SHA BIYU
by @zeeeyybawa
LIKITAN RUHI
Na
ZAYNAB BAWA
Arewabook @Zeeeyybawa
SHAFI NA GOMA SHA BIYU
A lokacin wayarsa tafara ruri ƙarasawa yayi bakin gadon ya ɗauki wayar anan yayi arba da sunan Mami yana yawo akan wayar murmushi yayi sannan ya amsa, sallama yayi ta amsa sannan tace.
"Hammad Habibi ka dawo ashe" tayi magana cikin sautin da yake nuna tana cikin farin ciki.
"Eh Mami na dawo jin cewa kina ɗaki ya sanya kawai na wuce domun nayi wanka"
"Toh shikenan ka shirya saika fito muci abinci kuma naji Hamrah ma tana nemanka tun tashinta da safe, na shaida mata kafita wajan aiki" Murmushin da yabi masa jiki yyi yace.
"Okay toh Mami na gama dama gani nan zuwa" sukayi sallama Hammad ya ajiye wayar domun ya ƙaras ashiryawa ya fita wajan Mami da ƴan uwansa.
Cikin nutsuwa ya ƙarasa shirin ya fito wajan mahaifiyarsa, Riga t-shirt ce a jikinsa sai wando wanda tsayinsa bai ƙarasa guiwa ba, sunyi matuƙar yimasa kyau, gashin hannunsa dana ƙafafunsa sun kwanta luff-luff sai sheƙi suke, haka ma gashin kansa sai sheƙi yakeyi. da sallama a bakinsa ya shigo palourn.
Mami yau ta wuni da jin daɗi a cikin ranta tunda Hammad ya shirya ya fice wajan aiki ta samu kanta cikin farin ciki, har ƙannensa saida ta sanarwa suka tayata. Mami tana son ganin Hammad yana walwala kamar kowa tana son ganinsa yana al'umuran rayuwarsa kamar kowane ɗan adam shiyasa a koda yaushe taga wani canji mai alfanu daga gareshi takan rasa yanda zata tsoma kanta saboda farin ciki. Ƙarasowa tayi kusa dashi ta tsugunawa akan guiwowinta ta dafa cinyarsa tana kallon fuskarsa da murmushi akan tata fuskar tace.
"Hammad Habibi ya wajan aikin? Fatan dai kaji daɗin fitar da kayi" kai ya gyaɗa yace.
"Sosai ma Mami bakiga hakan a fuskata ba"
"Tabbas nagani ɗan albarka” ta fada tana ƴar dariya. miƙewa tayi ta Sanya hannunta duka biyu a cikin gashin kansa mai yalwar cika da tsayi tace.
"Nakira su Hamrah yau duka suna gida tare zamuci abinci" Bata gama rufe baki ba suka fara shigowa da sallama, Abbad ne yafara shugowa da sallama a bakinsa Mami ta amsa batare da ta ɗago ta kalleshi ba tana cigaba da dai-daitawa Hammad gashin kansa shima Hammad amsa sallamar yayi.
Abbad ƙaramin yarone da bazai wuce shekara goma sha shida ba kyakkyawa sosai suna kama da Hammad shima gashin kansa curly ne amma nasa baida tsayi kamar na Hammad, da fara'a sosai ya ƙaraso wajansu Hammad yana faɗin.
"Barka da gida Yaya Hammad" Murmushin da ya zame masa jiki Hammad yayi bai kaiga cewa komai ba Mami tace.
"Ai yau yafita wajan aiki sai dai kayi masa sannu da aiki" Fara'ar fuskarsa ce ta faɗaɗa yace.
"Ah lallai Yaya Hammad yau kaji lafiya da yawa har wajan aiki kaje? Dana sani ai da zan tafi school na jiraka mun tafi tare kaga idan ka gama sai kabi ka ɗaukoni"
"Toh uban ƴan surutu rufawa mutane baki duk kabi ka cikawa mutane kunne da surutu" Nimrah wacce shigowarta kenan ta sameshi yana magana ta faɗa tana kaiwa karshen maganar ta tallafe kansa da mari. Sai alokacin Hammad yayi magana yace.
