🧑‍🍼 RABO...❣️

18

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode nineteen

Yana fitowa titi ya hangi Fanan tana kokarin shiga taxi din tausayin tane ya dirar masa sosai don yaga tana matukar kaunar kanwar tata  to ya zasuyi mahaifiyar su ce taja musu yana gani taxi ta wuce layin makarantar shi kuma ya wuce abinsa, bayan gama tattauna war Omar Abuja da Omar Kano ne yana shirin tafiya wayan Omar Abuja tasoma ruri da harya share kiran se kuma dauko wayan to ganin Maya ce ke kiran yasashi dagawa cikin hanzari muryan ta yasoma dukan kunnen sa 

    " Daddyn nawal Auta ta baby an sace min ita an dauke min Baby nashiga ukuna!!" Galala Omar ke sauraren ta jin kamar tana masa tatsuniya ne yasa shi saka wayan a speaker ya kura wa wayar idanu ta cigaba da cewa " Kadawo ka nemo min autata! Inba hakaba mutuwa zanyi Omar bazan iya jure rashin auta bah!" 

Yadda zuciyan sa take bugu ne tsaf yace zeyi shouting se zuciyan sa ta buga salati kawai ya fara yana kokarin hada kalamar daze furta " Ba Ban gane baby ta bata ba Maya?" Yadda takeyi kuka sam bata kuma bi takan saba ta kashe wayan, Omar Kano kuwa wani irin sanyayay yen farin ciki ne yake ratsa mishi zuciya saboda jin kukan wadda yafi tsani a duniyar nan cikin zuciyan sa yana cewa " Haba Maya! Ay wan nan is just the beginning " a fuska kuwa tausayi ne karara akan fuskan sa cike da damuwa yace " menake ji haka kuma babu dadi!" 

  " Wlh Omar kaji wai Baby ta bata! An dauke min autata baby shin dame zanji ne ni kuwa" Omar kano na shirin kuma yin wani magana ne ya mike yana me dafe kansa yace " sorry Omar letter ma karasa magana ina cikin wani irin tashin hankali yanzu bazan iya yadda da wan nan abun ba taya za a cemun an sace min baby? I can't trust that wlh " yana maganar yana hada ya nashi ya nashi suka fice daga cikin office din ko manager dinsa ma se awaya ya masa magana Omar kano da kansa ya bude masa mota ya shiga ya rufe san nan ya sunkuyo yace " Allah ya tsare ya takaita in Sha ALLAH babu abinda ze faru da ita " seda yadan kalle shi a takai ce yace " ameen summa Ameen Omar na gode " murmushi yadan masa yayi gefe yana gani ya bawa driver umarni suka tafi cikin zuciyan sa nata Addu'ah da kiran sunan Allah har seda motan sa tabar cikin company din ne yaje shima ya shiga nashi motan suka tafi fuskan sa cike da farin ciki ya kira Farid be daga ba wanda a yanzu tafiyan su tayi nisama shida Madam Farida ta cirewa baby uniform dinta tasaka mata kaya schoolbag dinta da uniform din ta kuwa cikin booth din motan suka boye shi har shoes da socks ta kwantar da ita kan laps dinta kamar itace manan ta ta wani basar se karatun daily trust takeyi koda sun gamu da jami ay basu da damuwa_

  Omar Abuja koda ya karasa gidan yasoma jiyo kukan su tunda ga compound  Fanan na ganin shi taje ta rungume shi tana cewa " Dad duka laifi nane! Ina zan tsoma rayuwa ta nice na tafi taro mana taxi tana jirana koda mukazo Dad bata nan babu inda bamu duba ba a unguwan har cikin school din bata nan tsautsayi ne ashe yasa inata mata magiyan ta buyoni muje titi taki tace rana!! Wlh narasa yadda zanyi da zuciya ta Dad ina baby zataje!" 

   Karfin hali kawai Omar yake yasoma rarrashi ta cikin aro jarumta dayay sam ya rasa wani tunanin ma zeyi ne ga driver din nasu gefe se kuka yake Maya tace se an kulle shi tunda ya bari aka dauke mata Auta tsamma nin jiran jami ay kawai suke babu wanda ya ankara se ganin Maya sukai akasa ta sume suduka a gigice sukayi kanta a time din kuma sega jami ay sun iso suma kuka Fanan ne kawai yake tashi ganin mummyn tata kamar an zare mata rai dole aka dauke ta akai ciki da ita seda aka riga fesa mata ruwan sanyi a fuska tukunna ta farfado taname jan dogon numfashi tana cigaba da kiran baby tana kuka gwanin ban tausayi taki sauraren kowa sadiya nata rarrashin Fanan da Omar din ne sukabi jami an har school din tasu aka kira shugaban makarantar tasu duka seda aka duba CCTV cameras babu wanda ta nuna abinda ya faru se tafiyan Fanan din da Baby san nan sun rigada sunyi signing suka bar school din don haka basuda ikon kama shugaban makarantar ko wani malami wan nan dalilin ne yasa hankalin su kara tashi mussam man Fanan haka suka koma gida ba nasara sukabar jami ay suna cigaba da bincike hauka tubaran taso yi musu Maya da suka koma ba Baby ta shake wuyan Omar kamar zata kashe shi aljanun ta sun tashi se driver da gateman aka kira suka kwaceshi idanun sa na neman juyewa da dabara da wayau sadiya da Fanan sukai sama da ita suka kulle ta a daki cikin wani hali ta rungume sadiya Fanan din tana kuka me taba zuciya wanda yasa tausayin ta kamata sosai don harga Allah ita batajin tausayin Maya da autar tata da aka dauke Omar ne yafi bata tausayi da Fanan mussam man laruran da yake fama da ita wadda duka tasan itace sila seda yadan maro daga shakar da Maya ta masa ne ya tafi gurin limamin unguwan su akayo mata rubutu tukunna ya dawo gidan su ukun suka hadu aka danne ta aka bata rubutun Tasha dakyar se faman bankare wa take tana wani irin gunji ganin taki tsayawa a shafe mata kanta da ruwan rubutun ne kamar yadda liman din yace seya daga goran ya tuttula mata akan nata ya guntsa ya soma fesa mata to san nan aka samu sauki jikin nata ya saki tafara bacci gaba daya sun hada uban gumi kashir ban haka ya fita ya basu guri Fanan na cigaba da kuka shima jiri ne ke neman yadda shi yasamu dai ya haura saman sa dakyar ya zube akan sofa zuciyan sa a cunkushe ya rasa tunanin yima_

   Zuciyan Omar Kano fes ya koma hotel din dasuka sauka sosai yakejin dadi a zuciyan sa seda ya cika tunbin sane yay wanka bayan ya shirya ne ya kira Doctor din Ammin tashi kamar kullum dai ya shaida masa ba labari bata farkaba, dukse ya kumajin babu dadi da wan nan damuwan ne suka tafi gurin malamin daddy nasa me magani ya masa bayanin laruran da Omar ke fama dashi ya shaida masa ay seyazo dakan sa tukunna yaga menene damuwan a jikin sa, dukda hakan dai seda ya bashi wani rubutu yace aba mara lafiyan idan ma sammun ne yanasha ze soma jin afuwa yaji dadi Omar kuma ya masa alheri me kyawu ya kudurce kotaya seyasa Omar Abuja yazo an masa maganin masifar da Maya ta haddasa masa anan ya ci abincin daren sa sunata fira har bayan ishah sallah ma nan yayi tare da daliban sa yaja sallan kamar koyaushe_ 

