🧑‍🍼 RABO...❣️

27

by @nanabmb

🧑‍🍼RABO!!❣️

*NA* 

       NANA BMB

Episode twenty eight 

Maya tana tsaye mamaki ya hanata magana face din Zainab kawai ta zuba wa idanu cikin wayan shugaban jami an ne yace " hajiya duka bayanan daki Kai mana beyi dai dai da abinda muka gani ba dangane da mutana nan sam babu alamun daya nuna akwai diyar ki a cikin gidan nan tayiwu dai wadan da suka kawo miki maganar basu gani da kyau bah, bamu samu hujja ko dayaba babu Tayadda za ayi mu kamasu" a time din kuma Omar yasamu damar gaya ma Maya magana son ransa kiri kiri tanaji tana gani ta zama kurma se idanu datake rabawa har suka kare magana da jami an suka tafi yana wurga mata kallo me cike da mugun ta da tarin ma anoni, ko gidan be koma bah ya kira Farid yana dagawa cikin fada yace " Farid jiya meyasa zakayi sakacin da akaga lokacin da kashigo da yarinyar nan gidannan?" cikin rashin fahimta Farid yace "ban ganeba Omar me kake nufi wanine yazo gidan?" "Farid Maya da kanta itada jami ay agidannan yau sunzo bincike,zan nunawa Maya batada wayau don haka yanzu wasan ya sauya salo,dole tareda ita zaka tafi New York din kuma kada kazo gidannan saboda tsaro,koma me ake ciki zan kiraka anjima nasanarma" katseshi Farid yayi yace "Omar ina kakai yarinyar to dabasu gantaba kajirani dai anjima zan kiraka yau ko office ba zaniba sai komai ya daidaita" baijira amsar farid ba yayanke wayar, binciken gidan omar yafara kozega an aje masa wata camera amma baiga alamun taba dukda haka saidaya kira securities suka bincike gidan,suka tabbar masa babu wata alamun camera agidan sannan yasaki jikinshi kai tsaye part din Daddyn nashi ya koma cikin sauri yake kokarin bude baby don ya tabbatar a yanzu ta jigata gurin ba wada tattar iska yana zarota kuwa ta fado masa a jiki tajike da gumi tana jan ajiyan zuciya don tabbas ta wahala seda tadan marone kawai tasaki marayan kuka sam be saurare taba ya janye seda ya maida komai yadda yake tukunna ya kamo mata hannu suka fito ya maida kofan ya rufe kai tsaye ya maida ita dakin Ammin shi yabar ta a tsaye tanata masa kallon mamaki ta waje ya kulle ta ya koma dakin sa don yin wanka, bata wani ji tsoron kulle tan da yayi bah tashiga bathroom din dake parlour tayo wanka itama da brush ta fito daure da towel zulum zulum tasoma kalle kalle a parlour din tana yaba kyan daya mata a fili, tanata kurda wa harta shige bedroom tasau baki tana kallon aljannar duniya, Abin da ya bata mamaki ne yasa ta saurin karasa wa jikin bedside drawer ta dauka hoton Zainab itada Eshan dasuka yi time din yana raye sunyi matukar kyau sosai, tanata murmushi tasoma shafa hoton tana cewa " kece aina gane ki kinada kirki Sosai tun daga ranar ban kuma ganin kiba me sunana, ina komawa gida zan cigaba da takura wa daddy yakaini gurin ki" ita kadai taketa surutan ta abinta, 

  Omar kam be sake wai wayar taba seda yamma tukunna ya je dakin mamaki ya kamashi dayaci karo da kayan ta ta kwabe a parlour din kuma be gantaba ga kofar bathroom din a hangame bare yace tana ciki kansa tsaye ya wuce bedroom daya gani a bude shima, aikuwa sedai ya hange ta tayi dai dai kan gadon Ammin tashi towel duka ya tattare gashi ya kunce saurin kauda idanun sa yayi yama rasa taya ze tasheta ga hoton Ammin sa dayaga ta matse a cikin ta ta rike da hannun ta baccin ta kawai take hankali kwance, ganin yana zama sususune yasashi mika hannu yana kokarin zare hoton Ammin tashi ta bude ido ganin abinda yake shirin yine yasa tai azamar rike hoton ta mike zaune cikin muryan bacci tace 

  "  Ina kasamo hoton tah? To bari kaji, Hoto nane wan nan karma kace zaka kwace min shi sena mayar mata da abinta don bansan inda ka sato mata shiba" 

Gyara tsayuwan sa yayi cikin kallon mamaki dayake mata yace " wacece ita din a gurin ki?" 

