PAGE 6
*AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE* _Jama'a kada ku bari wannan garabasa ta wuce ku,muna da nau'i magungunan gargajiya masu kyau da inganci_ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... *** domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda inganci da sahihancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai-dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_
_nfection_ _Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace *SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI💯☑️*_
_Muna sayar da supplement gangariya irin wadanda ba su da matsala sai da su gyara garkuwar jiki da inganta lafiya, muna bayar da sari duk wani supplement muna da shi, kuma muna sayar da daya muna bada sari akan farashi mai sauki, muna tura kayanmu ko wane gari domin neman karin bayani a tuntunbi wannan lambobinmu dake kasa._ ***** *****
Yadda Mom ta hango Joy a hannu Papa tana kakkafewa yasa ta 'karasa da gudu, a rud'e take tambayar shi me ya same ta, cikin wani irin yanayin yace "Alice I don't no nima haka na shigo yanzu na same ta." "Jesus!!!" Mom ta ce lokacin da ta d'aura hannunta a goshin joy jin yadda ya dau zafi radau, "Mu kaita asibiti honey karmu rasata." Ta fada tana shirin fashewa da kuka, "Na kira Dr solo ya ce yana zuwa yanzu." Papa ya amsa mata, gyada kai ta yi tana share hawaye.
Wayar Papa ne ya dauki ruri, ganin Dr ke kira yasa ya daga da sauri, yana cewa "ka iso ne Dr." Dan dakatawa yayi kafin ya daura da "OK ka karaso da sauri Dr ka hawo sama tana dakinta." Cikin kankanin lokaci Dr Solomon ya karaso dakin Joy yana d'auke da jakar kayan aikin shi, ganin yanayin da take ciki yasa ya nemi da su Papa su bashi guri, da kyar suka fita suka tsaya a bakin kofar dakin, Mom rungume jikin Papa tana kuka shi kuma sai bubbuga bayan ta yake yi idanu jajur,
Minti talatin Dr Solomon ya kwashe akan Joy, ya gano damuwace da yawan kukan da tayi ya haifar mata da zazzabi da ciwon kai mai tsanani sai ulsanta daya ta shi saboda rashin ci da sha, take ya bata duk taimakon daya da ce, ya mata allurai tare da daura mata drip, barcin wahala ne ya kwasheta kasancewar a cikin alluran da ya mata har da na barci, sai da komai ya daidaita sannan ya fito.
Da sauri suka yiyo kanshi suna rige rigen jero mashi tambaya, ajiyar zuciya ya sauke kafin ya shiga yi musu bayanin abinda ya gano yana damunta, cikin kwantar da murya ya daura da cewa "kuyi hakuri yanzu dai komai zai dai dai ta don na bata duk taimakon daya dace na daura mata drip na mata allurai, yanzu haka barci ya dauketa saboda alluran da na mata masu karfi ne kuma akwai na barci a ciki zaku iya shiga shiga ku ganta."
Tare suka koma dakin da Dr , zama kusa da kanta Papa yayi ya kamo daya hannunta da babu canula ya rike yana binta da kallon zallar kauna da tausayawa, Mom kuwa ta wurin kafafunta ta zauna ta zuba mata idanunta mai dauke da danshin hawaye ganin yadda ta rame ta kara haske a cikin yini guda.
Gyaran murya Dr yayi duk suka kalle shi ya ce "Mr and Mrs James ni zan koma hospital dan na bar aiki sosai na taho nan, amma zuwa safe zan dawo na sake dubata na kuma kawo magungunan da zata sha, sannan ruwan da na daura mata zai Kare nan da sha biyu na dare, za kuma ta iya farkawa nan da hudun asuba idan ta ta farka Ku tabbatar ta ci abinci kafin na iso." Godiya suka mishi Papa ya rako shi har parking lot na gidan, tare da mai alkawarin kafin ya isa gidan zaiji alert kudin siyan magunguna dana shan mai, shima godiya ya shiga yi, don yasan yau account din shi zai kwana da nauyi.
