HARIJAR YARINYA

Chapter 7

by @pinkyjay

🫦*HARIJAR YARINYA*🫦

( Romance and sexy story)

🔞
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay ce 


***
_______________________________
Following this to join my Whatsapp channel Domin samun Update ɗin wannan liltafin da sauran liltafaina ***

PAGE 1️⃣1️⃣➡️1️⃣2️⃣

Ummie na zaune har yamma shiru ba wani labari hankalinta ya ƙara tashi anya ba kashe su akayi ba kuwa tunda ya kamata ace an kira don su faɗi abinda suke buƙata amma shiru, ita ya zatayi wayarta ta soma ringing da sauri ta daga ganin Sajjad ne yake kira ta video call Whatsapp, yace "Ummie ya kike ina kiran wayar Yusrah bata zuwa lafiya kuwa na ganki haka.?" 

Ummie tace "Sultan kome kakeyi ka dawo gida an sace su Yusrah an kashe me gadi har Yanzu ba wani labari babu kalar binciken da jam'ian tsaro basuyi na amma shida ɗaya aka samu ta Cc TV Camera gidanka ƴan kidnapers ne suka shigo gidan suka ɗauke su bayan sun kashe Mai gadi." Ta faɗa tana fashewa da kuka sai yanzu yazo mata." Sajjad kuwa dake kawai ya yi yace "Ki dena kuka Ummei kesan ba lafiya ce dake babu abinda zai samesu in sha Allah 

yanzu zanje Airport idan akwai jirgi yau zan taso in Sha Allah." To kawai tace masa ya kashe wayar ruwan sanyi ya dauko ya sha yana haɗa kayansa ne zame ko ina sai Airport ya yi sa'a saira awa ɗaya jirgin Najeriya ya tashi ya biya kuɗi kana ya zauna jiran lokacin tashin jirgi, kiran Ummei ya sake yi ya sanar da ita yana filin jirgi nan bada jimawa ba zasu taso addu'a tayi masa kana ya kashe wayar sai lokacin ya tina bashi kaɗai yazo kiran wayar Daddy ya yi har sai biyu be ɗauka ba, 

Sai gab da jirgin su zai tashi ya kira Sajjad nan yake sanar da shi hanlinda ake ciki Daddy yace shima gobe zai dawo don daya sanar dashi tare zasu dawo, 

Ɓanagren su Salma kuwa ganin yamma tayi ne ba'a neme su ba sai shigowa akayi da wasu mata su biyu ɗaya juna biyu gareta kamar dai Yusrah ɗaya kuma dattijuwa ce, ta fito babu wanda ya kulata gun Ogan nasu taje tace "Kai ya haka ne wai taya zaku aje mu har yamma tayi baku haɗa mu da ƴan Uwanmu ba suga muna cikin ƙoshin lafiya kana ku nemi kuɗin fansa a biya ku, ga wurin nan duk sauro ne da shi idan nan zamu sake kwana a nemo min nent kar zazzabi ya kama mu." 

Kallonta ya yi kana ya kece da dariya yace "Lallai yarinyar nan kanki naja har Kesan yadda akayi kenan to bari kiji an riga an biya mu kuɗin ɗaukar ku samu akayi mu dauko me cikin muka tarar daku biyu ne shine aka bamu umurni harke a dauko saboda haka ba gida zaku koma ba kashe ku zamuyi umarni kawai muke jira." Jikinta ne ya yi sanyi amma sai ta basar tace "Yo amma ko waye wannan ya saka a sace mu anyi ɗan asara wallahi kuma ka sanar ma ko waye matsawar muka bar wurin nan a raye to wallahi, ya gina ramen mutuwarsa,

Kai kuma da yaranka hamm wallahi sai Allah ya saka muna azzaluman banza kawai mucuta." Dariya ya yi babu alamar damuwa ko imani a tattare dashi yace "Ai bake ce ta farko ba bazaki zama ta ƙarshe ba kega daga miki kafar nan da mukeyi saboda ba'a bamu umurnin duka ko kisa bane da tin daren jiya kun bar duniya don ke saike rigar yar uwarki mutuwa." 

Salmah tace "Yo an gayama Ina tsoron mutuwa ne ai ni ke biyar mutuwa tana guduna saboda haka ana cewa ka kashe mu to idan kai ɗan halak ne ba shige ba ka fara dani kuma a bamu gidan sauro ko ina cire wanda keke shiga." Banza ya yi da ita be ƙara magana ba wayar Yusrah data gani gefensa ce ta ɗauke batare da ya ankara ba ta wuce, gidan sauro ta ɗauko ta shiga kicaniyar daura musu, bayan ta kammala, ne ta zauna gefe tana tunanin hanyar da zasu bi 

don tsira da rayuwarsu tabbas mutanen nan basu da imani amma waye wannan ya biya kuɗi a sace Yusrah shine abinda take tunani ya tsaya mata a rai, duhu ne ya sauka ba haske sosai, ga me cikin da suka dauko kamar na ƙuda ta kamata fitowa tayi waje gaba ɗaya dakarun taga sun ƙaru sun zagaye ko ina kamar masu haƙon zaki, sai cewa tayi "To ƴan wahala a bamu fitila muna buƙatar haske naga ai ba makafi kuka aje ba." 

