SHA DAYA
by @zeeeyybawa
LIKITAN RUHI
Na
ZAYNAB BAWA
Arewabook @Zeeeyybawa
SHAFI NA GABA
Misalin ƙarfe biyu na rana Hammad ya baro babban kamfanin da yake jagoranta, Al-malik Law Firm domin komawa gida a motarsa, A lokacin rana tana tsaka a sararin samaniya, haskenta da zafinta suna haskaka gabaki ɗaya illahirin garin Zari'a. Hammad danna wayarsa yakeyi a seat na baya da yake zaune amma a zahirin gaskiya tunani ya lula, tunanin yanda duniyarsa ta juya lokaci guda, tunanin yanda yake a shekarun baya kafin jinya ta cimmasa, Hammad ba irin ragwayen mutanen nan bane da suke wasa da aiki ba, baya barin wajan aiki da wuri saboda gajiya, A'a. ba haka yake ba kowa ya sanshi kusan koda yaushe shine ƙarshen barin ofis masu gadi kawai yake bari a wannan ma'aikatar sau dayawa bayan magrib ne lokacin barinsa office, Duk ranar da Hammad yatashi aiki tare da ma'aikatansa toh shakka babu wani aikine ya cimma ma'aikatan har suka kai wannan lokacin. A ganinsa barin ofis kafin magrib tamkar karya ka'ida aiki ne, ka'idar da shi da kansa ya ginata, ya kuma ɗora rayuwarsa a kanta. A lokutan da yake cikin cikakkiyar lafiya, ba ya barin ofis har sai rana ta faɗi, bayan ya tabbatar komai ya tafi yadda ya tsara, sannan ya bar ma'aikatan tsaro kaɗai su rage a kamfanin, suna kula da komai a madadinsa.
Shi jajirtacce ne ƙwarai a fannin aiki. Ba ya tsoron nauyi, ba ya guje wa aiki, kuma ba ya mika wuya ga kasala. A wurinsa, shugabanci ba kujera ba ce kawai nauyi ne da aka dora shi kansa Shugaban. Dalilin da yasa ake girmama Hammad ba wai don dukiyarsa ba ce kaɗai, sai don yadda yake tafiyar da ita cikin hikima, tsari, da hangen nesa.
Gashi a yau, dalili yayi dalili ya sanya yana barin ofis da wuri, har indai ya samu halartar office dinma kenan, Idan ba rashin lafiya ba, Hammad sam ba ya nuna rauni, koda zuciyarsa ce ta buƙaci ya huta. baya hutawan.
Motarsa tana tafiya cikin nutsuwa a titin da zai sadashi da gida, iska mai ɗan sanyi haɗeda zafin rana tana shigowa ta gefen taga da ya ɗan buɗe. Drivern Hammad yana tuki ne ba tare da gaggawa ba, domin Hammad baya buƙatar gaggawa a duk lamuransa yakance abi komai a sannu jajircewa kawai yafi buƙata. idanuwan Hammad suna a kan waya amma zuciyarsa tana wani wuri daban. Akwai abubuwa da yawa da suke zagaya masa a ƙwaƙwalwa
Motar Hammad tana shiga layinsu. gidansu ya bayyana daga nesa babban gida ne, wanda girmansa ya zarta kaff gidajen layin yana da ginshikan gini mai cike da ƙawa da ɗaukar ido."
AL-MALIK RESIDENCE
Gidan yana nan tsaye tamkar ƙasaitacciyar alqarya a tsakiyar anguwar. Wannan ba gida bane irin na ƙasashen mu nan ba, gini ne mai ɗauke da al'adu na Larabawa, Gate ɗin gidan yana da girma da faɗi tamkar mashigar wata masarauta, Gefe da gefensa akwai manya-manyan ganuwar da suka tsaya masa tamkar garkuwa. ginannun wall din fararene tass masu sheƙi, sannan an yi musu ado da launin zinare a kowane kusurwa.
