Chapter 10
by @pinkyjay
🫦*HARIJAR YARINYA*🫦
( Romance and sexy story)
🔞
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay ce
PAGE 1️⃣7️⃣🔜1️⃣8️⃣
"Kai gayamin gaskiya kona fasa kanka da bindiga yanzu nan ba Office ɗin ƴan sanda bane da ku ka raina nan barikin sojoji ne." Nan ya sanar da Ahmad yadda akayi su Salmah suka tsare amma basu kashe ko ɗaya ba sai dai basu faɗi cewa saka su akayi ba haka Ahmad ya fito ya koma Office ɗinsa Nura ne ya shigo yace "Yallaɓai yarinyar ta farfaɗo yaron dake tare da ita yana cikin ƙoshin lafiya amma taki magana ko zaka zo ne.?" Ahmad yace gashi nan zuwa
Ya jima kafin ya fita zuwa asibitin dake cikin break din inda take kwance ya nufa ya zauna batare da ya kalleta ba yace "me yasa ba kya magana ko ke kurma ce.?" Buɗe idanunta tayi tana kallonsa da sauri ta zabura har ta ɗan tsorata shi bakinta na rawa tace "Kai Abokin Ya Sultan ne.?" Da mamaki yake kallonta yace "Wane Sultan kike magana kesan ni ne.?" Tace "Eh nasan ka hoton dake parlon Ya Saltan kuna sanye da kayan nan da kuma parlon Ummie nah."
Zare idanu ya yi yace "Kece Salmah.?" Daga mai kai tayi da sauri yace "Alhamdulillah ina Yusrah take ne wancen yaronki ne.?" Salmah tace "Eh Aunty Yusrah Allah ya yi mata rasuwa a hanya lokacin da muka gudu." Nan ta sanar da shi yadda akayi suka gudu har mutuwar Yusrah da zuwan su ƙauye." Ai jikinsa har rawa yake ya dannawa Sajjad kira yace ya saka Direba ya kawo shi bariki shi da Ummie, Sajjad yace" Itama sun kashe ta ko.?"
Ahmad yace "Kaga kuzo kawai kasan bansata ba." Haka suka fito shida Ummei jikin kowa ya yi Sanyi kiran Muhammad tayi suka zo su uku Ahmad ya yi musu jagora har zuwa inda Salma take zaune Azan ya tashi sai kukan yunwa yake tana bashi nono yana sha suka shigo yadda Ummie hango Salmah sai kuka ya kwace mata da sauri ta karasa inda take suka rungume juna itama Salmah kuka takeyi, Azan ne ya saka kuka jin nono ya fita bakinsa,
Salmah kuwa kunya ce ta kamata sai jan zane tayi ta rufe jikinta tana bashi nono, Sajjad kuwa kasa karasawa ya yi wajen Ahmad ne keyi masa bayanin abinda Salmah ta faɗa Yusura mutuwa tay bayan ta haihu ba kashe ta akayi ba wannan yaron na hannun Salma ɗansa ne Muhammad kuwa tasayin ƙanwarsa ne ya kamahi yadda ta koma cikin kwana biyar ga kanta da bande ji da ƙafarta da hannunta, Ummie kuwa ta maida Salmah Tv yadda take shayar da Azan har ya yi bacci kana ta fito da shi Ummei ta karɓa wasu zafafan hawaye suka zubo mata,
Allah me yadda yaso Sajjad ne ya ƙarasa ya karɓe yaron yana kallo kamarsu ɗaya babu inda ya baro sa Muhammad ne ya karasa inda Salmah suka rungume juna tana kuka tace "Yaya ina Inna lafiya take.?" Yace "Tana Lafiya Salmah kullum saita yi muku addu'a Allah ya tseratar daku ashe Aunty Yusrah ta rigamu gidan gaskiya Allah yaji ƙanta da rahama." Ta karɓa da Amin Nan ta shiga basu labarin yadda sukayi kwana biyu a hannun kidnapers har ta saka musu ruwan ganye cikin abinci sukayi bacci,
kana suka gudu sun jinjinawa Salmah sosai tayi jarumta Inna ya kira ya haɗata da Salmah kana sukayi waya da Ummie tayi musu jaje tace ina sha Allah zatazo ta duba su." Kana suka wuce gida bayan an ƙara duba Salmah Azan kuwa lafiyarsa ƙalau, ruwan zafi Ummei ta haɗawa Salmah ta gasa jikinta kana tayi wanka tea ta fara sha mai zafi kana taci Abinci sai da taji kamar zatayi amai, magani ta sha kana ta karɓe Azan dake kuka Ummei tayi masa wanka an shirya shi cikin kaya masu kyau da tsada,
cikin hijab ta saka sha yana shan nono kunyar Ummie take ji sosai, har ya koshi kana ta ɗora shi a kai faɗa tana shafa bayansa, sai da safe tayiwa Ummie ta shige ɗakinta don gajiya take ji sosai a jikinta, sai lokacin Sajjad ya shigo yake sanar da ita an sanar da iyayen Yusura abinda ke faruwa amma har yanzu Babanta yace be yarda ba ƙara zai kai shi a kotu. Ummie tace "Allah ya kyauta Allah yana tare da me gaskiya." Sosa kansa ya yi kana yace "Ina su Salmah ne.?"
