SHA HUƊU
by @zeeeyybawa
LIKITAN RUHI
Na
ZAYNAB BAWA
Arewabook @Zeeeyybawa
SHAFI NA GOMA SHA HUƊU
Ina fita daga ICU kai tsaye na nufi admin block, wannan farfadowa da patient da yayi yasa naji wani ɓari na nauyin dake zuciyata ya ragu. wani irin nutsuwa ke ratsani wacce da ke zuwa bayan doguwar jira. Ba tare da ɓata lokaci ba na sanar da bangaren gudanarwa game da farfaɗowar patient ɗinmu, domin su isar da sahihin bayani ga dukkan masu ruwa da tsaki, daga kan Prof Dalhatu har zuwa Director na asibiti. Duk da kasancewar akwai lambobinsu a wayata, amma ba dabi’ata ba ce yawan kiran mutane, sai dai idan al’amari ya kai matakin da babu yanda zanyi.
Na sanar da su cewa patient ɗin ya fara nuna alamun farkawa, partial awakening kuma halin da yake ciki yana dai-dai da hasashen da muka yi tun farko. bayan na gama sanar dasu hakan, na wuce office ɗina, domin na san akwai marassa lafiya da dama da suke jirana, kowannensu cike da nasa damuwar ko ince cuta, sannan kuma zuciyoyinsu cike da fata da kuma sa rai ga samun waraka da cutar da take damunsu.
Patients ɗin da nake dubawa a wannan asibitin yawansu na musamman ne ƙwarai . A tsawon shekarun aikina, ban taɓa cin karo da yawan marassa lafiya irin wannan ba. Wani lokaci nakan tsaya in tambayi kaina dalilin wannan cin-cirindo na marassa lafiya da ake turamin, Can yanda na baro duk da yawan marassa lafiya masu son ganina amma ba’a tara mun ayyuka da yawa haka, bambamcin yanda na baro da nan shine can akwai waɗanda ba za su bari a ɗora mun irin wannan nauyin ba. Amma duk da haka, al’amura sun fi min yanda nakeso a nan fiye da can, duk ayyukan da zanyi a nan duk yawansu na kwammaci zaman nan ɗin domin can akwai fuskokin da sam banaso nayi arba dasu.
Tun daga nesa na hango yawan mutanen da suke jirana, Ajiyar zuciya na sauƙe, Regina da kanta ta faɗa min irin cigaban da asibitin ya samu ta fuskar yawaitar marassa lafiya masu ziyarta tun bayan zuwana. Sai dai abin da nake yawan lura da shi, shi ne, yawancin patients ɗin da nake dubawa masu hannu da shuni ne. sai dai abunda basu sani ba shine kuɗi ko talauci bai taɓa zama ma’aunin darajar maras lafiya a wurina ba. Dukansu dai mutane ne, masu rai, masu fatan samun lafiya.
Ina ƙarasawa wajan marassa lafiyan da suke jirana naga gabaki ɗayansu sun fara murnar ganina, cikin sauri n awuce na sanarwa regina tafara turosu, Abin da ya fi ba ni mamaki shi ne yadda fara’a ke mamaye fuskokin marassa lafiya da zarar sun samu damar ganina. Yadda suke kallona cike da yarda da amincewa, kamar sun ajiye rayukansu gaba ɗaya a hannuna. Wani lokaci nakan tambayi kaina, shin na kai wannan matsayi da suke bani a zukatansu? Me ya sa suke ɗora min irin wannan nauyin begen da yafi girman ayyuka na?
Ta’iya yiwuwa hirarrakin (interviews) da ake yawan yi tare dani kuma ana yadawa ne suka haifar da wannan sanuwa. Amma ni kaina na san gaskiyar al’amari. Allah ya hore min baiwa da yawa, baiwar da ban taɓa jingina ta da iyata ba. Allah ne kawai.
Duk da cewa shekarun aikina ba su yi yawa ba, amma har yau Allah bai taɓa haɗa ni da maras lafiyan da na kasa gano ciwonsa ba. Wannan ba saboda wayona ba ne, kuma ba wata dabara ta musamman bace.
A sanina, zan iya cewa duk marassa lafiyan da na taɓa kulawa da su sun samu sauƙi ko waraka da ikon Allah. ba ni da tsafi, ba ni da sihiri, ba ni da wata asiri face addu’a, jajircewa, da kuma cikakken dogaro ga Ubangiji. Na yi imani ƙwarai da cewa idan Allah ya nufi bawa da ɗaukaka, babu irin baiwar da ba zai saka masa ba.
A cikin hikimarsa, Allah yana tafiyar da al’amurana ta hanya mai ban mamaki. Duk wani majinyaci da har bazan iya warkar da lalurasa ba Toh Allah baya taɓa haɗa hanyata da wannan maras lafiyan. Sai ka ga ana ta shirin ganawa, amma kullum ana samun tsaiko har sai Allah ya aikata mai yiwuwa akan wannan maras lafiya. wannan wane irin lamari ne in ba ikon Allah ba? Wa zan danganta wannan baiwa gare shi, in ba Shi ba? Dukkan al’amurana na a karkashinsa suke. Yadda yaso haka yake tafiyar da rayuwata, yana jarraba ni, yana ɗaukaka ni, yana kuma rufe min wasu ƙofofi domin kariyata.
Ban iya tsafi ko maita kamar yadda wasu ke yadawa ba. Allah ne kawai yake nuna ikonsa a kaina, yana fallasa rahamarsa ta hanyata. Jin ƙai irin nasa ya tsamo ni daga cikin mantuwa, ya wanke min idanuwa, ya kareni daga shiga wata baƙar duniya da wasu daga cikin makusantana har yanzu suke makale a cikinta. Ni kuwa, mai zance akan hikimar Allah a kaina? Babu. Sai dai godiya tsantsar godiya zan kuma bauta masa da kare duk wasu hakkinsa.
Kafin nagama ayyuka na na ranar maras lafiyanmu ya samu cikakken farfaɗowa, amma har yanzu yana bukatar kulawa ta musamman daga ƙwararrun likitoci. Na shaidawa manyan consultant batun cikekkiyar farfaɗowar kuma Conference zai gudana gobe idan Allah yakaimu kamar yanda aka tsara. Prof. Ɗalhatu ya sanar da isowarsa a safiyar ranar da za'ayi conference ɗin.
_______________
WASHE GARI.
Babban ɗakin taro na asibitin ya cika tun kafin lokacin fara taron, Wannan ba irin taron da ake yawan yi ba ne, conference ne da aka kira saboda cikakkiyar farkawar patient bayan heart transplant da akayi masa wanda kuma hakan aikine ba wanda aka saba yi ba. Manema labarai daga sassa daban-daban sun hallara, kowannensu rike da na’urar ɗaukar sauti da cemara, fuska cike da tambayoyi.
A gaban cikin hall ɗin conference ɗin akwai babban teburin da yake ɗauke da manyan likitoci.
Director na asibitin, Prof. Dalhatu (Cardiologist), ICU consultants, Internal Medicine, da ni kaina, Dr. Khadija Ajiya a matsayina na ɗaya daga cikin likitocin da muka yi assisting sannan nayi close monitoring bayan aikin.
Lokacin da Director ya shigo, sai hayaniyar ɗakin ta lafa domin shigowarsa itace zata bada dama a fara tattaunawar, Kowa ya zauna a kujera, masu camera suka gyaggyara,
Director yayi gyara murya, alamar fara conference. sannan ya fara magana cikin hikima ilimi da kuma sabo da yin conference din.
“Mun gode da zuwanku. fatan kowannen yazo lafiya. Mun kira wannan conference ne domin sanar da jama’a da kuma su kansu sauran likitanci cikakkiyar farkawar patient ɗin da ke ƙarƙashin kulawar asibitinmu wanda aka sauya masa zuciya kwanaki huɗu baya ya samu, Za mu yi magana kawai akan akan bisa aikin da muka gudanar.” Ya juya ya kalli Prof. Dalhatu.
“Prof, Bismillah.” Prof. Dalhatu ya miƙe tsaye. Murya tasa a kwance take, amma da alamu yana cike ƙwarin guiwa.
“Patient ɗin da muke magana a kai ya samu complete return of consciousness misalin ƙarfe shida na yammacin jiya. Ya buɗe idanu da kansa, ya gane inda yake, ya gane mutanen da ke kusa da shi, kuma ya amsa tambayoyi cikin nutsuwa.” ma nema labarai suka fara motsi suna ƴan rubuce-rubuce da alamu suna ɗaukan bayani akan abunda ya faɗa.
“Babu confusion, babu agitation. Heart rhythm ya daidaita, blood pressure stable, kuma Nunfashi ma ya dawo normal.” Wani ɗan jarida ya ɗaga hannu.
“Prof, shin wannan farkawa ta wucin gadi ce?”
Prof. Dalhatu ya girgiza kai.
“A’a. Wannan cikakkiyar farkawa ce, ba partial ba.”
Ya kalli Director ya zauna. Director ya karɓi magana.
Sannan Prof ɗalhatu da shi ya jagoranci aikin yayi bayani akam yanda aka gudanar ba tare da ya buɗe confidential abu ba.
“Za mu ci gaba da bayar da sahihin bayani a kan aikin yanda ya dace.” cewar Dricetor bayan Prof Ɗalhatu ya gama bayanansa. sauran likitocin da suke da abun tofawa suma suka yi iya kacin bayanin da zasuyi sannan, Wani ɗan jarida ya tambaya.
“Shin za mu iya ganin patient ɗin?” Director ya amsa cikin girmamawa.
“A’a. Hakan bazai yiwu ba domin sirrinsa da lafiyarsa suna da muhimmanci.”
Bayan bayanin likitoci, ɗakin taron ya sake yin shiru na ƴan dakiku. Manema labarai sun yi shiru kamar suna jiran wani abu, tambayar da ba kowa zai iya yi ba.
Wani ɗan jarida daga sahun gaba ya ɗaga hannu.
“Tambayata tana ga Dr. Khadija Ajiya,” ya faɗa cikin ladabi.
“Za mu so jin technical clarification daga bangaren assisting surgeon. Me ya bambanta wannan surgery da sauran heart transplant ɗin da ake yi a baya sannan menene ya bambamtaki da sauran likitoci kamar yanda naji ana faɗin kasancewarki ta daban"
Dukkan idanu suka sauka a kaina.
#ZEE ALABURA
#LIKITAN-RUHI
#SOYAYYA
#ƘADDARA....