AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Page 11
Yau ta kama Monday, ranar da Zahra zata zana final exams ɗinta. Da sassafe ta farka daga bacci, ta miƙe da jan jiki ta yi sallar Asuba. Bayan ta idar da sallarta, ta zauna a kan darduma tana mai addu'oi cikin natsuwa.
“Ya Ubangiji, Ina godiya da aron rayuwa da Ka bani har na wayi garin wannan babbar rana da zan zana jarabawa ta ƙarshe as an undergraduate. Yau rana ce mai muhimmanci a gare ni da masoya na. Allah Ka bani nasara a wannan jarabawar da zan rubuta. Ka shiryar da lamurana gaba ɗaya, ka yi min tuni a gurin da na manta, Ka yi mini jagora.”
Ta zauna har saida zuciyarta ta yi sanyi sannan ta miƙe don fara shirye-shiryen tafiya makaranta, domin paper ɗinta na safe ne.
Ta zabi wata doguwar rigar material ruwan sararin samaniya wanda aka yi masa ɗinki mai tsari da kyau, aka kuma ƙawata gabansa da duwatsu masu waiƙiyya. Tana gama shirin ta sauko zuwa kitchen inda masu aiki ke faman hidimar haɗa breakfast.
“Ina kwana Mama Ladi,” ta faɗa cikin ladabi.
Mama Ladi, wacce ke tsaye a gaban tanda tana zuba ƙullun wainar masa, ta juyo da fara’a.
“Lafiya lau Hajiya Zahra. Kin tashi lafiya?”
“Alhamdulillah. Allah ya tashe ni lafiya.” Zahra ta amsa tana ɗan murmushi.
“Masha Allah. Haka na ke so in ji kullum.”
Zahra ta duba cikin tanda sannan ta ce, “Wannan masan ne na farko ne ko akwai wanda kika soya da farko?”
“Na farko kenan Hajiya,” Mama Ladi ta amsa.
“Okay. Da Allah, idan ya soyu ki ba wa Saude ta kawo min a dining area, Ina da jarabawar safe.” Tana faɗin haka ta fice daga kitchen din ta nufi dining table, ta zauna tana jiran abincinta.
Saude, wacce ke ɗauraye kwanuka a sink, ta ji kamar ta yi tsalle saboda farin ciki. Tun da daɗewa take jiran damar da za ta cika umarnin Mama ba tare da an samu matsala ba. Da har ta cire ran samun nasara saboda Zahra bata fiye son a yi mata aiki ba. Sai gashi komai ya zo mata cikin sauƙi.
Mama Ladi na kwashe round na farko na masan, ta zuba a plate sannan ta ɗauko bowl ta cika shi da cow head pepper soup. Sai ta miƙa komai wa Saude.
“Gashi, ki kai wa Hajiya ƙarama a dining.”
Saude ta karɓa, ta ajiye a kan wani karamin table na gefe tana faɗin, “Bari in ɗaura mata ruwa da cokali.”
Ta buɗe cupboard ta ciro cup, ta ɗora a kan tray, sannan ta buɗe fridge ta ɗauko bottle water. Da ta lura Mama Ladi ta maida hankali sosai wajen juya masa a tanda, sai ta kunce haɓar zaninta ta zaro wani garin magani da Mama ta ba ta kwanakin baya. Maganin pills ne da aka niƙa ya koma gari. Cikin sauri ta zuba cikin miya, ta motsa da spoon, ta jefa spoon ɗin a sink sannan ta ɗauko wani sabo.
“Saude, me kike jira? Ki kai mata abinci mana, ba ta da lokaci fa.”
“Yanzu zan kai mata,” ta amsa, tana ɗaukar tray ɗin abincin, ta fita.
Zahra na zaune tana duba wayarta lokacin da Saude ta shigo da tray, ta ajiye a gabanta.
“Ga abincin Hajiya.”
“Thank you,” ta ce a takaice, ta janyo tray ɗin tana duba agogo. Lokaci yana tafiya, tana kuma son ta ƙara ganin Mommy kafin ta fice. A hankali ta fara cin wainar masa cikin nutsuwa. Bayan ta kusa cin komai sai ta share bakinta da tissue, ta tashi ta nufi ɗakin Mommy.
