JAAFAR🌹 By Buhari Yusuf IBr

Jaafar

by @buhariyusufibr0

JAAFAR🌹 
THE OBSESSION

By Buhari Yusuf IBr 


...10
***
Zaune suke cikin babban hall ana gabatar da meeting. Alh lawal ne a tsaye yana yin bayani game da kayan su da aka yi seizing a US.
Jaafar kawa bin su da ido kawai yake, amma ko kadan hankalin shi baya a gurin, baya ma fahimtar me ake tattaunawa a gurin.

Karar shigowar text yaji daga wayar shi, zaro wayar yayi daga gaban aljihun shi ya duba, unknown number ce ta turo sakon cikin gajeren bayani da ba zai wuce layi biyu da rabi ba, "work has successfully been done. Fatima is with us."
Wani dogon numfashi ya ja da har na kusa da shi saida suka kalle shi na kusa da shi yace,
"Are you okay, sir." 
"No, no problem at all." Ya fada yana kara gyara zaman shi. ya maida hankalin akan meeting din kacokan. Anan ne ya tsinkayi wani yanki daga cikin jawabin baban shi yana cewa,
"Dan haka, jaafar ba zai je US yanzu ba saboda wasu yan dalilai. Farooq da Shu'ab, za su wakilce shi."
'What!,' jaafar ya fada cikin zuciyarsa but the speech was almost above a whisper.
Daga haka baice komi ba, har aka tashi daga meeting din.

Bayan an tashi daga meeting, jaafar shine ya tuka motar suka hau kan titin zuwa gida shi da Dad din shi, akan hanyar yake tambayar sa menene yasa yace ba zai je US ba bayan kuma yayi duk wasu shirye-shiryen da ya kamata na tafiya?
Kallon shi Alhaji lawal yayi yace, 
"That is the reason, jaafar. Kwana biyu gaba daya baka cikin normal sense naka, that girl came in late time and destroyed your normalcy. Yanzu dai ka duba, duk dogon bayanin da na yi a gurin meeting, da dalilan da yasa ba zan tura ka US ba, amma duka baka ji ni ba. Kazo nan kana kara tambaya ta dalili. Aiki mai mahimmanci za'a je yi a US, dan haka ana bukatar gamsassun bayanai kafin a yi releasing kayan mu, and Farooq can do and handle the case as you can, that's why I excluded you daga cikin masu tafiyar."

Shiru jaafar yayi bai kara cewa komi ba har suka iso gida, mai gadi ya bude masu kofa ya shiga yayi parking motar a inda ya kamata, ya fito ya bude ma Dad din shi, shima ya fito.

Yana shiga wanka kawai yayi– ko da wasa tunanin Fatima bai rabu da zuciyar shi ba, duk kowane second daya, yana jin kamar zuciyar shi na bugawa ne domin ita, bai iya yin zaman mintuna biyar ba tare da tunanin ta yayi masa dillike zuwa cikin kwakwalwar shi ba– ya fito ya koma dining table ya debi abinci yaci. 
Kallon maman su yayi yace.
Mum, bari nazo na dan je wani guri. Ba zan dade ba insha Allah. Ya fada yana daukan makullan motar shi akan teburin.

***
In a house on the outskirts of the city of lagos. birds chirping, and it's silent from human chaos have made the house peacefully. 
Gang din scorpion zaune a waje suna shakatawa ana hira ana dararraku.
"Menene plan din mu na gaba scorpion?" Commanda ya tambaya. 
Wata siririyar dariya scorpion yayi yace, 
"Plan na gaba ya danganta ne da abinda su wadanda suka bamu aikin suka yanke, they promised us that za mu yi ci biyu mu karbi kudin fansar Fatima + mu karbi kudin sallamar mu da gurin jaafar, miliyan 25 muka shirya da shi. And you know that girl, she is the daughter of Alh Yusuf, a well known man, so a karance bamu amshi kudi ba mu amshi 50M."
"Woohoo, sai da kai scorpion." Suka fada tare. 
Black ne ya shigo gurin, hannun sa rike da abinci ya ajiye yace gashi scorpion. 
"Good, my man. Commanda kai ne mai taushin zuciya a cikin mu, dauki abincin nan, ka lallaba ta har sai ta ci. Dole mu lallaba ta yanzu saboda ita din kadarace gare mu. ko b haka ba, guys." Ya juya ya kalle su yana tamabayar su.
"Gaske kawa oga."
"Wannan haka yake"
"Laaa fi hazal kalaam."
Suka bashi amsa kusan a tare.
Daukar abincin commanda yayi zuwa cikin karamin gidan me dauke da kananu kananun shukoki da kuma manyan bishiyu.

