona mata zuciya,yanzu da mallakar ta warware a cikin uwar ɗaka yake ibadarsa duk da yasan sarai bata so. Zama bai ga mazaunanta ba, dole ta miƙe ta samo wa kanta mafita tun kafin wankin hula ya kaita dare. Ɗakin ta shigo ta canja kaya zuwa ɗauron ƙirji ta bi lafiyar gado bayan ta aika wa ƙeyarsa muguwar harara. Dauda Imamu da bai san tana yi ba ya ci gaba da karatunsa har zuwa ƙarfe 3:30am ya kabbarta sallah
Washegari
Da asuba
Kamar koyaushe,kowane ɗaki ya je ta tayar da su,mazan sun yi alwala suka tafi masallaci tare. A hankali HAFIZA ta miƙe daga kwancen tana addu'ar tashi daga bacci,bin Hamida ta yi da kallo har ta shiga bayi,ɗauke idanuwanta ta yi daga kallon ƙofar bayin ta bisu Aunty Saudah da ke sharbar bacci har da minshari. Yatsine fuskarta ta ɗan yi tana jan siririn tsaki. Ta lura da 'yan gida ba ma'abota ibada ba ne musamman sallar asuba idan ta cire Yaa Hamida da Yaa Yasir. Da safe ma idan suka tashi ba wanda take gani ya yi sallah. Ƙaramarsu ce wani lokacin takan ganta tana burbura sallarta. Dogon numfashi ta ja ta sauke a lokaci guda,wardrobe dinta ta bude ta cire brush da toothpaste ɗinta wanda Yaa Yasir ya siyan mata,gidan kowa da kwandon wankan da brush ɗinsa. Matsa toothpaste ɗin ta yi a saman brush ɗin sai ta miƙe. Hamida na fito daga bayin ta shiga,tsarki ta yi sannan ta wanke bakin ta ɗauro alwala ta fito. Ta iske Hamida na sallame da sallah,dogon hijabinta na islamiyyarsu ta Gusau ta saka,ta duba jakarta islamiyyarta da ke rataye a kusa da ɗan ƙaramin gadonta. Hisnul muslim ta cire ta ajiye a gefan daddumar,sai ta mayar da jakarta inda take. Kabbarta sallah ta yi,cike da natsuwa ta gabatar da raka'atul fijr ta sallame,ta sake mikewa ta kabbara sallar asuba. Bayan ta idar ta yi lazumi sannan ta ɗauki Hisnul muslim dinta wanda Ammuna ta bata shi kyauta ta fara karantawa,a nutse ta kammala azkhar ɗinta sannan ta fara muja'iar haddarta har safiya ta yi.
''God! What the fucking hell is this! Mutum yana baccinsa cikin kwanciyar hankali ana damunshi da karatu! For what!. Abin da ba za mu dauka ba kenan a gidan nan!" Aunty Saudah ta faɗa a hasale tana zuwa inda HAFIZA take saman dadumar. Bata tanka mata ba kuma bata daina karatun ba, ran Aunty Saudah ya sake ɓaci ganin ta yi buris da ita.
''Ke dan uwarki ba da ke nake ba...!"
''A'a fa! Wannan ne kuma abin da ba zan ɗauka ba! Karki sake tsomo uwarmu a cikin zancenki! HAFIZAN da ta miki laifin ki tsaya a kanta amma ban da uwarmu'' abin da Hamida ta faɗa kenan tana ajiye kayan da take linkewa a gefe. Sheƙeƙe Aunty Saudah ta tsaya tana kallonta,haka ma su Amina da ke shirin makaranta cak suka tsaya suna mata kallon mamaki. Yaushe Hamida ta yi baki da har za ta mayar da magana. Ita da ko autarsu Maryam ta saka aiki babu musu take yinsa,amma yau take mayar ma babban yayarsu magana cikin ido.
''Eh lallai Hamida! Wuyanki ya isa yanka! When did your dirty mouth start to throw back words on me! Ni sa'arki ce'' Aunty Saudah ta furta rai a ɓace. Taɓe baki Hamida ta yi bata amsa mata ba,linke kayan ta ci gaba da yi abinta. HAFIZA ma karatunta take sosai ba tare da ta ji tsoron tsayen da Aunty Saudah ta yi a kanta ba. Kallon mamaki Aunty Saudah take bin Hamida.