A gefe akwai sashe na security ma'aikata masu tufafin Kaki suna tsaye suna sa ido.
Yayin da motar Hammad ta zo, security ya riga ya buɗe gate don tun kafin driver ya danna horn. Daga nesa ma sunga motarsa ta cameras na tsaro da suke manne a kowace kusurwa ta gidan
Motar ta shige cikin harabar gidan mai azabebben girma dake shimfiɗe da furanni kala-kala. A gefe-gefe akwai manyan bishiyoyin furanni suna fitar da wani kamshi mai tsabta da natsuwa wanda ya mamaye dukkan illahirin harabar gidan. babban katafaren gida wanda tsarin sa ke ɗaukar ido nan take. An yi ginin da salo na Larabawa, A saman ginin, akwai manyan verandah masu hawa biyu, inda aka ɗora kujerun lounge masu launin zinariya na fata mai laushi, suna kallon lambun da ke kewaye da gidan.
Lambun gidan cike yake da furanni masu kamshi, kamar rose mai ja da fari, jasmine, lily, tulip da lavender. Ana jin ƙamshinsu mai sanyaya zuciya koda daga wajen harabar gidan. A cikin lambun akwai titunan dutse masu kyau da aka tsara daidai, suna kaiwa zuwa wuraren shakatawa da fountains masu tsarkakakken ruwa, inda za a iya jin sautin ruwun dake bayyanar a hankali. Akwai kuma shingayen bishiyoyi masu inuwa wadanda ke ƙara sanyi da kwantar da hankali a wurin.
A gefen dama kuma kawai wata veranda ce ta akayi mata gini mai cike da ƙawa da kujerun lounge na fata masu launin Baƙi an ƙawata wajan sosai yana da girman da zai iya dauƙan mutane a ƙalla ashirin ko sama ta haka, tagogin wajan gabaki ɗayansu na gilashi ne da yake bawa hasken rana damar shugowa da view na furannin dake garden ɗin dake zagaye da wajan.
A gefe guda na harabar gidan, akwai lambu mai girma wanda ya cika da bishiyoyin kayan marmari iri-iri, lambu ne da kallo kaɗai ya isa ya sanyaya zuciya domin dai an tara ni'imar Allah a wuri guda, sabida kusan kowace irin bishiyar marmari da mutum zai buƙata, suna nan babu wadda babu a wannan lambu. Daga mangwaro, zuwa lemun tsami, lemu mai zaƙi, ayaba, dabino wanda shi nasa gefen na dabanne dan a ƙalla bishiyoyinsa sun kai guda ashirin, guava, apple har da rumman duk suna cikin wannan lambu, Iska idan ta ratsa cikin lambun, sai ƙamshin ganyayyaki da furanni ya gauraye da ɗanɗanon 'ya'yan itatuwa, yana cike sararin da wani irin salama da ba a baki bazai iya bayyana ta ba. Wannan ba lambu na adon bane kawai lambu ne da ke nuna yadda gidan ke cike da albarka da yalwa komai.
Gidan yana da ma'aikata masu yawa, masu tsaro a gate, masu lambu da suke kula da furanni da bishiyoyi, masu girki da masu hidimar daki da sauran ayyukan gida. Kowannensu yana da sashi na musamman, wato kowane ɓangare na gidan yana da ma'aikata da ke kula da shi kai tsaye. Misali, akwai wani sashi na musamman da ake kira "Garden Unit" wanda ke kula da lambu da furanni, sannan akwai "Household Unit" da ke kula da daki da falo, sai "Security Unit" da ke lura da tsaro. Kowanne sashi yana da ma'aikata masu ƙwarewa, kowannensu suna cike girmama wanda suke yi wa aiki kamar gasa haka sukeyi kowa burinsa shine suyi aiki da yafi na ɗan uwansa.
_______
Akwai driveway mai girma ya ɗan faɗi, wanda ke bawa motoci zuwa harabar gidan cikin sauƙi, babu tudu ko gangare, wanda ke bai wa Hammad damar tafiya da wheelchair ɗin sa cikin sauƙi. Driveway Drivern Hammad yabi har izuwa ƙofar da zata sadashi da cikin gidan tsayar da motar yayi ya fito da sauri ya buɗe butt sannan ya cirowa Hammad Wheelchair ɗinsa yakai ƙofar da Hammad yake zaune ya buɗe masa ƙofa haɗeda ajiye masa wheelchair ɗin, Hammad cikin sabo da amfani da its yahau kai, sallama sukayi da drivern ya fara tafiya har zuwa Babbar ƙofar palourn da a ƙalla mutum huɗu zasu iya wucewa a lokaci guda batare da sun matsi junansu ba.
Falon gidan babban wuri ne mai ɗaukar mutane da yawa, an yi shi da interiors na Larabawa, farin fenti mai sheƙi, a sama kuwa akwai babban chandelier mai haske wanda ke watsa haske cikin gidan. An saka kayan alatu kamar sofas da aƙalla sun kai saiti uku masu launuka mabambamta na fata mai laushi, teburorin dining an zagaye shi da kujeru masu ado da ƙyawu tamkar zinare. Window kuwa duka na gilashi ne masu sheƙi suna ƙara bayyana kyawun palour, sannan sun bawa hasken rana damar ratsa cikin gidan Duk wani ɓangare na gidan yana akwai tsabta, sannan yana yin gidan yana nuni kwanciyar hankali da mutanen da suke rayuwa a ciki suke da ita, inda duk wanda ya shiga zai ji kamar yana cikin wani babban sarauta.
Da sallama ɗauke a bakinsa Hammad yashiga cikin palourn babu kowa sai ma'aikatan da suke ƴan aikace-aikacensu, Sallamar Hammad ce ta sanyasu tsayawa da abunda sukeyi suka juyo suna gaidashi, amsawa Cike da fara'a da sakin fuska ya amsa musu domin sam shi Hammad baida girman kai kuma yana da fara'a, yana girmana hatta da shukar da take tsire a cikin gidan bare ɗan adam dake aiki a ƙarƙashinsa, hakan yana ɗaya daga cikin halayaensa shiyasa ma'aikatansa suke girmamashi, Hammad mutum ne mai sauƙin kai. ba ya jin daɗin hayaniya, ba ya son nuna iko a kan mutane. A maimakon haka, yana amfani da shiru da nutsuwa wajen sarrafa al'amura. Wannan ne ya sa ma'aikatansa ke girmama shi fiye da tsoronsa suna girmamashi kamar kowane mamallaki mai daraja duk kuwa da yana tattare da nakasa, suna girmamashi domin yana sa su ji suna da muhimmanci,
"Mami fa tana ina?” ya tambaya cike da sabo dsa sakin fuska, cike da girmamawa suka sanar masa tana ɗakinta. Juyawa Hammad yayi ya nufi ƙofar da zata sadashi da nasa sashin jin cewar Mami tana ɗakinta. Tunda yafara tafiya bai haɗu da kowa ba saboda ma'aikatan wajansa duk sun gama ayyukansu sun fita saboda shi bai son hayaniya. Daga palour ya canja wheelchair zuwa wanda yake amfani da ita a gida sannan ya ƙarasa zuwa ɗaki, yana shiga ɗakinsa jikin bed yaje ya ajiye wayarsa sannan ya cire hular kansa ya ajiye, hannu yasa ya zare rubber band daya ɗaure gashinsa dashi lokaci guda black shiny curly hair ɗinsa dake kama dana larabawan middle east ya babbaje wasu suka zuba a wuyansa yayinda wasu suka rufe fuskarsa hannu yasa ya sharo wanda yake fuskarsa yayi dasu duka baya sanna ya rage kayan jikinsa ya shiga wanka. tsaftace jikinsa yayi yafito mai ya shafa sannan ya sanya ƙananun kaya.
#ZEE ALABURA
#LIKITAN-RUHI
#SOYAYYA
#ƘADDARA..