HARIJAR YARINYA

Chapter 9

by @pinkyjay

🫦*HARIJAR YARINYA*🫦
( Romance and sexy story)
🔞
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay ce 
 ,

PAGE 1️⃣5️⃣🔜1️⃣6️⃣

Laure tace "Aini abinda ya daure min kai bana samun wayar Mk har yanzu shiru ba wani labari ya kamata ace ya kirani saboda gashi dai za'a bada kuɗin da suka nema karsu yaudare mu fa.?" Hajiya Falmata tace "Aini in dai sun kashe yaran gaba ɗaya banda matsala suje suci kuɗin amma ina son asan inda suke bayan sun kammala wannan aikin mu kashe su da hannunmu kega shikenan babu yadda za'ayi magana ta fita ko nan gaba." 

Laure tace "Kuma fa haka ne amma kesan dole ki ƙara min kuɗi ko .?" Falmata tace "Bakida matsala da wannan kuɗin waje zan baka ya za'ayi su Mk su shigo hannu.?" Laure tace "Ai wannan me sauƙi idan har na samesu zan sanar dasu in dai akan kudi ne su riƙe bamu buƙata zamu basu sabon aiki so zo mu haɗu daga nan mu saka musu guba cikin abinci ko abin sha da sunci ko sun sha shikenan magana ta ƙare." Falmata tace "Gaskiya ƙawata kanki naja,

Sai ki fara bincike." Haka suka kammala wayar saiga Farida ta fito gefenta ta zauna kana tace "Mommy nifa wannan abin beyi min ba taya za'a ƙalawa Sajjad sharri idan aka kashe sa fa ko aka rufe sa gidan yari kenan taya zamuyi aure nida shi gaskiya a sauya wannan tsari ga kuma uban kuɗin da aka saka musu zasu biya haba Mommy dukiyarsa zai kwashe gaba ɗaya ya bayar.?" 

Hajiya Falmata tace"Yaro yaro ne to bari kiji Sajjad da Uwarsa sunfi karfin wannan kuɗin da kowa keganin sai an haɗa dukiyarsa data ubansa za'a iya karɓar Salmah to idan baki sani ba bara na gaya miki dalilin da yasa na yarda ki auresa saboda suna da dukiya ta ban tsoro Mahaifiyar Uwarsa kakarsa kenan ƴar ƙasar Jiddah Company gareta na kanta ginar zinari ake mata ana sarrafa shi a Companynta kana a fitar da shi wasu ƙasashe Kakan Sajjad sana'arsa kenan a chan ya haɗu da ita har alaƙa ta kullu sukayi aure, 

 bayan ta haife Hajiya Ummie bata ƙara haihuwa ba saboda haka ta maida sunan Ummei kan duk wasu kadarorinta data mallaka, Ummei nada shekara shida a duniya Mahaifiyarta Zaliha ta rasu daga nan Alhaji Ali ya dawo Najeriya ya yi sabon Aure saboda kulawa da Ummie harta kammala karatun bako ta fita kasar Masar tayi digiri kana ta dawo lokacin ya damƙa mata dukiyarta gaba ɗaya data gada matar daya aura ƴaƴanta biyu duk Maza ya dora su akan kasuwancisa 

A Dubai ta haɗu da Alhaji Hameed suka kulla soyayya harta kaisu ga aure bayan aure da shekaru shida ta haife Muhammad Sajjad tana kiransa da Sultan bayan shekara biyar ta sake hihuwa lokacin ina gidan nan yanzu haka Sajjad ke kulawa da dukiyarta don ta maida komai da sunansa wasu abubuwa ne kawai suka rage nasan ko waye take yiwa wannan tanadi saboda haka kega suna da dukiyar ɓoye wacce ba kowa yasan da ita ba." 

Farida tace "Allah me iko to ina abinda ta koma haihuwa.?" Falmata tace"Wannan kuma be shafeki ba zancen sharri kuma ai zai wuce don suna da dukiyar da zata fito da shi ya cigaba da rayuwa ba zancen kisan kai, saiki shirya zama matarsa Uwar ƴaƴansa." Farida tace"Idan basu kashe Yusrah ba fa.?" Cike da ƙosuwa da zancen Farida Falmata tace "Ko an kai kuɗi kasheta zasuyi ko ba a kai ba ma mutuwa zatayi kega tashi zuwa inda zakije ke dameni." Haka Farida ta fita dama gidansu Ramlah zataje,