''Aunty Saudah ki kyaleta! Don ta ga Auntynta ta duki mama ne shi ya sa ta yi baki yanzu! ga Baba ya dawo ji da su'' cewar Amina tana shigewa bayin wanka.
''Fine! Wannan ya zama kashedin karshe da zan miki! Idan kika sake shiga gonata i will teach a great lesson!" Tana fada tana nunata da ɗan yatsa.
''Na dai faɗa karki sake tsomo uwarmu da ke kwance cikin kabari a maganarki idan har kin son zaman lafiya a gidan nan''
Tsaki Aunty Saudah ta ja tana yin ƙwafa ta koma saman gado. Wayarta ta ɗauka ta shiga Whatsapp duba saƙonnin da aka turo mata. Kwata-kwata bata da walwala, maganar Hamida ta kwashe rabin farincikinta da ta farka da shi yau. HAFIZA na kammala muraji'arta ta ɗauki Hisnul muslim dinta ta mayar cikin jaka,ta ɗauke daddumar ta ajiye a saman wardrobe ɗinta. Kakkaɓe gadon ta yi ta gyara.
A can Falon, Ɗayyaba, Gwaggwon Bugaje da Sahura suke zaune a falon suna jajanta abin da ya faru da ita. Ɗayyaba ta shiga ruɗu a safiyar yau da ta fito ɗora abin kari kamar koyaushe. Ba su yi maganar da Sahura ba a kan zuwan Gwaggwon Bugaje ba,sai dai ta gantaa kamar a mafarki idonta ɗaya a rufe da bangeji tana bacci. Take zuciyarta ta halba tana ƙarasowa inda take tana sake duba fuskar Gwaggwonta. Sunanta da ta ambata ya farkar da Gwaggwon Bugaje daga bacci mai daɗin da take,daidai Sahura ta fito daga ɗakinsu Amina tashinsu shirin makaranta. Zama Sahura ta yi kusa da Gwaggwon Bugaje haka ma Ɗayyaba suna kallon fuskarta. Babu abin da ta rage na daga abin da ya faru da ita a hamadar boka Ataka,sun jimanta sosai musamman Ɗayyaba da abin da taɓa zuciyarta sosai. A raunace ta wuce kicin ɗora abin kari kar yaran su makara. Ɗan muskutawa Sahura ta yi tana sake duban fuskar Gwaggwon Bugaje
''Gwaggwo da wuri da mu je asibitin kar mu tarar da layi''
''To! Asibitin akwai tsada?" Ta tambaya.
''Eh. Da tsada gaskiya. Cikin kuɗin da nake ajiyewa na hidimar bikin Aunty Saudah idan ya ta so zan ciri wani abu a yi miki maganin! Lafiya ta fi komai''
Murmushi Gwaggwon Bugaje ta yi tana jinjina tausayi irin na ɗiyarta.
''Karki damu Uwata! Mene ne amfanin su Bashiru da Hayatu. Yanzu nan zan ɗaga waya na kirasu. Ki adana kuɗinki da kyau saboda fita kunya''
''To Gwaggwo'' Sahura ta furta tana jin sanyi a ranta. Miƙa ma Sahura wayar ta yi don ta kira mata su. Sahura bayan ta amsa ta nemo lambar Hayatu,har ta tsinke bai ɗauki kiran ba,ba tare da gajiya ba ta sake kiransa a nan ba bai ɗaga ba,sai da ta jera kira kusan shida babu wanda ya ɗauka sai ta haƙura. Lambar Bashiru ta kira,wayar ta shi ma a kashe take. Fuskarta ɗauke da damuwa ta kalli Gwaggwon Bugaje ta ce
''Gwaggwo babu wanda na samu a layin,ɗaya bata shiga,ɗayan kiran bai ɗauka ba''
''Too! Yanzu ya za mu yi kenan? Gaskiya bana son ki taɓa kuɗin ajiyar biki''
''Bari na kira Baban Hamid na ji ko zai taimaka mana da wani abu,jiya na yi yana waya da wani soja yana masa godiyar ya ga abun alkhairi,sai dai bai faɗa mini abin ya samu ba'' ta faɗa tana ɗaukar wayarta daga hannun kujera.
''Allah ya sa a dace''
''Ameen Gwaggwo'' ta faɗa tana kara wayar a kunnunta. A bugu biyu ya ɗauki kiran yana mata sallama.
''Wa Alaikumussalam! Barkha safiya''
A can Dauda Imamu ya ce
''Barkha dai''
Tattaro da natsuwarta ta yi tana gyara zama ta ce
''Daman Gwaggwo ce nake son na kai asibiti idan mun karya,shi ne na ce zan samu wani abu a hannunta na haɗa da nawa''
A can Dauda Imamu ya yi ɗan jim,har ta cire rai da amsarsa ta ji ya ce
''A gaskiya kuɗin da ke hannunta na amfanin yau ne,domin ina son na kai HAFIZA boko kar a yi mata nisa a karatu. Ba Kawu Kabir yana nan ba,ta kira ta ji ko za ta samu kuɗi a hannunsa. Na san ma za ta samun in shaa Allah ''
''To'' ta faɗa tana katse kiran. Malolon baƙin ciki ta haɗiye tana bin wayar da kallo. Dauda Imamu ya gama raina mata hankali,yanzu saboda 'yar iskar yarinyar nan ne zai ƙi taimaka mata ta kai uwarta asibiti. An ya za ta iya ci gaba da shan ruwan takaici daga wurinsa a kan HAFIZA kuwa! Yaushe kambun ikonta zai dawo hannunta? Dole ta miƙe don zama bai ganta ba!....
''Uwata lafiya na ga kina bin wayarki da kallo? Ko bai da kuɗi ne?" Ta faɗa tana katse mata tunani.
''Ko ɗaya Gwaggwo! Dole na miƙe tsaya na samar wa kaina mafita! Baban Hamid bai taɓa ɓata mini rai irin na yau ba'' Sahura ta yi maganar tana share ƙwallar takaici.
''Me ya ce miki Uwata?'' ta faɗa tana kallon Sahura.
''Ni Baban Hamid zai ma cin fuska! Na kawo mishi ƙoƙon barana amma ya watsar saboda shegiyar yarinyar mai zubin aljanun ruwa!"
''Ni fa ban fahimci inda zancenki ya dosa ba?" Gwaggwon Bugaje ta ce tana ɗan gyara zamanta.
''Gwaggwo cewa ya yi yana da kuɗin amma na amfanin yau ne zai kai HAFIZA makarantar boko kar a mata nisa a karatu! Don Allah ki ji wannan banzar maganar!"
Taɓe baki Gwaggwon Bugaje ta yi zuciyarta na mata suya tamkar gyaɗa marau.
''Da sake kam! Na ga alama zaman wannan zabiyar yarinyar a cikinku ba alkhairi ba ne! Bari na samu sauƙi sosai,zan nemi wani bokan mu ji ko za a dace. Ƙarfen ƙafa za ta zamo muku daga ke har yaranki. Tun kan a je ko'ina ya fara nuna baki da daraja a wurin shi! Da sake kam!....''
Faɗa sosai Gwaggwon Bugaje take kamar ta ari baki,Sahura na tayata. Ran Gwaggwon Bugaje ya yi matuƙar sosuwa,miƙa ma Sahura wayar ta sake yido ta kira mata mijinta wato mahaifin Sahura. Amsar wayar ta yi ta kira shi, a bugun karfo ya ɗauki kiran. Ba tare dogon magana ba ta ce ya san yanda zai yi ya turo mata dubu hamsin kafin azahar,bata jira amsar ba ta katse kiran. Babu wanda ya san abin da ya faru da Gwaggwon Bugaje har shi mijin nata bata damu da ko bashi ne ya ɗauka ba burinta ya turo. Ta ajiye wayar a gefenta kenan za ta yi magana HAFIZA ta fito daga ɗakinsu za ta je kitchen ɗaukar tsintsiya. Kamar kurayen da suka ga abin farautarsu, kallon tsana suke binta da shi. A tsawace Gwaggwon Bugaje ta ce...✍️
Narrnarhh Bukar's Amazing pen ✍️
***