Zaune take ta rakube cikin dan salokon dakin ta cusa fuskarta tsakanin cinyoyin ta, tana kuka mara sauti. tayi kukan har ta gaji, tun hawaye na biyowa har sun kafe, tun tana tambayar kan ta su waye waÉ—annan kuma menene suke so daga gun iyayen ta da suka kawo ta nan har ta gaji, saboda babu wanda zai bata amsar tambayar ta.

Jin karar bude kofa yasa ta dago fuskar ta da ta yi jajur tana kallon mutumin da yake shigowan. Gurin ta ya karaso hannun sa dauke da kula da plate na abinci. A hankali ta fara jaa da baya da baya, tsoro bayyane a fuskar ta.
A jiye abincin yayi gaban ta, cikin sanyin murya yace,
"Kwantar da hankalin ki madam, ba cutar dake za'ayi ba." Ya tura mata cooler abinci da plate ya cigaba da cewa,
"daure ki dibi abincin kici, your health is your everything, and it's the matter..."
"Su waye ku? Me yasa kuka kawo ni nan? Me na yi maku?" Ta tamabaya.

"Kici abincin tukuna sai mu yi wannan maganar, kin ji." Ya fada yana debo abincin daga cikin cooler ya zuba a plate ya mika mata.
She quickly shoved away the plate, tace,
"Ba zan ci ba, ban san ku su waye ba, ban sa me ye maufar ku ba, don me ye zanci abincin da kuka bani."

Murmushi yayi ya tashi ya dauko abin shara ya yi mooping abincin da ta ture sannan ya kara zuba wani a plate din yace,
"Kada ki damu Fatima. Wanda ya saka mu yana nan zuwa nan gurin ba da jimawa ba. Kuma shi din ba makiyin ki bane ina da yakinin hakan, saboda na gani a cikin idanun shi, Please, stop reacting this way, ci abinci."
Hankalin ta ya É—an kwanta kadan da kalaman sa, ita kanta ta amince da ba cutar da ita za su yi ba, ta yanda suke tarai-rayar ta tun bayan zuwan ta gurin, amma kuma menene yasa suka baro da ita daga gabn iyayen ta? Shi ne tambayar ta.
Bata kara cewa komi ba, ta mika hannu ta amshi abincin tace, 
"Shi kenan, zan ci." Ta fada a takaice.
Mikewa yayi ya É—an koma daga gefe yace,
"Ina nan ina jiran ki, cos ba zan iya tafiya ba sai na tabbatar da baki cikin barazanar yunwa."...

***
Sir,Abdul ne cikin office din sa zaune yana duba wasu takardu da HOD ya bashi aikin su. Wayar shi ce da ke akan desk ta fara ringing, dubawa yayi yaga sunan Sadiq ne ke yawo a wayar. 
Hannu ya saka ya dauko ya kai kunnen sa bakinsa dauke da sallama. Bayan sun gama gaisawa Sadiq yace,
"An yi kidnapping din Fatima."
Sir, Abdul bai san lokacin da ya tashi tsaye ba, take jijiyoyin maganar sa suka dauke, ya fara jin ka sa na sara masa. Kusan minti ɗaya ya dauka a tsayen yana ƙoƙarin tattaro kalaman sa da suka gudu na wucin gadi sannan yace,
"What did you just say? Taya, ina taje, su waye suka yi hakan?" Sir, Abdul ya tambaya hankalin shi a tashe. 
Numfashi Sadiq ya ja mai kauri daga can b'angaren yace, "mu kan mu har yanzu bamu da waÉ—annan amsoshin Abdul, amma insha Allah muna nan muna bincike akai."
Daga kai sir, Abdul yayi kamar kadangare yace nima ga ni nan zuwa yanzu gidan. Kun fadawa police ne?" Abdul ya tambaya. 
"No bamu kai ga fada masu ba tukuna, abun bai wani jima da faruwa ba, kaine mutum na farko da yasan wannan al'amarin." 
"Bai kamata mu yi sake ba, zan turo maka number CSP,khalid he is a friend of mine, office din su bashi da nisa daga unguwar ku, nima yanzu zan karaso gurin."

