HARIJAR YARINYA

Chapter 5

by @pinkyjay

🫦*HARIJAR YARINYA*🫦

( Romance and sexy story)

🔞
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay ce 


***
_______________________________
Following this to join my Whatsapp channel Domin samun Update ɗin wannan liltafin da sauran liltafaina ***

PAGE 7️⃣🔜8️⃣

Laure tace "Hamm Ƙawata kenan ai na kwasa tin kafin muzo nan sai na dawo Akwai labari." Falmata tace "To shikenan a dawo lafiya ƙawas." Ta aje wayar tana sakin Wani murmushi da ita kaɗai tasan ma'anarsa,  

Bangaren Hajiya Ummei kuwa washegari suka fita ita da Salmah tayi mata komai ta makaranta islamiyya da Boko kana suka dawo gida sai murna take yi, basu jima da dawowa ba saiga Muhammad ya kira yana bakin get Salmah taje tayiwa get Man magana ya buɗe suka shigo tare tana maƙale dashi bayan sun gaisa da Hajiya Ummei Salmah ta kawo mai abinci da ruwa da lemo ya huta kana ta kira Sajjad 

yace mata yana hanyar gidan be jima ba ya ƙaraso suka gaisa da Muhammad kana ya wuce parlon Ummie Salmah na kwance ƙan cinyarta suna hira, tashi tayi tana faɗin "Oyoyo Ya Sultan Barka da rana." "Barka kawai yace mata." Ita kuma ta fita da gudu ta kawo mai Lemu da ruwa tace " Ya Sultan ga wannan bamu baka abinci ka koma gida ka ƙi cin na Auntyna." Ta faɗa tana dariya har kumatunta na lotsawa, 

bata jira abinda zai faɗa ba ta fita wurin Muhammad ta koma suna ta hira abinsu tana bashi labarin school ɗin da Ummei ta sakata gobe zata fara zuwa yaji daɗi sosai ya ƙarawa yiwa Salmah faɗa ta dage da karatu banda wasa ko ƙawance da yaran da basa son karatu kuma ɗauka Ummei ce ta sauƙo parlo tare da Sajjad nan suka ƙara gaisawa ya karɓe takardunsa ya duba ya yi mamaki sosai ganin kwallin karatun Muhammad saboda haka yace, 

Ya ɗauke sa ai ɗayan Companyninsa zai kaisa a matsayin MD godiya sosai Muhammad ya yi Account ɗinsa Sajjad ya karɓa ya tura masa dubu ɗari uku yace yaje ya yi siyayya kayan sakawa na fara zuwa aiki, sannan akwai Motar Company da zata dinga zuwa daukarsa gidan da zai bashi ya zauna iyaka ranar juma'a 12 na rana suke tashi aiki zai iya zuwa gida yaga Inna ranar Monday ya dawo, 

Salmah kuwa kallon Sajjad tayi kana tace "Ya Sultan Allah ya biyaka ya faranta ma kamar yadda kayiwa dan Uwana Allah ya kare ka ga dukkan sharrin mutum da aljan ya ƙareka daga sharrin maƙiya da mahasada Allah ya yima jagora ya shiga lamarinka, Allah ya ƙarawa Ummie lafiya da nisan kwana ya gwada mata ƴaƴanka Allah yasa ka gama da ita lafiya." Mamaki ne ya kamasa jin yadda take addu'a kamar wata babba, 

Ummie ce ke karɓawa da Amin tare da Muhammad suka fita ya kaisa ma saukinsa kana ya wuce inda zaije Salmah kuwa washegari ta fara zuwa school kuma taji daɗi sosai saboda a kwaita da shiga rai har tayi ƙawa me suna Ilham data dawo take wucewa islamiyya Direba ke kaita ya maida ta, ta maida hankalinta Sosai gun karatu bata wasa, 

wata uku da auren Sajjad Yusrah ta fara rashin lafiya sukaje hospital gwajin farko ya nuna tana da ciki na wata biyu da sati uku, farin ciki gun Sajjad ba'a magana, tin hospital ya sanar da Ummie lokacin Salmah sunyi hutu a school yazo ya tafi da ita saboda taimakawa Yusrah da aikin gida tana ɗebe mata kewa, haka zai dawo ya tarar dasu sai hira suke tana hidima da Yusrah sosai, ko nan da chan bata bari tayi aiki, 

komai ita keyi, har suka koma School Direbansa ke kaita ya dawo da ita, wani lokaci gidan Ummei suke wuni, har cikin Yusrah ya kai wata 8 sai shirye shiryen kayan haihuwa kawai suke yi, Salma kuwa tayi kyau abinda hutu da kulawa ya ratsata,  

