ƊABI'A KO HALITTA

ƊABI'A KO HALITTA

by @fatimaoumshaheed479

*DABI'A KO HALITTA*




Free book....


Shafi Na 1



*Gajeren labari mai ɗauke da tunasarwa, ilmintarwa, wa'azantarwa, nishaɗantarwa, nuni ga wasu kurarai....*



_yadda na fara lpy Allah ka bani ikon kammalawa  lpy cikin Amincin ubangiji, Allah y bani ikon Rubuta daidai y habeni da rubuta ba daidai ba_


Dedicate to ƴan Amana ta *KUMIN UZIRI GROUP FANC*....




   "wai meye hakane Ajmal kakeyi? So kake sai kowa y fahimci me ake ciki, bayan gulmar banza wanan abun gaba ɗaya kai akama gata ba wani ba ka tsaya ka durji...." Sameer be idar da abun da yake son idar wa ba, Ajmal ya dakatar da shi d cewa.

  "uban me zan Dirja, malam kar ka ƙarasa Aman kalaman ka, bacin kasan komai, ko so kake muta maimaita zance ɗaya?"

"Hmmm, Nifa n fara gajiya d halin ka, inajin sai na barka da mai gayya mai aiki wato, Mommah" Sameer Y firta Yana shirin barin wajen da, Ajmal yake.

Da sauri Ajmal y kamo hannu Sameer ɗin ƴa fara Mai wani kallon firgita da na hango kwance a idanun shi da tun d aka ambaci sunan mommah ya tsinci kanshi da tsunduma ciki.

"sake ni malam, kai ba baka ɗaukan shawara ba, an san *halitta* ce kamar yadda kace ba *ɗabi'a* ba Kamar yadda mommah take ganin abun, to kai abun nan d akayi ba wani abu Allah ke nufin ka dashi ba, musamman in ka rungume shi hannu bibiyu kuma da kyakyawan niya, kasan me Allah zema a gaba? "  Sameer Y firta Yana sake tsare shi d idonduna masu nuna kulawa ga abokin nashi d kullin cikin tausayin shi yake...

Ajmal ne ya katse musu shirun da fita" toh Naji, Amman ka Dena nuna min zaka dinga sanar ma da mommah abun da yake faruwa tsakanin mu ko nida waccan.... "sai yayi shiru y dafe goshin shi... Alamun shi kaɗai yasan me yake ji duk lokacin d yayi tozali da ita ko y tuna ta ma a cikin rayuwar shi..

" to tashi muje mu sami su Uban shagali ayi komai lafiya taron nan ya watse lafiya, Kodan farin cikin da muka gani kwance a fuskar mommah" Sameer Y Ja Ajmal suka fita, kowa n mamakin yadda mommah yau ta saki fuska har tana fara'a da nuna ma ɗan nata tillon namiji cikin mata wata iriyar kulawa da ya rasa samun ta a baya tun bayan fahimta wata halitta a tattare da shi da ta fassara hakan da ɗabi'a wani lokacin ma ta kira shi da saɓanin haka.

Sosai waje ya cika y kacame da mutane maƙil sakamakon taron ɗaurin Auren da akeyi na tilo ɗan mommah da tillon ƴar Alhj Hafeez manufashi, Auren da ya kasance wani cukurkuɗaɗen makirci ne ya sa aka haɗa shi har aka kai ga ɗaura shi yau ba tare da shawarar ko wanen su Naso ba tsakanin Amaryar da angon, sai dan cimma wata manufa ta mutane biyu da ya kasance basu d abin da suka fi son gani kamar wanan Rana ta Auren kowannen su dan cikar birin su...


Haka aka gama ɗaura Auren Ajmal da Jumana  kowanne ɓangare na farin cikin saɓanin ango da Amarya da kowa na cikin fargaban be san me ze tarar ba.

****
  "yeeee An ɗaura! An ɗaura kin zama matar..... Wama sunan angon ku tuna min gulma da miya har n manta sunan shi" furuci wata daga cikin ƙawar amarya daga cikin masu  zumuɗin kai ta ɗakin ta.

Amarya kuwa tunda taji ana shewa da guɗar an ɗaura ta nemi ragowar yaƙen da take yi ta rasa, sai ji tayi dama ta mutu a wanan ranar sai yanzu dake kokwanto shin wai da gaske ita ta amsa da bakin ta ta amin ta da Auren? Ko dai a mafarki ta amsa? Ita da za ace an kunce auren a yanzu shine abu mafi farin ciki da zata tsinci kanta a ciki..

"Jumana congrats, kin fita daga sahun mu, Muma Allah y nuna mana wanan Rana da zamu kara daraja kamar dai ke a yau" cewar shamsiyya.

Firgigit! jumana ta juya tana son sake tabbatar da abin d suke faɗa, da ƙayar bakin ta ya iya firta "Wai da gaske kuke ba mafarki nake yi ba, dan Allah kuce mafarki ne ba gaskia bane, Nifa bance Ina son....." ji tayi Aminiyar ta da take jinta kamar ƴar uwar ta, tasa hannu ta toshe mata baki tana cewa.