**
CSP khalid da tawagar sa mutum biyar suna zaune akan kujera suna sauraren Alh Yusuf akan yanda abun ya faru. Bayan ya kai aya CSP khalid ya daga cikin gamsuwa sannan ya kalli Sadiq da ke a gefe yace, 
"Please can you take me to the right place where they had halted your car?"
"Yes, sure." Sadiq ya fada. CSP ya kalli daya daga cikin yaran shi yace zo muje. ku kuma ku tsaya, ku bincike ko ina cikin gidan, duk kankantar shaida, kada ku yi wasa da ita."
"Yes sir." Suka amsa.

Daidai inda abun ya faru suka je, cikin natsuwa CSP khalid yake scanning din gefen titin da kuma gidaje da suke kusa da gurin– wanda ke da ƙarancin cunkoson mutane duk da cikowar garin Lagos.
"These people were perfectly planned it. Sai da suka tabbatar yankin nan babu wani CCTV cameras tukuna suka zabe shi suka aiwatar da shirin su. And gaba daya ba kai ne plan din su ba. Fatima itace plan din su, kawai sun yi amfani da kai ne a matsayin tsanin da zai kai su ga Fatima, kuma sun samu nasara." CSP Khalid ya fada a dai lokacin da idanuwanshi ke akan gefen titin still yana kara duba wajen ko zai ga wata shaida komin kankantar ta. 
Kusan minti goma yana gurin yana dube dube, amma bai samu komi da zai nuna a matsayin wata kafa da zata taimaki binciken ba. Komawa yayi cikin motar yayi ma Sadiq alama da ya shigo su tafi.

Shiru parlon ya dauka, banda kukan ac da ke dakin babu abinda kake ji, "Alh Yusuf, ina son ka fadi mana, kana da wani mutum wanda baku shiri da shi, wanda kuke faÉ—a haka dai, ko kuma sabani na wajen kasuwanci?"
"Bani da wani abokin fada CSP, gaskiya bani da shi, kaga yanda ka ganni gurin nan haka, to a haka nake, ko tashi bana iya yi na taka da kafafu na. Idan kaganni a waje, to ranar juma'a ne, sai kuma idan wani abun ya kama dole inje– kamar dai yanda ta faru dazu– duk wani kasuwanci nawa ina da yara da suke tafiyar min da shi daidai, kuma Sadiq shine ke wakiltar kome da ya shafi kasuwanci na, so ban tunanin ina da wani da zai iya min wannan danyen aiki."

"Ka yi tunani, Alhaji. Ko kai ko yaran ka." Shiru Alhaji Yusuf yayi ya shiga tunani mai zurfi. A wannan tunanin kwakwalwar sa ta kawo masa hoto jaafar.
"Jafaar! yes jafaar, definitely he is the one done this." Kara kyara zama CSP yayi akan kujerar yace,
"Shi jafaar din waye shi?" 
In brief Alhaji yayi masa bayanin waye jaafar da da yanda yace ba zai aura masa Fatima ba da duk wata takaddama da ke tsakanin su.
"Good, wonderful." CSP ya fada bayan gama sauraren bayani daga Alh Yusuf. 
"Ko zaka iya saka yaron ka ya kai mu gidan su, idan ba damuwa?" 
"Ai wannan ya wuce Sadiq yaje shi kadai CSP, har da ni za'a gidan nan" ya fada yana juya wheelchair din shi zuwa hanyar fita daga gidan. CSP Khalid da mutanen da suka bi bayan shi.
Juyowa Alh Yusuf yayi yace ma Sadiq ya dauko masa file na nan a cikin drawer ya same su waje...

***
Duk yanda jaafar yaso ya fita gidan zuwa gurin Fatima amma abun ya gagara, har ya fita waje ya tayar da mota dad din shi ya kira shi, dan dole ya ya dawo.