Kusan a kanta suka kwana suna bata kulawa, cikinsu babu wanda yayi barcin kirki, sha biyu ruwan ya kare kamar yadda Dr ya fad'a, Mom ce ta cire mata, bata farka four kamar yadda Dr ya ce ba sai gurin six na safe har sun fara damuwa suna tunanin kiran Dr ta farka.
Dishi dishi ta fara gani, kafin a hankali komai ya daidaita, tar ta ware idanunta akan mahaifinta wanda zuwa lokacin shi kadai ne a dakin, da sauri ya karasa kusa da ita ya kamo hannunta yana mata sannu, kura ma shi ido tayi tana kokarin son tunano abin da ya faru,
Dai dai time din Mom ta turo kofar dakin ta shigo, motsin kofar yasa ta maids idanunta gurin, idanunta ne ya sauka cikin na Mom, take abin da ya faru ya dawo mata tsab, shesshekan kuka ta fara, ganin haka yasa Mom karasawa da sauri ta kama daya hannunta, girgiza mata kai ta shiga yi, alamar kar tayi kuka, a hankali ta bude baki hawaye na bin gefen fuskarta ta ce "Mom ki yi hakuri ki yafe min."
Hannu Mom tasa tana share mata haware, kafin ta ce "Ya isa haka daughter ki daina kuka, kinga baki da lafiya." "Bazan daina kuka ba har sai kin yafe min Mom, bazan iya jurar fushin ki ba." Dauke kai Mom tayi cikin dan bata fuska ta ce "zan hakura amma sai kin mini alkawari babu ke babu wannan yarinyar." Ba tare da tunanin komai ba don a lokacin mafita da sassauci kawai take nema ta ce "Na yi miki alkawari Mom daga yau babu ni babu ita har abada." Murmushin farin ciki da nasara ne ya kwacewa Mom ta rungumeta tana ce wa "nagode daughter ina son ki ina tsananin kaunarki." Dariya ta saki mai sauti cike da jin dadi ta ce "I luv u 2 my Dear Mom."
Gyaran muryar da Papa yayi ne yasa Mom sake Joy, kallon tuhumar da yake mata yasa ta yin murmushi, da ido ta mai alamar yayi shiru zata mai bayanin komai anjima, bai ki ta tata ba, kawai yaja bakin shi ya tsuke.
Tea Mom ta hada mata, papa ya taimaka mata ta zauna, da kanshi ya ringa bata tana sha har ta shanye, abinci mai saukin nauyi mom ta shiga kitchen da kanta ta samar mata, ganin yadda Mom ta sake da ita yasa ta kwantar da Hankalinta ta ci abincin sosai, kan kace koba sai gata ta gyagyije, da kanta tayi wanka ta shirya, cikin riga pink mai hannun singlet da wando legis fari,
Karfe takwas Dr Solomon ya iso ganin yadda patient din shi ta gyagyije yaji dadi sosai, magungunata ya bata ya musu sallama ya tafi.
*********
Sai da taci kuka ta koshi kafin ta mike jiki ba kwari ta kwabe kayan ta canza zuwa dogon rigar atamfa, ta dauke dan madaidaicin hijabi ta sanya, ninke wadancen kayan tayi ta kwaso ta fito dakin, ganin baya tsakar gidan yasa ta nufi hanyar zaure, sallama tayi da yar siririyar murya, amsa mata yayi tare da bata izinin shigowa, a bakin kafifar shi ta same shi zaune, har zuwa lokacin fuskarshi a hade babu rahma, daga nisa ta tsuguna, cikin sanyin murya ta ce "Yaya kayi hakuri bazan sake ba." Ta karashe tana mika misha kayan, bai amshi kayan ba kuwa bai amsa mata ba, ganin haka yasa ta sake cewa "Yaya dan Allah da manzonsa ka yafe min, wlh tsautsayine na yi maka alkawarin bazan sake ba" sai kawai ta fara shesshekar kuka.
