JAAFAR🌹 By Buhari Yusuf IBr
Chapter 7
JAAFAR🌹
THE OBSESSION7
By Buhari Yusuf IBr
...07
Lokaci na tafiya, kwanaki na kara shudewa, amma a kowane tafiyar second masifaffen son ta na kara huda cikin zuciyar shi kamar kara ɓara zuciyar shi ake yi ana cusa masa son ta. He really wanted to focus on his job but he couldn't. He was watching her ghostly self wandering before his eyes , her scent hitting his nose as if she is very close to him and her delusional voice striking on his ears.
Kan shi duke yake akan elegant desk da ke cikin office din sa. Busying himself thinking unnecessary things, that is his always condition. He is neither monitoring employees– in the company nor work. Shi dai kawai ga yanan zaune koda yaushe kamar wani statue.
Knocking kofar aka yi a karo na uku, sai yanzu ya dago jajayen idanun sa ya dora su akan kofar shigowar, muryar sa can ciki yace,
"Who is there?"
Duk da can kasa ya yi maganar amma wanda ke knocking din yaji shi tarwai, hakan ya zame masa wata kirkirarriyar dabi'a tun sati daya bayan ya dawo companyn da aiki.
"I'm, Sanusi." Wanda yayi describing kan sa da da Sanusi ya fada da karfi yanda jaafar zai iya jiwo shi.
Shiru jaafar for approximately thirty seconds kafin yace,
You can now come in." Ya mike daga kan desk din da yake zaune ya dawo kan manyan couch dake a cikin office din ya zauna ya dora kafa daya kan daya.
Tun daga nesa yake kallon Sanusi– hannu sa ɗauke da file– har ya karaso inda yake zaune.
"You can sit." Jaafar ya fada yana nuna masa kujerar dake gaban sa.
Babu musu sanusi ya je ya zauna ya ajiye file din akan mini table dake tsakiyar su yace,
"Barka dai"
Daga kai kawai jaafar yayi ba tare da yace komi ba sannan yace,
"Ina jin ka. Me ke faruwa?" Ya tambaya a takaice.
"Yallabai, bayan ka tafi hutun kwana hudu, your deputy, Umar farooq, has signed to import goods from Canada's montreal." Ya fada yana jawo file din ya tura shi zuwa gaban jaafar yace,
"Wanan shine documents din." Ya cigaba da cewa "kayan mu sun taso daga Canada yanzu suna U.S. port an yi seizure din jirgin gaba daya. And... Bamu san me yake faruwa ba har yanzu amma dazu naji Farooq na yin magana da jami'an jirgin, sunce wai anga something illicit a cikin jirgin. So yanzu dai ana neman masu kaya su je zuwa can US din." Sanusi yayi bayani.
Shiru jaafar yayi, baice komi ba na dan lokaci sai kuma yace, "dad yasan da wannan maganar?" Jaafar ya tambaya.
"Not yet, sir. But we are preparing to inform him, cos he is supposed to be involve. It's a very big issue."
"Okay, do so. And, ka zan tura maka visa ta idan na koma gida. You have to book a flight for me. Akwai bukatar muje UK."
"Okay, sir. Za'a yi hakan."
"You can go, now." Ya fada. Ya jawo file din ya fara duba shi daki-daki. 'this is a very simple case, I guess.' he said barely a whisper. And dropped it down the table.
'This's the right time, wannan shine dai-dai lokacin da ya kamata na dauki shawarar Kayode. I have finished scanning every nook and cranny to find an easy solution da zai sa na mallaki Fatima, and I saw no way. everyway to have her as a wife is leisurely slipping away from me. So, I must act strongly.' ya fada a zuciyar shi. Sannan ya dauko wayar shi ya kara danna wayar Fatima a karo na É—aruruwa amma it still says 'the phone is switched off.'
Murmushi yayi mai ma'anoni da yawa and bitten on his lips by his white well-decorated-teeth.
Juya akalar kiran yayi zuwa ga Kayode, bugu biyu ya É—auka
"Hello brother na how are you doing?" Jaafar ya fada da murmushin kwarin gwiwa a fuskar shi
For the very first time since from the start of this chaos he felt his heart untightened.
"My friend, I heard your voice sounded very happy today. Have u got engagement with that girl, abi?" Kayode ya fada daga can b'angaren.
Murmushi jaafar yayi, yana sosa keya yace,
"Not at all wlh. Kawai na yi tunanin yin amfani da shawarar ka ne. I think it's an only one way to achieve my goal. Please, help plan it for me. I'm on my way to your home right away."
"Jaafar! Don't embark on a journey you can't finish." Kayode warned.
Murmushi jaafar yayi confidently yace,
"Kada ka damu."
