LIKITAN RUHI

TAKWAS

by @zeeeyybawa

LIKITAN RUHI

Na

ZAYNAB BAWA

AREWABOOK@Zeeeyybawa

SHAFI  NA TAKWAS

  Patients ɗin suka fara shugowa, na zauna na fara ganin kowannensu cikin natsuwa da jajircewar da aikin likita ke buƙata, amma duk da haka zuciyata na dawowa kan maganganun da na ji a lecture room ɗin , ba don sun dame ni ba, a'a, kawai ina tunanin ikon Allah yadda mutum zai samu wata baiwa ta daban, sannan sai wannan baiwar ta zama abin tsoro ko mamaki ga wasu ban bari lokacin sallah ya wuce ba ina cikin duba patients aka kira la'asar na tsaidasu nayi sallah kafin nacigaba da dubasu,  A ƙarshe na kammala ganin patients ɗina na kashe system ɗin da na adana bayanansu a ciki domin buƙatar wata rana, sannan na ɗauki wayata na fice zuwa duba patient da kulawarsa yake a ƙarƙashina.

Cikin nutsuwa da kamewa nake tafiya ina dannan wayata na nufi hanyar ICU domin sake duba patient ɗin kafin nabar asibiti, Duk sanda nake shiga ICU ina cike da natsuwa, domin gurin yana bukatar nutsuwa ta musamman. Ina shiga nayi sallama, sannan na tafi a hankali zuwa gadon marar lafiyar. Wannan karon na lura yana motsa yatsunsa kadan-kadan, alamar farfaɗowar da muke jira. Naji daɗi sosai a Zuciyata ta amma bai bayyana a fuskata ba, Zuciyata kaɗai ke farin ciki amma fuskata da Ruhina sam basu samu wanna damar ba, wannna aiki da akayi tabbas yana bayar da sakamakon da ake so.

  Na ɗauko chart ɗin nasa ina rubuta abubuwan da na gani, na gyara drip ɗin da ya dan kwance kadan, sannan na kira nurse Domin ta duba oxygen reading da monitor ɗinsa. Bayan na tabbatar komai yana tafiya yadda yake so, na juya zan fita sai na ji muryar consultant ɗin da yake supervising patients ɗin surgical ICU.

"Doctor Khadija." Ya kira sunana, juyawa nayi na kalleshi, fuskata sam babu walwala, cikin nutsuwa nace., "Na'am" Ya matso kadan yana kallona da irin kallon nan na manyan likitoci, kallon da yake cike da nazari, kafin ya furta maganar da zata fito daga bakinsa har sai zuciyata ta tantance min. abunda yake son fada nasan dai bazai wuce yabo akan aikin da mukayi ba, likitoci da yawa a asibitin nan na lura dasu suna son dinga yin amfani da hakan domin suna shigemin,

"I heard about your performance in the theatre two days ago. You did well." Allah nagode maka shine abun na fada a zuciyata, shi fa wannan likitan ko kallonsa ban taɓa yiba har ya akayi sa'an ƙoƙarina a cikin ɗakin tiyata, wato koh, itafa ɗaukaka kamar yanda na faɗa tana zuwa da ƙalubale, a cikin rayuwata gabaki ɗaya babu abunda yake takurani kamar mutane suna kulani can asibitin dana baro sanin halina yasa magana idan bawai ta dole ba babu mai tunkarata da ita domin ba kulawa zanyi ba. amma nan ma da sannu zasu gane halina

"Thank you" na faɗa da ƴar ƙaramar muryar da bata cika sauti ba. Yayi dariya, sannan yace,

“I also heard a lot more. but I will ask you when the right time comes." ban iya bashi amsa ba harya juya ya tafi ko  abakin wa zaiji amsar tambayar da zaiyi oho?.

