HARIJAR YARINYA

Chapter 6

by @pinkyjay

🫦*HARIJAR YARINYA*🫦

( Romance and sexy story)

🔞
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay ce 


***
_______________________________
Following this to join my Whatsapp channel Domin samun Update ɗin wannan liltafin da sauran liltafaina ***

PAGE 9️⃣🔜🔟 


MK kuwa kallon yaransa ya yi su Jagu yace "Kai mu shiga Mota muje mu ƙadamar musu." Basu zame ko ina sai gidan Sajjad sai dai abin mamaki Get ɗin gidan a buɗe haka suka shiga gawar Mai gadi suka fara cin karo da ita Mk yace "Jagu yi sauri ka duba muna ta bayan gidan nan meke faruwa zamu shiga daga ciki." Jagu yace "Inaga fa mun samu wa ƴanda suka yima aikin da aka sakamu." MK yace "Bana don surutu jeka duba." 
su uku suka shiga ciki dama su huɗu ne suna shiga parlon suka je a rufe su da duka daga nan basu ƙara gane komai ƙarfe uku da rabi na dare suka farfaɗo daga dogon suman da sukayi, a jeje suka ga kansu ga Yusrah da Salmah kwance a gefe ɗaya an ɗaure su da igiya, har yanzu basu farfaɗo ba, Mk kuwa tsoro ne ya mamaye zuciyarsa yana so ya tina abinda ya faru amma ya kasa, 

kallon su Jagu ya yi dake baje kamar gawar waki ya kai musu duka amma shiru, hankalinsa ya yi mugun tashi wayarsa ce dake cikin aljihu ta soma ringing, dubawa ya yi Hajiya Laure ce zai daga yaji an daka mai wata uwar tsawa sai da ya zabura wasu gardawa ne sun kai su goma sha wani abu riƙe da manyan makamai da bindigogi ɗaya daga cikin su ne yace "Kawo wayar." Ba shiri ya bada kashe kiran ya yi kana ya saka wayar Aljihu ya bada umarni a ɗaure su gaba ɗaya, 

Lokacin Salmah ta falka dafe da kanta dake mugun ciyo kallon mutanen tayi ba alamar tsoro ko fargaba a tattare da ita kana tace "Kai zoka kwance ni fitsari nike ji tsabar walakanci shine kuka ɗaure mu kamar wasu dabbobi." Ta faɗa tana ɓata fuska ɗaya daga cikin su ne ya daga mata tsawa yace "Ke kama bakinki nan ba wurin wasa bane karki yi muna iskanci yanzu na aika ki barzahu." Dariya ta fashe da ita kana tace 

"Wai Ni zaka aika barzahu yo ai zai idan aikawa ta biyu ce zakayi min don na jima da mutuwa kazo kana wani ihu kamar kare idan bazaka kwnace ni ba ka saka yaranka su kwnace ni tin kafin raina ya ɓaci." Kasa ɓoye mamakin su sukayi gaba ɗaya wannan wace irin yarinya ce da bata tsoron mutuwa muryarta sukaje tana faɗin "Ina ne banɗaki yake.?" Da mamaki suke kallonta harta kwance kanta ta mike tsaye tana waige waige, 

Tsawa Ogansu ya daka mata yace tayi fitsarin a nan wani kallon baka da hankali ta watsa mai cike da tsiwa tace "Kutumar Uba ni Salmah Yar jagaliya zan buɗe jikina nayi fitsari a gaban gardawa ai wallahi baku isa ba kunsan bakuda makewayi ubanwa yasa ku dauko ni iyye to wallahi bari kuji yasin bazan yi fitsari a nan ba haka kawai yo hauka akeyi ne idan ka isa ka saka Matarka ko Ƙanwarka ta tube gaban abokon iskancinka tayi fitsari aikin banza kawai." 

dariya ce ta kwacewa ɗaya daga cikinsu yadda ta riƙe ƙugu tana zabga masifa kamar wata Uwarsu yarinyar da wani ƙaramin duka ya isa aikata lahira amma take wannan cika bakin, yace "Ke wai kesan a ina kike kuwa kuma kesan a gaban suwaye kike.?" Taɓe baki tayi kana tace "Sosai kuwa ina gaban ƴan kidnapers masu satar mutane suna karɓar kuɗin fansa daga baya kuma su kashe mutane, ba kowa bane ku face ƴan wutar jahannama masu cin zalin jama'a, 

talakawa da basu ji ba basu gani ba abinda zasu ci ma gagarar su yake yi bayan haka kuna da wata kamace data wuce wannan.?" Ta faɗa tana nuna su da yatsa." Ogan su ne yace "Baki faɗi ƙarya ba haka muke amma wutar ai bata Uban ki bace....."Kai wallahi sai dai Ubanka ni zaka zaga ka godewa Allah ya yi maka tsayin da ko tsalle nayi bazan cinma fuskarka ba wallahi da saina watsa ma mugun mari don ni ba'a zagin Iyayena, Ubana ya yi min tarbiyyar da bana satar abin kowa 