***
A bangaren Fatima itama sun yi kamanceceniya da irin halin da jaafar yake ciki. Ta rame, ta tsomaye ta kara tsawo. Zaune take a tsakiyar parlorn gidan ta zabga uban ta gumi. A yan kwanakinnan, hakan ya zame mata dabi'a, musamman da ta gama tabbatar da cewa; mahaifin ta da gaske yake shirye shiryen aurar da ita ga wanda ba ta so. In fact ba ta taɓa ganin sa bama a gaba daya rayuwar ta. A yau ne yayan ta Sadiq yake fada mata cewar za tayi bako, wanda ake shirin hada su aure zai zo, amma ga ta anan ko wanka babu, kuma babu niyyar yin balle kuma wani abu wai kwalliya.
Khadijah tare da Khairat ne suka shigo parlorn zuwa gurin Fatima. Khadijah ce tace,
"Yaya Fatima ga shi can ya karaso, yana jiran ki a dakin baki."
Ko daga idanu Fatima ba tayi ba. She felt like kada taje but if she dare, follow the made-up of her heart. definitely, the consequences will follow after.
Tashi ta yi ba tare da ta kalle ko wane daga cikin su ba ta shiga dakin ta, hijab din ta kawai ta jawo– da yake akan gadon ta– ta fito zuwa can guest-room din.
Tun daga nesa take kare musu kallo ba tare da jin ko ɗigo na kunyar sa ta kama ta ba– kamar yanda shima yake kallon ta.
Her heart went dried. she's no longer fear to say her mind. She's shameless to whoever is trying to interfere into her personality.
Zama ta yi akan kujerar da ke dan nesa da shi,
Shiru dakin ya dauka na dan lokaci kafin mutumin ya É—an gyara zaman sa sannan yayi gyaran murya yace,
"Ni suna na Abdul Rahman Sa'ad, amma ana summarizing din sunan da Abdul, kuma anfi kira na da Abdul din ma, + ni lecturer ne a University of Lagos– nasan kin sanni ai, tunda ina yawan ganin ki a school din, saide,,,, ba mu san juna ba, ba mu san muna da wata alaka da juna ba har sai zuwa yanzu." Abdul ya fada, ya ɗan yi shiru kamar mai nazari sannan ya ja dogon numfashi sannan ya cigaba da cewa,
"Dady ne ya turo ni zuwa gare ki domin na nemi soyayya da kuma yardar ki. Yace su abokai ne kuma aminan juna, kasuwanci ne ya hada su tun da dadewa, kuma ana tare ana zama na mutunci. Dan haka suke so su haÉ—a mu aure domin kara strengthen din alakar da ke tsakanin su." Abdul ya fada cikin kwantar da murya, yana kallon ta ido cikin ido.
Shiru dakin ya dauka mai dan tsawo.
Duk abinda Abdul ya fada ta saurare shi, taji shi, kuma ta san shi kamar yanda ya fada din, infact, she was shocked by seeing him as a man da ake so a ƙaƙaba mata.
"Ina jin ki, menene ra'ayin ki, Fatima." Abdul ya fada curiously to hear her own side.
Gyara zama ta yi sannan ta kalli Abdul ido cikin ido,– after she wore a serious face– tace,
" Sir, Abdul. Kamar yanda ka fada a bayanin ka, na sanka kwarai na sanka, kai malami na ne, so duk abinda da zan fada maka it should be a pure truth,,,... Ban son ka wlh, there's someone I love, he might neither better than you, nor capable than you, sir but, Ina son shi a hakan. Kuma zan aure shi." Fatima ta fada, her voice firm and stable.
Shiru ne ya ziyarci dakin, tun da Fatima ta gama fadin maganar da ke bakin ta, ta koma ta daidaita zaman ta kan kujera ta yi shiru.
Abdul kawa ya kasa dauke idon shi akan ta, tunani yake 'wane irin dakewar zuciya ne gare ta haka da har take gut da zata iya fitowa karara ta fadi magana haka, kan ta tsaye?
"To yanzu me kike nufi, i mean,,, how do u want to face this issue?" Abdul ya tambaya bayan yin shiru na tsawon lokaci. Duk wannan shirun da aka yi na tsawon mintuna idanun shi ko sau daya basu saukan daga kan fuskar ta ba.
Jin wani sanyi ta yi ya ziyarci zuciyar ta jin abinda sir, Abdul din ya fada, fuskar ta ta dan yi wasai for the very first time tun fara conversation din a tsakanin su.
"Yanzu ce musu zaka yi baka so na, kana da wacce kake so, ko kuma kace ka ganni ban yi maka ba." Ta fada cikin kasa-kasa da muryar as if somebody could hear what they discussing.
Kallon ta sir Abdul yake yi ko kiftawa babu, deep down Yana tunanin rainin hankali na yarinyar, she was totally wanted to outsmart him. Murmushin gefen baki yayi ya mike ya koma daidai inda take zaune ya tsaya, sai kuma ya fara zagaye kujerar da take zaune while clenched his hand to a fist yana buga hannu da yake a dunkule din akan daya tafin hannun nasa. Sai da ya zagaye kusan sau uku, sai kuma ya tsaya ya kalle ta yace,
"Nine kike so na fadawa iyaye na cewar bana son ki ko, Fatima? To ni ban iya karya ba, domin kawa naji ina son ki. Kafin yanzu dai kam naji tantamar kamar ba zaki yi daidai da wacce nake so ba, amma bayan haduwa da ke na karyata kai na." Shiru yayi, sai kuma ya koma kujera, dan gefe da ita ya zauna ya cigaba da cewa,
"Amsa ta ga magabatan mu itace, ina son ki, kuma ko yau aka shirya daura maki aure a shirye nike na amshe ki hannu bibbiyu a matsayin mata ta. So, You should better get ready too." Ya mike ya nufi hanyar fita daga dakin, sai kuma ya juyo ya kalle ta yace,
"Koda ace kin furta cewa baki so na, koda ace iyayan ki sun canza shawarar baki wanda kike so Fatima, I'll fight!, I will fight to have you as my wife. They have made a great mistake for involved me into you, into this conflict. na gan ki kuma ina son ki. Likewise noone could ever diswave ocean is the same as nobody could stop me from loving you!" Daga haka, ya fice daga gidan.
Kasa motsi Fatima tayi a gurin. Bakin ta ya kasa rufuwa. Taji zahirin kwarin gwiwa a kalaman shi. To menene mafita, ta tambayi kanta da kanta...
***
Tafiya Jaafar yake cikin motar shi shi kadai m, yana sauraren wakar ckay, a lokaci guda kuma yana tunanin ta yanda plan din shi zai tafi successful ba tare da cikas ba. Gangarawa yayi bakin katon restaurant din yayi park din motar shi sannan ya dauki wayar shi da ke a gefe ya lalubo number Kayode.
"Hello, I'm at the exact place you asked me to come." Jaafar ya fada.
Daga can b'angaren kayode yace,
"Okay, gani nan zuwa. Yanzu zan karaso." Ya fada with his broken Hausa.
Zaman mintuna biyar yayi a cikin motar sai ga Kayode. Ya bude gaban motar–wajen dan zaman banza– ya shiga ya zauna, ya mika masa hannu suka gaisa.
"About our recent conversation, Kayode. I'm now ready. Zan yi duk abinda kace indai har ba za'a kwace Fatima daga gare ni ba."
Murmushi kayode yayi sannan ya gyara zaman shi, then, cleared his throat and said,
"Indai har kayi duk abinda aka tsara, to, i have 💯 sure no body can even come closer– near her. Every body would despise her, disdain her and,,,, a wannan lokacin kuma, shine naka. Shi ne zakai amfani da shi domin cimma muradin ka na mallakan ta a matsayin matar ka."
Wani madaukakin murmushi jaafar yayi sannan ya kara kallon kayode yace,
"To yanzu fadi min yanda ya kamata ayi."
"Her phone number, call her and we'll take her to an unknown destination."
"Number ta baya tafiya ai Kayode, ina tunanin sun yi seizing din wayar."
Shiru kayode yayi ya É—an tafi dogon nazari kafin nan yace,,, "
Kada ka damu, there's another way." He said and pulled out his phone from pocket ya shiga search din wata number, sannan ya kara a kunne shi.
"Scorpion!" Ya fada da ƙarfi bayan an dauki wayar daga can b'angaren."
"I havs very task for you, bana son wasa, kuma nasan baku da wasa kuma."
"Baka da case oga, just name the task, and consider it done." Wanda aka kira da scorpion din ya fada.
"Baka da damuwa, yanzu haka ina kan hanyar zuwa gurin ku, kuna ina ne?"
Shiru scorpion yayi, sai kuma yace, "my K,,, you don sabi how the risky of our work, this is our secret, so, let it be like always, I'll fix the place and I'll let you know immediately..."
Dariya Kayode yayi yace,
"Shege mutumi na kasan hannun ka, but I'm waiting pls, it's urgent.
"Baka da case." Daga haka ya katse kiran.
Kayode kallon jaafar yayi yace,
When did you scheduled your departure from 9ja to UK?"
"Ina tunanin nan da kwana hudu. But my visa yet to be ready." Jaafar ya bashi amsa.
"Okay"....
***
Avoid errors.
***
To be continued.