ƊABI'A KO HALITTA

ƊABI'A KO HALITTA

by @fatimaoumshaheed479

*ƊABI'A KO HALITTA*





Free book....



Shafi Na 3



Maman shaheed (Fatima Abubakar)




       
       _jumana_
Tun da aka ɗauko amarya take kuka na zuci da na zahiri har za a tafi da ita wani matashi ya zo gaban motar yace "ku tsaya dan Allah zanyi magana da Amarya" Jumana na jin muryar shi ta fito da sauri tazo inda yake bata jira wata wata ba ta faɗa jikin shi ya rungume ta suna ta kuka a tsakanin su kowa ya tsaya yana mamakin Ganin shi a wanan lokacin da zuwan shi kenan ko gida be shiga ba ko mahaifiyar shi be nema ba sai ita, mahaifiyar shi kuwa da ta kasance uwa ga Amarya mutuwar tsaye tayi mamaki ze kashe ta dan bata yi zaton zasu haɗu ba kamar yadda ta tsara komai, sai gashi ya bijire mata ya dawo a yadda ba tayi zato ba.

"sis Jumana kiyi haƙuri da komai nasan kin fahimci mai nake nufi, Auren ki khairan Insha Allah, Ina miki fatan Alkhairi da neman da cewa....." be ƙarasa ba yaji ana fizgo shi ana ƙoƙarin raba jikin shi da n amaryar.

Itama ji tayi na ƙoƙarin raba su, rabon da ta sami jikin da zata faɗa tayi kuka mai isar ta koda baza'a rarashe ta ba har ta manta, sai yau da ta samu na ƙanin ta suhail da aka nisanta tsakanin su, sai yau da aka rabata da gidan mahaifin da d sunan Aure.

"suhail nagode kuma Naji zan ƙoƙarta in Sha Allah, dan Allah kafin ka tafi kazo in sake ganin ka koda shine ganina da kai na ƙarshe dan Allah" ta haɗe hannu biyu tana sake rushewa da sabon kukan, lokacin d akaci nasarar raba su.

"kai kana hauka ne, matar wani ce fa, ka kusan kun girma bane kai da ita, kuna ka sake kaje gidan ta kayi kuskuren da kayi yanzu n haɗa jiki da ita sai mijin ta ya gwada ma hauka dan baida seti akan ta, mahaifiyar ka kawai zaka gwadama wanan tausayin da jin ƙan, ba wata bare ba, dallah mu tafi"wata yayar hajiyar Shi ta ja shi.

Hajiya kuwa ta cika tayi fam duk annurin fuskar ta ya gushe y koma tsananin ɓacin Rai, shigo sai wagen motar su Jumana yake yi.

Itama har aka shiga da shi tana kallon shi.

Wasu daga ƴan uwan hajiyan shi ne suka dinga mai faɗa, akan y dinga gudun duk abin d mahaifiyar shi zata yi fushi da shi, har hajiyan ta fusata ta fara magana "Ku rabu da shi ai har yanzu besan ida yake mai ciwo ba Amman da sannu zan ganar da shi yanzu, kai ban isa na baka umarni kabi ba ko? Yau nace kazo ko sai gobe? Yaro sai kafiya da taurin kan masifa, bansan wa ka gado ba wallahi, inajin sai dai ubanka, to ko shi sai da na seta mai ɗaurarun notinan da suka sa kan shi yake tauri sukayi laushi luguf, Dani kake zancen"fuuuu ta nufi ɗaki. 


"shi ko duk be damu da fushin uwar ba hankalin shi na kan ƴar uwar shi musamman d yaji auren da aka mata baso take ba, ya rasa meye matsalar hajiya meye take taƙama da shi, ko shi wani lokacin tana tauye mai haƙƙi da sunan nuna bambanci da kulawa da ninka so da take mai, shi kuma be taɓa ganin hakan ba ko kuɗin da take bashi be taɓa ganin hakan a matsayin so ba sai dai yana ɗaukan hakan matsayin gatan nesa, ba gatan cikin gida ba, Amman ze rabu da ita ya fara rayuwar shi duk yadda yaso kome ze faru sai dai ya faru, tun da taƙi fahimtar yafi son kusan ci da ita a matsayin ta na mahaifiyar shi, ita kuma kullin nesan ta shi take da ita da tun yana tunanin ko da Jumana take haka to ai yanzu tayi aure, anan dai ya sha alwashin matuƙar Bata barshi ƴa dawo gida ba to she buɗe shafin sabuwar rayuwa tunda haka ta tsara mai... 



    _Ajmal_
Tun da ya fara jiyo guɗa da hayaniyar ƴan kawo amarya ya sake jin ɓacin ran shi ya ninku dan haka ya bar falon ummah zuwa ɗakin shi da ke daga shigowa harabar gidan.

Yana fitowa daidai d a shigo da amarya, be ganta ba bata matso inda yake ba, kawai alkyabbar da aka rufe ta da shi ya gani ba tare da yaso hakan ba, Amman sai da wani babban lamari ya kawo mai ziyara da ya rikita lissafin shi ya kuma kasa gane dalilin haka, da sauri y ƙarasa ɗakin nashi ya turo ƙofa kamar Ance mai nan za'a kawo ta, yana sauke wani gajiyayen numfashi. 

Bayan an shigar d ita, su Sameer suka zo suka same shi a kwance alamun yayi nisa cikin tunani, yin duniya y fito yace "sai sun bar gidan" ganin ba fitowar zeyi b suka rabu da shi. 

Sosai momah ta ƙarɓi Jumana da fara'a Har ummah ma kowa nata murna har da kyautu tukan turaren da kuɗi aka ba amarya, suka tashi aka nufi gidan ta da ita....

Sosai mutane suka tafi kai amarya duk an tafi da yawa har su hussy d safna...

Sameer Ne Kawai d shadow suka rage, suna jiran su tafi da ango in mutane sun ragu dan sun san sai sunyi fama kafin ya yadda su kai shi,..

"ni dai wlh macce nasan ake ma Auren ƙi tana gocewa Ana sai an kai ta, to yau ga mutumin ma dai yana neman ɓata mana shagali Wan dinner, Gara Iya Gara Amman...." shadow be ƙarasa Amman kalam shi ba, Sameer yace.
"dallah malam Wai kai wanne irin ɗan iskan ne mai tada zaune tsaye, baka so a zauna lafiya, ko ba gara ba? Banza kawai ɗan ka iss.." 

Ƙwafa kawai Ajmal yayi, ya fara cire babbar rigar jikin shi dan ji yake beƙi su barshi ya kwanta ba a nan har ya kwana ma, shi ji yake kamar suna neman ɗaura mai dala babu gammo ne. 

" Ajmal Dan Allah meye haka kake yi to meye na cire rigar kuma? "Sameer ya tambaya. 

" zan huta ne kafin na mayar "Ajmal y bashi amsa. 

" Hmmm, Ai ka kusa mayarwa da sa'ed ya dawo zamu tafi " in ji Sameer. 

      _jumana_
An Kai Amarya gidan ta kowa na yaba gidan dan an kashe mata kuɗi saboda ubanta ya tara kafin ya koma ga mahalicin shi, wasu ma ƴan kawo amarya har an mayar da su gida, sai tsiraru, Hassana da Hussaina da safna da Safiyya, Wai sai an kawo yayan su zasu tafi, sai y rage a dangin miji sune kawai suka rage. 

Dangin Amarya ma dangin mahaifiyar ta ne ƙarshen tafiya bayan sun mata nasiha da rarashi, sai ƙawayen ta su biyar aminiyar ta haleema (haly) na gefen ta tana ta aikin gyara mata fuska da bata baki itama sai zakiyya da take taya ta sauran ko cewa suke a barta tayi kuka aure is not easy, ga shi ta rabu da wata rayuwar bata san wacce zata faɗa ba. 

Haly ce ta ce "wai meye haka dan Allah kukyi, in ba zaku rarashe ta ba kuja baki kuyi shiru, ko wacce ba aure ne d ita ba cikin ku har me kuka sani a auren da zaku wani abu? Ku tsaya a falo inda ba khairan zaku faɗa ba pls" suka tashi kuwa suka koma falo, suna cewa "abar mu mu gaya mata gaskiya dai, ai ba sai munyi ba nawa muka gani muka ji labari" 

Su hussy ne suka shigo suna ta murna suna son ganin fuskar Amarya, zakkiya ta buɗe musu dan taga suna ta ɗokin Amaryar, suna ganin ta kuwa cikin hawaye shaɓe _shaɓe Amman a tare suka haɗa baki wajen yabon kyan ta da ma Auren nasu Addu'a, sai hakan ya birge haly da zakiyya. 

Wayar safna ce ta fara ringing tana dubawa taga ya Ajmal ne, da sauri tace "laa yaya ango ne" 

"hello yaya Kuna Ina MU kufa muke jira d ƙawayen Amarya" 

Daga ɓangaren Ajmal MA cewa yayi "kuna ina? Kun san bakwa kaiwa dare haka a waje ko? Maza kuzo gida yanzu" 

Safna Sai ta kwaɓe baki kamar zatayi kuka ko irin na shagwaɓaɓun nan "yaya yau fa ranar mu ce dan Allah please yaya promise, Kuna Zuwa zamu tafi, sorry yaya kar kace a'a please kaji yaya" baya son su dinga mai magiya duk yadda yaso hana su abu dole yake barin su Kodan yadda suke girmama shi da jin maganan shi da yadda yake jin sauƙi ta gefen su d kore mai damuwar da mommah take yawan saka shi. 

"OK, ku nutsu, ki faɗa ma biyun nan masu rawar kai, sai Sameer ƴa mayar da ku" ya bata amsa. 

"yauwa yaya yanzu zaku taho ko? Dan dare nata yi...." be bata amsa b ya katse kiran. 

Tabi wayar da kallo tana dariya dan dama tasan bazata samu amsawar shi ba. 


Sosai ganin yadda yake ma ƙanen shi ya birge zakkiya da haleema, banda Amarya da ba komai take ganewa ba duk da taji maganar da sukayi da ƙanwar shi sai ma tsanaita faɗuwa da gabanta yakeyi . 


"yauwa sorry Amaryar mu ga angon ki nan zuwa" safna ta furta cikin farin ciki da nishaɗi. 

Sai ko haly ta sake gyara ko ina da saka turaren wuta mai ƙamshi, su hussy ma suka taya su gyara ko ina. 

"oya tashi ka canja Kaya malam dan wallahi ba zan ɗauke ka da wanan yamutsatsun kayan ba a ganka kamar wanda aka ƙwato daga bakin kura ranar angwancin ka guda" Sameer ya ba Ajmal umarni. 

"kai babu abin d zan canja uwar mai zan maka ko aikena akayi a daren nan da sai na canja kaya" Ajmal ya firta yana sake gyara kwanciya. 

"a'a kawima fa sameer ka fiye Sanabe Ko a haka ya tashi mu tafi ina abun da ya yamutse anan mutumin da ba kokuwa yayi ba, kasan fa sunan mutum a lalaɓa auren zamani ka bari mu tafi kar ya ɓotsare...." be idar ba, Ajmal ya taso a zuciye ya buga mai filo, yana huci Har cikin ran shi shadow yake ƙular da shi. 

Sameer ko yana cin daɗi kunna shi da yake aranshi a zahiri kuma sai ya nuna baya kyauta wa, dan Y rasa ya zema abokin nashi. 

Da gudu shadow yabar ɗakin Yana dariyar Mugunta, dama haka yake so. 

"Bro yi haƙuri dan Allah mu Dena abu guda mufa ba yara bane, Kaga sa'ed ma yana kira na nasan sun juyo tashi ka canja mu tafi, yi haƙuri nasan sai an cuci mutum ake bashi haƙuri Amman babu yadda zamuyi yi haƙuri mutumin tashi dan Allah" 

Badan yaso ba ya fara shirin saka babbar rigar, sameer ya riƙe yana girgiza mai kai ya karɓe ya ninke ya ajiye a gefe ya buɗe drower ya ɗauko Mai wani farin yadi mai taushi da kyau ya miƙa mai.. 


Ƙin karɓa yayi sai ma cewa da yayi "kai wallahi....." sameer yayi saurin rufe mai baki ya fara mai magiya da rarashi kamar ƙaramin yaro, har sa'ed ya shigo, da shadow, Aiko sameer ya  kora shadow waje suka haɗu da sa'ed sukai ta bashi Baki had ƴa canja kayan, akace ya fesa turare yace, bai da shi, sameer yace "Muje mota ni ina da shi, duk ta inda ka billo Ai zamu toshe, gidan suka koma suka ma mommh da ummah sallama, ummah har mota ta rako shi tana ta shafa shi da shimai Albarka, idon shi tab da ƙwalla. 

Mota ko sai da aka raba musu mota da shadow, dan Ango cewa yayi sai dai a kaima Amarya shadow Ba Dai Shi ba, indai be bar motar ba, dole sameer ya canza mai mota suka tafi da sa'ed. 


Kafin ango y fito a shiga gidan ma sai da aka ci kwakwa, dan sai da shadow ƴa fara tsokana Shi ya fito a fusace, shadow ƴa gudu, Yana mai gwalo. 

Suna shiga wani ƙamshi y daki Hancin su, sai shadow Yace "Anyi tuya fa an manta da Albasa, gida iya gida ango iya ango, Amarya iya amarya da zamuje mu tarar Amman banga tsarabar ledar da Ango ya sabo shigowa da ita ba da kayan shaye_shaye...." sameer ne ya bashi amsa da, "kai dai akwai munafuki wallahi to mu mun gama komai ko da kai za'a jira" 

Ajmal Har ya tsaya da tafiyar d yake, kamar mai shirin yima shadow wani abu, sameer ya riƙe shi yana bashi baki akan kar ya kula shi, dan duk sun san halin shi, barkwanci ne da shi acikin su duk yadda suke cikin ɓacin rai in suka haɗu Sai ya kular da mutum ko ya bashi nishaɗi, kuma yana da kirki kuma duk abokanai ne, gashi cikin tsokana ze faɗa ma gaskia. 

Bayan sun zauna a falo, hussy suka fito suka zo wajen su, suka fara mai sannu da zuwa, kafin su cika shi da surutu ya kamo hannu safna yace "maza ku wuce ku tafi gida sameer ze mayar da ku, kar ku bari na sake muku magana" duk yadda suka so suyi hira ganin kamar baya farin ciki kuma sun san komai, sai ma tausayi da ya basu, sai suka mai sai da safe, shima ya musu, sameer yace su jira shi a mota.



***