Mommy ta fito wanka tana shafa mai lokacin da Zahra ta shigo.
“Good morning, Mom,” ta faɗa cikin fara’a.
“Morning my dear. How was your night?”
“Alhamdulillah. Fita za ki yi ne da safen nan?”
“Eh, ina da aiki a office yau da safe.”
“Okay. What time are you leaving?”
“Karfe takwas nake son fita.”
“Mu fita 7:40 please, ki sauke ni a makaranta kafin ki wuce office.”
“What’s the time now?”
Zahra ta duba wristwatch, ta ce, “Five minutes past seven.”
“Okay, zan gama on time. Me Ladidi ta dafa for breakfast?”
“Masa da cow head pepper soup.”
“Nice. Je ki kawo min tawa, I’ll just eat here.”
Zahra ta fita ta haɗa mata breakfast. Lokacin da ta dawo, Mommy ta riga ta shirya cikin wani haɗaɗɗen purple lace ɗin da aka yi mata ɗinkin boubou mai kyau. Mommy ba baya bace wajen iya ado da ƙawata jiki. Zahra ta koyi dressing daga gare ta ne.
“Mommy, gaskiya this lace looks really good on you,” Zahra ta faɗa tana kallon Mommy cike da sha’awa.
“Really?”
“Wallahi, it makes you look young, beautiful and very elegant. Kiyi sauri ki sa hijabi, kar wani ya gan wannan kyau ɗinki. Ina taya Daddy kishi fa.”
“Allah ya shirya ki Zahra,” Mommy ta ce tana murmushi.
“ Ai gaskiya na faɗa,” Zahra ta ce tana ɗan dariya.
“Ke kika sani. Pass me my food please.”
Zahra ta mika mata abincin, tana cigaba da ƙare mata kallo.
“Hope I’m safe da irin wannan kallon?”
“Wallahi wannan lace ɗin ya fitar da dukkan kyanki.”
“Oh Zahra please...”
“Da gaske nake fa!”
“Na ji, amma daina kallona haka, kar na hadiye abinci da iska.”
Zahra ta yi murmushi ta tashi, ta je gaban madubi, ta gyara zaman veil ɗinta, ta ɗan shafa humra a jikinta, sai ta mayar da dukkan abin da Mommy ta yi amfani da su wajen zamansu.
Mommy na gama cin abinci, ta je gaban madubi, ta cancara ɗauri kamar wacce za ta shiga gasar sarauniyar kyau ta duniya.
Zahra, tana gefe tana kallonta, ta yi gyaran murya
“Hajiya Mommy mai capacity! Allah ya ƙara miki nisan kwana.”
“Zahra, da alama zolaya ce ta tashi da ke yau, amma ni ba zan biye miki ba,” Mommy ta ce tana fita daga ɗakin bayan ta ɗaura lifaya saman kayan.
Zahra ta yi dariya ta ɗauki tray ɗin kayan abincin, ta bi bayanta. Palourn shiru, har yanzu mutanen gidan ba su fito breakfast ba. Zahra ta kai tray ɗin kitchen sannan ta fito, ta sami Mommy a parking lot tana warming engine.
Ta buɗe ƙofa ta shiga motar. Tun a hanya Zahra ta fara jin wani irin murɗawar ciki, amma ta daure.
Mommy ta dube ta da damuwa. “Lafiya kike ta motsi?”
“Eh lafiya, kawai ciki na ne ke murɗa min. I think I want to use the toilet.”
“Yanzu kuma me za mu yi?” Mommy ta tambaya cikin damuwa.
“Don’t worry. I’ll use the toilet in the department when I get to school.”
Mommy ta ƙara speed ɗin motar. Within minutes suka isa makaranta, har department ɗinta Mommy ta kai ta. Ta yi parking tana faɗin, “Allah ya ba da sa’a Zahra. I’ll come and pick you later...”
Amma kafin Mommy ta ƙare zancen, Zahra ta fice daga motar da gudu.
