1&2
by @autaralheri
💋💋💋*BIG UNCLE* 💋💋💋
(SHUGER DADY RETURN) 🫶❤️
AS NEW NAME IS 👇
💋*BIG UNCLE*💋
🔥🔥Hot love with a new sexy romantic story 💋💋💋
By
Dr Yasmeen Ahmad 🥳🥳
Autar alheri ✍️💃
Writer of👇
ME & MY LION
ABBANAH
SHGER DADY
AND
OTHERS 💃💃💃💃
Ayanzu tazo muku da Sabon kabce me ɗauke da Sababbin abubuwa, na soyayya bar Kwanci, shauƙi, ƙauna, cin amana, da kuma reality love na haƙaƙa, duk acikin book ɗin *BIG UNCLE* (SHUGER DADY RETURN)
kugyara zama kana kubiyoni acikin wannan sabon kafce me ɗauke tallafin nutsuwa, dugunzuma tinani, gakuma sanya nishaɗi🥳 kudai kawai mu kafta aciki.💃💃
HAPPY SALLAH ALL MY LOVELY MUSLIM❤️🥳🥳
بسم الله الرحمن الرحيم
Book 1
Chapter 1 & 2
"Shirin zuwa wurin dinner faty suke yi cikin gaggawa sunayi suna duba a gogon dake manne cikin bedroom ɗin domin sun makara gasu kuma sune manyan abokanan ago kuma wakilansa.."isham yadace muwuce haka fa kunga bayin Allah nan sekiranmu sukeyi. Ɗaguwa wanda aka kirada isham yayi kana ya duba agogon Sekuma taja ɗan gajeren tsaki yana cewa "ni wlh duk jikinane amace faruk domin domin bantaɓa ganin dinner aure hakaba, biki ba ango kuma kusan amaryar mazataji daɗi ba. "Hum to ai itace tace taji tagani kai miye naka acikine mlm? Ni wlh ko ajikina domin tana waye JAY kuma ta yadda ta aureshi ahaka. Cewar harun yana dariya. Miƙewa Yusuf yayi yana faɗar "dan Allah muje nasan yanzu kowa muyake jira amma fa wlh duk ku kashe wayoyinku domin gujewa Kiran Mami, yawwa. Daga Hakan duk suka fice daga hotel room ɗin dasuke suka shiga motocinsu tare da nufar tudun wada kaitsaye unguwarsu amarya.
"Hello Muna ƙofar gida kufito. "Okay Muna zuwa. "Kai kutashifa ga angayenan sunzo, haneefa ƙawar amarya. Miƙewa duk suka suka fito sun sawo amayar atsakiyarsu tasha kyau harta gaji, gata duguwa kuma meji Masha Allah domin kab tafi ƴammatan nata girma. Mota aka buɗe mata tashiga taname sauke ajiyar zuciya. Kafin ƙawayenta su shiga sauran motocin suka ɗauki hanyar zuwa wurin dinner faty ɗin.
Suna isa aka sake waker amarya da ango ana rerawa cikin lafazi me daɗi. Hakan suka shiga cikin hold ɗin wanda da shigarka ƙatuwar bana zata tarbeka me ɗauke da picture ɗin amarya kawai, aƙasa kuwa anrubuta *SALMAH ADAM & JABEER IDRIS DIKKO* kallon Sunan jabeer ɗin takeyi harta zauna mazauninta. Kafin aka fara abinda yatarasu awurin.
Haneefa da wata yayarta mesuna Hajara sukazo wurinta. Hajara tace "wai salmah ina jay ne? Mitasa bezoba dama baya cikin motar ashe ke kaɗai ce? "Humm baya ciki Anty Hajara aikine yariƙeshi besamu shigowa garinnan ba kuyi haƙuri please. Ido suka waro atare kafin Anty Hajara tace "anya kuwa salmah Kinsan inda kika jefa kanki? Wannan wanne irin abune Hakan ace ranar aurenka ka kasa halarta wurin dinner? To yanzu idan aka kaiki gidan shi wa aka kaiwa kenan? Tunda bema shigo garinba? "Kai Anty Hajara dan Allah kidena wannan zancen please muyi abinda yataramu kar hankalin mutane yadawo kanmu please, tafaɗa kamar zatayi kuka. Wata muguwar harara Anty Hajara ta Banka mata kafin taja tsaki kawai tabar wurin.
Ɗagawarta keda wuya, seka text yashigo wayar salmah. Anyi gajeren rubutu kamar Hakan. *KARKI DAMU DA DUK ABINDA ZA'A FAƊA AKAN ZUWAN JAY WURIN NAN DOMIN KIN RIGADA KISAN PLAIN ƊINMU KAI KARKI ƁATA MANA SHIRI OKAY.*
tana gama karantawa tasaki wani ƙayataccen murmushi wanda ya bayyana tundaga zuciyarta.
Hakan aka cigaba da gudanarda faty kamar kowanne sedai wannan babu ango babu dalilinshi. Sedai manyan abokananshi su baza capacity haƙarya musamman Yusuf da faruk, kai harma da isham.
Ana cikin hidima har ankusa tashi Sega tawagar yayun ango mata sun iyaso. Cikin shiga ta alfarma, wanda kallo ɗaya zaka musu kasan cewar nera tayi kuka ajikinsu. Manyan matane masu aji da class kuma masuji dakansu, atare dasu akwai ƙananun yara huɗu se matasan ƴammata uku wanda bazasu wuce shekaru 15, zuwa 16, yarane tsintsar yarama. Kyawawan gaske, kuma black beauty San kowa ƙin wanda yarasa, musamman ta tsakiyarsu wanda Allah yayiwa baiwar diri na ɗaukar hankali kyawunta yafita daban dana sauran domin jikinta da yanayinta tamkar ƴar ƙasar itopia ce. Zuwa sukayi har inda mc. Kana ɗaya daga cikinsu ta karɓa tace "assalamualaikum jama'a ina me matuƙar bada haƙuri akan zuwanmu kurarren lokaci, ayimana anfuwa please, kana zamu Siya fiskar amarya ayan kasan cewar bamu samu damar halartar buɗar kai ba in sha Allah zamuyi ayanzu, ngd sosai. Tafi aka shiga yi sosai ana sowa. Hakan mc ya karɓi spiker yana cewa "Masha Allah Hajiya bilkisu idris dikko megadon zinari, ƙorafinki yakarɓu hajju. Haneefa ce tazo taƙara rufewa Salman fuska, kana Anty Hajara dawasu daga cikin family ta sukazo suka tsaya, kamar yadda akeyi. Mc yace "to yayun amarya anawa Zaku buɗewa yayun ango fuskar amaryar tamu? Ɗan yatsina fuska Anty Hajara tayi kana tace "millan ɗaya (1m) "to'to'too Hajiya bilkisu kinji yadda sukace farashin fuskar amaryarsu 1m ne. Jinjina kai Anty Billy tayi kana tace "bakomai mc ai banice zansiya jay fuskarba ƴaƴanshi ne? "IKRAM, IMAN, and IKLAS., kunji farashin fuskar amaryar uncle jay ko? "Murmushi iman tayi taka tace "nasiya a 1.5m mom. "Tofa kaji mc tace taƙara musu 500k akai. "Nikuma nasiya 2m mom, cewar ikram. "Woww Masha Allah lallai baby's kunaji sa amaryar uncle Ɗinnan naku kenan. Tofa jama'a ciniki yafaɗa domin dai Anty Hajara yayar amarya ta tsayar a 1m, amma ƴaƴan ango sun suya a 3.5m Masha Allah. Ihu aka ɗauka da sowa cikin jin daɗi Anty Hajara se watsar baki takeyi duk fishin rashin zuwan jay a wurin yakau sabida wannan uban kuɗin, takowa ikram tayi zata buɗe fiskar amaryar kenan taji saukar sweet voice ɗin iklas cikin wata irin murya me shegen daɗi cikeda tsintsar taɓara wanda ke nuni da cewar ita ɗin sangar tacciya ce ta ƙarshe kuma sarkin Tsiwa. Tana cewa. "No ikram nice zan buɗe fuskar amaryar big uncle fa kima Dena ɗauki. Tafaɗa tana murguɗa baki. "Dariya duk mutanen wurin sukayi, kana Anty Billy tace "to sarkin rigima bayan bakece kika Siya fuskar amaryar ba kuma zakice kezaki buɗe? Baki taturo gaba cikin cikin sakalcinta tace "No mom aini ba'ajira nasiyaba kawai taje zata wani buɗe. "To ƴar lele kuma ƴar daukar family Alhaji Idris dikko, ayi mana afuwa please abisa rashin jiran farashinki, munajinki ke anawa Zaki Siya? Seda tawani sha ƙamshi ta jujjuya manyan idanuwanta masu Kamada madara kana tace "nasiyawa uncle jay fuskar amaryarsa 5m. "Yeeeee wow big girl Masha Allah, wurin yaɗauki ihu da sowa yana tafi cikin, isa da class iklas tazo tare da fiddo wayarta ta kalli Anty Hajara tace account no. Ai cikin zumuɗi Anty Hajara ta gaya mata account ɗin, atake tatura musu 5m. Kana tasaka wayarta acikin jikarta taduƙa tare da yaye mayafin amarya salmah. Hakan yasa sukayu ido huɗu da juna wanda ya haddasa wa Salmah faɗuwar gaba sabida ganin tsananin zalmar kyaun iklas me birkita lissafi. Murmushi ta sakar mata wanda yasa saura kaɗan yawu suzubo daga bakinta, tayi saurin taresu tana jawo nata murmushi me Kanada kuka agaban iklas tayi mata. Duk wurin aka ɗauki ihu tana tafi. Cikin farin ciki da nishaɗi.
Tunda suka shigo wurin idon harun ke kanta tamkar ya haɗiyeta yakeji wani irin son yarinyar yaji yakamashi lokaci ɗaya, domin betaɓa ganinta ba se yau, musamman yanzu datake magana baƙaramin tafiya da duk mazan dake wurin tayiba kan cewar ta Sanger tacciya kuma komai cikin taɓara da tsiwa takeyinshi. Wannan dalilinne yasa taƙara gigita duniyar harun..Hakan har aka gama aka watse amma besamu ganinta ba domin tana tare da Mom ɗinta dakuna sister's ɗinta su iman.
Bayan an tashi daga dinner ne su Anty Billy da Anty fiddausi, Anty mimi, suka ɗauki amarya zuwa gidan mijinta tare da rakiyar abokanan ango, bayan sun Kaita ɗakinta ne suka buƙata ci Abar mata ƙawayenta nan sukwana tare kasan cewar ango baya gari kuma haryanzu be isoba, Hakan kuwa akayi, nan akabar haneefa, Maryam safiyya, zasu taya amarya kwana, bayan su Yusuf sun ajiye musu komai na buƙata har kazar amarcinta, kana sukayi musu sallama suma suka tafi...!
Tofa 🤔 yanzu da game ɗin ze fara, wannan wanne irin aure ne ba ango babu dalilinsa?
Autar alheri ✍️