  Na fita daga ICU cikin tunanin, son shiga sabgata da Likitocin asibitun suke son fara yi wanda hakan ba ƙaramin takura zai zamamun ba,

  Yawan aikin da nayi a kwana biyun nan babu hutu yasa naji duk  jikina a gajiye sosai. ina zuwa aka bani Surgical Rotation, aikin surgical rotation ba wasa bane, ga yawan patients da nake gani marassa iyaka in banda ƙasar nan da muke da ƙarancin likitoci ta fannin Neurosurgeons  ba ta ina za'a tarawa ƙaramar likita kamata ayyuma har haka? Kodan suna kallona da wata baiwa ce yasa hakan?

A waje na hango Regina tana tahowa da ɗan gudu kamar wanda aka kirata. da maroon uniform a jikinta, tana rike da wani file.

"Doctor!" Ta kira ni cikin rawar muryar dake nuni da tayi ta zagayen nemaana bata sameni ba.

"Na'am?" Na tsaya ina kallonta.

"Daman ana nemanki wajen admin section. They said Prof Dalhatu ya kira daga Kano, saboda jin halin da patient yake ciki an sanar masa kece mai dubashi so yana son jin bayani daga gareki" kai kawai nayi nodding batare da nace komai ba,

tasan banda yawan magana hakan yasa bata sake cewa komai ba, Sallamarta nayi cewa mungama da ranar idan babu wanu abunda zatayi zata iya tafiya sannan nikuma na nufi bangaren admin.

   A lokacin da na karasa harabar admin hallway sai na hangi Director na asibitin tsaye yana magana da wasu high ranked consultants. Director yana kalloni ya saki murmushi yana yin kallon da yake mun yana kama da na Uba,  murmushi yake mai nuni da gamsuwa da kuma alfahari.

"Dr khadija Ajiya." ya furta a yayin da nake ƙarasowa wajan da yake ina dan sadda kai, "Na'am."

"Ya yanayin patients dinki? Ina fata akwai sauyi domin tomorrow morning, za'a yi pre-conference briefing. We will address the media two days from now. I want your presence. A matsayinki na daya daga cikin doctors da suka yi assisting a cikin surgery, your explanation matters." kai na jijjiga cike da ladabi nace.

"Alright sir, I'll be there in sha Allah"

Yayi gyaran murya kamar zai ƙara magana, amma wani consultant ya katse shi da gaggawa don tattaunawar da suke yi. Sai kawai ya ɗaga min kai alamar ina iya tafiya.

  Ina zuwa aka kira Prof ɗalhatu nayi masa bayani cike da gamsuwa yace.

"Madallah da jin wannan baya nin dama anyi schedule na conference nanda 2days shiyasa nakeson naji"

"In sha Allah zai tashi” nace domin datse sauran maganar. Sallama mukayi dashi cikin sauri  na juya na nufi hanyar fita daga admin block din, zuciyata tana ƙara yin nauyi. Duk da kasancewa likita mai tarin baiwa  da nafi dubannin likitoci, ban taɓa son fitowa fili ba. ban taba bukatar wani attention ba, sam banson yawon interaction da mutane hakan ba karamar wahala yake yimun ba, yin cudanya da mutane yafi bani wahala akan Karatuna na Neurosurgery, dalili daya yakesa nake halarta wannan conference da ake yawan yi dani, dalilin da yasa ko naji bazanyi ba nakanyi nayi saboda wannan dalilin. wannan dalilin zan iya cewa ya kasance dalilin rayuwata a halin yanzu, daba dan shiba toh tabbas da zan roki Allah ya dauki rayuwata kawai.”

  Ina hanyar komawa office sai wayata ta yi vibrating. Na zaro wayar na ina kallo, number ce wacce bani da ita akan wayar kamar bazan dauka ba domin sam ni ba mai son amsa kira bace duk kuwa da hakan ba hali ne mai kyau a wajan likitoci ba amma kowa yanada tasa tawayar ni tawa a fannin aiki a rashin daga waya take. kamar bazan amsa ba na danni zuciyata na danna green icon nayi picking call ɗin.

"Hello, Doctor Khadija Ajiya ce?" Muryar mace ce, tana magana da sauri.

"Uhmm itace ."  na fada don ban gane muryar ba,

"Thank you. I am calling from the National Medical Press Association. We received confirmation of your inclusion in the surgery team and—" Ba ta gama maganarta ba nasan inda zancen ya nufa. Nan take na katse muryarta cikin tsantsar rashin son takura  karfin hali kawai nake nace.

"I'm sorry, but I am unavailable for any media request except the official conference da asibitin zai shirya. That is the only one I'll attend." Ta yi shiru na dan lokaci sannan ta ce,

“Alright, Doctor. Thank you for the clarification."

Na kashe wayar, na lumshe ido ina sauke ajiyar zuciya. ina mamakin yanda ta samu lambar wayata domin ni ko conference akayi dani ban yarda nasaka lambata a jiki, ji nayi kamar nayi blocking dinta domin na san ba su da hakuri, gobe sai sun nemi wata hanyar sun nemeni..

  

lokacin da na dawo office, ana kiran sallah, anan nayi sallah domin koda yaushe bana barin office har sai karfe takwas, yauma hakan na bari na nufi gida.

   ina parking motar na fito a gajiye na nufi ciki yau su Ummi na palour harda miemie. miemie tana jin sallamata tayi saurin miƙewa ta nufo ƙofar jakar hannuna ta karɓa saboda alamun gajiya da nake tattarre da ita, tare muka ƙarasa ciki. Na zaune a kujera sannan nace.

"Sannu da gida Ummi" Cike da fara'a Ummi ta amsa tana faɗin.

"Yawwa sannu Ameerah, wannan aiki naku Ameerah sam babu hutu? Allah dai ya saka muku da alkhairi na taimakon jama’a babu dare babu rana” sadda kaina nayi ƙasa harta gama magana sannan nace.

"Ummi bari nayi wanka na fito"

"Toh Ameerah idan kika fito sai kici abinci" Ba tare dana amsa ba na shige ciki domin babu tabbacin zan iya cin abincin tunda nazo zaria ko sau ɗaya ban taɓa cin abincin da aka dafa a gida ba, duk da wani fanni na zuciyata yana sanar dani Ummi bazata taɓa cutar dani ba amma abunda idanuwana suka gani, da wanda kunnuwana sukaji yasa zuciyata takai matsayin da bata taɓa yarda da kowa bata iya bambamce mugun mutum dana kirki,

   

Wanka nayi na tsaftace jikina sosai bayan na fito zallan deodorant na goga na sanya inner wear sannan na zura doguwar riga na fito a yanda nabar su Ummi anan na samesu kusa da Miemie na zauna kaamr jirana take ina fitowa tafara faɗin.

"Ameerah kinsan saurayin Anty Samha, zuwansa biyu wai Anty samha ta bashi labarin zuwanki  ta dameshi akan sai yazo ya ganki, sai dai baya sa’ar samunki, nace masa har indai yana son ganinki sai dai yabari a weekend yazo, kar kiso kiga yanda yake ɗaukin ganinki yace Anty samha kullum tana cikin bashi labarinki" Ummi ce ta katse mana zancen da faɗin.

"Miemie tashi ki kawo mata abinci saiki cigaba da surutun" Miƙewa tayi ta nufi kitchen bata daɗe ba ta dawo hannunta riƙe da plate da cokali a ciki Ajiyewa tayi sannan ta koma ta ɗauko ruwa da lemo, a hankali nake cacckula abincin amma nakass kaiwa bakina su dukansu sun lura da nakasa cin abincin, daga Ummi har Miemiee suna tausayin halin da nake ciki, A tunaninsu basu ga wani abu da har zai jefani cikin irin wannan halin ba, inada uwa uba da ƴan uwa duka a raye da gata ta kowane fanni ga ɗaukaka da Allah yabani a ƙananun shekaru a gabaki ɗaya iya tunani sunyi amma har yanzu basu gano wani kwakkwaran dalilin daya maidani haka ba, Abba yakan yawan cewa ɗaukaka ce ta maidani haka amma  a ƙasan zuciyarsu sunaji kamar akwai wani abu na daban dake damuna."

#ZEE ALABURA

#LIKITAN-RUHI

#SOYAYYA

#ƘADDARA..