Cillo mata fitila akayi ta ɗauka ta koma ciki, ta ɗora ta kan wani dutse da taimakon dattijuwar da Salmah Matar ta haihu ta samu ƴa Mace Yusrah na bacci batasan abinda ke faruwa ba Salmah ta fita zuwa madafa ta haɗa musu ruwan zafi aka yiwa yarinyar wanka uwar ta gyara jikinta, kana suka koma ciki Salma ta gyara wurin, kayan shayen data ɗebo da safe ta duba ta haɗawa me jegon ta sha, kana suka kwanta da mayafin matar aka naɗe yarinyar ba kaya ga sanyi, 

bayan sun kwanta ne kowa ya yi tsit wasu duk sunyi bacci itace kawai batayi ba wayar Yusrah ta kunna dake kashe ta sakata a silent jin ƙarar Mashin da Mota yasa ta tashi zuwa bakin ƙofa ta laɓe gun wata runfa taga wanda ya fito cikin motar ya nufa gaba ɗaya masu gadin sukayi chan ba tsoro ta fito a hankali har zuwa gefen rumfar ta laɓe magana sukeyi da me motar yana musu faɗa saboda mi zasu dauko wa yanda suka zo daga baya da kawai su kashe su,

Ogan yace "Kaga Yallaɓai sun riga sun tarar damu muna kwasar kayan abinci idan gasu da makamai kuma fa yarinyar suka zo kashewa idan muka saka wasa matsala za'a samu shiyasa muka zo dasu gaba ɗaya kai jeka zo dasu." Ya faɗa ai kuwa aka fito dasu MK dama ba wuri ɗaya aka jesu ba gudun karsu kashe Yusrah din kallonsu guy ɗin ya yi fuskarsa sanyi da baƙin gilashi kura masa idanu Salmah tayi amma bata sanshi ba, saboda gilashin da ya saka, 

kallon su Mk ya yi kana yace "Kai waye ya turo ku kashe matar Sajjad amsa ɗaya nike buƙata idan kukayi min ƙarya mutuwa zakuyi a banza." Mk yace "Idan muka faɗa bazaka kashe mu ba." Yace "Ba tabbas amma faɗar gaskiya zai saka ku tsira da ranku." MK yace "Maganar gaskiya ba kisan kai muka je yi ba sace matar gidan muka jeyi idan muka ga abin bazai yu ba mu kasheta Hajiya Laure ce ta bamu wannan aikin 

da farko munce bazamu yi tace "Aikin Ƙawarta ne Matar Alhaji Hameed mai zinari idan mukayi abinda aka ce za'a bamu miliyan ɗari shida zamu aje yarinyar ne muyi mata fyade mu ɗauke video mu turawa mijinta mu nemi kuɗin fansa naira biliyan dubu ɗaya idan ba'a kawo ba mu kasheta har yaron cikinta, mu jefar da gawa idan an kuma an kama mu muce "Mijin yarinyar ne ya saka mu aikata hakan saboda baya sonta 

Mahaifinsa ne ya haɗa auren, wannan shine gaskiyar abinda na sani." Tafi guy ɗin ya yi harda fito kana yace "Ashe akwai Macen da tafi iya makirci fiye da Namiji ai wannan tsari zamu bi kafin a kashe su don ko an biya kuɗin da aka nema ba tsara sukayi ba wallahi saina ɓatawa Sajjad suna a idon duniya saina saka shi dana sanin a rayuwarsa dani yake wasan, dana kuɗin sun shigo hannu ko kasheta kawai har yarinyar dake tare da ita banaso a samu matsala,

su kuma wa ƴan nan ku gama dasu kawai don basuda amfani." Mk ya fashe da kuka sai rokon guy ɗin sukeyi amma ya yi banza dasu a gabansa suka harbe su gaba ɗaya Salmah kuwa toshe bakinta tayi don kukan yazo mata da sauri ta bar wurin ta koma ta kwanta jikinta har rawa yake yi, tsabar tashin hankali duba wayar Yusrah tayi lokacin ta ɗauke ba charge cikin jikinta ta ɓoye wayar bacci kuwa don yana ɓarawo ne kawai ya ɗauke ta, 