          KANO

Babu wani matsala dasu Farid suka samu a hanya har suka shigo garin kano seda suka tsaya a wani Mall suka siyama baby kayan makwalashe da ice cream san nan suka nufi unguwan tudun yola daidai wani dan madai daicin gida suka tsaya layin shiru babu alamun kowa sukai horn me gadi ya bude musu gate suka shiga ciki Farida ta dauko baby a hannu suka shige ciki bayan Farid ya anso key gurin me gadin komai tsaf dashi a gidan an gyara ko ina nata kamshi ta shimfide ta akan sofa sam batasan wainar da ake toya waba, basu tsaya yin komai ba seda suka gabatar da sallolin da ake binsu tukunna Farida ta shiga kitchen don sama musu dan abin tabawa kasance war an tanaji komai ne ta silala musu spaghetti time din kuma Farid ya fito cikin sauyin kaya saboda wankan da yayi sauri sauri Farida taci abincin kada baby ta tashi san nan ta mike suka fita ya maida ta gidan ta a hanyar sa ta dawowa ne yakira Omar yana shaida masa sun isa lpy har yanzu baby bata farkaba hankalin Omar ya kara kwanciya dayaji sun isa kano yanata kawata smile dake fuskan sa koba komai yanzu yasan baby ta shigo hannu, seda ya koma gidan ne ya tsaya gaban baby cikin murmushi me sauti yana cewa 

  " OHH!! Baby duk wan nan tsiwar taki jinin ki bashi da karfi har yanzu baki farka ba" TV kawai ya kunna ya zauna yana kallah dukda idanun sa nakan TV din hankalin sa naga Fanan yana tunanin ta, 

     Maya lpy kalau ta farka daga bacci abeba dan sun sauka jiki duk yay tsami tayo wanka tayi sallolin ta dukda haka hawaye be fasa zuba a fuskan taba jin gidan take kamar ba nata ba saboda babu abar kaunar ta baby a cikin sa, yau daya Maya aka dau carbi saboda anshiga masifa saboda asara se mutum ya shiga cikin masifa ze tuna da Allah, sadiya tanata dariyar ta son ranta a zuci a fili kuwa tausar zuciyan ta kawai take da lallami Saboda girman kan maya da bakin hali daga ita se sadiya gidan kaf makota babu wanda yazo mata jaje don itama ba zuwan takeba, tana cikin jan carbin ne tana sharar kwallah da tissue sejan hanci take murya na rawa tace " sadiya Allah yasa ba 'yan yankan kai bane suka sace min autaba, nashiga ukuna ni Maya kiduba har yanzu shiru ba kabarin ta! Ina zansa rayuwa ta naji dadi zuciya ta kamar zata tarwatse nakeji sadiya meyasa haka zata kasance dani meyasa!! Ina aka kaimin baby tana Ina?" Ta karashe maganar tana me kara fashewa da kuka cikin tausaya wa iya fuska sadiya tace " Haba Maya kidena irin wan nan maganar dayar dar Allah baby tana cikin koshin lpy za a ganta babu abinda ze sameta kada ki cika tayarwa da kanki hankali kinsan bakya da cikakken lpy idan kina wan nan kukan Fanan tazo yanzu ta ganki a haka kara daga mata hankali zakiyi kidena kukan nan mucigaba da Addu'ah kinji kukan ba shi bane mafita please ki dena" tana maganar tana share mata hawayen,

   Farid yana kallon TV yana waya jefe jefi yana juyawa ya kalle baby juyowa na karshe dazeyi gurin tane yaga kamar tana motsi seya tsaida idanun nashi akan ta harta bude idanun ta tangaran tana kallon sa dake saitin face din ta yana a ta site din sa, wayan dayakeyi ya katse yanata mata murmushin mugun ta kwakkwaran motsi ta kasa seda tayi kusan 5 minutes tukunna tayi karfin hali mikewa zaune tana dafe kanta dayay nauyi komai na dakin takebi da kallo da suturan dake jikin ta a hankali duka abinda ya faru yasoma dawo mata a brain cikin murmushi Farid yace 

   " Baby irin wan nan bacci haka se yanzu Allah yay miki tashi!" Shiru tayi dashi tana kallon sa cikin shocked dariya ce taso kwace masa ganin yadda tasoma kebare fuska gimtse dariyar kawai yay yace " oya a tashi ayi wanka se kizo kici abinci ga ice cream dinki Kuma" time din kam tsoro ya gama shigan baby kawai ta mike tsaye heart dinta na racing tasoma kiran mummy....✍️