🧑‍🍼 RABO...❣️

14

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode fourteen 

" Koda Zainab keda gaskiya Esmaeel batada mafita ko a kotu kuwa, saboda itace taje har inda yake batare da kowa ya sani ba, kaga kuwa kome yace ta aikata dole ta aminta tayi tunda taje kuma ga shedu ya nuna haka! So kada ma na karajin kana wan nan maganar" Alhj yana maganar yana kallon sa inda yake kuma yaki kallah Esmaeel din huci kawai yake, Ummah ce tace " ay zama ta aikata abinda yafi haka indai akan Omar ne Zainab tayin nema babu sharrin dazeyi mata" sam Zainab taki sakin baban yaya Haseen da zuciyan tsiya yaje ya mata wani irin warta ya jefar kan kujera suka sakai sukai waje abinsu auntie Hashmat nata matsan kwallah son din nata yana zaune koda wasa ya kasa dago fuskan sa tai jajir ga hawaye masu zafi dayakeyi zuciyan sa na kuna da tiriri matuka jin yadda akewa Ammin tashi cin mutum ci, tabbas ta bawa Alhj tausayi seya dake be nuna mataba don ta kara gane kuskuren ta ta kiyaye gaba, 

  " Zainab inaso kisani, tunda abin naki yakai ga haka to kifito da miji na aurar dake kowa ya huta" Alhj ke gaya mata haka, caraf Esmaeel yace " nine nan zan aureta Abba, tunda wanda ta kwallah fa rai a rayuwar ta yaci amanar ta duk duniya babu wanda ya can canci yazama mijin ta inba niba!"   "Esmaeel ko ayau Zainab tace kai takeso zan aura mata kai din, to amma zabin ta daban naka daban, saboda haka nabaki nan da kwana 30 ki fito da miji nayi miki aure, inba hakaba zan aura miki wanda naga dama, mutum ci ne kin rigada kin zubar danaki dana gidan nan zaki gani a kwaryar shanki nan kwana 30 ina jiranki, daga yau banason sakejin abunda yafa ru a bakin kowa magana ta rigada ta kare tashi zamuyi muma mu tafi yanzu" 

  Sam hajiya batace kala ba don hukunci da akayi dama shi takeso awa Zainab din " Omar bakayi sa ar uwaba" shine Kawai abinda tace da Omar sukayi musu sallama suka tafi suma, sosai Maya farin ciki ya isheta, Esmaeel kam kallon tsana yake watsa wa Omar Abuja wanda yaketa zubar hawaye, yariga da ya kudur ce a ransa dole ya auri Zainab kodan ya nuna wa Omar Abuja karshen sa, zuwa tayi ta rungume dan nata tana cewa " na rokeka yarona koda kowa ya barni a duniya kai kada ka juya min baya kaine kadai dana a duniya idan kayi min haka mutuwa zanyi, mikewa kawai yay ya kama mata hannu suka haura saman, har dakin ta ya maida data tukunna ya fito, yana saukowa ne daga steps Maya ta dago idanun ta suka hada idanu kam taga yadda ya kura mata idanu yanason tuna inda yaga fuskan nan tata Esmaeel ya katse shi da cewa " Omar mune muka rigada muka kirashi shida matar sa dole mu basu masaukin kwana washe gari kuma su tafi kamar yadda kayiwa Zainab Omar nima daga yau duka na yanke duka wata alaka dake tsakani na dakai, wan nan ay babban cin mutum ci ne kayi min tozar ta matar yaya na kuma na gode Sosai da hakan" 

   " Haba Esmaeel! Yanzu kenan mijina shine me laifi kenan Koh! Meye laifin sa anan ne? Saboda ya fadi gaskiya kake wan nan maganar haka, da ace shine ya biyo ta wan nan munji bamuda mafita amma da kafar ta taje tajawowa kanta, so kaga yanzu wa gari ya waya?" 

Wani wawan tsaki Esmaeel ya buga gami da mikewa ya fice yana shaida ma Omar Kano yasa a basu masauki idan zasu iya zama in bazasu zauna ba kuma sukama hanyar su, inda suke kuwa shima be kallah bah ya kira Lisa kawai yace daji dasu yafice sallan magrib, sosai Maya ke sakin wani irin murmushin keta shikuwa Omar a yanzu ko hawayen ya nemesu ya rasa kansa kamar ze tarwatse yakeji, ga magan ganun Esmaeel dasuka kara daga masa hankali ko tashi zuwa masallaci kasawa yay Omar don yana mikewa faduwa zeyi, ganin hakan ne yasa Maya kama abinta suka shiga masaukin da aka basu na Baki,

             WASHE GARI

  Tun da asusuba Eshaal ta diro gidan babu wanda ya tashi a bacci don haka nema taje kai tsaye shashin Zainab tana zaune kan sallaya dan lokaci ta wani kojale ido ya zogaye baki ya bushe, kawai jitai an bugo kofan da karfi, tadago a matukar razane sukayi ido biyu taji mumma nan faduwan gaba kuwa don kaf cikin 'yan uwan Eshan itace basa jituwa nuna mata itaba 'yar kowan komi bace, 

   " Kedai anyi asarar ra watsatsa mara mutum ci, kindaiji kunya wlh sam tunda fari nasan yaya na beyi dacen mace ta gari bah daga yau sekin bar cikin family din mu tunda da abinda zaki saka mana kenan, kije can gaban iyayen ki kiyi karuwan cinki acan tun a jiya naso nazo nasame ki su Abba suka hanani dakinyi mamaki na ajiya wlh karya kawai mebin maza" tass ta karewa Zainab cin mutum ci da zagi son ranta wanda ita ko daga kaima ta kuma kallon ta batayi ba, sedai zubar hawaye kawai tana jinta bayadda zatayi tagama tsiyar ta ta juya ta bar gidan ko zama ma batayi ba bawanda yasan tazo se Omar Kano yana tsaye jikin window yana kallon motan ta tafice ya rigada kuma yasan meya kawota gidan cin mutum ci ne kuma tayi ta tafi shikenan, sam shima basa wani jituwa yadda takewa Ammin sa yasa shima baya sonta sam, to su Maya ma da wuri sukayi shirin tafiya zuwa yanzu jikin Omar yay zafi sosai dakyar yake iya bude eyes dinsa saboda ciwon kai, ko takawa ya kasayi se fitowa tayi ta nemi agaji gurin securities suka te makawa Omar din gurin fitowa akasashi a mota Esmaeel da Omar suna tsaye a compound din gidan yana gaya wa Esmaeel din zuwan Eshaal gidan, koda Esmaeel yaga yadda aka tarai rayo Omar yasashi karasa gurin motar yaga yanata miko masa hannu ashe, ita kuwa Maya da karfin hali gurin Omar kano din ta karasa tana cewa " bari naje gurin maman taka muyi sallama don wan nan abun daya faru bayasa kuma gaba tashiga tsakanin muba saboda bamusan me gaba zatayi bah" jinjina mata kai Omar yay gamida kiran Lisa a waya, tafito san nan ya sata takaita gurin Ammin tashi zugui zugui maya aka wuce, Omar yabita da wani irin dan iskan kallo, seda ya tabbatar da a yanzun tana cikin dakin yashiga cikin parlour din slowly ya haura saman yaje ya manna saitin kunnen sa jikin kofar yanajin Amon Maya tana cewa " nayi miki hakane domin ki gane shidin nawane ni kadai next bazaki kara gangancin shiga gonar mijina ba, zuwa yanzu mutum cinki babu shi a idanun jama a to ki godewa Allah dana barki iya haka idan baki hankal taba wlh abinda zan kumayi miki seyafi wan nan ciwo, keme masoyi ko harda cemin akanki ze wula kantani, to yanzu gashi da isata da izzata nasashi agaban iyayen ki da surukan ki ya wulakan taki, duka ina sonda kike ikira rin yana miki yanzu? Nazo ne dama nafidda ki a duhu kisan wanda yamiki haka bah! To nice nan don haka seki kiyaye" 

   Tafiyan dayaji anzo bude kofan yasashi hanzarin juyawa ya sauka akan steps din da matsanan cin sauri yafice kai tsaye ya nufi parking space saboda yadda jikin sa ke tiririn masifa ga Farid ya ishesa da kira rasa ina me ze nufa yayi, sam hankalin Esmaeel naga Omar Abuja bega fitowan Omar ba su suna bakin gate ne ya rankwafa yana masa magana wanda ko kuka ya gagare shi se magiya dai kawai dayakewa Esmaeel din yana shaida masa bashi da lpy ya temake rayuwan sa kansa ze tarwatse da heart dinsa, Maya na shirin fitowa ne wayan ta yayta ruri seda ta dauko ta duba taga aminiyar tata ce sadiya ta kuwa saki murmushi tayi saurin fito wa wajen compound ganin Esmaeel na magana ne da mijin nata yasata hanzarta yin gaba ta daga kiran da sadiya keyi mata se waige waige takeyi shirun data kuma jine yasata karasa wa gurin parking space tsakanin motoci tasoma amsawa sadiya maganar ta 

   " Kai sadiya Alhmdlh aiki na ya tafi yadda nakeso wlh, kinji yadda nake farin ciki, jiya ta wulakan tu wlh hatta iyayen ta sun salla mata, aini hakan yamin dadi gaba kinga seta nisance shi, takarfi gashi nasa tsanar sa a zuciyan ta tsanar da bazata kuma marmarin sake ganin saba, haka shima, but abu daya dake daga min hankali sadiya wan nan ciwon kan da yakeyi na menene ne? Jiya har kusan tsoro ya bani fah abinda ya ringa yi a Wall yaketa buga kan nashi ayau kuma mun tashi harda matsanan cin zazzabi baya iya tafiya saboda jirin dake diban sa, anya kuwa nidai bazaki je a warware asirin nan bah, kada injawa mijina wata masifar fah! Tom shikenan idan kinzo kam semusan abinyi, ta wani bangare ina gaya miki inajin zafin sa matuka saboda totally yagama raina min hankali, ashe sunan ta ne baby taci, haka zalika itama danta sunan sa Omar, ayni ban saniba seda naji ana kiran dan nata da Omar din abin ya dawo min a rayuwa kuma wlh zeyi mamaki na zan kumajin wanda ya isa ya cigaba da kiran Baby da wan nan sunan, kedai bari kawai kada maganar mu yacika yin nisa kada azo ajini ay zakisha news yadda shegiya matar ta koma dama ciwon zuciya ze kamata yay ajalin ta muhuta" shewa tadanyi Maya bata daga muryan taba sosai kana tace " tom shikenan semun dawo" ta yanke kiran batare da tunanin komai ba tafice cikin motocin nan, Omar Kano yana daga durkushe da yayi hawaye na zarya a face dinsa gaba daya ya daskare a gurin saboda mamaki da al ajabin kalaman maya, yana cikin wan nan yanayin ne har suka bar gidan be saniba, hakimar ma itace taja motan don Omar kam baze iyaba haka zalika Esmaeel ya gagara fahimtar sa dukda yaji tausayin Omar din matuka a yanda yake ganin sa to amma haushin sa yakeji baze iya temakon saba a yanzu don ba karamin jin zafin sa yake jiba, Farid kuwa gajiya yayi da babatu a waya ya kashe don kotashi Omar bayayi,haka ya koma ciki zuciyan sa na tsanan ta bugawa saboda kaduwa, direct ya wuce gurin Ammin tashi sedai kuma yana shiga bazato ba tsamma ni yaci karo da ita a yashe gefen bed ga goran ruwa gefen ta ya fadi ruwan ciki duka ya malale a kasa har jikin ta, a sukwane ya isa gareta kamar zararre yasoma girgiza ta yana kiran sunan ta sema jikin ta dayaji yasaki jiki na bari yakai hannun sa gefen wuyan ta yaji jikin yayi sanyi kalau ko kadan ba alamun numfashi a tare da ita, 

  " WAYYO ALLAH NAH!!"

Shine kawai abinda Omar ya iya furta wa cikin karfin da besan yanada shiba ya ciccibe ta yayo waje....✍️