Bangaren su Salmah kuwa sai bayan sallar azahar ta falka Matar mai gari ta kawo mata kunun jego ta sha sosai kana tace ta dinga ɗora Azan akan nono yana ja haka nan a hankali ruwan nonon zasu zo in dai tana shan kunu ta saka mata tamne ƙuwa a cikin garin kunu yadda ruwan nono zasuyi saurin zuwa, bayan ta fita ne Salma ta kalle Inna tace "Ai bani na haifeshi ba taya zan iya shayar da shi.?" Inna tace "Ai ba dole saika haife yaro ba zaki iya shayar da shi Yar nan saboda yanzu kece uwa a gareshi,

amanar da kika karɓa ne Allah zai baki lada saboda haka ki ɗaure kiyi abinda akace karki ƙara nunawa bake ce kika haifesa ba kinji." Salmah ta daga kai cike da gamsuwa, haka Inna ta gwada mata yadda zata ɗora Azan akan nono ai kuwa bakinsa na kai ya chafke saida ta zabura Inna ta riƙe ta sha kawai yakeyi amma ba komai a ciki har ya gaji ya saki bacci ya dauke sa Inna tace "idan ya tashi kika bashi madara ki ƙara ɗora shi a kai ya cigaba da sha ta haka ruwan nonon zasu zo." kwanan su uku ruwan nono suka zo ai kuwa Salmah hadda kuka idan yana sha saboda ciyo take ji sosai gashi nonota sun ƙara cikowa sosai., 


Ɓangaren Sajjad kuwa Ahmad na iya ƙoƙarinsa na binciken hanyar da zata sada su da kidnapers ɗin da kyar suka samu wata makama ta hanyar sabon videon da suka saki ai kuwa suka shirya shiga jeje, 

Ɓangaren ƴan kidnapers kuwa haka suka dawo suka kira wanda ya sakasu ɗaukar Yusrah suka sanar da shi abinda ke faruwa cikin tashin hankali yace "Kai ya akayi hakan ta faru kuyi iya yinku domin ku gano inda suke kwana biyu kawai na baku." Ya kashe wayar Ogan ya kalle sauran yaransa yace "Kaji min wani iskanci tin farko daya bari an kashe su ai da haka bata faru ba amma yace ba yanzu ba sai an karɓe kuɗin fansa gashi kuɗi ne masu yawan gaske,

gaskiya mun gaji babu inda zamuje saboda yanzu haka ina da tabbacin jam'ian tsaro sun bazu ta ko ina suna jiran suga wani motsi mu sanar da shi mun kashe su gaba ɗaya shine kwanciyar hankalin mu." Ɗayan yace "Nifa inaga sai idan wani ne yazo ya ɗauke su amma duk girman jejen nan da yawansa ace cikin awa uku sun ɓata basu ba sawunsa anya yarinyar ba mayyar gaske bace kasan babu abinda mayu basa iya yi shine suka ɓata." Ogan yace 

"abinda nike tunani kenan saboda na ɗan tsorata da yanayinta yadda akayi ta hango taliyar da naci a cikina bayan koda naci bacci sukeyi babu wanda ya fito na tabbatar baza su koma gida ba akwai inda suka nufa ko Mota suka hau sai dare zasu kai cikin gare." Haka suka cigaba da tattaunawa har zuwa dare kana suka saki videon gawar wata mai ciki da suka ɗauke ba'a turo kuɗin fansa ba suka kashe ta kana suka rufe gawar akan Yusrah ce suka kashe saboda ba'a turo kuɗin ba, 

suna jiran kudin fansar Salmah zuwa gobe da safe idan ba'a kawo ba itama zasu kasheta, Sajjad na arba da videon sai zubewa ya yi ƙasa ba lumfashi a tattare dashi, asibiti suka nufa da kyar Likitoci suka iya dai daita bugun zuciyarsa, Ummie hankalinta ya gama tashi jininta ya hau sosai, kwantar da ita akayi saboda ko wane lokaci tana iya faduwa, ciyon sashe ya kamata, 

Ahmad ne ya shigo ɗakin data ke shida Abba suna dubata kallon Ahmad tayi kana tace "Don girman Allah kubari a kai musu kuɗin nan tunda akwai su kaga sun kashe Yusura har abinda ke cikinta yanzu Salma ce kawai ta rage amana ce na karɓo yar mutane bana so itama tayi mutuwar wulaƙanci a hannunsu please." Ummie ta faɗa tana zubar da kwallah, Abba yace "Nima abinda na faɗa kenan amma ba'aji maganata ba aka nuna min bansan abinda nikeyi ba 

gashi nan sun kashe ta a banza akan dukiyar da an tara ta ba'ama san iyakarta ba duk wanda keda Company da ƙasar waje ana sarrafa masa zinari ai wannan kuɗin ba komai bane a wajensa, yanzu wa gari ya waya ba'a shiga jejen ba aka ceto rayuwarsu ba'a bayarda kudi ba." Ya faɗa yana ai kawa Ahmad mugun kallo Ummei tace "Ƙaddara ta riga fata alhakin mutuwar Yusrah na kanmu don Allah kar ayi wani kuskure in rasa Salmah duk yadda za'ayi a taimaka a karɓo min ƴata, 

