JAAFAR🌹 By Buhari Yusuf IBr
Jafaar
JAAFAR🌹
THE OBSESSION9
By Buhari Yusuf IBr ✍️
...09
'Hakan wata alamace ta wani katon ibtila'i, masifa ko kuma wani abu daban yake tunkaro ni?.' jaafar ya tambayi kan shi.
Tun lokacin da ya farka daga wannan mafarkin mai ban tsoro, bai kara runtsawa ba, koda yayi ƙoƙarin hakan, tashin hankalin abinda ya faru a mafarkin ne yake kara replaying a cikin kwakwalwar shi.
Bashi daga cikin mutanen da suka yadda cewa; akwai mafarkin mai ma'ana da har zai iya zama gaskiya, amma a karon farko zuciyar shi tana so ta karyata wannan yardar. He definitely spotted the intense alarm from that dream, tabbas akwai wani abu da ke shirin faruwa. Ya yadda cewa akwai wani bala'i da ke kusanto shi, to amma daga ina?, hanyar da ya biyo domin mallakar Fatima– the apple of his eye? – 'No ba shi bane.' to ko kuma yunkurin aurar da Fatima da ake yi? Dole dai akwai wani abu da ya ɓace min a lissafi. Ya fada yana mikewa daga zaunen da yake ya fara zagaye parlon yana kara nutsa kwakwalwar sa domin ta gano masa wata makama. Ya kai kusan mintuna uku, pacing around the big parlor. Tsayawa yayi 'Fatima's claim that her dad found out his father was not his biological father.'
"Son, tunanin me kake haka? Baka fita aiki bane yau?" Hajiya Fatima ta tambaya tana masa kallon kuralla as if she wanted to look beneath his heart and see his mind.
"Yes mum, ban fita ba."
Kallon breakfast din shi ta yi dake akan dining table har yanzu bai dauka ba, sai kuma ta kara kallon shi tace,
"Son, me ke faruwa? Fada min. Hope it is not about that girl." Ta tambaya tana shafa gashin kan shi just to make him composed.
Girgiza kai yayi yace,
"Not about her, mum. I had a dream last night, a terrifying one. Na kasa mancewa da mafarkin ko daya, ji nake mafarkin yana dawo min– so fresh– a cikin kwanya ta. Ina ganin kamar mafarkin yana da wata boyayyar ma'ana amma na kasa ganota."
Hannun shi ta kama zuwa kujerun da ke kusa ta zaunar da shi, calmnessly ta tambaye shi,
"Wannan wane irin mafarki ne, son? Tell me, may be I can offer help."
Gyara zama jaafar yayi sannan ya É—an yi tunani na seconds da baifi bakwai ba ya fara fadin,
"Na yi mafarki; na ganni cikin sahara babu kowa sai ni kadai, babu bishiya kwalli daya da zaka shiga domin samun sassauci daga azababbiyar ranar da ake talakawa, babu gida. Tafiya nake babu takalmi duk da yanda yashin gurin ya dauki zafi, ga ƙishirwa ga yunwa, tun ina iya tafiya har na koma rarrafe, kwatsam! sai ga wawakeken rami a gaba na ya bayyana, ya fara waftawa yana yo kaina, ina jaa da baya har aka zo lokacin da karfi na ya kare na fada ciki."
Hajiya Fatima kallon shi kawai take, tana sauraren shi.
"Yes, this dream seemed meaningful but sanin ma'anar sa sai waÉ—anda suka san fassarar shi, but ka kwantar da hankalin kada ka damu, everything will come and pass, okay."
Daga kai yayi alamar gamsuwa sannan tace,
"Now tashi kaje ka yi breakfast ka wuce office, naji dad din ka yace kuna da meeting a company."...
***
Scorpion ne tsaye su kuma sauran gang din suna a zaune akan kujere kowa ya nutsu yana sauraren bayanin sa.
"Bana son mu yi rashin nasara akan wannan aikin guys, like I said last time, if we play our cards well, money will fill our bank accounts, we'll get double payments. So please, I don't want even a little mistake from you all."
"Yes, scorpion. Ba ka da matsala " suka fada in chorus.
"And,,,, all of u know our rules, ko anyi mistake, aiki ya kwabe, bama kama sunan wanda muke yiwa aiki kawai ka mika wuya, kada kace komi kuma kada ka yi komi, our bosses will take care and settle the rest."
"Kullum sai ka fadi hakan scorpion just go straight, tell us the mission is on hand." Wani daga cikin gang din ya fada.
"Okay, mission din shine; We'll divide into two, rabi commanda zai jagorance su zuwa gidan su Alhaji Yusuf– na tura maku address din gidan–, buzu, ƙaura, bahago da devil kune za kubi commanda." Jakar goyo ya dauko daga gefen shi ya bude ya ciro pistols guda bakwai da keyn mota ya rarraba musu.
Sannan ya cigaba da bayani,
"Zaku tsaya kofar gidan har sai kun amshi umarni daga guri na,,, sannan koda na bayar da umarni ku bari sai kunga fitar mai gadi daga gidan. mun baku bindigane ba don ku harba ba sai don ku tsorata mutanen gidan, sannan za mu yi kokarin fitar da mai gadin saboda ba mu san wane irin makami ne gare shi ba. Kamar yanda nace, bama son a harba bindiga, domin karar zai iya sawa aikin mu ya kwabe. kun fahimta?."
Duka suka amsa da "Yes scorpion."
Juyawa scorpion yayi ya nuna wani baƙin mutum kakkarfa yace,
"Black zaka taho tare da ni zamu tsaya kan babban titi, inda muka samu labarin cewa tanan Sadiq yake zuwa," sannan ya kalli commanda yace,
"Comanda kune ke da alhakin sanar da mu idan ya taho"
"Sai kuma shamuloki, Mrs,chain da labaran zaku yi normal shiga, wanda babu wanda zai zarge, daya ya tsaya daga farkon layi daya kuma ya tsaya karshe, idan kuka danger, let us know, sai kuma daya zai taho tare da mu, amma shima zai tsaya daga nesa. Kun fahimta?" Duka suka amsa cikin kwarin guiwa da gamsuwa da duk wani tsarin sa.
"Good! Now is almost 8am zuwa 8:40am kowa ya ya zama ya isa gurin sa." Yana fadin haka ya fice daga parlon suka suka bi shi domin shiri...
*
Everybody stayed in a place he was ordered to stay, commanda shi da tawagar sa and scorpion da shi da Black.
Zaune scorpion suke a cikin mota JP kowane ya makala Bluetooth a kunnen sa, suna dan nesa kadan daga gidan. mutum daya a waje ya tsaya kusa da gidan, waya kare a kunnen sa kamar mai yin waya da gaske.
9:19pm dot mai gadi ya fara buÉ—e katon gate din gidan, hancin motar Sadiq ya kunno kai daga cikin gidan. Hankalin mutumin da ke wandering tun dazu wajen ya dawo kan motar.
"Sadiq is out, I repeat, sadiq is out, LAG09AD is his flat number," mutumin ya maimaita yana barin kofar gidan.
"Copied", commanda ya fada, ya juya akalar kiran sa zuwa ga scorpion.
"Scorpion, Sadiq yana yowa ta nan gurin ku– nan da mintuna bakwai approximately, flat no. LAG09AD,"
"Copied." Scorpion ya amsa.
Zaune scorpion yake cikin mota daga gefen titi, ya tada ta ya bar tana slow. black yana daga can baya, nesa da su kadan, headphone manne akan shi. duk da waya ce a hannun shi, Amma hankalin shi na akan titin, yana lure da motoci da ke wucewa lokaci bayan lokaci.
Number motar ya hango daga nesa, kallon ta yake har sai da taxo dab da shi, sannan ya duba photon da ke cikin wayar shi ya kara kallon mutumin da ke cikin motar domin tabbatarwa.
"Sadiq na karasowa zuwa inda kake, zan maimaita Sadiq na karasowa gurin ka."
Tayar da motar scorpion yayi ya hau saman titin, gaba daya yayi blocking din hanyar.
Tun daga nesa Sadiq ya lura, duk tunanin sa mai motar yana so yayi reverse din motar ne, don haka sai ya fara taka birki a hankali har ya iso dai-dai inda motar scorpion take ya tsaya. Bude kofa scorpion yayi ya fito daga motar ya tunkaro motar da Sadiq yake ciki, hannun sa na cikin aljihun sa.
"Down your glass." Scorpion ya fada yana gesturing da daya hannun shi.
A hankali jaafar ya fara zage glass din motar, domin jin abinda mutumin zai fada.
Scorpion ya ciro daya hannunsa daga aljihu ya nuna Sadiq da bindiga cikin muryar rashin imani yace,
"If you dare move for even an inch, I'll gun you down, handsome man." Scorpion ya fada ciki ciki yanda shi kadai zai iya jin abinda yace.
"Who are you? Me nayi maka malam? Ba ni kake nema ba wata kila ka yi kuskure," Sadiq ya ya fada as his whole body began trembling.
"You should better keep quiet, and help yourself. Ka fito, ka shiga cikin motar can, bana son hayaniya. Your scream could also cut your life short." Da sauri Sadiq ya fara kokarin fitowa daga motar ya nufi motar da ke a parke a gaban su, hankalin shi tashe.
Shiga yayi backset din motar shi kuma scorpion ya shiga gaba still bindigar na kan Sadiq. Black da ya iso gurin tun dazu ya jaa motar suka bar layin.
Saida suka É—an yi tafiya mai tsayi tukuna black ya shiga wani lungu yayi parking motar.
Shima Black fiddo tashi pistol din yayi ya nuna Sadiq da ita, in a nasty voice black said,
"Bani wayar ka,"
Hannun shi na rawa ya ciro wayar daga aljihun sa ya mika ma Black. Bai amshi wayar ba, yace,
"Unlock it, go to your contact list and dial your father's number." Ya bashi umarni fuska a murtuke.
Hannu na karkarwa ya fara cire keyn wayar but three attempts amma keyn wayar yaki ciruwa. hankalinsa a tashe.