Mommy ta bita da ido tana mamaki. “In banda abinki Zahra, me ya hana ki yi amfani da toilet a gida kafin fitowa?”
Da sauri Zahra ta shige cikin toilet da ke department. Zawo ne mai tsanani ya riƙe ta, har sai da jikinta ya saki gaba ɗaya. A hankali ta fito daga bayin tana jan ƙafarta. Ta duba lokaci ;saura minti biyar su shiga exams.
Wurin da sukan saba zama da Sofia kafin exam ta nufa. Sofia na zaune tana duba littafi. Zahra ta ƙaraso, amma kafin ta zauna, sai cikinta ya murɗa da ƙarfi. Cikin hanzari ta shige toilet ɗin kusa. Ta kwashe fiye da minti goma kafin ta fito da gajiya. Tana zuwa exam hall ta ga ana arranging students.
Sun fara rubuta paper ba a kai 15 minutes ba, cikinta ya sake tashi. Da sauri ta miƙe, ta ɗauki permission ta fita.
Mintuna goma bayan ta dawo sai ta sake fita.
A karo na uku da ta nemi fita, invigilator ya hana ta. Sam ya ƙi yarda da yawan fitan da take yi. Zahra ta roƙe shi sosai, tana mai ƙoƙarin haɗiye hawayen da ya ciki a idanuwanta, amma sam ya ƙi.
Cikin rudewa ta ji zawo na ƙara tashi, ta miƙa masa booklet ɗinta wanda ba ta rubuta komai na kirki ba, ta fita da gudu.
Toilet ta sake shiga for the fifth time, amma this time ba zawo kaɗai ta yi ba, har da amai mai tsanani. Tana gamawa da ƙyar ta gyara jikinta ta fito. Amma tana fitowa – sai jiri ya ɗauke ta, ta zube a ƙasa.
A wannan lokaci wani saurayi ke fitowa daga office kusa da restroom. Da sauri ya ruga tare da wani security suka ɗauketa.
“Let me rush her to the school clinic,” saurayin ya ce cikin damuwa.
“Kai ɗalibin makarantar nan ne?”
“Eh, MSc na ke yi. Nazo ne wajen supervisor ɗina.”
“Zan iya ganin ID ɗinka?”
Saurayin ya ciro ID card daga aljihunsa ya miƙa ma sa.
Security ɗin ya rubuta bayanai a wani littafi, sannan ya tattara duk kayan Zahra da suka zube daga jaka, ya maida mata su ciki.
Ya miƙa wa saurayin kayan, yana cewa
“Zaka iya tafiya da ita, Mallam Kabir.”
A 360, Kabir ya ja motarsa cikin sauri zuwa school clinic...
A 360 Kabir ya shigo harabar school clinic, ya yi parking motarsa sannan ya fito da sauri, zuciyarsa cike da tashin hankali. Ya nufi ƙofar shiga asibitin cikin hanzari, yana ihun
"Likita! Likita!! Wai shin ina ma'aikatan asibitin ne?"
Wata nurse ce ta fito da sauri tana faɗin
"Lafiya Mallam? Me ya sa kake mana wannan irin ihu? Ko ba ka san akwai marasa lafiya a ciki bane?"
"Nima ai mara lafiya na kawo. Taho da kujerar gungura mara lafiya da sauri, please!"
Ba tare da wata jinkiri ba ya fice daga ciki ya koma wurin motarsa. Nurse ɗin ta bi shi da hanzari, zuciyarta cike da mamakin me ya samu wannan kyakkyawan saurayin da ya saka da a irin wannan ruɗani?
Cicciɓar Zahra suka yi a hankali, suka ɗora bisa kujerar gungura mara lafiya. Gungura ta suka yi zuwa cikin Asibitin.
A gado aka kwantar da ita kafin ɗaya daga cikin likitocin asibitin ya zo ya fara dubata. Bayan ƴan dabaru irin na likitoci, aka samu ta farfaɗo, sannan aka yi mata ƙarin ruwa.
Kabir ya koma cikin motarsa ya ɗauki jakarta, ya ciro wayarta. Ya kunna wayar, sai dai akwai password. Ya buɗe wajen SIM ya zare a hankali sannan ya rufe. A cikin ɗaya daga cikin wayarsa ya saka SIM card ɗin, zuciyarsa na harbawa da sauri.