na kasa sanar da mahaifiyarta abinda ke faruwa Yayanta ne kawai ya sani ina da tabbacin da besan ko suye mu da Allah kaɗai yasan abinda zai faru yau kwana haɗu ko yunwar cikinta kawai ta isheta." Ahmad yace "Ummei za'ayi yadda kika so a shirya kuɗin kawai zanje na kai in sha Allah zan dawo miki da Salmah har gida." Wani murmushi Abba ya yi kana ya fita, saboda wayarsa dake ringing chan baya ya nufa ya amsa wayar kana ya dawo yace zai fita ya karɓo wani saƙo sai dare zai dawo,


Ahmad kuwa room ɗin da Sajjad yake ya nufa har zuwa lokacin bacci yake yi be farka ba, gefensa ya zauna kusan mutane talatin kana ya soma buɗe idanunsa bakinsa ɗauke da addu'a har ya tashi zaune sannu Ahmad ya yi mai kana yace "Sajjad a shirya kuɗin kawai zanje na kai musu a karɓo Salmah." Sajjad yace "Kana da tabbacin zasu baka ita kuwa anya basu kashe ta ba tinda haka sukeyi fa." Ahmad yace"Jikina baya bani sun kashe ta,

saboda ita kaɗai ce ta rage musu idan suka kashe ta sun san babu wanda zai kai musu kuɗin fansa." Sajjad yace "Haka ne kira Dr yazo ya sallame Ni." 

Abba kuwa ya fita Motar ya shiga sai ga kira ya shigo ɗagawa ya yi yana faɗin "Kai Musa Yanzu nike tunanin kiranka kasan an kashe matar Sajjad saura ƙanwarsa.?" Musa yace "ina zan sani bayan kana chan maƙale da shi ka zama maye ai wallahi naji daɗin hakan sosai Allah yasa har ita a kashe." Dariya Abba ya saka kana yace "Wai kai har yanzu muguntarka na nan ko dai kaine ka saka a sace ta.?" 

Musa yace "Hamm wallahi dana samu wannan damar tsaf zan aikata ko waye wannan Allah dai ya biyasa ai da sun haɗa har Sajjad ɗin." Abba yace"Ai an jaraba hakan be samu bane sai wannan lokaci." Musa yace "Kai Abba ya akayi ka san an jaraba anya biri na mai." Dariya ya yi kana yace "Sai idan beji wuta ba amma Ni babu abinda na aikata ina dai....kai sai anjima ga Sajjad na kirana." Ya katse wayar 
Don ya kula tsaba musa zai saka shi ɓarin baki,


bangaren Salmah kuwa suna samun kulawa sosai Azan na samun kulawa ga ruwan nono sun samu, ba laifi ƙarfe biyu na rana suka soma jin hayaniyar mutane anata gudu sai harbin bindiga daga nesa ai kuwa Salma tayi Wuff ta goya Azan ta haɗa kayansu ta kulle ta fito, kowa gudu yake yana neman mafaka saboda kidnapers ne suka shigo garin, ai kuwa Salma ta soma cin tayoyinta gudu kawai takeyi batasan inda take jefa ƙafarta ba har suka fito titi karaf kake ji muta ta buge ta ta zube ƙasa kanta ya ƙara fashewa da jini 

Sauran motocin dake baya ne suka dakata Me motar daya kaɗe ta ne ya fito Ahmad kenan ya ɗauke ta ya saka a wata Mota yace motar ta juya a kaita hospital suka kuma suka shiga cikin garin don taimaka musu musayar wuta sukayi sosai da ƴan bindiga sun samu nasarar kashe wasu an kama wasu saura sun gudu sai gab da magriba suka shigo cikin gari,

Bayan sunyi sallah ne Ahmad ya ya tuna da karɓar Salmah suka fita wayar kidnaper ɗin ya kira sai ringing yaji kusa da shi ya ɗaya daga cikin wayoyin kidnapers ɗin da suka kama ne ke ringing dubawa ya yi don tabbatarwa ai kuwa da sauri ya tashi ya fita chan inda aka tsare su yace "Kai cikin ku waye me wannan wayar sukayi shiru ai kuwa nan aka fara jibgarsu sai da suka sha wuya kana Ogan yace"Wayarsa ce damko wuyansa Ahmad ya yi kana yace,


"Kai ina Matan da kuka sace kun kashe ɗaya ina Salmah take." Cikin tsananin azaba yace "Wallahi bamu kashe ko ɗaya ba guduwa sukayi." Wani mugun mari Ahmad ya yi masa sai da hancinsa ya koma fashewa yace,


Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay