Jafaar
JAAFAR🌹
THE OBSESSION12
...12
...rike ta yayi daga yunkurin cakumar da ta kawo mashi, fuskar ta cike da fushi, takaici da kuma tsantsar tsana. Idan akace mata zata tsani Jaafar kafin yanzu, she'd say no and never.
Gam ya rike hannayen ta ta yanda ba zata iya tabuka komai ba, cikin kwantar da murya mai kama da raɗa yace,
"Fatima ki kwantar da hankalin ki, please. Believe me, this is the only way out. Abdul nema yake ya tarwatsa komai, don Allah kada ki lalata mana tsari kema, I believe this'll work for us." Ya karasa maganar kamar yana shirin yin kuka.
Fatima kuka take yi sosai tsabar tashin hakkali har sauti ya daina fita, bama sauraren abinda yake fada take ba, her heart now filled with regret; da na sani take na sanin shi a rayuwar ta. Ji take ta tsane shi, ba ta son ganin shi—bama shi ba, duk wani mai hali irin wannan shima ji take ta tsane shi...
**
Bayan kwana biyu, Scorpion da yaran shi zaune suke suna kirga makudan kudaden da Jaafar ya kawo masu a matsayin sallama.
"Oga nan sun cika cass," Black ya fada yana maida rafar yan dubu-dubu da ya irga zuwa cikin jakar goyo ya zuge.
"Yanzu Alh. Yusuf ya rage. Yace zuwa yamma zai hada 75m, amma ina zargin yana hulda da police a hidimar sa. Ya kuke ganin zamu yi masa?" Scorpion ya tambaya yana kallon su.
Kowa shiru yayi ya shiga nazarin mafita. Commanda ne ya mike ya kalli Scorpion yace, "Ba zai gagara ba ai, akwai yanda za'ayi Scorpion, amma akwai kasada."
"Muna jin ka, Commanda," Scorpion ya fada.
"Zamu tura account number din Busayo Moses yanzun nan—I have full access to her account because she was my wife before she died, kuma nine next of kin din ta. Amma kafin nan, zamu tura dan leken asirin mu zuwa gidan Alh. Yusuf to make sure babu police din da yazo, and zamu yi masa barazanar kashe ta muddin har yayi gigin fada ma wani dan sanda ko wata hukuma. Ni kuma awa daya zata wadace ni naje na cire kudin sannan na yi transfer su a wani account din, sai kuma na goge account din gaba daya."
"Wow! BINGO! What a great plan!" Suka hada baki wajen fadin hakan, wasu kuma suna murmushi.
"That is why I love you so much. Kan ka na aiki," Scorpion ya fada bayan ya gama tusa abinda Commanda ya fada a kwakwalwar shi.
Kamar yanda Commanda ya tsara, haka suka aiwatar and the mission was successfully completed.
Parking yayi a daidai kofar gidan Alh. Yusuf ya waigo ya kalli Fatima yace,
"Hajiya mun karaso. Nan suka ban address din na kawo ki." A hankali ta bude idon ta da suka yi mata nauyi ta kalli kofar gidan ta tabbatar nan din ne, sannan ta fara kokarin fitowa.
Ganin ba zata iya tafiya da kanta ba yace,
"Madam ko ayi magana ciki wata tazo ta taimaka maki?"
Bata ce komai ba, kawai komawa tayi cikin motar ta zauna, resting her head on the car seat.
Fita yayi yayi knocking gidan, mai gadi ya leko. Mai taxi ya nuna motar shi yace,
"Please, matar da ke cikin motar can za'a taimaka mawa a kira yan uwan ta su dauke ta. Kamar bata da lafiya," ya fada innocently.
Lekawa mai gadin yayi don ganin wacce mai taxi yake magana akai. Saida ya kalleta sosai tukuna ya tabbatar da Hajiya Fatima ce. Da sauri ya koma ya nufi babban parlon gidan da gudu.
Duk mutanen dakin waigowa sukai suna kallon kofar don ganin wanda ya banko ta ba tare da sallama ba.
"Lafiya?" Sir Abdul ya tambaya yana mikewa tsaye da sauri.
"Hajiya Fatima ce wani mai taxi ya sauke yanzu," ya fada yana maida numfashi na gudun da yayi.
"Ka barshi ya tafi?" CSP Khalid ya tambaya. "A'a yallabai, nace ya ɗan jira, yana ƙofar gida." Da sauri mai kama da gudu, Khalid ya fita daga parlon zuwa waje. Khadijah da Khairat suma suka rufa masa baya.