Zaune yake yanzu dinma a cikin parlo shi da Alh Lawal suna duba wasu files duk akan tafiyar da za suyi zuwa US ne. Jaafar jin shi yake kamar akan kaya yake zaune. Ji yake kamar ya ɓace daga cikin parlorn ya ganshi zuwa inda Fatima take.
Hajiya Fatima ce ta shigo parlon hannun ta É—auke da abinci ta ajiye akan dining table din tace, 
"Ga abinci na hada kuzo kuci, tun dazu kuke abu daya har yamma ta yi amma baku samu kun ci abinci ba..." 
Knocking kofar da ake yi ne yasa gaba daya hankalin su ya koma kan kofar. Alh lawal ya bada umarnin a shigo.

Mai gadi ne ya shigo har zuwa gurin Alh kawai ya duka cikin ladabi yace, 
"Alh wasu mutane ne wai suke neman ka, akan motar yan sanda suke, sai kuma mutum biyu a cikin mota mai kyau." Mai gadin yayi bayani.
"Yan sanda?, cikin gida na?" Alh lawal ya fada, sai kuma ya kalli jafaar da tun shigowar mai gadin yaji zuciyar shi ya fara bugu yace,
"Ka yi wani abinda ba dai-dai bane jaafar?"
Ni,,,, ban yi komi ba, tun dazu fa muna nan tare da kai dad." Ya fada a dan daburce kadan. Amma idan ba ka lura sosai ba ba zaka taba gane hakan ba.
Tashi Alh lawal yayi ya fita waje. Tun daga nesa yake kallon su har ya karaso inda suke, sai kuma ya maida kallon shi kan Alh Yusuf da ke a cikin mota saboda lalurar kafar sa yace,
"Alh Yusuf lafiya kawa? Kai ne da kanka a gida na a wannan lokacin."

Daga masa hannu Alhaji Yusuf yayi ya kauda kan sa na sakanni daga kallon Alh lawal yace,
"Daka ta malam lawal, stop pretending and call your son to bring back my daughter..."
Kallon shi Alh lawal yayi na dan lokaci, yana tunanin wace irin magana Alh Yusuf yake ne, wace daughter yake magana akai.
"Alh can you elaborate me more, ban gane me kake nufi ba." 
CSP Khalid ne ya karbe zancen yace, 
"Alh lawal can you please fetch out your son" Dan jinkirtawa Alh lawal yayi kamar mai tunanin wani abu, ya bude baki zai yi magana sai ga Jaafar ya bude kofa ya fito. Dakewa yayi ya karaso gurin ya kalle su yace, "good evening."
Harzuƙa Sadiq yayi ya kamo kwalar rigar sa yace, raina mana wayo zaka yi? Mu ne zaka mayar shashashu? Ko dai ka fito da Fatima ko kuma na rantse da Allah sai mun yi duk mai yiwuwa mun daure daga kai har wannan uban naka na bogi."
Kafin CSP ya kai ga kwakumo hannun Sadiq dake kan jaafar shima jafaar din ya cukumi kwalar Sadiq cikin zafin zuciya yace, 
"Waye uban bogi yallaboi? With due respect sir, yanzu a gidan mu kake, kuma a gaban mahaifi na, so bai kamata ka dinga fadin duk maganar da yazo bakin ka ba." Jafaar ya fada. CSP Khalid da tawagar sa ne suka shiga tsakanin jafaar da Sadiq suka raba su. 
Alh Yusuf dake cikin mota yayi dan murmushin gefen baki yace,
"Alh lawal menene amfanin boye masa gaskiyar? kai ba uban sa bane, ba kai ne ka haife shi ba–duk wani evidence yana nan" ya mika ma jafaar file din dake gefen shi "kawai ka fito ka fadawa yaro gaskiya ya nemi mafita kafin lokaci ya kure masa." Kallon Alh lawal jaafar yayi yana jiran yaji martanin da zai maida masa amma shiru. Ya kasa cewa uffan, duk wasu alamun rashin gaskiya sun bayyana a fuskar sa, wata zufa ta fara ɓullowa daga cikin farar rigar sa.

Jaafar ji yayi kamar ya rike wani katon abu mai masifar, ji yayi kan shi na juya masa. And from that moment, he fainted...

To be continued.