Bangaren Hajiya Falmata kuwa sai lokacin Ƙawarta Laure ta dawo, saboda Farida ta sakata a gaba zuwan Hajiya Laure ya kwantar mata da hankali saboda ta sanar da ita babu wacce zata iya zuwa Kogi state Wurin wannan boka face Hajiya Laure saboda Malamn nan basu iya aiki sosai ba bokayen chan sufi su saboda har tsafi sunayi babu abinda basu aikatawa, 

Laure tace "Ƙawata nifa inaga mu fara kawar da matarsa kafin a kai ga maganar zuwa gun Boka kega dai yanzu juna biyu gareta abinda zai faru mu salwantar da rayuwarta ita da abinda ke cikinta kar mu bari ta haifesa kega ana gama jimamin mutuwarta zancen aurensa da Farida zai tashi ko ya kika ga." Hajiya Falmata tace "Ai kuwa ke kawo shawara wallahi to yanzu ya za'ayi ne naji Alhaji na magana da Sajjad akan tafiyarsu Japan ina ga satin nan zasu tafi kuma bada ita zaije ba, sati ɗaya zasuyi." 

Falmata tace "Yauwa abinda zan tsara zai tafi da kyau ba wata matsala ko wani abu da zai kawo muna cikas.", Falmata tace"Yanzu miye shirin.?" Tace kawo kunnenki kiji." Ta rada mata magana a kunne suka bushe da dariya Hajiya Falmata tace "Kai amma wallahi ke muguwa ce kesan kaina be kai chan ba kega riba biyu kenan to ai shikenan sai kije ki fara shiri suna ɗagawa ƙasar nan zan sanar dake, 

Tofa masu karatu ko me suke shirawa Allah masani muje zuwa, 

Farida kuwa Hajiya Falmata tace ta kwantar da hankalinta nan da wata ɗaya biyu zata mallake Sajjad, Ni kuwa nace anya kuwa wannan aure zai yiwu ga Nihal a gefe ɗaya tana neman yadda za'ayi ta mallkesa, 


Yusrah da Salmah na zaune parlo sun kammala cin abinci Salmah na matsawa Yusrah ƙafafunta da sukayi kumburi irin na masu ciki, hira sukayi Salma taji shiru tace "Auntyna ko keyi bacci.?" Ɗagowa tayi ganin Yusrah ta lula duniyar tunani ta ɓata tayi tace "Auntyna me kike tunani haka keda bakids lafiya.?" Murmushi tayi kana tace "Kesan wani abu kuwa shawarar da zan baki karki yarda ki aure Namjin da baya sonki saboda duk abinda kika yi masa na kyautatawa kina kulawa da shi be zama lallai ya soki ba, 

duk abinda zai yimiki besa ga dole ne yana sauke nauyin da Allah ya ɗora masa ne a kanki ba wai don yana sonki ba ko wannan kulawar idan ke samu me ilimi ne da tsoron Allah shine zai kula dake ya sauke miki hakkin ki ina faɗa miki wannan ne domin nan gaba bake ba ko kawarki inda hali ki bata wannan shawarar sai abu na biyu Salmah don Allah ko bayan raina ki kulamin da abinda zan haifa nasan zakiyi min wannan." Jikin Salma ne ya yi sanyi duk da ƙanƙantar shekaru irin nata,

Amma akwai fahimta Sosai kallon Yusrah tayi cike da kwarin gwiwa tace "Babu inda zakije Aunty Yusrah zaki hauhu lafiya ki raini abinda kika haifa kuma in sha Allah auren soyayya zanyi." Murmushi tayi kana tace "Salmah kenan jikina baya bani zan raini abinda na haifa amma na barmiki amanar Ɗana ko ƴata." Salmah dai to kawai tace saboda bata son zancen mutuwa tsoro take ji, 

Haka Sajjad ya dawo ya tarar dasu kamar wa yanda akayiwa mutuwa abin ya bashi mamaki suda yake tararwa suna hira basa ma jin shigowarsa wani lokaci kamar zai wuce sai kuma ya dawo yace "Babyn Ummie lafiya kuwa na ganku haka keda Auntynki." Kukan data ke riƙewa ne ta fashe da shi gaba ɗaya hankalinsu ya tashi har Yusrah,

zama ya yi yana tambayar ta lafiya, cikin kuka tace "Ya Sultan kacewa Aunty Yusrah karta mutu ta barni ina sonta da yawa ta tsaya ta kula muna da babynmu Ni banaso ta tafi ta barni." Dariya abin ya bashi itama Yusrah duk halinda take ciki sai da tayi dariya tace "Kega Salmah mutuwa tana kan kowa fa kuma ai ba cewa nayi zan tafi na barki ba kawai magana ce mukayi nida ke yi hakuri bazan koma ba." 

Sajjad yace "Ai Ƙanwarki bata son zancen mutuwa kwanakin baya da Ummei tayi rashin lafiya ai dena cin abinci tayi sai kuka da sallah bataso Ummie ta mutu itafa ko zancen mutuwa bataso ayi." Yusrah tace "Na manta fa mutuniyar bata son zancen mutuwa yi hakuri na dena jeki dauko muna Ice cream kizo musha." Kin tafiya tayi cikin muryar shagwaba data zame mata jiki tace "Bazani ba fa sai 

Yimin alkawarin zaki zauna tare dani da Ya Sultan da babyn mu." Dariya ta baiwa Sultan sai tashi ya yi yana faɗin ni kam nayi gaba idan kun gama shirmen ku zaki iya kirana muje kiyi wanka." Salmah tayi Wuff tace "Lah Aunty Yusrah ashe Ya Sultan keyi miki wanka baki jin kunya." Gaba ɗaya dariya suka saka shi dai ya wuce ya barsu nan suna dirama, washegari da safe ya shirya kayansa tsaf kana ya zauna gefen bed yana tayar da Yusrah wanka tayi kana ta dawo sai da ya kusance bayan sun kammala sha'ani ya sanar da ita tafiya zaiyi shida da Daddy sati zasu yi,

saboda haka ya kula da shan magani akan ƙa'ida rungemsa tayi tana kuka da kyar ta lallashe ta jikinsa ya yi sanyi ba yau ya saba tafiya ba amma ji yake kamar ya fasa tafiyar, haka sukayi wanka ya shirya ta rakosa har bakin mota ita da Salmah har ya shiga Mota tace "Ya Sajjad ina sonka Sosai da sosai Allah ya sadamu da alkhairy ka yafe ni." Wani irin yanayi yaji a ransa harta juya zata koma ciki saboda tasan ba cewa zaiyi yana sonta ba amma ta tsinkaye muryarsa ya kira sunanta cikin wani Irin yanayi ta wai go da sauri,

yace "Nima ina sonki Yusrah tah i really love you more than anything my wife." Batasan lokacin da hawaye suka zubo mata ba watansu 9 da Aure cikin na tara zasu shiga 10 zasu shiga beta cewa yana sonta ba ko sex Sukeyi sai dai kalamai na yabo amma ba soyayya, fitowa ya yi Mota suka rungume juna sun jima a haka ya yi kissing ɗinta Salmah dake gefe sai kwallah ta Zubo mata sun burgeta sosai 

Raɗa ya yi mata a kunne sai da tayi dariya kana ya shiga Mota suna ɗagawa juna hannu har ya bar gidan suka koma ciki wani farin ciki take ji sosai wanda bata taɓa jin irinsa ba bedroom ɗinta ta shiga ta buɗe kayan lefenta kusan kala goma da zabarwa Salmah da kayan kwalliya su turare ta kawo mata parlo Salmah kuwa hadda tsalle bedroom ɗinta taje ta aje kayan ta dawo suka dinga hira ita kanta tasan yau Yusrah na cikin farin ciki, 

har fita suka yi Direba ya kai su yawo suka wuce gidansu Yusrah sai bayan magriba suka dawo gida Salma ta samo kyaututtuka gidansu Yusrah ba kaɗan ba gidan Ummei suka je a nan suka ci girkin dare kana suka wuce gida sun gaji sosai wanka sukayi kana suka baje parlo suna kallo, Yusrah kuwa tana shan magani sai bacci, Salma ce kawai a falke tana kallo, 

Bangaren Hajiya Falmata kuwa Laure ta dannawa kira bugu ɗaya ta daga wayar tace " Kawas sun tafi fa matarsa ma bata jima da barin gidan nan ba saboda haka zaki iya turasu ayi abinda ya kamata." Laure tace "Yauwa dama kiranki kawai nike jira yanzu haka yaran na layin Unguwar Ni kawai suke jira na kirasu. Saboda haka sai ke jini." Ya datse kiran,

Tare da dannawa Mk kira buga ɗaya ya daga tace "Yanzu zaku iya shiga gidan kuyi abinda ya dace karku bari a samu matsala." 

Tofa masu karatu ko me zai faru?

Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs