JOY

PAGE 3

by @aishanalado88

Fuskarta cike murmushi ta tura ƙofar falon ta shiga, ta na kwalama Mom kira, a bakin ƙofa ta taka birki murmushin fuskarta na ɓacewa, lokacin da idanunta ya sauka akan Mom da David da ke zaune a falo, duk ido suka zubo mata, shaf ta manta da wani David da alwashin daya dauka yau a kanta, ganin irin kallon da Mom ke jifanta da shi yasa taji gabanta ya fadi, a ranta ta ce shike nan na Shiga uku David ya gama dani.

Sai da ta hadiyi miyau mukut! Kafin ta kirkiro murmushin dole ta sakar musu , cike da fargaba ta nufi Mom don ta rungumeta kamar yadda Mom d'in ta sabar mata, hankad'e ta Mom tayi saura kad'an ta fad'i Allah ya taimaketa ta dafa kujera, cikin tsananin bacin rai ta ce "kar ki kuskura ki ta'ba ni Joy!!!" Ta karashe maganar a kausashe.

A razane ta sauke manyan idanunta da lokaci d'aya suka tara kwalla a fuskar Mom, cikin karaji Mom taci gaba da ce wa "kije na yafe musu ke,tunda sun fini a ajenki kije kqai tunda ke kince baza kiji magana ba."daga haka ta mike a fusace ta bar falon ba tare da kara kallon gefen da Joy take ba.

Lumshe manyan idanunta zuciyarta na wani irin tsinkewa, hakan da tayi ne yaba hawayen dake kwance a idanunta daman zubawo, minti biyu ta dauka a haka kafin ta waresu akan David dake kallonta yana sakin murmushin mugunta.

Gaban shi ne ya fad'i ganin yadda lokacin d'aya manyan fararen idanunta suka rine zuwa launin jaa, take yaji wani shakkarta da tsoronta ya kama shi duk da kuwa ya girme mata don ya bata kusan shekara daya a haihuwa.

Bai gama fita daga wannan yanayin ba ya tsinkayi muryarta a kunnayenshi, a kausashe ta ce "David!!! Burin ka ya cika yau ka hadani da iyayena ko, nasan kaji dadi ranka yayi maka fari ko? To ka rubuta ka ajiye na rantse da wanda ya busa min rai da numfashi sai kayi nadamar wannan abin da ka aikata." Mikewa tayi ta kama hanyar hawa upstairs.

Ji yayi duk ya muzanta ida ta wuce bai mayar mata da martani ba zata ga kamar ya tsorata da furucinta ne haka yasa ya danne zuciyar shi tare da ce wa "Joy James." Da karfi, dakatawa tayi tare da juyowa suka hada idanu, takowa yayi ya iso gabanta ya tsaya, kamar zai fadi wani magana, sai kawai ya barke da wani mahaukacin dariya mai ban haushi, wani irin yawun takaici Joy ke hadiya a jejjere, ganin kuka na shirin kwace mata yasa ta juya a guje ta karkare hayewa saman bata zame ko ina ba sai dakinta kan gado ta fada tare da fashewa da kuka da iya karfinta.

Mom koda ta shiga dakin ta kasa zama tayi safa da marwa kawai ta shiga yi ta kai gwouro ta kai mari, hankalinta a matukar tashe, girgiza kai tayi a bayyane cikin irin yaren da David yama Joy magana d'azu a school ta shiga ce wa " meke shirin faruwa da ni ne ni Alice, kardai asirin da na rufe tsayin shekaru goma sha biyar ke shirin tonuwa, tabbas ya kusa tonuwa." Bango ta kai ma duka kafin kamar zararriya ta ce "Ina!!! Ba zan taba bari hakan ya faru ba indai na haifu cikin pastor Samuel da Mrs Deborah." Da sauri ta rarumi wayarta ta danna ma wani lamba kira, ringing wayar keyi amma ba'a daga sake kira tayi still ba,a daga ba jife tayi da wayar a kan gado tare da zama da'bas tana tafa hannaye, can wayar ta dake kan gado daga bayanta ya fara ringing da sauri ta raruma don duk a tunanin wanda take ne ya biyo bayan kiran, ganin sunan me kiran ne yasa gabanta yankewa ya fadi, *Dr Hassan* ta ambaci sunan a bayyane tana zare ido lallai bata ga ta zama ba wai an saci san barawo.

