3&4
by @autaralheri
💋💋💋*BIG UNCLE* 💋💋💋
(SHUGER DADY RETURN) 🫶❤️
AS NEW NAME IS 👇
💋*BIG UNCLE*💋
🔥🔥Hot love with a new sexy romantic story 💋💋💋
By
Dr Yasmeen Ahmad 🥳🥳
Autar alheri ✍️💃
Writer of👇
ME & MY LION
ABBANAH
SHGER DADY
AND
OTHERS 💃💃💃💃
Ayanzu tazo muku da Sabon kabce me ɗauke da Sababbin abubuwa, na soyayya bar Kwanci, shauƙi, ƙauna, cin amana, da kuma reality love na haƙaƙa, duk acikin book ɗin *BIG UNCLE* (SHUGER DADY RETURN)
kugyara zama kana kubiyoni acikin wannan sabon kafce me ɗauke tallafin nutsuwa, dugunzuma tinani, gakuma sanya nishaɗi🥳 kudai kawai mu kafta aciki.💃💃
HAPPY SALLAH ALL MY LOVELY MUSLIM❤️🥳🥳
بسم الله الرحمن الرحيم
Book 1
Chapter 3&4
"Suna fita Anty mimi ya shiga Kiran contact jay, amma harta yanke be ɗagaba, Hakan taƙara Kiranshi still be ɗagaba ba, kallon Anty Billy tayi cikin takaici tace "Billy wlh jabeer yarenamu fa, wannan wanne irin danyen aikine yayi haka? Yanzu fisabilillahi idan Abba yaji baya garinnan aka jawo yarinyar nan yakenan zamuyi? Kinsanfa sam ba'a kyautaba Allah. "Humm anty Mimi kenan to idan ma baki saniba kisani domin kuwa jay yana U'S bayama ƙasar wlh kawai dabarace yayi mana. "Whatt? US fa kikace Billy? Yoshe yajeto bayan ko ɗazu nayi waya dashi da sim ɗinshi na Nigeria kuma yacemin yana Abuja? "Hum idan baki yadda ba tambayi Yusuf kiji, ɗan Ball ne fa kuma babban ɗan Ball da manyan ƙasashen duniya ke alfahari dashi, tayaya keke tunanin baze iya juya sim ɗinshi Aduk ƙasar dayakesoba? Hum to idan baki saniba kisani wlh jay yana U'S kuma acikin darenan ze wuce engilan sity domin sunada wasa gobe, amma idan baki yadda ba gobe idan Allah yakaimu ki kalli Ball ɗin daza'a buga tsakanin Real Madrid da Barcelona, Zaki ganshi aciki, domin Kinsan yanzu yana cikin ƙunguyar real Madrid ne kafin yawaske musu tunda bashida alkibla. "Hu'unm tab ɗijam lallai jabeer kuwa yayimin wasa da hankali ya jefamu arame daga Allah ya fiddamu. Ni narasa uwar data yake ƙiyayya da wannan Auren abu kamar me ahafar aljannu, kodai aljanna ta aureshine Billy? Cewar Anty mimi. "To Anty Mimi Allah kaɗai yasan wannan lamarin amma dai abin akwai ayar tambaya aciki, domin ba yadda za'ayi cikakken namiji me jini ajiki dan shekaru 37, ace bayason aure, kuma wai wanda ke rayuwa acikin aturawa. Sedai kuma idan sune suka ɗauke hankalinshi. "No Billy kima Dena wannan zancen domin kab azuriarmu babu fasiƙi gaskiya. "Hakane kuma. Hakan sukaci gaba da tattaunawa har suka ƙarasa family house ɗinsu, gidan Alhaji Idris dikko.
U'S
Wani haɗaɗɗen matashi ne ke kwance acikin gidan motsa jiki, yana training, kallo ɗaya zaka mishi kasan cewar shiɗin majiyi karfi ne kuma kyakkyawan namiji ajin farko, farine tas domin baka isa ka banbantashi da farar fatar ƙasar ba, yana cikakkiyar ƙira me ɗaukar hankali, ga kyau na ban mamaki. Akwai dogon hanci kamar birro, ga wata kyakkyawar suma daya bari tayi riskarshi ƙawanya, gaskiya wannan guy ɗin handsome ne ba kyarya domin duk inda ake son handsome yaje tashi yama wuce nan. Sedai fa duk abinnan nashi fuskar nan a murtuƙe take tamkar besan minene dariya ba. "Hi Jay. Cewar wani matashin Bature tadaya ƙaraso wurin. Seda yamaula kafin ya ɗago yana kallon Baturen dawasu irin idanuwa nashi masu kama dana turawan domin ƙwayar idonshi lite blue ce me sheƙi, gwakuma idon a Lumshe tamakar ɗan shaye shaye, wanda suka ƙara fidda mishi asalin kyawunshi me ɗaukar hankalin duk wani me kallonshi. "Hello joun. Yafaɗa da wata shegiyar murya me bala'in shiga jiki, kafin yamiƙe daga kan ingin ɗin yana baya joun hannu suka gaisa, kana ya fara takawa cikin wani irin class da jarumta, yana goge lallausar sumar kanshi da towel, inda ya ajiye wayoyinshi ya nufa, yana zuwa ya ɗauki ɗaya, Anan yaga 5 miss call daga Anty mimi, 4, na Yusuf, 8, na Salmah, se kusan miss call 16 na abokananshi, Sekuma ɗaya da wata baƙuwar nomber wadda besan ko nomber waye ba, domin Kiran beshigo yadda duka sauran suka shigaba sabida indai bayada nomber mutum to kira baze shigo yadda yadaceba sedai kawai yaga alamar wanda yakirashi amma kaida kakira bazaka sameshiba.
Ɗan gajeren tsaki yaja yaname shafa lallausar sumar kanshi, yasan duk wannan bala'in Kiran baze wuce sabida wannan kaddararren Auren bane. Tsaki yaƙara ja kafin yabi Kiran Anty mimi. A lokacin wayar na hannun ikram tana game, tana kira yashigo an rubuta "bro jay. "Laa barana bawa Anty mimi wayarta big uncle ne yake kira, tafaɗa tana miƙewa tsaye, domin duka kuwa Hakan yake kiranta da Anty mimi ƴaƴanta da ƙanne. Dasauri iklas tace "kawo nakai mata, batajira cewar ikram ɗin ba ta karɓa tafice daga bedroom ɗin. Kaitsaye bedroom ɗin momma. "Momma Ina Anty Mimi uncle jay ne ke kiranta. "Aiko tana bayi ki ɗaga kigaya masa kafin ta fito kafin ya hasala ya fara yiwa mutane tijara, cewar Momma tana ficewa da bedroom ɗin. Ita kuwa iklas baki taturo gaba tana mita domin Allah yasani batason abinda ze haɗata za uncle jay tunda mugune. Ganin wayar na neman yankewa ne yasa ta ɗaga tare da karawa akunne, amma batace komaiba. Shima kuma bece komaiba harna tsawon minti biyu, kafin taja ɗan gajeren tsaki yace "wai Anty mimi dama dan kimin shiru tasa kika kirani ne eye? Yafaɗa cikin sweet voice dinshi. "Tana toilet, yaji saukar muryar da yarigada yasan kota wacece. Taune lips ɗinshi na ƙasa yayi kafin yace "baki iya gaisuwa bane dan ubanki, dazaki ɗaga min waya kimin shuru? Tajishi sarai amma seta turo baki kamar yana gabanta, tana ƙuƙunai ƙasa ƙasa. Tsawa yadaka mata cikin faɗa wadda tasaka seda iklas ta yadda wayar jikinta na rawa tana zare ido takebin wayar da kallo cikin mugun tsoro tamkar shi take kallo a wayar domin tasan waye uncle jay, ba abinda ze hanashi cin ubanta inda tana gabanshi. "To rasa kunya wayar tawa kika jefar? Cewar Anty mimi tana ɗaukar wayarta. Arazane iklas ta kalli Anty mimi domin gabaki ɗaya atsorace take. Cikin mamaki Anty mimi tace "wai ke miyasameki ne ko wani kika jawo ne eye? Tana tambayarta tana ɗauko wayarta da haryanzu jay nakan layin. "Au keda jay ne kenan yayi Miki kyau kunfi kusa ai, tana fama faɗar Hakan ta ɗauki wayarta tare da zama akan bed tana faɗar"to ɗan renin hankali seyanzu kaga damar kira kenan. Sumsum iklas tafice daga ɗakin cike da tsoron abinda ze biyo baya tsakaninta da uncle ɗinta. "Lumshe lulu blue eyes dinshi yayi kana yace "Anty mimi bana kusa da wayarne. "Humm wlh jabeer karenamu kayi mana wasada hankali sanranka, yanzu ashe baha ƙasar nan kacemin kana Abuja? To mikake nufi da yar mutane ne jabeer? Tafaɗa cikin takaici. "Kai Anty mimi wai dan Allah miyasa kikeda damuwa ne? "Damuwar ƙaniyarja jay, yanzu fisabilillahi idan Abba ko Momma suka gane abinda ke faruwa yakakeso muyi? Sannan kasan tasu duk me sauƙi ce akan ta Dady ko kuma wlh yana hanya acikin satin nan zedawo Wlh Allah jay baka kyauta mana ba domin nida Billy kasaka adamuwa sabida fiddausi kowa cewa zeyi babu ruwanta shirinmu ne? Miyasa zakiyi haka please? Akawoma yar mutane dan ka mayardamu mutanen banza jabeer kagudu kabar ƙasa? Yanzu to gunwa ka barta kenan? Kuma yazakayi da hakkinta? Shiru yayi tamkar batajin abinda take yafaɗa. Ganin Hakan yasa tace "au sharenima zakayi yayi ma kyau barana sanarwa da momma duk abinda ke faruwa ita sekayi mata bayani. "Kai Anty mimi wlh kinada hayaniya. "Eh lallai zaka gane inada hayaniya kuwa yanzu. "Please Anty Mimi dan Allah Abar zancen anan ahaka please. "Kasan Allah jabeer wlh Allah kadawo Nigeria goge ko jibi idan ba hakaba wlh dakaina zan kira dady nagaya nasa komai, kafin ta kwaɓe mana kai zan fara ƙwaɓama ita wlh. "Innalillahi shikenan zan dawo jibi amma ba gobe ba domin gobe munada wasa, ƙit yakashe wayarshi. Da kallo Anty mimi tabi wayar tana girgiza kanta tare da jinninawa hali irinna ƙanen nata.
Gidan amarya.
Washe gari da safe ƙawayenta suka ƙara wuni nan, da yamma suka tafi abinsu, kuma duka yan uwanta ba wanda yasan jabeer baya gari aka kawota, inba anty Hajara ba ita kuwa kuɗi sun rufe mata ido, Hakan tasa bata sanarwa da iyayensu ba. Awannan ranar ma Hakan Salmah ta kwana ita kaɗai, kwana na biyu kenan, se washe garin ranar ne, Anty Billy takirata tana sheda mata jay ze dawo yau domin ta shirya tarbar mijinta. Wannan labari yayi mata daɗi matuƙa domin tanaganin dawowarshi shine cikar nasarar aikinsu.
Airport
Kusan mota takwas taje ɗaukeshi, kowacce ɗauke da nomber me Sunanshi Jay DK 1, har no 8, Hakan kuma data abokananshi Yusuf faruk dakuna isham, seta kanenshi jalal, da jafar, dukkansu jiran isowarshi suke yi cikin so ɗaukin ganinshi. Ahankali yatafara takowa daga matattakalar benen jirgin yana sanye da kanun kaya na adidas, sunyi bala'in karɓar Fatar jikinshi, lulu blue eyes dinshi sanye da medical glass, yana tako cikin kuzari da jarumta irinta ƙaƙƙarfan namiji meji da kanshi. Yan uwanshi na hango shi duk suka washe baki suna jiran isowarshi, domin bancin soyayya tajini, akwai soyayya gado ga matasa, wato soyayyar Ball, kamar yadda ake nunawa duk wani ɗan Ball do Hakan family shi ke nuna Mishi tankar wani baƙon tauraro acikinsu. Ai yana gama saukowa yan jarida da sauran mutanen dake airport ɗin suna mishi chaa, duk suka zagayeshi kowa burinshi yasadu da wannan cikakken dan Ball wanda manyan kasashen duniya ke alfahari dashi, JABEER IDRIS DIKKO KENAN, INKI JAY DK. Cikin hanzari escort ɗinshi suka taso suna shiga tsakaninshi da mutane wanda dakyar da suɗin goshi suka sama mushi hanya har ya shiga mota, cikin hanzari suma duka faɗa motocinsu sukabar harabar wurin batareda ko mutum ɗaya daga cikin family shi yasamu ganinshiba, sabida mutane bazasu bariba, Hakan duka nufi katafaren gidanshi kaitsaye, domin su Mamma basusan baya ƙasar ba balle yanafi family house doline sedai gidanshi.....!
Humm akwaifa gwarama aƙasa domin kuwa tana ƙasa tana dabo.
BIG UNCLE paid book ne akan 1500 kacal 👌 spcial group, VIP kuma 1k, amma duka yan group ɗin MY HOME, zasu biya 1k ne kuma a special group, 🧏 zaku iya tura kuɗinku a wannan account ɗin 👉 9112799371 moneipoint sha'awanatu kasim, kana kutura shedar biyanki a wannan nomber 👉 *** on WhatsApp 🙏
Wannan book ɗin baze jimaba domin baze kaimu azimiba in sha Allah kuma azimin yazo game yawancin rayuwa. Kiyi hanzarin shiga domin kar ayi babu ke🧏
Autar alheri ✍️