JAAFAR🌹 By Buhari Yusuf IBr
Jaafar
JAAFAR🌹
THE OBSESSION8
By Buhari Yusuf IBr
...08
***
Gang ne guda wanda da ka kalle su kasan imanin su ragagge ne. Iskanci da fitsara ya samu gindin zama. Kusan su goma ne a cikin parlon amma babu wanda hannunsa ba rike yake da sigari ko dular wiwi ba sai mutum biyu daga cikin su, kuma suma din hannayensu rike yake da kofi cike da giya suna sha.
"Scorpion, ga mu duka mun hallara, jiran bayaninka kawai muke." Wani mutum ya fada, kyamusashe da jajayen idanu da ƙatuwar murya.
Wani shuumin murmushi scorpion yayi sannan yayi ma sigarin da ke hannunsa dogon zuka and threw the rest away.
"Iblis, kasan me yasa na yi shiru?" Scorpion ya tambaya yana kallon wanda ya kira da iblis.
"No, scorpion. Sai ka fada." Iblis ya fada yana gyara zaman shi.
"We have a big task which will bring massive money if we play our cards well." Ya fada ya koma kan kujerar shi yayi relax.
Kananun maganganu ne suka cigaba da tashi daga cikin dakin kowa na tattaunawa da na kusa da shi, abinda suka fi tattaunawa a tsakanin nasu shine, 'wannan wane irin aikinne da har scorpion yake kira da zaa samu massive money bayan manyan kudaden da suka samu kuma suke kan samu.'
"Wane irin aikine haka, scorpion?" Daya daga cikin su ya tambaya.
Numfashi yaja mai kauri sannan ya kalle su gaba daya yace,
"It's very simple task, all we need is to abduct one of the daughters of Alh lawal, he's well known, a prominent man in Lagos state and the entire North." Ya fada.
Yana saka hannun sa cikin aljihu ya fiddo hotuna ya watsa musu. Ya cigaba da cewa,
"She is Fatima– our target. Abinda nake bukata gare ku shine aiwatar da aiki yanda aka tsara. tsara yadda aiki zai kasance kuma zamu damqawa commada."
Wani matashin saurayi ya bayyana, fari, dogo. kai idan ka ganshi ba zaka taba tunanin ko kusa zai iya engaging kan sa cikin bad gang irin wannan ba.
Tsayawa yayi a tsaye yana kallon su kafin yace.
"Barkan ku mazaje"
"Barka." dukan su suka amsa in a choir.
Sannan ya cigaba da musu bayanin yanda aiki zai kasance. Kusan mintuna ashirin da biyar ya dauka yana bayani. Ya rabawa kowa aikin sa da abinda ya kamata yayi, sannan ya tabbatar da kowa ya san position dinsa. Sannan ya koma yayi joining da su, ya zauna kan kujera.
Scorpion da ya gamsu dari bisa dari da tsarin commanda ya mike ya jawo kwalbar wine ya zuba a kofi ya kurba sannan yace,
"Guys, our mission will commence tomorrow. Cheeerrrrr" ya fada yana daga kofin giya da ke a hannun sa. Suma suka hada baki wajen maimaitawa...
***
Zaune sir, Abdul yake akan couch cikin kayataccen parlon. His dad's face (Malam Sa'ad) was masked in seriousness. And beside him was Sadiq– Fatima's brother.
Sir, Abdul ya daga kan shi ya kalle su duka ya fara magana,
"Mun hadu da ita dad, ni a bangare na bani da jaa akan hadin da kuka yi ƙudurin aiwatarwa– Allah yasa hakan shine mafi alheri–, matsalar na daga gare ta, she said she has someone she loves."
"That'll never be a problem as long as you love her, sir, Abdul. Wanda take so mu kuma bamu son shi. Because of some reasons. Zan yi ma Dad bayanin abinda ka fada min yanzu, kuma insha Allah zaka jini nan kusa." Sadiq ya fada.
Malam Sa'ad was shocked by his son's response. Bai taba tunanin zai amince haka da wuri ba. He had tried this several times but was unsuccessful.
"kana nufin ka amince zaka aure ta?" Malam Sa'ad ya tambaya again just for confirmation.
"Yes, dad. Ko gobe ma akace za'a daura a shirye nake."
Wani yalwataccen murmushi ya bayyana a fuskar malam Sa'ad sannan ya mike yana kallon Sadiq yace,
"Sadiq, wannan labarin ba kai ne ya kamata ka kai shi ba. ni ne. Jira ni ina zuwa." Ya fada yana shigewa cikin dakin shi...
***
Karar gudun fanka da kukan AC– a tare– ne kawai kake ji a cikin madaidaicin parlon. Her eyes were busy looking outside through the window. Kadawar bishiyoyi da kukan tsuntsaye take saurare wanda suke saka mata nutsuwa a lokacin tsanani. Kalaman sir, Abdul na karshe suna repetition din kan su a cikin kwanyar ta.