Ummie tayi dariya tace "Cewa zakayi ina Ɗanka suna ciki Yanzu suka shige idan ka dubasa sai da safe Ni na shige ko zan samu bacci yau kam." Yace "Allah ya tashi mu lafiya." Ta shige bedroom ɗinta inda Salmah ya nufa norking ya yi jin shiru ya tura kofar dakin ya shiga kwnace ya hango ta maƙale da Azan da nono a bakinsa ƙarasawa ya yi tare da zama gefen bed yana shafa kan Azan wata irin soyayyar yaron yake ji a zuciyarsa, a hankali ya zare da daga nono ai kuwa ya saka kuka saiga Salmah ta zabura tana buɗe idanunta,
kunya ce ta kamata ganin Sajjad da sauri taja zane ta rufe nononta, tana miƙa hannu ya bata shi amma yaron ya yi shiru saboda a kafaɗa ya dorasa yana shafa bayansa sai da ya yi bacci kana ya yi mai addu'a ya aje mata shi kana ya fita,
Bayan kwana biyu jikin Salmah ya warware saboda kulawar data ke samu gun Ummie Azan kuwa ya murmure Maman Yusura tazo ta gansa a ɓoye saboda Alhaji ya hana kowa zuwa kana ta koma gida, Ahmad kuwa yana kan bincike saboda ɓarayin sunki faɗar wanda ya turosu sai cewa sukayi sune suka saka kansu shi kuwa ya kasa yarda da hakan,
an yankawa yaron ragon suna ƙaton maraƙi Aka yanke da rago huɗu aka suya naman aka rabawa jama'a har gidansu Yusrah an kai Babanta ya dawo da shi, bayan suna da kwana biyu Ummie da Sajjad na zaune parlo tace "Muhammad magana zanyi da kai akan shawarar dana yanke jibe ranar assabar za'a daura aurenka da Salmah saboda ita kaɗai ce Macen data fi dacewa da kai,
nasan zaka ji abin wani iri amma haka shine dai dai idan na kyale ka haka zaka cigaba da zama yau sati biyu ta rasuwar Matarka, Salmah yarinya ce me biyayya da hakuri ga kamun kai uwa uba ga addini yarinta ce kwai a cikinta har yanzu sai kayi hakuri ko ba komai ɗanka bazai yi maraicin rashin Uwa ba yadda nike hango soyayyar yaron a idanunta har mamaki abin yake bani na tabbatar ko Uwarsa iya abinda zai samu kenan kayan barkar dana haɗa suna nan kaɗan kawai za'a karo a bata a matsayin lefe maganar sadaki kuma,
Kai zaka biya na kira Alhaji na sanar da shi komai ya yi magana da ƙanen Babanta sun Amince zasu baka aurenta Sadaki kawai zamu biya a daura auren taje gida ta kwana biyu gun Mahaifiyarta idan ta dawo saita tare amma idan akwai wata matsala saika faɗa.?" Sajjad kuwa bema san abinda zai faɗa ba shi dai gaba ɗaya burinsa ba zai cika ba na auren kalar Macen da yake so ba sai yara ake aura mai har Yusura tafi Salmah ƙiba amma bazai gujewa umurnin Mahaifiyarsa ba ko don saboda yaronsa yace "Ummie banda wata matsala da hakan Allah ya tabbatar da Alkhairy Ni zan koma sai da safe."
