WAYE MIJINA TAKON FARKO

1&2

by @autaralheri

*WAYE MIJINA ???*🤔


By Yasmeen Ahmad

    
          Autar alheri ✍️

Romantic love story 💋 


*Gargad'i*


Wannan novel na matan aurene kawai anyishine domin fahimtardasu zaman takewar aure da matsalar da mace ke fuskanta da Kuma yanda zatayi maganin ta insha Allah

*KARKIBARI YARA SUKARANTA*

Dayawa ana kirana ko,aturomin sak'o danneman shawara to kitsaya kikaranta wannan novel zewarware Miki komai insha Allah.



Free page 


Page 1 & 2


  Jos 

___wani katafaren State nahango Wanda fad'in girmansa B'ata lokacine. State d'in malakar wasu bayin Allah ne su biyu *gali da Sami* Kuma Y'an uwane na jini uwarsu d'aya ubansu d'aya Amma yanzu basa raye se iyalansu kawai. Gali yamutu yabar matan aure ukku y'ay'a 9. Salmu, itace uwar gida se ego itace tabiyu se Kuma laure. Salmu y'arta d'aya mace wato bintu salmu mace,ce matsana,nin hak'uri da kauda Kai ga duk wani abunda akayimata ko y'arta.. sab'anin ego datakasance masi faffiyar mace da mita.yaranta biyar ak'ilu,sule,Hamza,saude,sahiya..

Laure itace k'arama itako halin ko inkula ne da ita ammafa Muna fukace tabugawa ajarida.y'ay'anta ukku Amina,sadiya,bala

Sami kuwa yabar Mata biyu y'ay'a 6. kulu itace uwar gida Kuma itama Kamar salmo take mace,ce mehakuri da kawaici da San mutane. y'ay'anta 4 jafaru,gambo,idi,se autarsu zenabu,

Hari itace tabiyu mace,ce dazakarasa gane Ina tadosa domin komai nata adukunce takeyinshi. Yaranta biyu suwaiba..uwani

Ayanzu dukkansu suna rayuwane acikin State din  daga su har iyayensu bayan rasuwar mahai fansu maza wato gali da Sami...rayuwa sukeyi cikin duhun jahilcinnan namaguzawan farko abun sedai ace Allah ya kyauta.


Bintu kyakkyawar yayince wadda gabaki d'aya family su tafisu kyau.kasancewar mahaifiyarta salmu bafulatanar dajice. Acan gali ya,aurota.

Duka yaransu auren gida akamusu wato auren had'i..jafaru shiya auri bintu..Buhari ya,auri sahiya..gambo ya,auri saude..sule ya,auri zenabu..hamza ya auri suwaiba..buhari..ya,auri uwani..dukkaninsu anan suke zaune Kuma har sun Tara iyali.

Iyayensu kuwa yanzu tsufa yazo Amma duka yaransu Mata bawadda Bata d'auko halin mahai fiyartaba..bintu da jafaru yaransu ukku salmanu aliyu faruku..hakama duka sauran kowa nada nashi Yara.

Aduk cikin wannan family jafaru da buhari Sufi kowa tsanar rayuwar dasukeyi cikin duhun jahilci Amma basusan yazasuyiba.

Dukansu basajin komai aransu Dan wannan yarungumi matar wannan ko yarik'a hannuta ko sutab'a in,anafira Dade makamancin hakan sallah ba,adamu ayi cikin lokaciba.baruwansu da rabawa yaransu maza da Mata wurin kwanciya..yaya ze iya k'anciya da k'awarsa ko yarungumeta ko suyi bacci a makwanci daya Kuma dukansu baliggai duk Wannan badamuwarsu bace.


Jafaru yanada wani amini Wanda ba Dan garinba awurin kasuwancinsa suka had'u..yakoka Masa Yana so yaranshi suyi karatun islamiyya Dana zamani..shiyabashi shawarar yakaisu KD suyi karatu acan zehadasu da yaranshi surink'a Yi tare..yaji dad'in hakan sosai.nantake yahada yaranshi yaturasu KD 

Sunfara karatu cikin sa,a domin duk abunda akekoyardasu baya gagararsu..yayinda mahaifinsu yasaki kud'i sosai.amininshi alh.Musa nakula Masa dasu..har Allah yatemakesu suka Gama lpy..sunfito da saka mako mekyau..abbansu yy murna sosai har farincikinshi baya,iya boyuwa..yayinda aketa zaginshi acikin State din anafadar yatura y'ay'a yawon duniya..Amma yasharesu domin shi bayada burin dayawuce yarabasu da irin dabi,un dangin nasu.aliyu duk yafi k'ok'ari aciki domin takardunsa sunfi kyau.dashi da D'an alh.musa atiku..shiyasa alh.musa yace suhada k'arfi suturasu saudiya karatu..hakako,akayi

Antura aliyu da atiku Jami,ar madina.kuma sunfara karatunsu cikin nasara..salmanu da faruku sukawuce A.B.U Zaria Suma suka Kama karatu gadan2.


Masha Allah rayuwa mesauyi lokaci zuwa lokaci Inda ayanzu watanni sunshud'e shekaru sunja..ahalin alh. jafar wato jafaru ada.sunkammala karatunsu cikin nasara harsunzama manyan mutane..aliyu yazama babban likita.kuma saudiya tadaukeshi aiki acan haryayi aurenshi dawata balarabiya.

Suma k'annen shi duka sunkammala karatunsu.inda furuk yafito soja Salman ko lauya. Kuma Suma sunyi sure anan cikin State din.dasu da sauran Yan uwansu..Kuma ayanzu alh.ali da k'anen shi faruk da Y'ay'an shi Salman suke kulada y'ay'a Yan uwansu sundage akan se y'ay'an su Dana Yan uwansu sunyi karatu. Bayanda iyayensu suka iya Dole sukabarsu..Amma fa hassada fal zukatansu.

Ayanzu Salman Wanda sukekira da abbah yanada Yara hud'u.jafar Wanda yaci sunan mahaifinsu,se jabir, Usman,se Jalila.domin shi alh.jafar yafara yiwa aure saka makon Yana fama da matsanan ciyar sha,awa wadda idan tataso Masa harsuma yakeyi.wannan dalinne yasa yake tab'a Al,adarsu Yana matsar k'annen su mata danyasami sauk'in abunda kedamunsa to da alh.jafar yafahimci hakan se ya aura Masa diyar Dan uwansa buhari wadda akekira adwiyya.

Daga baya yayiwa faruk Ida shi yanzu y'ay'an shi ukku ne harun,Kamal,se haidar Wanda yaci sunan yayan mahaifinshi wato alh.ali Wanda shima yanzu Yana can saudiya da iyalanshi. 

*Wannan shine takai taccen tarihi wannan family mekaratu katsaya kanutsu afahimci tarihinsu hakan zesa kafahimci sakon da labarin kisan isarwa cikin sauk'a*


Saudiya

Hakeem,Hakeem,waibazaka fitobane kuyi breakfast d'in kutafi kabarsu se jiranka sukeyi ah,ah

Naji wata kyakkyawar dattijuwa balarabiya Dake tsaye bakin k'ofar bedroom din tana fad'a.ganin ba,ayimaganaba Kuma ba,abud'eba yasa tabude k'ofar tashiga..hango shitayi duk'unk'une acikin blanket serawar sanyi yakeyi.nashiga ukku mikedamunkane Hakeem?dama bakada lpy ne duk acikin larabci take maganar.

Tana yaye blanket d'in dayarufa dashi.hannu takai tadafa jikinshi taji zafi rau "innalillahi Hakeem miye yakedamunka kayi magana mana uhnm..Bude dara,daran Ida nuwansa yayi dasuke alumshe kamar nad'an maye yawatsa matasu..salati tasake,saki ganin yadda ida nuwansa sukayi jajir.sakamakun azabar ciwon dayakeji.

Tashi yy zaune dakyar Yana cizon leb'enshi nak'asa yad'ago fuskarsa.masha Allah nafurta araina sakamakon tozali da wannan kyakkyawan matashin balaraben.

Yaro matashi Wanda baze wuce shekaru 18 ba Amma haibarsa tazarta tad'an shekara 25.yanada manyan Ida nuwa masu shek'i da walwali suna Tara ruwa acikin kamar k'wallah.bakinsa kuwa Kamar bakin asusu zaka iya rantsewa spoon baze shigaba.sumar kansa da girar idanuwansa abun ba,acewa komai.sabida bak'in ta da shek'i.hancinsa kuwa dogo ne medan fad'i kadan Wanda yadace da kyakkyawar fuskarsa.befitadda saje ko gemo ba Amma duk wanigu daze fitarda Suma ajikinshi tafidda alama.abin gwanin Sha,awa.

"Mom bakomaifa naji sauk'i..ah,ah Kam Hakeem dubi yanda kk hada gumi kace bakomai tashi muje hospital gasu dadyn ku cannajiranka kufita se mufara zuwa hospital kajiko..no mom naji sauk'i fa karki damu bara nayiwanka muje shopping Moll din kawai.

Shikenan inbazakajeba bara nagayawa dadyn ku yadobaka idan kafito..tashi yy cikin k'arfin halin yashiga bathroom d'in.bataredayace komaiba..da ido tabishi tana karantar yanayinshi har yashige bathroom d'in.kana tamik'e tafita..shiko wankan yayi adaddafe yafito daure da towel ak'ugunsa.komai beshafaba yasaka Kaya marasa nauyi yafito.

A dining yasamesu su hud'u zaune mom dady da wani natashi Wanda baze wuce sa,ar Hakeem ba se baby girl Dake zaune saman ciyar dady.

K'arasowa yayi yazauna yanafar "good morning Mom & dady.had'a Baki sukayi wurin fad'in morning my son ya jikin naka? Dasauk'i dady..okk Yi breakfast se muje hospital adubakako..okk kawai yace Dan baya iya yiwa dady shi musu.

Sannu bro y jikin..juyawa nayi inda naji wannan maganar mekamada ta Hakeem kutttt nace Ina tasbihi ga ubangijin talikkai daya halicci way'an,nan bayi nasa masu matsanan ciyar kama.dumin bashida banbanci da Hakeem komai nasu iri daya hatta tabon da Hakeem yakedashi adamtsen hannu wannan saurayin nadashi.

"Naji sauk'i bro.okk Allah yabaka lpy.ameen yace atak'aice.

"Ya hafees miyake damun ya Hakeem ne? Cewar wannan yarinyar mekama dasu.murmushi  Wanda takira da Hafees yayi kana yace"Nima bansaniba lil kitambeshi Mana inyagayamiki muma muji.

Harara Hakeem yadallahmasa kana yad'oki cup yahad'a coffee.yadauko danufin Kai bakinsa kenan....




Tofa kobiyoni domin jin yaza,ayi wannan mird'ad'd'iyar rayuwar a cikin wannan family.








Autar alheri✍️