Balle na sace mutum na kawo sa jeje ina neman kuɗin fansa." Ɗaya daga cikinsu ne yace "Ogah rabuda ita taje tayi fitsari wannan yarinyar Yar rigima ce Na lura ko kwana zamuyi a nan duk ka faɗa saita mayar ma da magana bata da tsoro." Kallonsa ya yi yace "Bari kaga yadda zata tsorta yanzu." Karasa ya yi gaban Salmah ya saita ta da bindiga yace "Mai maita abinda kika faɗa yanzu idan ke cika kona fasa miki kai yanzu." Dariya ta saka kana tace "Wai idan na mai maita shine zaka barni da rai to wallahi ba zan mai maita ba sai dai ka kashe ni a karo na biyu,

Kuma wallahi kona sake mutuwa dawowa zan koma yi na cigaba da rayuwa cikin jama'a saukar da bindiga ya yi kana yace "Kai zo ka rakata tayi fitsarin ta dawo." Koda suka je wurin fitsari sai da tayi masifa da wanda ya rakata ya jaye ya bata wuri kuma ya idan ya waigo ya kalleta saita fasa mai ido ɗaya." Shi tsoro Salmah ke bashi suna dawowa Yusrah na falkawa lokacin gari ya fara haske ganin inda suke hankalinta ya yi mugun tashi da gudu Salma ta karasa wurinta, 

tana faɗin "Auntyna ke falka kenan kega inda Allah ya kawo mu ƴan iskan ga sun sace mu." Yusrah kuwa addu'a kawai takeyi harta ji ƙirjinta ya dena dukan uku uku, mafarkinta ya zama gaskiya kenan ɓarayi sun sace su kallonta Salmah tayi kana tace "Aunty Yusrah yunwa kike ji ne nasan lokacin cin abincin ya yi bara nayi musu magana su kawo abinda zakici." Kallon Salma tayi cikin wani yanayi,

Tace "Salmah karki je su illata ki, dan Allah nan ba wurin wasa bane." Dariya tayi kana tace "Mi dai ci uban juna jirani kawai ta ruga da gudu zuwa inda suke zaune tace "Waye babba a nan." Babu wanda ya yi magana tsaki tayi kana tace "Ƴan wahala karku yi magana to Auntyna ta falka daga bacci abinci take buƙata saboda abinda ke cikinta." Ɗaya daga cikinsu ne dake mugun jin takaicin Salmah yace "Ke bamu da abinci a nan ina ruwan mu da cikinta." 

Salmah tace "Kai ɗan wahala waye ya kasa da kai da shugaban ku nike magana saboda ai kuɗi za'a biya a karɓe mu bazai yu a barmu da yunwa ba idan ba haka ba wallahi cewa zanyi kar a biya kuɗi a bari ku kashe mu." Shugaban ne yace "Kai jeka madafa ka karɓo musu abinci." Salmah na tsaye aka dawo farar shinkafa da gishiri wani kallo tayiwa abincin kana ta zubar tana faɗin "Kan Uba wallahi baza muci wannan ba ai naga har kayan abincin mu kuka kwashe, 

Saboda haka a ɗibo muna kayan mu muci haka kawai mu jakuna ne Ni ko a rayuwata ta farko ban taba cin wannan ba." Shugaban yace "Wai ke meyasa kike haka ne idan fa kika matsa min kashe ki zanyi na baiwa karnuka namanki su cinye." Yadda ya yi magana haka ta mai maita cikin murya kamar tasa da mamaki suke kallon ta anya yarinyar nan ba aljana bace suka dauko, 

Ganin kallon da suke mata ta sake sauya murya irinta yara yan shekara biyar tace "Za'a bamu abinda zamu ci ne ko saina dauko da kaina." Ogan yace "Jeki dauko idan kesan inda suke." Dariya tayi kana tace "Wannan ai ba matsala bace naga taliyar da kaci bata gama narkewa ba gata nan tana yawo a cikin hanjinka idano ya zare yana son yi magana amma ya kasa da kyar yace "Ke mayya ce.?" 

Dariya tayi tare da yin Muryar manya tace "Sosai kuwa ina cin mutane bana gashi masu maiƙo nike ci amma kai naga baka da shi wancan ya fika maiƙo a jiki." Ta faɗa tana nuna wanda ke bayansa, zare idanu sukayi duk sun tsorata amma suka basar ita kuwa kai tsaye wata runfa ta nufa ta buɗe wani buhu kayan tea ne a ciki babu abinda babu su ai kuwa kwaso ta fito inda suke dafa abinci ta nufa akwai ruwan zafi ta ɗebo da cup kana wuce suka rakata da idanu, 

Yusrah kuwa da mamaki take kallon Salma harta kammala haɗa mata tea ta sha kana itama ta haɗa ta sha tace "Babyn Ummie ya akayi suka baki.?" Salmah tace " ina magana suka bani wai yaushe za'a sallame mu ne naga basu kira kowa ba a kawo kudin fansa." Yusrah tace "Inaga kashe mu zasuyi shiyasa." Salmah tace"Wa zai tsaya su kashe sa chaf kima dena Wannan zance." 

Bangaren Hajiya Falmata kuwa da Hajiya Laure sai kiran wayar Mk sukeyi a kashe gaba ɗaya hankalinsu ya tashi, 

Bangaren gidan Sajjad kuwa sai lokacin sallar asuba maƙota sun fito zuwa masallaci aka ga get ɗin gidan buɗe sai gawar Mai gadi a bakin kofa da yake ko ina na gidan a haske ne kamar safiya, nan da nana jama'a suka taru aka kira jami'an tsaro aka shiga gidan ba kowa a ciki ta hanyar Cc TV Camera dake gidan aka ga shigowar ɓarayin har fitarsu tare da su Yusrah sai dai babu wanda aka samu ganin fuskarsa, nan fa labari ya bazu, ɗaya daga cikin jami'an tsaro ne yaje gidan Alhaji Hameed,

Saboda ya yi ta kiran wayrsa amma bata shiga get Man yaje ya sanar da Hajiya Ummei anyi baƙo da yake da kayan gida yaje, tace Ya shigo parlo bayan sun gaisa yake sanar da ita abinda ke faruwa suma ne kawai Ummei batayi ba faɗar irin tashin hankalin data ke ciki ɓata lokaci ne, har wani jiri take ji gashi Sajjad da mahaifinsa basu ƙasar gaba ɗaya ta tabbatar babu wanda za'a samu a cikin su sai zuwa gobe, 

Da kyar tayiwa ɗan sanda bayani yace zasuyi iya ƙoƙarin su idan kuma ƴan kidnapers din sun kira waya ta sanar dasu ya karɓe number wayarta kana ya tafi akan idan wani abu ya taso zai dawo, Ummei kuwa ta rasa ta inda zata fara neman taimako fatanta su kira kawai su faɗi abinda suke buƙata a basu su sako mata suruka da Salma,  

tunani ta shiga yi wai suwaye suka aikata wannan ɗan yen aikin babu wanda yasan tafiyar su Sajjad daga ita sai Hajiya Falmata dasu Yusrah wannan abin ai shiri ne wallahi Allah ya tone asirin ko waye don tasan idan Sajjad zai bar ƙasa babu wanda yake faɗawa sai dai idan ya isa ya kirata wasu hawaye ne suka zobo mata ko a wane hali Yusrah take ciki gashi tana iya haihuwa ko wane lokaci ga Salmah da girma ya tasowa kar su lalata mata ƴa tinda abinda sukeyi kenan, Wani lokaci 
addu'a take tayi a bakinta wanka tayi kana ta fita bata zame ko ina ba sai Makarantar Malam Liman koda taje yana karantar da almajiransa cikin gida ta shiga Wurin Matarsa ta jira shi sai da ya shigo kana ta sanar da shi abinda ke faruwa taje don Allah a taimaka mata da addu'a zata aiko kayan wasu kayan abinci a linka fiye da kullum yace ai ko yanzu akwai buhu goma cikin wa yanda ta aiko tace ai wannan na sadakar daban ne har jama'ar unguwa da basuda shi sai a basu ba iya almajirai ba, 

dubu ɗari biyu ta bar tace a fara cefene kafin ta aiko sako kana ta dawo gida, 

Hajiya Falmata kuwa har lokacin batasan abinda ke faruwa ba saboda Farida ta dena zuwa part ɗin Hajiya Ummei, gashi wayar Mk a kashe har yanzu ƙarfe biyu na rana ba wani labari, in dai ba kamasu akayi ba ai kashin su ya bashe asrinta ya gama tonuwa don ana kama Mk sunan Hajiya Laure zai faɗa ita kuwa tasan matsawar Laure ta shiga hannu to shikenan har aurenta da Alhaji Hameed sai ya mutu bazata kai labari ba, 

Ummie kuwa tana makale da waya tana jiran a kirata ga datar wayarta a kunne tana duba Sajjad ko yana online ta sanar dashi halinda ake ciki ko menene ya barshi ya dawo gida asan yadda za'ayi a cece rayuwar su Yusrah 

Bangaren su Yusrah kuwa 
Tofa masu karatu shin su waye suka sace su Salmah bayan Ɓarayin da Hajiya Laure ta tura an haɗa harda su ya zata kasancewa su Salmah za'a sallame su ne ko ya ya Sajjad zai dawo kuwa 
Asirin Hajiya Falmata zai tunu? Muje zuwa dai
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay