10
by @pherty001
Har suka iso gida ba wanda yayi magana acikin su cos basu ga fuska a gurin shi ba.
Gab da zai shiga bedroom ɗin sa, Rayhaan yace "Eshraq atleast ka gayamana menene ya bata ran ka haka, tun da ka katse call ɗin bamu ji komai ba".
Eshraq ya dube su kafin ya tsaida idanunsa akan Yusuf yace "yarinyar bata da nutsuwa da kamun kai, har ni take gayawa kada na mayar da ita sex machine idan na aure ta".
Duk suka zuba mashi ido cikin mamaki, ya gyara tsayuwar sa yana jin wani bacin rai sabo a tare dashi yace "dama haka soyayyar take? Dama haka kuke zuwa zance kuna batsa suma matan suna yi? I mean yanzu babu wannan kunyar tsakanin mace da namiji, kai tsaye mace zata iya furta wa namiji wannan kalmar?
Yusuf ya girgiza kansa da sauri yace " wallahi a'a, girlfriend ɗina bata taba min haka ba, bata taba min magana akan sex ba, even goodnight hug da ƙyar take bari nayi mata duk ranar da naje, amma abin mamaki ace wannan ƙaramar yarinya tana mgnr sex".
Rayhaan yace "same too, tawa girlfriend tana da kunya sosai, I once kiss her in the car shima Sai da ta nuna min bacin rai, but dirty talks on phone or chat muna yi sosai, amma idan ta ganni wlhy bata yi".
Wani sabon takaici ya rufe Eshraq bai yi magana ba kai tsaye bedroom ɗin sa ya shiga.
Yusuf da Rayhaan suka gimtse dariyar dake cin su, Yusuf yace "is normal a wannan zamanin, is because he is not used to Soyayya ne, bai taba zama da wata mace ba shiyasa yake mamakin wannan yarinyar, kawai tayi saurin yi masa maganar ne a yanzu tunda shine haduwar su na biyu".
Rayhaan yace "da alama bata da kunya, meyasa ma zata masa wannan mgnr, wai kasan banda son container ɗinnan da yake wlhy na rantse zai ce bazai qara haduwa da ita ba".
Yusuf ya jinjina kansa kaɗan yana faɗin "Nima haka nace a raina".
*
Kallonsa tayi sanda ta shigo sitting room kafin ta sami guri ta zauna jiki a sanyaye cos bata yi tunanin zuwan sa ba, shima idanunsa akan ta, yana kallon sauyi da yawa a tare da ita.
He knows her too well tun kafin su fara soyayya har zuwa sanda suka fara, “NIHAL…” ya kira sunanta softly, “What’s happening to you?”
Ta lumshe idanu na ɗan lokaci, tana ƙoƙarin daidaita zuciyarta dake bugawa da sauri da sauri kafin ta buɗe su akan kyakkyawar fuskarsa tana kallon idanuwansa da suka nuna tsantsar soyayya da damuwa acikin su.
Ya cigaba da faɗin “Did I do something wrong? Me nayi da nake deserving such punishment from you? Ki gayamin a shirye nake da na kai gwiwowina ƙasa domin baki hak'uri".
Zuciyarta ta cigaba da bugawa da sauri da sauri, tace "you didn't" yace “Then why does it feel like I’m losing you?” ya tambaya, idonsa akan ta kamar zai mata kuka.
“NIHAL, I’m begging you, Idan akwai laifi, ki faɗa min, I can fix it. I swear I can.” tayi saurin dauke idanunta akan sa cos bazata jure kallon yanayin da yake ciki ba.
Jibril yana son ta sosai she knows, yana kula da ita, kuma duk abinda take so yana yi mata, ba don Jibril bai cancanci soyayya ya saka zata haqura dashi ba, sai dan zuciyarta tafi samun nutsuwa da TYCOON daga kallo daya da tayi masa a ranar farko da suka soma haduwa.
Daga kallo ɗaya taji babu wani namiji a duniya da take so bayan sa, Eshraq wani irin mutum ne da bata san yanda zuciyarta zata misalta shi ba, komai a tare dashi tana so, kuma komai nashi burgeta yake yi.
Shirun sa ko fushinsa ƙara masa kwarjini yake yi sosai, wata irin kamala ke gare shi da kwarjini mai daukar hankali da ba duk ‘yan adam suka mallaka ba, kuma tun da take haduwa da samarin kala kala bata taba haduwa da namijin da daga kallo ɗaya taji tana son sa ba.
A cikin muryar sa akwai maturity da intonation mai nuna sanin ciwon kai, wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka fahimci ilmi ya wadata a tare da shi, sannan bai nemi komai ya rasa a rayuwa ba kamar Jibril.
Shine namijin da she always dream of samun irin sa, kuma sai gashi ta same sa meyasa zatayi sake da damar da ta jima tana roqon Allah?