"Koda ace kin furta cewa baki so na, koda ace iyayan ki sun canza shawarar baki wanda kike so Fatima, I'll fight!, I will fight to have you as my wife. They have made a great mistake for involved me into you, into this conflict. na gan ki kuma ina son ki. As no-one could ever diswave ocean is the same as nobody could stop me from loving you!"
Ta kasa mance yanayin zumma, karsashi da kwarin gwiwar da yayi magana da su. Da gaske yake magana babu ko kwallin wasa a idanun sa.
Her heart malfunctioned– ta kasa kawo mata takamaiman mafita da za ta yi relying akai.
Tashi ta yi ta nufi zuwa babban parlon gidan zuwa dakin maman su, tun daga nesa take karewa mutumin dake cikin parlorn kallo. So take ta É—auke kan ta daga kan shi amma ta gagara yin hakan, ji take kamar an daure kan ta kyam zuwa ga fuskar shi. shima kallon ta yake murmushi manne a fuskar shi har ta karaso cikin parlon. The more she came near the more their resemblance with sir abdul appear.
"My daughter-in-law an fito?" Ya fada murmushin da ke akan fuskar ya ƙi disappearing.
Da kyar ta fisgo gaisuwar da tun da ta fara tunkaro cikin parlon take ta kokuwar ta furta ta.
"Good evening." Ta fada tana dan rusunanawa.
"Good evening, dear. Hope you're doing well." Daga kai kawai ta yi bata iya amsawa ba.
A cikin ranta kuwa, wani tukuki take ji, yan hanjin ta na juyawa, lokaci daya taji dan kwanciyar hankalin da yayi saura yana bin iska, zuciyar ta ta kara saurin bugu, idanun ta suka canza, wasu sabbin hawaye suka fara zarya a gefen idanun ta suna jiran umarnin sauka.
"Zo ki zauna nan."ya fada yana nuna mata kusa da shi–muryar dad din ta ya katse ta daga dan gajeren tunanin da ta tafi.
A hankali ta karaso gurin ta zauna. Tana raba idanun ta cikin parlon kamar mara gaskiya. 'Yes tasan cewa da gani suna tattauna magana ne game da ita, amma menene fa'idan kuma kiran ta ta zauna anan din' Fatima ta tambayi zuciyarta.
"Wannan shine Alhaji Sa'ad, mahaifin Abdul Rahman,,,, yazo nan ne akan tambayar aurenki, sannan ni kuma na bashi, har mun yanke ranar da za'a daura aure. So, nan da wata daya mai zuwa insha Allah za'a daura maku aure ke da Abdul Rahman."
Kasa dago kanta ta yi daga kasa, wasu zafafan hawaye Masu dumi suka cigaba da wanke mata fuska, her hands began trembling but, babu wanda ya lura da hakan.
Take wani zazzaɓi mai zafi ya dirar mata. 'Wannan wace iriyar rayuwa ce? A wofantar da mutumin da kake so kuma a nemi a ƙaƙaba maka wanda ko kadan baka jin son shi a ranka'
Sun kusan minti goma anan gurin zaune suna kara tattaunawa a tsakanin su kafin Malam Sa'ad yayi sallama ya bar gidan.
Itama tashi Fatima ta yi rai babu dadi ta nufi upstair, part din maman su. Kafin ta shiga ta tsaya daga waje ta daidai kanta.
Bakin ta É—auke da sallama ta shiga gidan. Zaune Hajiya Rabi'atu take akan dadduma, she had just finished pray tana zaune akan daddumar tana lazimi. Juyawa ta yi don ganin mai shigowa.
"Barka da yamma, mum." Fatima ta fada tana kokarin boye damuwar da ke kan fuskar ta.
"Kada mata kai kawai ta yi, ta cigaba da lazimin ta." Zaman kusan mintuna sha biyar ta yi sannan ta shi ta nannade daddumar ta ta ajiye ta inda ya kamata ta koma saman kujera inda Fatima take tace,
"Ya kike, kin yi sallah ko?"
"Eh na yi, " she lied.
Waige-waige Fatima ta fara yi, tana duba parlon a natse. She had come there for a purpose. She wanted to steal away her mum's phone.
Can ta hango wayar an jona ta caji. Tasan cewa mum dinta ba wai damuwa ta yi da rike waya ba. Indai kaga ta waiwayi wayar ta, to akwai dalili, either she wants to call someone or she's going to pick up an incoming call.
"Su Fatima sun gama abinci ne, yunwa nake ji," Fatima ta fada tana yastine fuska.
Kallon ta Hajiya Rabi'atu ta yi na dan lokaci, sai kuma tace,
"To ko Alhaji yace zai aura maki jaafar din naki ne?"
Sai da gabanta ya fadi, domin ta fama mata targaden da ke a zuciyar ta. Dake wa tayi ta kakalo fake smile akan fuskarta cikin shagwaba tace,
"Kai mum, dan Allah mu bar wannan maganar."
"A'a ya kamata ayi, yaushe rabon da kinemi abinci a gidan nan, saide fa wanda yaga Allah yaga Annabi ya diba ya kai maki, hatta dan kitchen din nan ma baki shiga yanzu kin barwa yara su Khadijah da Khairat saide su yagwangwana yanda suka ga dama, na bawa Alhaji shawarar a kawo yar aiki ko ɗaya ce amma ya ƙeƙashe kasa yaki yadda." Hajiya Rabi'atu ta fada.
Murmushi kawai Fatima ta yi., a zahiri sauraren abinda mahaifiyar ta ke fada take amma kuma a badini waccan wayar da ke akan caji kawai take hange.
Mikewa Hajiya Rabi'atu ta yi ta fice daga parlon, dama jiran fitar ta Fatima ke yi, yana fita kawa tayi tsalle ta ruga gurin wayar ta dafe ta, ta boye a hijab ta dawo ta zauna.
Dauke da abinci ta dawo ta ajiye mata a gaban ta tace,
"Ga yanan ki ci, da kikace baki ji, yar bantan uba." Hajiya Rabi'atu ta fada teasingly.
Murmushi kawai Fatima ta yi ta dauki abincin ta fara ci, ci kawai take domin kujewa zargi. She really needs the phone. So ba zata so a ganeta ba.
Tana gama cin abincin ta mike tace, mum Isha'i ya kusa bari naje na yi alwala. Fatima ta mike ta wuce zuwa dakin ta.
9 PM, zaune take akan katon gadonta tana saka number sa da ta riga ta haddace zuwa cikin wayar da ta É—auko.
***
Zaune yake a kasa, ya mimmike kafa kofi a tsakiyar cinyoyin sa, ga wata ƙatuwar kwalba a gefen hannun sa na dama.
Wayar shi ce ta kara kuka a karo na biyu ya mika hannunsa ya jawo ta daga karkashin sa, ko tsaya kallon number bai yi ba ya daga.
"Hello." Ya fada cikin disashewar murya.
Daga can b'angaren fatima tace,
Hello, jaafar nice, ko har ka fara bacci ne?" Ta tambaya jin yanayin fitar muryar shi.
Kara gyara zama yayi sannan ya tattara duk wata sauran nutsuwar shi ya maida ta kan Fatima.
"Eh wlh. Fatima na kira wayar ki so babu adadi amma ba ta shiga, kwace maki ita suka yi ko?" Ya tambaya muryar shi na fita da kyar.
"Ba wannan na kira mu tattauna ba jaafar, jaafar iyaye na nema suke su yi min auren dole kamar yanda suka kudurta yau sun saka min ranar aure nan da kwana talatin,,,. Ko ka daina so na ne?"
Ta tambaye shi, jaafar da maganar ta daki dodon kunnen shi tasa ya watsake daga mayen da ya shiga yace,
"An bayar da ke Fatima?, nan da kwana talatin? Please tell me this is jocking, dan Allah ki ce kawai pranking dina kike Fatima."
"Jaafar dagaske nake wlh, we need act fast, akowane dakika lokaci kure mana yake karayi."
Shiru jaafar yayi na dan lokaci sai yace,
Fatima, rain or shine, I'll never ever let you go of me, zan yi duk wani abu mai yiwuwa na ganin na mallake ki, the mission will start, so get ready. Sai da safe." Daga haka ya katse wayar shi yayi relax anan gurin yana tunani yanda gobe zata kasance, and sannan yana addu'ar samun nasara.
Fatima mamaki ta cika da shi, to me yake shirin yi? Me yake nufi da 'the mission will start tomorrow, wannan wane irin mission ne,? Menene ya shirya? Bata da amsar tambayoyin dan haka ta koma kan gado ta kwanta tana addu'ar Allah ya bashi nasara.
__Jaafar was in a desert area, walking tirelessly barefoot and the dust of the Sahara whirlwinding and splashing all over him. Ƙishirwa, gashi babu gida gaba babu gida baya, babu wanda zai kawo agaji. Tun yana iya tafiya da kafafun sa har ya fadi ya koma rarrafa. All of sudden. Wani katon rami ya bayyana a gaban shi, and begun eroding toward him. Da sauri ya fara jaa da baya trying to escape himself from fallen into the hole, but bakin alkalami ya bushe. afkawa yayi cikin katon ramin.__
Da sauri ya farka daga mugun mafarkin da yake, zufa duk ta rufe shi. And remnants of the dream were still unshakable in his heart.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raajiun" ya fara ambata. Ji yake kamar a zahiri abun ya faru, bit by bit yake revising abinda ya faru a mafarkin. 'To me wannan mafarkin ke nufi?' ya tambayi kanshi...
Masu fassarar mafarki Please a fassara mana a comment section🥰...
Follow the NOVELS LIBRARY. channel on WhatsApp: ***
***
To be continued.