"Kwantar da hankalin ka, idan kaga mun cutar da kai to ka sabawa umarnin mu ne. so, be careful." Scorpion ya fada bayan yaga hankalin shi yaki nutsuwa yama gagara fidda securityn wayar.
Finally, ya samu ya cire security. Hannun na rawa ya shiga cikin contact list din shi– kamar yanda suka umarta– ya dial din number ta fara, ringing.
Mika hannu scorpion yayi ya warce wayar ya kara a kunne sa yana jiran a dauka.
"Son, me ya faru? You just left home and now....,,,"
"Your son was abducted Alhaji Yusuf. Yana hannun mu, and you are the one will decide,,, zai rayu ne ko kuma mutuwa zaiyi.
"What!? Abducted? Sadiq din" Alh Yusuf ya fada muryar shi na karkarwa.
"Kana mamaki ne?,,, okay bari kaji muryar sa." Scorpion ya fada ya kanga wayar kusa da Sadiq yace, "yi magana!"
"Yess,,, dadddy,, ina hannunsu..." He stammered.
Dauke wayar daga gefen Sadiq yayi yace, "yanzu ka tabbatar ko, ya rage naka yanzu ka saurare ni ka yi min biyayya domin tseratar da rayuwar yaron ka, ko kuma kaƙi saurare na ka bijire min ni kuma na kawo karshen rayuwar yaron ka."
"Insha,, Allah. zannn yi duk abinda kace." Alhaji Yusuf ya fada.
"Yanzu ruwan kudi nawa ne a cikin gidan ka?" Scorpion ya tambaya.
"Ban sani ba amma nasan da kudi."
"A kiyascen za su iya kaiwa nawa?" Scorpion ya tambaya again.
"1Million haka." Alh Yusuf ya fada wata zufa tana gangarowa daga ciki hular shi zuwa kan fuskar shi.
"Ku nawa ne a cikin gidan yanzu haka"
"Ni, da yaya na su uku sai kuma uwargidan." Ya fada muryar shi a tsorace.
"You excluded gate man, isn't he a human? And you didn't mention the maids..."
"Wlh babu yan aiki a gidan, saide me gadin. Ka yi hakuri wlh mancewa na yi da shi." Ya fada Hankalin shi a tashe.
"Okay, give him that one million, kaima ka biyo shi ku taho tare, zan kara kiran ka. Mintuna goma na baku. Na rantse da Ubangijin al'arshi Ubangiji Musa da Haruna, idan ka sake ko da wasa ka fadi ma police, hmmm, your son and you...... Ba sai na karasa ba." daga haka ya katse wayar.
Kira ne ya shigo a wayar scorpion ya dauka. "Scorpion ga yanan yanzun nan motar su ta fice daga gidan, da mai gadi da kuma shi Alhaji Yusuf din." Commanda ya fada.
"Good, yanzu zaku iya shiga, sauran duk mata ne"
Tada motar suka yi suka zo dai-dai kofar gidan suka yi parking din ta mutum hudu suka shiga aka bar driver nan waje...
Gaba dayan iyalan gidan– harda Fatima suna zaune cikin katon parlon sun yi jugum-jugum. Suna jiran abinda Allah zai yi suka ga an bude kofa an shigo kowa da bindiga hannun shi, kururuwa suka fara yi, devil ya saita su da bindiga yasa hannun shi daya a baki "shiiiiiittttt, duk wacce ta kara min ihu, ko wani sautin da ban gamsu da shi, zan harbe ta a gurin nan." Devil ya fada, fuskar shi babu wasa.
Cikin tashin hankali kowace ta kama bakin ta, duk da sanyin ac da ke dakin amma da ka kalli fuskokin su za kaga kowace gumi take...
"Ke, come over" commanda ya fadi yana nuna Fatima da bindigar da ke hannunsa.
Tashi ta yi, jikin ta na rawa ta zo, ya nuna devil yace,
Raka ta cikin mota, tana yi maka gardama ko hauka, ka harbe ta, this is an order.
"Yes, sir." Ya fada sannan ya nuna ta da bindiga yace,
"Lets go Madam."
Bayan wucewar su sai da suka tabbatar da ya isa gurin motar sannan suka fice daga gidan da sauri sauri. Suna fita suka tarar da mota na slow su kawai ake jira. Suka shiga drivern ya tada motar ya fisgeta da gudu suka bar layin.
A bangaren scorpion kawai yana amsar sakon daga commanda akan aikin su yayi nasara ya kalli Sadiq da ke zaune cikin mota hankalin shi tashe yace,
"Get out." Kallon shi Sadiq yayi cikin rashin gamsuwa yace, "Yes, jeka."
"Ba zaku harbe ni ba?" Sadiq ya tambaya cikin rashin nutsuwa. Wata shedaniyar dariya scorpion yayi sannan ya bude murfin motar yace,
"Ka fadawa dad din ka ya tanadar mana kudi kafin mu bukace su." Sannan ya hankada shi waje. Suka jawo karfin motar su suka rufe suka tada motar su suka bar layin a guje...
***