Addu'a tayi mai sosai yaji sanyi a ransa kana ya wuce Salmah kuwa tazo fitowa ta Kawo mai Azan taji abinda suke tattaunawa har amsar daya bayar dole ta koma ciki bata fito ba har ya tafi kwnaciya tayi tana kallon Azan har bacci ya dauke ta, Ɓangaren Hajiya Falmata kuwa batasan abinda ke faruwa ba saboda bata gari Mahaifin Farida ne ya rasu shine sukaje a raba gado a baiwa yarta,
Washegari Ummie ta zauna da Salmah ta sanar da ita hukuncin data yanke itama Salmah bata yi musu ba tace ta haɗa kayanta dana Azan zasu tafi Wamako suyi kwana biyu ai kuwa taji daɗi sosai wata goma rabonta da gida Direba ne ya kaisu Muhammad ya bisu daga baya, tin ranar da sukaje Inna ta soma tsuma Salmah ta kayan gyaran jiki
Washegarin ranar data zo aka daura aurenta da Sajjad har gida yazo suka gaisa da Inna kana ya suka koma gida Salmah kuwa kwananta huɗu Ummei tazo suka tafi Inna tayi mata faɗa sosai da addu'a tana kuka suka dawo gida Itama Ummie ta dauko me gayran jiki aka fara yiwa Salmah cike da waje har kazar amarya Ummie ta dafa mata ita kuwa Salma cin abinta takeyi duk abinda aka bata,
ana gobe zata tare Ummei ta saka aka kwashe kayan Yusura gaba ɗaya aka zubawa Salmah sabbi masu tsadar gaske gayran gashi akayi mata da lalle ja da baƙi tayi kyau sosai ta fito sak Amarya, ranar Hajiya Falmata ta dawo sai Alhaji Hameed ne kasanr da ita abinda ke faruwa har auren Sajjad da Salmah, ai kuwa ta shiga tashin hankali na maisfa don batayi tsammanin haka ba yanzu shikenan su Mk zasu tona masu asiri Farida kuwa na jin abinda ake faruwa ta soma kuka wai saita kashe kanta Hajiya Falmata tace
"Farida kwantar da hankalinki matsawar ina raye saike aure Sajjad ki bari wannan ƙurar ta lafa zamuje Kogi state Wurin Boka bazamu dawo ba har sai Sajjad ya kiraki da kansa yana nemanki."
Tofa ai haka kuwa
Ɓangaren Sajjad kuwa ko yazo gidan baya jimawa yake fita idan yaga Azan gun Ummie ya ɗauke shi idan be gansa ya tafiyarsa yau ne Salma zata tare Ummei da kanta ta shiryata cikin kaya na alfarma ita da Azan kana ta kira Sajjad yazo ya haɗa su tayi musu faɗa sosai da jan kunne kana tayi musu addu'a ya ɗauke ta suka wuce gida dama tunda yamma direba ya kaiwa Salma kayanta na sakawa ita Azan gaba ɗaya,
Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen free page na book One sai mun haɗu a book2
Don jin Yadda wannan labari zai kasance shin asirin Hajiya Falmata zai nuno kuwa ya zata kasance idan sunje wurin boka Sajjad zai aure Farida ya zamansu zai kasance da Salma zai sota ne ko ƙaƙa shin waye ya saka a sace Yusrah saboda ya ɓatawa Sajjad suna menene tsakanin su ya akayi Sajjad ya bar aikin soja shin ina ɗan uwansa da Hajiya Ummei ta haifa
duk zaku samu amsoshin wa'yan nan tambayoyi a cigaban wannan littafin
Writer ✍️ bey Pinky darling Mrs Jay