“There’s nothing to fix,” ta furta a hankali, “Because you didn’t break anything and baka min komai ba” a raunane yace “To me you’re breaking everything, cos kin san irin son da nake miki,” ya qarasa mgnr cikin zafi da nuna bacin rai.
A sanyaye tace “Don’t make this harder than it already is.”
“Harder?” ya maimaita yana mata wani irin kallon mamaki, “You think this is easy for me, you are ignoring my calls, my chat, Idan ma kin ɗauka sai kin bani uzuri kin katse kiran, wani lokacin ma idan na kira busy kina waya kuma it takes you long, Ko kin gama bakya bibiyar call ɗina, yau gashi nazo babu wannan farinciki a tare dake na ganina, babu wannan kwalliyar da nake samu idan nazo kina min, and you're expecting me to take it easy?”
Taja numfashi kaɗan cos duk abinda ya faɗa gaskiya ne ta canza mashi, ko friends ɗin ta sun mata wannan complain jiya akan ta daina basu time sun daina fita sosai tare kamar yanda suke yi.
Yawan waya da chat da take da TYCOON ya ɗauke hankalin ta akan kowa, tace "am so sorry nima bansan meke damun kaina ba, but I will change".
Ya sauke numfashi yana jin wani sanyi a ransa kafin ya saki murmushi yana faɗin "shikenan, Ina so mu fita gobe". tayi jim kafin ta gyada kai alamar amincewa batare da ta shirya hakan ba.
Sai yaji daɗi sosai ya soma jan ta da hira duk da bata da nutsuwa sosai akan sa hankalin ta na gun wayar ta da ta bari a bedroom ta san Eshraq zai yi ta kiran ta.
Fitowar ta wanka yayi dai dai da shigowar sa ɗakin, a razane take kallon sa, fuskarsa cike da damuwa, ta qarasa da sauri tana faɗin "Daddy am sorry, wallahi kana raina".
Cikin damuwa yace "you totally changed NIHAL, kin daina check up akai na, bakya nema na, mahaifiyar ki tana min complain akan itama kin canza mata what's wrong?
Tayi qoqari maida hawayen dake son fito mata, ta rungume shi sosai tana faɗin " Daddy pls kayi hak'uri, ni kaina bansan me yake damuna ba".
Cikin kulawa yace "are you sick? ta girgiza kanta tana janye jikinta daga nashi, yayi shiru yana kallonta kafin yace" you need medical check up, lemme call Dr Elenora tazo ta duba ki".
Ta girgiza kanta "Allah daddy am ok babu abinda ke damuna", cikin tsokana yace "ko tunani da tsoron auren ne kika fara yanzu, kina tunanin yanda zaki bar Daddy".
Itama murmushi tayi ta gyada kai tana kallon sa, yace "kullum muna tare ko bayan auren unless bana gari, kada ki damu ko ɗaga hankalin ki, ki shirya yanzu ki sauko muci abinci", ya faɗa yana juyawa daga ɗakin, tace "Ina zuwa".
Washe garin ranar da Jibril yazo akan su fita ta nuna Sam bata san zancen ba cos she don't feel like going out with him, abinda nayi matuqar harzuqa shi sosai akan ta kuma ransa ya baci matuqa.
"Despite all abubuwan da kika ɗora a kaina babu wanda nace a'a duka na amince zan yi, na amince akan ki zama mijin na zama matar sai yanda kika yi dani duk hakan bai maki ba, sai wulaqantani kike yanda kika ga dama, haka kike so ayi auren, wai menene laifin da nayi maki haka NIHAL?
Tace "nace bana jin daɗi, gobe zamu yi fitar why are you shouting at me bayan kasan bana so?
Bai yi magana ba, cike da bacin rai ya bar gidan kuma duk rigimar da suke akan kunne Hajiya salima, bayan fitar sa taje ta sami NIHAL cikin bacin rai tace" shi Jibril ɗin menene laifin sa da kike masa wulaqanci a yanzu, wannan ce tarbiyar da nayi maki, mijin da zaki aura yana magana kina masa tsawa?
Ta dubi mahaifiyarta kafin tace "Mamee hak'uri fa na bashi akan gobe zamu fita bafa cewa nayi bazan yi duka ba, meyasa yake min faɗa?
"Dole zai maki faɗa tunda kece a ƙasan sa, haka kika ga ina zama da mahaifin ki, wallahi ki kiyaye ni akan yaron nan, duk hak'uri da yake akan ki yau kin kai sa maƙura cos ban taba jin ya ɗaga maki murya ba sai yau".
NIHAL ta tunxuro baki batare da tayi magana ba, har Hajiya ta gama faɗan ta. Jibril kuwa yana fita kai tsaye office ɗin Alhaji Bilal ya nufa, cike da damuwa kamar zai yi kuka ya sanar da CG duk abinda NIHAL take masa.