" Bari kaji itadin auntie nace kuma kawar Dad ina sonta sosai tanada kirki ina komawa zansa Dad ya kaini gurin ta nabata hoton ta" cikin rashin fahimta yace" wani Dad din kike magana? Kuma a ina ya Santa?" 

  " Kai yasanta mana ranar da mukaje siyan kaza suka hadu da Dad dina harma tasai min ice cream kuma har gidan ta mukaje tacewa Dad ya kaini da daddare nataya ta kwana kuma shine be kaini bah tun a lokacin idan na tambaye shi yaushe ze kaini gurin me sunana seyay min shiru harna ji haushi nadena tambaya sama gashi ya hanani fadawa mummy" takarashe maganar kamar zatayi kuka shi kam kallo ta kawai yake harta kare maganar ta ya lula duniyar tunani ita kam tasami abin kalla a gareshi cute face dinsa kawai tazuba ma idanu tanajin dadi babu zato kuwa yaji softness hand dinta a gefen face din nashi tana  shafawa harara ya buga mata ya aje mata tray din daya shigo dashi yay ficewar sa tana rakashi da idanu cikin jin haushi ta juya ga tray din daya aje mata na abincin tace " stupid kawai don ma kasamu ina sonka! Kuma bazan ci abincin bah" tana hararar abincin ta sauke shi kasa ta juya masa baya, shi kuwa Omar daki ya koma zuciyan sa fal da tunani kala kala har seda akayi sallan magrib da ishah tukunna ya dawo cikin gidan yanata tunanin kayan daze daukar ma baby din don Farid ya tafi da jakar kayan ta a boot din motan sa gajiya yay da dube duben sa ya sauka kasa ya shige room din da Ammi ke aje masa komai nasa dayayi amfani dashi ada aciki ya dubo suit din dayake ganin ze mata dai dai ya dau ka ya nufi sashin Ammin tashi yana shiga yasoma jiyo kukan ta sama sama yana shiga bedroom din ya sameta rakube gefen bed ta rike ciki tanata kuka tray din daya kawo mata ne ya kalla yaga bataci abinci ba kawai se yay guntun murmushi ya fice be wani juma da fitaba sega shi ya dawo dauke da cup din tea a hannun sa, seda ya ajeshi kan stool ne ya saka hannu ya dago ta kamar tsutsa haka take komawa tana kanan nadewa seda ya ajeta a kasa tukunna ya dauki cup din ya saita mata a baki sam batasan meye a cikiba tana cikin kukan tane taji ya hankada mata tea din me zafi a baki, itama cikin tsananin gigita batasan time din data feshe masa fuska da tea din ba, takaici ya kama Omar matuka cikin jin haushi ya daga kanta sama ya take mata kafa tayage baki zatayi ihu yasoma kwarara mata tea din cikin baki azaba goma da ashirin ya tura kofin sosai cikin bakin ta bazata iya rufewa ba tana hadiye wa jikin ta na wani irin tsuma seda ya karar da tea din duka tukunna ya saki kan nata ya daga mata kafar ai kuwa tasaki wani irin kara tana tumami a kasa tana rike bakin nata daya kona mata jin azabar take har tsakiyan kanta, kobi takan ta beba seda ya shiga toilet ya wanke face din sa ya gyara ta tukunna ya fito ya babbale suit din yazo cikin rashin imani ya fisgo ta ya cilla ta kan bed din ya fisge towel din jikin nata yasoma kokarin saka mata rigan tahau kai masa duka cikin zafin ciwo take masa shouting tana cewa " ka sakeni azzalumi mugu kawai Allah ya isana, kada ka kara tabani banaso mugu kaw.....pauuu!! ya dauke ta da wani hot slap din  da yasa ta sake fashe wa da kuka tai lakwas tanaji tana gani ya saka mata wandon suit din da rigunan duka ya dora mata wani hulan sa hat ya boye mata duka gashin ta a ciki tukunna ya jawo mata hannu har suka fita parking space tana kuka har suka shiga cikin motocin bayan sun zauna ne Omar ya kalle ta yace " koki rufe min baki anan kona tattakaki!" Baby ganin yadda yay maganar ne yana kwalo mata mayun idanun sa dake tsora ta ta tai mukus sedai tsiyaya hawaye seda aka gama bincike layin tsaf ba wani dan leken asiri tukunna guards suka koma cikin motocin nasu suka tafi suna hawa kan titi ilai kam wan nan motan ya cigaba da binsu murmushin mugun ta yasaki Omar ya juya yana kallon baby dake gefen sa tayi shabe shabe da hawaye da majina cikin iya murmushi mugun ta yake kallon ta ita kuma tana masa kallon al ajabin na tunanin datake a zuciyan ta dama ashe mugu ne 😂....✍️