Ya fara bin contacts ɗinta da ido, ya ma rasa wanda zai kira. Ya yi tunanin kiran mahaifiyarta ko mahaifinta, amma sai wata tsoro ta dirar masa; "iyayen ta za su iya kasancewa manyan mutane, what if suna da hawan jini? Idan ya faɗa musu cewa ƴar su na kwance a asibiti unconscious, kar su suma suma su faɗi?
Ya na cikin wannan tunanin sai idonsa ya sauka a kan wani number da aka saving da Bro Abdul. Cikin hanzari ya kira, amma ba a ɗaga ba. Yana ƙoƙarin ƙara kira sai aka bi bayan kiran.
Abdul, wanda yake tuƙi, ya hango kiran Zahra. Nan take ya nemi waje ya yi parking, sannan ya kira ta baya.
"Hello Zahra, lafiya?"
"Ba ita ba ce."
"Waye ne? Me kake yi da wayarta?"
"Calm down man. She's unconscious so I rushed her to the hospital. Shine na yi tunanin kiran ɗaya daga cikin family ɗinta."
"Ok, nagode. We will be there right away."
Sai dai Abdul yana da emergency meeting mai muhimmanci da zai yi attending, kuma lokaci ya yi matuƙar ƙurewa. Don haka ya kira Musharraf cikin gaggawa.
Musharraf na zaune a parlour tare da Daddy suna magana a kan sabbin ma'aikatan da za a ɗauka a kamfanin Daddy. Wayarsa ta yi vibrating—Abdul ke kira.
"Why's Abdul calling me? Shi da ya fita yanzu," Musharraf ya faɗi yana ɗaga gira.
Daddy ya yi murmushi ya ce: "Pick up mana, za ka ji dalili."
Ya ɗaga wayar "Ya ne?"
"Babu lafiya."
Musharraf ya gyara zama da sauri "Me ya faru?"
"Zahra is admitted in the hospital."
"Subhanallah! What's wrong with her? Which hospital?"
"I don't have all these answers because I'm not there. Nima wani ne ya kira ni yanzu ya faɗa min. I have a meeting to attend in the next five minutes. Shi ya sa na kira ka, ka je ka ji me ke faruwa."
"Ta yaya zan je ban san hospital ɗin da take ba?"
"Call her number, wata ƙila guy ɗin ya ɗaga."
Musharraf ya katse kiran yana sauke nannauyen numfashi. Allah ya sani yana bala'in ƙaunar Zahra,ƙaunar da yake ji ba kawai a zuciya ba, har cikin jijiyoyin jikinsa.
Daddy ya dafa kafaɗarsa "Ya dai? Na ga duk ka sauya, Musharraf. Me ya faru?"
"Daddy, Zahra ce bata da lafiya."
"Subhanallah! Me ke damunta? Ina take yanzu?"
"I don't know yet. Let me call and find out."
---
Bayan ya kira Kabir ya samu address, Musharraf da Daddy suka nufi parking lot. Musharraf ya buɗe driver’s side, zai shiga, Daddy ya riƙe masa hannu
"Let me drive. Na san akan Zahra ba ka iya controlling kanka. Kar mu je ka ka jawo mana hatsari."
Musharraf bai ce komai ba, ya miƙa masa key sannan ya shiga passenger side. Daddy ya kunna motar ya kama hanyar clinic.
A hanya Daddy ya kalle shi ya ce da tsokana
"Musharraf, you need to man up. Be kamata ka bari kowa ya gane Zahra ita ce raunin ka ba. Besides, na daɗe ina son sanin kamar dai ka fi son Zahra akan mu iyayenka ko?"
"Ba haka bane Daddy. Ni kaina ban san iyakar shaƙuwar da ke tsakanina da ita ba. I don't know why I care for her more than myself. Ƙila saboda abubuwan da ta ke going through ne."
"Kar ka damu, she's going to be fine In Sha Allah."
Suka isa asibitin, Daddy ya tambayi wata attendant
"ƴarinyana, muna neman wata da aka kawo nan. Sunanta Zahra."
"Ko dai Dr. Zahra?" Ta tambaya.
"Eh ita fa."
"Ku biyo ni."
Tare suka shiga ɗakin suna biye da attendant ɗin a baya. Zahra na kwance tana bacci, idanunta suna lumshe, numfashinta na fita cikin rauni. Musharraf ya zauna a gefenta, ya riƙe hannunta yana faɗin
"My little Princess, me ke damunki? Please be strong for me, you hear?"
Daddy ya ce "Ka bar ta ta huta. She will be fine In Sha Allah."
"Ok Daddy. Amma ya kamata mu sanar da Mommy."
"No, kar ka ɗaga mata hankali. Bari idan Zahra ta farka sai na kira ta."
"Ok. Let me see the doctor."
---
Bayan awa biyu Zahra ta buɗe idanunta a hankali. Idanunta sun yi pale, bakinta ya bushe.
"Zahra, how're you feeling?" Musharraf ya tambaya cike da tausayawa.
Ta miƙa masa hannu alamar taimako, zai ɗaga ta sai ta saki wani ihu mai ƙarfi
"Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un! Yaya zan mutu!"
Kwantar da ita Musharraf ya yi da sauri, zuciyarsa na tsalle-tsalle.
Daddy ya matsa kusa "Mamana, menene? Me ya faru?"
"Daddy zan mutu. Hannuna ciwo yake min!"
"Hannu kuma? I thought the doctor said she's stooling, me ya kawo ciwon hannu kuma?"
"Wallahi abinda ban fahimta ba kenan. Cewa ya yi zawo kawai ta ke yi, shine aka ƙara mata ruwa. But let me get the doctor."
Kafin Musharraf ya fita, ƙofar ta buɗe. Kabir ya shigo da sallama, fuskarsa cike da damuwa. Ya na faɗin "sorry kun iso bana nan."
Musharraf ya tashi tsaye, idanunsa kamar wuta
"Kai Ina ka shiga tun ɗazu? We’ve been here since."
Kabir ya yi ajiyar zuciya "Please calm down. Na fita pharmacy ne, magungunan da likita ya rubuta basu da su a nan. Sai na fita wajen sayo."
Daddy ya ce "Alhamdulillah ka dawo. Amma ka gaggauta a bata, yanzu Zahra na cikin wani irin hali na ciwo."
Kabir ya kalli Zahra, zuciyarsa ta buga. Ya matso kusa yana faɗin
"Zahra, please ki daure. Komai zai yi dai-dai."
---
Motar mommy ne ya Kunno kai cikin department ɗin su Zahra. Parking ta yi, ta laluɓo wayanta don kiran Zahra.
A lokacin wayar Zahra ta yi ringing. Mommy ke kira. Musharraf ya kalli Daddy da Kabir, ya ɗaga cikin sanyin jiki.
Muryar Mommy ya ji ta cikin wayar tana faɗin "Hello Zahra, na iso makaranta yanzu. Ina kika shiga? Na yi ta kiranki, ki fito muje gida idan kin gama abinda ki ke yi"
Musharraf ya sauke nannauyen numfashi, ya furta a hankali
"Mommy... Zahra tana asibiti."
Shiru ya biyo bayan kalmarsa, sai kuma muryar Mommy da ta fita cikin tsananin firgici:
"Innalillahi! Wane irin asibiti? Me ya faru da ita?"
Kafin Musharraf ya ba ta cikakken bayani, Zahra ta sake sakin wani irin ihu mai ban razana
"Wayyo Allah na! Hannuna! Daddy hannuna kamar zai fita daga jiki na"
Muryar Mommy ta ƙara tsananta a waya
"Musharraf, me yake faruwa a wurin?!"
Daddy ya yi magana cikin tashin hankali
"Musharraf, ka katse wayar ka je ka nemo likita nan take!"
Musharraf ya yi gudu zuwa ƙofa, zuciyarsa na bugawa kamar ta fashe.***
AKASIN TSAMMANI
(Beyond All Odds)
By
Shamseeya Rabi'u Garba
(Jikar Garba)
YOTA