Tafi awa d'aya tana kuka kamar ranta zai fita, gaba daya ta hargitsa suman kanta ko takalmin school bata jire ba jakar ma jifa da shi tayi da shi can gurin kofar toilet, jinta take yi wani iri ji takeyi kamar ta aikata baban zunubi tunda take da Mom bata taba koda dungurinta bane, bata taba fushi mai tsanani da ita haka ba duk kuwa iya girman laifin da zata mata, amma yau ita ce Mom ke hankadewa lallai ta san ba karamin fushi Mom ta yi da ita ba, bata ga laifin Mom ba domin tun ba yau ba ta riga ta san yadda Mom ta kasance mace mai kishin addininta, tana tsananin kyamar addinin musulci, bata shan inuwa daya da musulmi, tana kyamarsu kamar me, ji tayi baza ta iya jurar fushin Mom, hakan yasa ta mike dakyar ta nufi dakinta.

*******

KANO STATE

*Dr Hassan special hospital Amenity word room number 5*

Wani farin dattijo ne me kimanin shekaru 65 a duniya ke kishingide akan gadon marasa lafiyar dake madaidaicin haddadden dakin wanda kwata kwata baiyi kama da dakin asibiti ba, hannun shi sakale da karin ruwa, saman roofing dakin fuskar shi ke fuskanta idanunshi a lumshe, idan ba ka kula da yadda yake motsa bakin shi a hankali da kuma yadda yake danna caunter dake sakale a daya hannun shi da babu Karin ruwa ba zaka dauka barci ya ke yi.

Daga gaban gadon wata dattijuwar mata ce zaune a kan daya daga cikin kujeru biyu dake dakin, a kalla zata kai shekaru hamshin da haihuwa amma tsabar hutu jin dadi jin iya kula da kai da yadda naira suka zauna zaka dauka batafi 38 to 40 ba, kallon dattijon mutumin nan take yi fuskarta cike da matsanancin damuwa, hannunta plate ne mai dauke da tuwon almaka da miyar alayyahu da nama, kasa ta yi da muryar a karo na barkatai cikin sanyi ta ce "Alhaji ka tashi kaci abincin mana gashi na zuba maka tun dazu yana hucewa." Bude lumsassun idanunahi yayi kafin a hankali ya ce "bana jin yunwa bazan ci ba." Shiru ta yi tana ci gaba da kallon shi tana tuna rabon shi da abinci tunda asuba da Dr yasa shi yasha tea lokacin da za'a daura mishi drip, kallon agogon dake manne a bangon dakin tayi karfe biyar harda mintuna biyu, ajiyar zuciya ta sauke, cikin son jaraba sa'arta ta sake ce wa "alhaji kayi hakuri ka tashi ka ci abincin nan, lafiya bazai samu ba idan har haka cin abinci." Wannan karan bai bude idanunnashi daya mayar ya lumshe ba kuma bai amsa ta ba, sai ci gaba da yayi da motsa bakin shi alamar yana ci gaba da lazumin shi, ganin haka yasa ta cigaba da yi mai magiya, jin ta dame shi yasa ya bude idanu tare da daka mata tsawa "keee! Nace bazan ci ba dole ne wai." Ta ke alhini da tausayin dake kan fuskarta ya bace bat lokaci daya bacin rai da bakin ciki suka maye gurbin su, ranta ya kai kololuwar baci , a hassale ta ce "wai har sai yaushe ne zaka cire wannan damuwar daga ranka? sai yaushe ne zaka dangana ka fawwalawa Allah lamuranka?, yau fa kimanin shekara goma sha biyar kenan, sai yaushe ne, iyeee alhaji na ce wai yaushe ne?" Ta karshe maganar cikin karaji tare da fashewa da kuka.

Bude lumsassun idanun shi yayi ya kalleta kika take yi bil hakki, guntun murmushin karfin hali ya saki, cikin muryar shi ta marasa lafiya ya ce " ya isa haka Lubabatu kina son kisan sai yaushe ne ko?" Da sauri ta gyada kai tana sharar kwallah, idanun shi ya saka cikin nata kafin yace a kausashe "sai ranar da asirin wad'anda suka kashe ta ita da abinda ta haifa Tonu...."

Yau ba yawa kuma ba editing🙏

Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lambar *** [12/29, 2:20 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀

*BY*

*AYSHA NALADO*

*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*

*LITTAFI NA ƊAYA*