"ki rufa mana asiri jumana, me kike shirin yi? Wai dama baki ɗauki shawara ta ba na ki dena furucin bakya son auren? So kike magauta suyi mana dariya bayan kin san komai shiryaye ne shirya shi akayi dan a cutar da ke, ni kuma ta ko ina Alkhairi na hango miki cikin wanan ƙadararen lamarin..... " jumana ce ta katse t da cewa. 

" ina Alkhairi yake haly ina yake ni kullin cikin haƙuri da uƙuba zan ƙare bani da gata ko na sisin kwabo, Aure fa? Aure da wanda ban sani b, ni bansan lokacin ma da nace na amince ba ni fa sharri aka min ke kika hanani magana " sai Jumana ta rushe da kuka mai taɓa zuciya..


Wata mata ce hamshaƙiya dirariya wacce taci ta tada wuya da naira ta shigo jikin ta duk gwala gwalai Ga wani tsadaden leshi a jikin ta, da ganin ta cikin zallah farin ciki take tana ta nishaɗin da bazaka gane daga zuciyar ta yake ba ko iya na kan fuskar ta ne, ta ƙaraso, kawayen Amarya Nata Mata sannu, sai mabiyan ta su huɗu da suke take mata baya suna ta zuba mata kirari...


 Gaki Amaryar Alhj marigayi Gaki Uwar Amarya, Kuma Amaryar ƙanin Alhj da komai ya dedeta, sannu ki uwar marayu, masu iyayen ma kece uwar su, sugari bakiyi farin banza ba, tattabara uwar alƙawari yau ga amanar da kika riƙe kunzo rabuwa, wani abun ma sai dai mu ce..... Ba a barta ta ƙarasa ba ta hannu damar uwar Amarya ta tsai da ita. 


"ya isa haka kar kiyi Sara a gaɓa, abar uwa ta gana da ɗiyar ta tillo ƴarta mace da Allah y bata mai ƙani Abeed da yayi nesa da su...." 

"Dota kiyi haƙuri haka Aure ya gada nima lokacin d aka bani mahaifin ki ban san shi ba, kuma gashi y zamar min Alkhairi, Ina baki umarni da kima mijin ki biyayya fiye da yadda mahaifiyar ki tama mahaifin Ki shine ribar ki a duniya da lahira..." tana mai nuna kulawa ga amaryar, da jin furucin ta yasa tayi saurin ɗagowa a karon farko don ganin itace mai wanan kalaman ko daga bakin wata hakan yake fitowa. 

Sosai ta shiga mamakin ganin ita ce dai mai wanan kalaman da ta rasa a mizanin da zata sa su... 

Kuka ta sake rushewa da shi, Kukan da ya kasan ce daga zuciyar ta yake fitowa, kowa kuwa na wajen gani yake kukan rabuwa ne da iyaye da kuma kukan sabuwar rayuwa da zata shiga ta gidan Aure saɓanin mutane uku a wajen da kowa da tunanin irin kukan da Amaryar take yi... 

Nan dai kowa ya ta mata nasiha da ban haƙurin da bama jin su take ba bare tasan zata iya amfani da su ko bazata iya ba. 


Wunin ranar komai bata kai bakin ta ba sai da ƙyar ƙawarta kuma Aminiyar ta haleemah (halee) ta sata sukaci shima sai da taga tayi fushi Sanan, tayi kuka na rasa mutane masu matuƙar mahimmanci a rayuwar ta a yau da ya kasance ranar da yafi da cewa tayi murna da farin ciki Amman sai taji kamar ranar da ta rasa mutane masu mahimmancin ce ta sake dawo mata dan haka aka kasa gane kanta, wasu suke ɗauka duk saboda Auren ne da ke war barin gida. 



******
Ajmal yau itace Ranar da nake tunanin zan samu salamar rayuwa daga gareka har n dinga nuna maka kulawar da kake min ƙorafi a baya, wanda har ka raba so da shaƙuwa da ƘAUNA irin ta uwa ka ba wata uwar bani ba ni kuma ka barni da rabi ne ma ko kwata zance... "ɗagowa Ajmal yayi yana kallon mahaifiyar tashi da rabon d yaga fara'a a fuskar ta yafi shekara ashirin, sai yau da suka ƙaƙaba mai Auren da bai da niya ko ra'ayi, har zeyi magana, sai Abokin shi Sameer ya taɓa Shi alamu kar yace komai. 

" zaman ka da matar nan shine ze zama sharaɗin yafiyar da ka jima kana nema daga gareni ka zauna d ita da ɗaɗi babu daɗi shine sharaɗin yafiyar, in har kamin haka na yafe maka duniya da lahira in ko aka sami a kasin haka to banya...." 

Da sauri Ajmal da Sameer suka ɗaugo suka zuba ma mahaifiyar tashi ido da take a matsayin mahaifiyar ango... 

Idanun angon Ajmal Har cikowa yayi da ƙwalla gashi y kasa firta ko mai .... 




Like and share... 



***