saboda idanunta babu abinda suke hasko mata face su Mk da aka kashe ga muryar Guy ɗin nan dake mata amsa kuwa cikin dodon kunne asubar fari ta falka saboda jin nishin Yusrah tana famar rafka salati da addu'a gurfane ta ganta sai gumi takeyi tausayin Yusrah ne ya kamata Dattijuwar nan ta duba Yusrah tace haihuwa ce amma da sauran lokaci sai zuwa anjima amma zata iya yawa tawa ko cikin bukkar da suke ne da taimakon Salmah Yusrah ta soma zagayen bukkar tana cikin wannan halin har gare ya waye, 

saiga gashi an fito dasu gaba ɗaya an gurfanar dasu tare da kara musu bindiga daya kuma na riƙe da waya Ogan yace "Yauwa sai ku yiwa ƴan uwanku magana kuna cikin wani hali su taimake ku su bayarda abinda akace daga yau zuwa gobe idan ba haka ba kashe ku zamuyi." Salmah tace "idan kuma muka ki faɗa fa.?" 

Ogan yace "Saina fasa kanki da bindiga amma ta kan wannan zan fara kiga mutuwarta daga baya mu kashe ki bayan munyi miki fyade." Dariya tayi kana tace "Wai hauka naji zan faɗa amma saboda Aunty Yusrah da abinda ke cikinta amma wallahi da ko gutsura namana zakuyi to bazan taɓa faɗar abinda kuke bukata ba ƴan wahala kawai." Dariya yayi tare da zungurar cikin Yusrah da bindiga saida ta zabura saboda azaba Salmah tayi Wuff ta kare cikin , 

cikin murar kuka da masifa tace "Wai kai jahilin inane marar imani da tausayi wallahi uwarka tayi asarar haihuwa da cikin Da irinka wallahi gwara ɓarinsa kuma Allah ya isa na rantse da Allah idan wani abu ya samu cikin nan gaba dayan ku saina ga bayanku koda kun kashe ne saina zama fatalwa na dawo na kassara rayuwar ku." Ta faɗa tana kuka wanda ke bayanta ne ya kai mata duka da bindiga saida ta zube ƙasa bakinta na jini, 

ɗayan kuwa sai video yake yana dariya tayar da Salma ya yi kana ya kai mata naushi a ciki da baki sai da hancinta ya da baki suka fashe Yusrah na kuka tana rokon su rabuda Salmah suyi mata koma menene amma saboda ƙarfin hali Salmah tace "Aunty Yusrah don darajar Allah karki ƙara magana ki rabuda su kawai wallahi bazan iya jurar ganin ana dukan ki ba." Ta faɗa ai kuwa suka ƙara mata duka ga kai ai kuwa ya fashe da jini har ya zubowa a fuskarta kana ogan yace su barta haka, 

yace "Maza ki fara magana." Salmah tace "Ya Sultan Ummie nah ku taimaka ku biya kudin fansa ku cece rayuwar Aunty Yusrah saboda tawa bata da amfani dole nasan daya daga cikin mu zai mutu amma bana so Aunty Yusrah ta mutu suna buƙatar naira biliyan dubu daya daga yau zuwa gobe idan ba haka kashe mu zasuyi gaba ɗaya ga Aunty Yusrah ta fara lebor." Ta faɗa tana dafe kanta saboda ta fara ganin dishi dishi 
 Kan Yusrah suka dawo kana sukace ke kuma cewa zakiyi iyayen ki su taimaka su cece rayuwarki saboda mijinki ya saka a sace ki a nemi kuɗin fansa Naira biliyan dubu biyu idan ba haka kashe ki zamuyi saboda yace baya bukatar abinda ke cikinki idan kuma kika ƙi faɗa to zamu yiwa wannan yarinya fyaɗe gaba da baya mu kashe ta a gabanki, kallon Salma tayi dake neman zubewa a wurin fuskarta duk jini girgiza mata kai Salmah tayi amma ina ko ba komai tana son Salmah ta tsira ta koma gida tare da abinda ta haifa don jikinta na bata kamar bazata bar wurin nan a raye ba, 

Allah ya gani tana son mijinta koma yaya ne be kamata tayi mai sharri ba amma tasan matsawar Salmah ta tsira dole gaskiya zatayi halinta Allah baya goyon bayan zalunci haka Yusrah tayi magana itama tana kuka kana aka mayar dasu ciki Ummie aka turawa videon kana aka turawa Sajjad tare da mahaifin Yusrah Alhaji Tahir,

Salmah kuwa suma tayi da kyar ta farfaɗo bayan Yusrah ta saka ɗan kwalinta ta ɗaurewa Salmah kai koda ta tashi har fuskarta ta kumbure da kayar taja ƙafa ta fita babu wanda ta kallah ruwan zafi ta ɗebo ta wanke fuska da jikinta kana ta dawo ciki ta zauna, kanta na mugun ciyo kamar zai rabe gida biyu, Lokacin na ƙuda dawowa Yusrah........

Tofa masu karatu ya za'ayi wannan chakwakiyar ta warware 
Daga wannan sai lest Free page a cigaba da payment saboda gobe promo zai kare har Free page 

Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs