TARA
by @zeeeyybawa
LIKITAN RUHI
Na
ZAYNAB BAWA
AREWABOOK@Zeeeyybawa
SHAFI NA TARA
Laɓɓansa ɗauke da ambaton ubangiji a lokacin da ya farka daga bacci, a hankali ya buɗe idanuwansa sannan ya sauƙar da ajiyar zuciya, fuskarsa ya juya gefen wayarsa da take ruri wacce take kan side drawer a hankali yakai hannunsa ya ɗauki wayar. Ajiyar zuciya ya ƙara sauƙewa ganin sunan Sagir dake kan wayar saida yaja ɗan siririn tsaki sannan ya amsa kiran. Cikin ƙulewa ya kara a kunnensa haɗe da faɗin.
"Wai kai Sagir fisabilillahi yaushe zakayi hankaline? Kira ƙarfe ɗaya na dare menene zaka faɗamin haka da bazaka iya jira gari ya waye ba?" ya ƙarashe maganar a zafafe, daga cikin wayar Sagir yayi dariyar data sake ƙular dashi sannan yace.
"Dan iska idan kiran da nake maka cikin dare yana damunka kayi zuciya kayi aure mana, nasha faɗa maka idan kayi aure zan daina kiranka cikin dare domun idan akwai ƴar mutane a gefenka inada tabbacin bazan kiraka a wannan lokacin ba" siririn tsaki yaja sannan yace.
"Bazanyi ba" yayi magana cike da kulewa, daga cikin wayar Sagir dake son sake ƙular dashi yace.
"Kaga kuwa bazan daina kiran ƙaton tuzuru a lokacin da raina yake so ba" siririn tsaki yaja sannan yace.
"Faɗi dalilin kiran ina jinka"
"Kasan dalilin ai Hammad domin har saƙo na tura maka amma baka maidomin da amsa ba" Sagir yayi magana cikin yanayin da yake nuni da ya ajiye batun wasa a gefe. Ajiyar zuciya Hammad ya sauke cikin yanayin dake nuni da yana ɗauke da damuwa da kuma son danne wannan damuwar yace.
"Sagir nayi tunanin a yanzu mun wuce wannan batun, tun ba yanzu ba munyi yarjejeniya sannan mun yarda da cewar zamu fawwalawa Allah komai muga yanda zaiyi damu, Sagir banda iko irinna ubangiji ba ka taɓa tunanin har zan kai wannan lokacin? Allahn daya kula dani har zuwa yau baka tunanin tunda muka miƙa masa lamuranmu shi zai kawo mana mafita?" Sagir muryarsa har ƴar rawa takeyi yace.
"Inaji a jikina wannan itace mafitar da Allah ya kawo mana ita, ta iya yiwuwa addu'ar da kullum mukeyi gareshi shine ya kawo mana mafita" Ajiyar zuciya Hammad ya sauƙe sannan yace.
"Shikenan naji"
"Ka yarda zakaje?" Sagir ya tambaya cike da jin daɗi.
"Yaushe zaka shigo?" Hammad ya canja zancen da sukeyi.
"Zan iya kaiwa nan da 10days zan kuma iya shugowa ko nan da wasu kwanaki har indai ka amince zakaje sai muje tare"
"Sai da safe" Hammad ya faɗa haɗeda saurin kashe wayar. Ajiyeta yayi yana sauƙar da ajiyar zuciya haɗeda lumshe idanuwansa yana sauƙe numfashi.
Mafarkin da yakeyi a lokacin da kiran Sagir ya shigo ya katse shi ne yafara dawo masa, kwana biyu kusan koda yaushe a cikin waɗannan mafarkan yake, amma ya alaƙanta hakan da yawan takurawar da Sagir yake masa akan lamarin babu ƙaƙƙautawa a koda yaushe.
Zuciyarsa sa ce tafara karkata da tunani akan maganar da Sagir yazo masa da ita zata iya kasancewa mafita. ta'iya yiwuwa hakan mafitace da Allah ya kawo masa, ko zai gwada yagani? Saurin girgiza kai yayi domun baya son sake sanyawa kansa damuwa akan wannan lamarin tsawon shekarun daya ɗauka a baya cikin damuwa ma ya isa yanzu so yakeyi kawai ya fuskanci rayuwar da take jiransa a gaba kamar yanda yace ya fawwalawa Allah komai har cikin ransa yake jin bazai sake takurawa kansa akan lamarin da baida iko, wayo ko dabara akansa ba. Saƙa da warwara kawai yakeyi na tsawon lokaci baccin ya kasa dawowa ya ɗaukeshi yana kwance idanuwansa a rufe bakinsa yana ambaton ubangij, ajiyar zuciya ya sauƙe sannan a hankali yaja jikinsa haɗeda miƙewa zaune ya jingina da jikin bed ɗinsa sannan yakai hannunsa ya ƙara hasken dake ɗakin lokaci guda haske ya wadaci ko'ina. kallo yake ƙarewa ɗakin kamar a lokacin yafara ganinsa. Wani irin ƙayataccen ɗakine kamar wanda akayi masa ado da ruwan danyan zainare saboda ƙallin da yake. Interiors da funitures hadda da paint na ɗakin gabaki ɗayansu fararene tass sannan ɗakin ya wadatu da hasken fitulu wanda ya ƙara ƙawatashi, gadon da Hammad yake kwance akai tsaruwarsa da siffarsa yasha bambam da irin gadajen da muka saba gani, bed ne kamar wanda aka ƙirƙireshi na musamman domun mutum ɗaya kuma ga dukkan alamu mamallakin ɗakin ya kasance mutumne mai tsaftar gaske domun komai na ɗakin farine ƙall amma kamar a lokacin aka sanyasu sai yalli kawai suke, ga wani irin sanyayyan ƙamshi dake fitowa daga kowanne lungu da saƙo na ɗakin.
Iska Hammad ya ɗan furza, zancen Sagir na cewa Allah ne ya kawo musu mafita yana sake samun muhallin zama a cikin ransa domin zancen ya zauna daram yaƙi barin cikin tunaninsa. Juyar da fuskarsa yayi gefen gadonsa ya ƙurawa wheel-chair dake gefen gadon ido lokaci guda zuciyarsa ta sake raunata a fili ya furta.
"Ya Allah kafini sanin dai-dai kuma komai kayi dai-dai ne ya Allah na fawwala komai na a gareka ina roƙanka daka karkatar da zuciyata izuwa abunda shine yake mafi dai-dai a gareni, Ya Rabbi mujibul mudtharra idha da'a, Inni mudtharra wa qad da'autuka Fa'ajibni" yayi ta nanata wannan addu'ar yana mai ƙan-ƙan da kansa wajan ubangiji. sannan ya jawo wheel-chair ɗinsa zuwa jikin gadon a hankali yaja jikinsa yahau kan keken cikin yanayin nutsuwa da sanyin jiki yake murza keken har izuwa bakin ƙofar da zata sadashi da toilet. hannu yasa ya buɗe ya shige ciki bai ɗauki lokaci sosai ba ya fito da alamu alwala yayi. saida ya saka jallabiya sannan ya isa izuwa kan Sallaya daga zaune akan wheel-chair yafara Qiyamul layl. Yana roƙon ubangiji akan alkahiri a cikin kowane lamari. Bayan yayi sallar maimakon yayi kokarin komawa bacci sai ya ɗauki alqur'ani yafara rerashi a hankali cikin wata iriyar murya mai zaƙin gaske yanayin yanda yake rero ƙira'ar ya bayyanar da zaman da Qur'ani yayi akan harshensa ma'ana shi ɗin ya kasance ma'abocin karanta alqur'ani ne, A hankali yake karatun iya wanda yake ɗakinne zai iya jiyoshi. Sai da aka fara kiran sallah sannan yayi Raka'tayl fajr ya fita zuwa masallaci. Koda ya ida sallar bai dawo gidanba har saida gari yafara haske.
Misalin ƙarfe bakwai ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin farar shadda sannan ya gyara black shiny curly hair ɗinsa da yake da yalwar tsayi har izuwa wuyansa, A al'adunmu bamu saba ganin namiji da gashi har haka ba, baza'ayi tunanin gashi irin haka zaiyiwa namiji kyau ba sai dai nashi ba ƙaramin kyau yayi masa ba, rubber band ya saka ya tufke gashin dake kansa sannan ya ɗauki hula mai kalar haske ya ɗaura akansa gabaki ɗaya ta rufe sumar babu wanda zaiyi tunanin akwai wannan gashin a kansa. Sai da ya kammala shiri sannan ya ɗauki wayarsa ya canja wheel-chair ɗin zuwa mai amfani da na'ura, ƙai tsaye ya dannata ya fice daga ɗakin duk yanda ya ratsa sai ƙamshinsa yayiwa wajan dabaibayi ƙamshine mai sanyin da daɗi sosai kuma baida ƙarfin ɗaga Hankali wani irin ƙamshine wanda koda wasa baza'a tsinci makamancinsa a wani waje ba. sai da ya ratsa palours guda biyu ma'aikata kawai yake wucewa kasancewar sanyayyar safiya ce iyalan gidan basu kaiga tashi ba, ma'aikatane kawai suka fito domin gudanar da ayyukansu. Duk yanda ya wuce sai sun tsaida ayyukan da sukeyi sun gaidashi, cike da fara'a sosai da sakin fuska yake amsa musu sam babu alamun wani jin kai ko girman kai a tattare dashi. Saida ya ɗanyi tafiya kafin ya shiga wata hanyar da zata sadashi da ainihin main cikin gidan. Gabaki ɗaya ginin gidan babu tudu ko gangare ta iya yiwuwa anyi hakanne saboda shi domin hakan ya saukaka masa wajan tafiya da wheel chair ɗinsa.
Wata matashiyar matace zaune a palour wacce bazata wuce shekara Arba'in da biyar zuwa da shida ba amma idan ba an faɗi shekarunta ba baza'ayi tunanun takai hakan ba domin sam basu nuna a jikinta ba kyakkyawar macece sosai sam batayi kama da hausawa ba suna matuƙar kama da Hammad sosai. Da Murmushi takai kallonta izuwa ƙofar shigowa domin ƙamshin Hammad ya sanar da ita yana kan hanyar shigowa yanda take. takai kallonta ga ƙofar Babu jimawa Hammad ya buɗe ya shugo akan kekensa da bai cika amfani dashi ba sai idan zai fita, A lokacin data ɗaura idonta akansa fara'arta ta ƙaru sosai hakwaranta sai haskawa suke samm takasa rufe bakinta har ya ƙaraso gaban kujerar da take zaune. Shima murmushin yake harya ƙaraso cikin muryarsa mai ɗauke da kwarjini ya gaisheta amsawa tayi ta kamo hannunsa tana ƙare masa kallo cikin yanayin ɗan damuwa tace.
"Hammad habibi naga idonka sun canja kamar baka Samu bacci jiya ba akwai yanda yake maka ciwo ne?" tayi maganar a lokacin da damuwar kan fuskarta take ƙaruwa, sannan yanayin yanda tayi maganar ya nuna kamar hausa batayi ƙarfi sosai a bakinta kamar yanda tayi a bakin Hammad ba, girgiza kai yayi yace.
"A'a Mami babu yanda yake min ciwo ki kwantar da hankalinki domin na kwana biyu banji ciwon ko'ina ba" ya faɗa yana shafa hannunta dake kan fuskarsa, ajiyar zuciya ta sauƙe sannan tace.
"Toh menene ya hanaka bacci?"
"Babu komai Mami nayi wani aikine" ya faɗa sannan yayi saurin canja zancen da faɗin.
"Mami breakfast ya kammalu?" ya faɗa yana juyawa zuwa dining saurin miƙewa tayi tabi bayansa har zuwa dining ɗin. Nasa breakfast ɗin tafara haɗawa sannan itama ta haɗa nata ta zauna kusa dashi. Tare suka karya, yana cin abincin cike da kulawa domun shi sam baya son datti bare kuma a jikinsa. Bayan ya kammala har harabar wajan motoci Mami ta rakashi sai da taga fitarsu daga gidan sannan ta dawo. Yau Mami ta tsinci kanta cikin farin cikin ganin Hammad ya shirya a wannan lokacin ya fita wajan aiki."
AL-MALIK LAW FIRM.
#ZEE ALABURA
#LIKITAN-RUHI
#SOYAYYA
#ƘADDARA....