Khalid Fatima ya fara dubawa sannan don tabbatar da lafiyar ta, sannan ya koma kan driver taxi din ya tambaye shi,
"Waye kai? A ina ka ganta ka dauko ta?" Kallon shi mai taxi yayi yana mamakin wannan wace iriyar tambaya ce ake masa.
Ciro ID card Khalid yayi daga aljihun sa yace, "I'm CSP Khalid. Wannan yarinyar da ka dauko anyi kidnapped din ta kwana biyar da suka wuce and the ransom of 75 million has been paid. So, we're inviting you to our office don amsa wasu yan tambayoyi."
Zaro idanu mai taxi yayi ya kara kallon Fatima da ake kokarin shigewa da ita zuwa cikin gida, sannan ya kara kallon Khalid yace,
"Yallabai ni ban san komai ba game da ita, ka yadda da ni..."
Daga masa hannu Khalid yayi yace, "Ba anan ba ya kamata, shiga ciki. Can we please go inside?" Ya fada yana nuna masa zuwa cikin gidan.
"Muna jin ka," Khalid ya fada yana kallon driver taxi din.
"Alhaji, ni wallahi ban san komai game da abinda ke faruwa ba—zaku iya tambayar ƴar ku. Kawai ni dai wani mutumi ya tsaida ni ya bani address din layin nan yace min na kawo ta gidan Alh. Yusuf. Kuma kusan kowane mai taxi ka tambaya musamman dan Arewa zai iya fada maka waye Alh. Yusuf. Yace min ai ƴar shi ce na kawo ta nan layin bata da lafiya ne, shine fa kawai na kawo ta. Bayan haka na rantse da Allah ban san komai ba, ban taba tunanin sace ta aka yi ba..."
Shiru dakin ya dauka na tsawon minti ɗaya. Sir Abdul ya kalli Khalid yace,
"Wadannan mutanen za su kamu kuwa Khalid? Account din da aka tura masu kuɗi sun goge shi. Mun tambaya ance gaba daya mai account din ta mutu shekaru biyar baya. Kuma ita da mijin nata dukan su ba yan Nigeria bane. Yanzu hoton shi kawai gare mu na camerorin banki da suka dauka; wane tabbaci muke da shi cewa shi din a Nigeria yake zaune?"
Shiru gaba daya dakin ya dauka kowa ya tafi tunani.
"Fatima, ba zaki iya gaya mana inda suka aje ki bayan sun yi kidnapped din ki ba?" Fatima da ke zaune akan kujera abin duniya duk ya ishe ta, tana tuna abinda ya faru tsakanin ta da Jaafar tace,
"Ni kawai gani na nayi a cikin daki. Ba zan iya gane gurin ba, kuma tunda naje basu bari na fito waje ba. Da kuma zasu sako ni, saida suka min allura suka tabbatar da bani a hayyaci na tukuna."
Kowa shiru yayi. Khalid ya amshi address din mutumin sannan yace masa za'a neme shi idan bukatar hakan ta tashi...
Zaune Jaafar yake kan kujera, zuciyar shi tana masa zugi. Zafi biyu ya hadu masa: barazanar Fatima kan ta tsane shi ba zata iya rayuwa da shi ba, sai kuma ta bangare guda, son gano shi wanene yana tsunkulin shi. Tun safe ya kamata ace ya fita aiki amma gashi har yamma tayi ya kasa fita ko ina. Hajiya Fatima ta yi juyin duniya ya daure yaci abinci ko ba yawa amma yaki ji. Ji yake ko yaci abincin saide ya cuci kan shi kawai, ba dadin abincin zaiji ba. Shi a yanzu pressure da ke kanshi kawai ya wadatar ya hana shi jin wani abu wai shi yunwa.
Kofar babban parlon aka buɗe aka shigo. Tun daga nesa Alh. Lawal ke kallon Jaafar har ya karaso cikin parlon ya ajiye jakar shi. Hajiya Fatima ta zo ta dauka ta yi barka da dawowa; ya amsa amma hankalin shi na kan Jaafar.
"Lafiya Jaafar? Yau ban ganka office ba?" Alh. Lawal ya tambaya.
"Yes dad, ban samu zuwa ba saboda ko naje ba zan iya aikin ba."
"Lafiya ko?" Alhaji Lawal ya tambaya.
"Lafiya lau, Dad. Dama game da abinda Alh. Yusuf ya fada ne kwanaki... nake so ka fada min su wanene mahaifina?"
Shiru Alh. Lawal yayi yana kallon Jaafar, sai kuma yace,
"Jaafar, ka rasa wani abu ne? Mun gaza yi maka wani abu ne da ka bukata?"
"No, Dad. Kunyi min duk wani abun da ya kamata ace ɗa ya samu a wajen iyayen sa. Ni kaina zan so ace banji wannan labarin ba, amma kuma tunda har na riga naji, ai ya kamata na san ni waye, ko?"
Mikewa Alh. Lawal yayi yace, "Ban sani ba. Kaje ka tambayi wanda kaji labarin gurin sa. Shashashan banza, shashashan hofi!" Ya fada ya tashi ya shige dakin shi...
Kwanaki suna tafiya, auren Fatima da Sir Abdul na kara matsewa. Tana jin a jikinta cewa ba zata iya rayuwa ba tare da Jaafar ba, amma kuma ta dake ta tankwara zuciyar ta akan lallai zata iya.
Jaafar ya yi kiran duniyar nan taki daukan wayar shi, daga karshe ma sai ta kashe wayar layin ya daina aiki kwata-kwata.
A hankali yayi parking a kofar gidan, ya fito ya ɗan leka kanshi cikin gidan babu kowa. Sai ya ɗan kwankwasa. Mai gadi ne yazo ya tambaya "Lafiya?"
Murmushi Jaafar yayi yace "Lafiya lau. Alhaji na ciki kuwa?"
"Ba ya nan, amma nasan yanzu haka yana dab da dawowa," mai gadin ya bashi amsa.
Jaafar really wants to see Alhaji; he's the only person who would tell him shi din wanene.
"Okay, let me wait for him in his guest room. Ga mota ta nan waje," ya fada yana shigewa ciki.
Tunda ya shigo dakin, idanun shi akan ta ya fara sauka tukuna ya kalli Sir Abdul dake kusa da ita. Wani zafi yaji a kirjin shi lokaci daya; yaji yana nema ya rasa nutsuwar shi. Yana so ya koma amma ji yayi kamar ana kara fisgo shi ya shigo cikin parlon.
Dukan su yake kallo; ya danne abinda yake ji ya karasa shigowa ciki yace,
"Barkan ku." Babu wanda ya amsa mashi daga cikin su tsabar shock and thinking about what has brought him here.
Kujerar gefe dan nesa da su ya samu ya zauna ya ciro wayar shi yana dannawa. Yes, physically he's pressing his phone, but a hakikanin gaskiya kuwa su yake sauraro. Fatima kuwa, ko ɗar na shakkar sa bata ji ba, ta saki jiki suka cigaba da hira da Sir Abdul, wanda ta gagara yin hakan kafin shigowar sa.
Ji yayi zuciyarsa na masa tukikin zafi, idanun sa suna lumshewa tsabar takaici. Yana so su hadu da Alh. Yusuf amma kuma bai jin zai iya danne abinda yake ji a zuciyarsa.
'Shi Fatima take son taci amana? Me yayi mata haka? Don kawai ya aikata abinda yake ganin shine daidai, shine zata saka mashi da wannan abun?' ya fada cikin zuciyarsa.
Mikewa yayi yazo gaban su ya tsaya yace, "Fatima, gurin ki nazo." Shiru ta yi tana kallon sa na dan lokaci, sai kuma tace,
"Kazo fada min ka nemo mahaifin ka ne?" Ji yayi wani mugun abu ya caki zuciyar sa. Take idanun sa suka canza launi, ya kalle ta cikin dakewar murya yace,
"A'a ban nemo ba Fatima, amma ina kan hanya. Kin san ina son ki, dan Allah kada ki min haka," ya fada yana daga hannayen sa biyu sama alamar roko.
"Unfortunately, Jaafar, I regret to inform you of this: I have already made up my mind. I no longer have any feelings for you. I can't marry you... please leave me alone." Ta fada tana nuna masa hanyar fita daga guest room.
Murmushi yayi mai kama da yake sannan ya kalli Sir Abdul, sai kuma ya kara kallon ta yace,
"Kin fada masa abinda ke tsakanin mu ko, ko ni na fada masa?" Ya fada yana kallon Sir Abdul da ya kama bakin shi yayi shiru yana kallon sa. Deep down in his heart, yana jin dadin duk wani musayar yawun da ke faruwa a tsakanin su...
Let me know tonight...
Buhari Yusuf IBr ✍️