"Kinga fa ke sam bakida girma ko menene na dukan nasa" a lokacin Mami ta gama gyara masa gashin tace.
"Ai kaga wannan ita ke tsokanarsa babu dama su zauna waje guda saita takaleshi” Mami tayi maganar tana harararta, turo baki Nimrah tayi ta wuce kan dining a lokacin itama hamrah ta shugo da sallama. tafiya take cike da nutsuwa harda karaso wajansu Hammad dafa wheelchair ɗin Hammad tayi tafara turashi a hankali tana gaidashi cikin sanyayyar muryarta mai cike da ladabi da nustsuwa, amsa gaisuwar yayi yana faɗin.
“Mami tace kina nemana?”
“Eh Yaya Hammad, tun da safe amma tace kafita wajan aiki"
“Uhmm na leƙa wajan aiki me zaki faɗamin?” ya tambaya. tana tura keken a hankali tace.
“Muci abinci tukunna maganganun sunada yawa”
Kai kawai yayi nodding tacigaba da turashi. keken da Hammad yake amfani dasu sam basu buƙatar turi kusan duka da na''ura suke amfani ko wanda yake amfani dashi cikin gida ma dannawa kawai yake yana controlling ɗinsa amma ita Hamrah har indai tana wajan toh ita ke tura keken da kanta. Saida ta kaishi bakin dining ɗin dai-dai mazauninsa sannan ta zauna a gefensa. saida kowa ya zauna sannan Mami ta dubi Nimrah tace.
"Wai ina Nawrah take? Ita koda yaushe saita ɓatawa mutane lokaci? ayita jiranta, ayita jiranta hakan daɗine dashi?" Shiru sukayi suna sauraran Mami tana bambami duk sun san saboda wa takeyi sam bata jurar taga anbar Hammad yana jira. Sai ranta ya ɓaci tayita faɗa, idan kuma Hammad ɗinne ko jiran awanni zasuyi masa toh bazai dameta ba" da gudu-gudu wata ƴar matashiyar budurwa ta shugo palourn kamarsu ɗaya sakk da Nimrah hatta da kayan jikinsu iri ɗaya ne alamu ya nuna su kamar ƴan biyu ne. Ita kuma Hamrah itace Babbarsu. tana zuwa Hammad yayi saurin katse Mami saboda karta sake yin wata masifar. Su shida ne a zaune a table ɗin, Mami, Hammad, Hamra, Nimrah, Nawrah sai Abbad. Daga ganin wannan ahali za'a fahimci suna cike matuƙa da ƙaunar junansu sannan yanayin ladabinsu ƙwarai ya nuna tarbiyar da suka samu.
Gyaran Murya Nimrah tayi babu wanda ya kalleta domun sun san Mami sam bata son surutu wajan cin abinci, kuma hakan ya samo asaline harda rashin son hayaniyar Hammad a yanzu, kasa hakuri Nimrah tayi tace.
"Yaya Hammad kasan birthday Anty Hamra a wannan watan ne yau saura 10days dan Allah kace Mami tabarmu muyi cerebrating" Harara Mami ta watsa mata tace.
"Bana hana magana yayin cin abinci ba? Wato ke Nimrah ba'a isa ace kibari ba koh?" Mami tayi magana cikin hausarta wacce ƙarfinta bai kai na yaranta ba, Hammad ne yace.
"In sha Allah wannan shekarar za'ayi celebrating birthdayn kowa bana Hamrah kaɗai ba"
"Kai Hammad" Mami tayi magana cikin son katseshi, girgiza mata kai yayi yace.
"Mami dan Allah, tsawon shekaru kenan yanzu gidan nan ba'ayin duk wani abu da zai nuna muna cikin farin ciki, sufa yarane meyasa a kaina za'ayita tauyesu? Ni bana jin daɗin hakan Mami bana son kuna hana kanku walwala saboda ni" Mami zatayi magana yayi saurin faɗin.
"Ku gayyaci duk wanda zaku gayyata In sha Allah za'ayi cerebrating birthdayn Hamrah"
"Wai shi kansa birthday celebration dinma menene hukuncinsa a addini?" Dariya Hammad yayi bai bawa Mami amsar tambayarta ba wanda yasa Mami girgiza kai itama tana dariya kawai domin ganin wannan dariyar akan fuskar Hammad yasa taji bazata iya hanasu celebration ɗin ba. Hamrah nisawa tayi sannna tace.
"Nikam dai Yaya Hammad na yafe wallh bana son wani celebration menene birthday kuma Allah na tuba da har zakace ana tauyemu akanka? Ganinka cikin wani hali har akwai wata murnar da zan iya ne?" Ciro waya Hammad yayi ba tare da ya kalleta ba ya fara dannawa yana faɗin.
"Ni nace miki ina wani hali Hamrah?" Kasa bashi amsa tayi hakan yasa tayi shiru shikuma yaja kekensa yabar wajan yana danna waya ya nufi kujera, ya canja mazauninsa zuwa kan kujerar yacigaba da danna wayarsa sukuwa su Abbad me zasuyi idan ba murna ba anbasu lasisin yin cerebrating birthday. itama Hamrah tashi tayi ta dawo kujerar da yake zaune ta zauna a kusa dashi sosai domin magana takeso suyi bataso kowa ya juyosu. Ganin ta zauna yasa Hammad ajiye wayar da take hannunsa ya maida hankalinsa a gareta.
"Uhmm Yaya Hammad dama Yaa sageer ne ya kirani" Hammad dama tun ɗazu jikinsa yabashi hakan, tacigaba da faɗin.
"Dan Allah Yaya Hammad meyasa bazaka duba maganarsa ba sai inaji a jikina akwai alkhairi a yin hakan" Haɗe rai Hammad yayi amma ba sosai ba yace.
"Saboda yasan damuwar da kike ciki a kaina shine ya kiraki ya sake ɗaga miki hankali koh?" Riƙo hannunsa tayi tana shirin yin kuka tace.
"Dan Allah mana Yaya" Ajiyar zuciya Hammad ya dauƙe sageer yasan kaff gidansu Hammad yafi son Hamrah kuma yafi jin maganarta kamar yanda itama tafi sonsa shiyasa ya shugo da ita wannan lamarin.
"Toh naji zamu ƙarasa magana dashi" Lokaci guda fuskarta ta yalwata da fara'a tace.
"Dan Allah Yaya ka amince?"
"Naji, nace miki zamuyi magana dashi koh? ai yace zai shigo gari nan da 9days ba?, shikenan Allah ya kawoshi" Amin ta amsa cikin jin daɗi, Daga kan dining Mami take leƙosu tana son ganin yanayin Hammad domin itama Sageer ya kirata bata so kai tsaye ta shiga zancen ne shiyasa tabarshi da Hamrah, ganin fara'a a fuskar Hamrah ya sanyata jin kamar Hammad ya amince ne.
"Yawwa ɗayan zancen kuma dana ina son sanin yaushe Abii sai dawo? Kwana biyu ina kiran wayarsa bana samunsa"
"Zai iya kaiwa kwana sha biyu ko fin hakan kafin ya dawo In sha Allah" Hammad ya bata amsa kai tsaye. Miƙewa tayi tabar Hammad awajan ta shige ciki shikuma yacigaba da danna wayarsa kafin Mami ta dawo wajan da yake zaune sukaci gaba da hira sai da aka kira la'asar kafin yashiga toilet dake palourn yayi alwala tare da Abbad suka fice masallaci..
#ZEE ALABURA
#LIKITAN-RUHI
#SOYAYYA
#ƘADDARA..