Rintse idanu yayi, jin kukarta yake kamar saukar ruwan zafi a zuciyar shi, yana jin Fatima a zuciyar shi fiye da tunani me tunani, yana mata so irin wanda kafin a same shi tsakanin yan uwa sai an tona, kukanta yakan yi saurin raunata zuciyar shi, matsayi uku yake takawa a rayuwarta UBA, DAN UWA, da kuma ABOKI, sun budi ido ne daga shi har ita basu san kowa ba sai junansu sai kuma Umminsu, hakan yasa suke ma juna wani irin so Mara iyaka, tunda ya fara girma ya fahimci basu da wani gata sai Allah sai Ummi mahaifiyarsu da take tsaye a Kansu dare da rana, ya kudiri aniyar zame mata gata, yadda yake maraicin rashin mahaifi ko wani tsayayyen dan uwa ita bazai taba bari tayi shi ba matukar yana numfashi, a komai nata yana tsaye da kafafun shi, ita macece mai raunice abar tausayi da riritawa.
Dakyar ya bude baki ya ce mata ya "ya isa haka Fatima na hakura share hawayenki." Hijabin jikinta tasa ta share fuskarta da shi, gaban shi ya nuna mata yace "ajiye kayan a nan." Babu musu ta ajiye, numfashi ya sauke kafin a tausaahe ya shiga yi mata nasiha akan kula da mutuncinta matsayinta na diya mace, sosai ta nutsu tana sauraren shi sai da ya dauke lokaci mai tsawo kafin ya dasa aya.
Godiya tayi kafin ta mike ta je kitchen ta dauko mai tuwon shi har zuwa lokacin Ummi na tsakar gidan tana sauraren shirin tsalle daya a radio.
Ajiye tuwon tayi a gaban shi tare da ledar yalon da ke damke a hannunta tun dazu, murmushi yayi ganin yalo, ya dago ya kalleta itama sai ta sakar mai murmushi, ya ce "Nagode yar gidan Yaya Ameen" dariya ta saka cike da jin dadin yabawan da yayi da kyautarta, wani dadi yaji ganinta cikin farin ciki sai ya tsinci kanshi da yiwa marigayin mahaifinsu addua wanda har yau ko a hoto Ummi bata taba nuna musu shi ko wani nashi ba, kawai abinda suka sani ya rasu da dadewa.
"Yaya sai da safe." Muryarta ya katsemai tunani, ya ce "har zaki tafi baza ki zauna muyi hira ba, ko barci kike ji da wuri haka?" Ta girgiza kai, ya ce "kinci naki tuwon ne ko?" Ta ce "A'a yanzu idan na shiga zanci." "Wanko hannu kizo muci tare." Ta amsa da "to Yaya" tare da shiga cikin gidan danta wanko hannu kamar yadda ya umarceta.
Cike da nishadi suka ci tuwonsu cikin kwarya daya suna wasa da dariya, a karshe ya saka katon loma, kukan shagwaba ta saka tana dire kafa, cinyewa yayi ya kara kai hannu da sauri ta dauke kwanan ta cinye guntun daya bar mata, tana tura baki, yana mata dariya da gwalo kamar bashi ne dazu ya rufeta da fada ba, bayan ta kwashe kwanukan wanko hannu tayi ta dawo, nan shiga bata labaran ban dariya yana cin yalo yana yabawa ita kuma dadi kamar ya kasheta, daga karshe ya saurari haddarta.
Ummi na tsakar gida tana saurarensu, tsakanin Al'ameen da Fatima sai Allah,ko ita data haifesu bata ce ga tsakanin subab, a haka bata san sanda ta fara gyengyadi ba.
Ba su suka ta shi ba sai gurin goma da rabi, shima ganin tana ta hamma yasa ya ce taje ta kwanta, koda ta shigo gida ta samu Ummi tayi barci radio a kunne tashin ta ta yi, suka wuce daki bayan sunyi alwalan kwanciya.
Washegarikamar kullum ta gudanar da aiyukanta na safe tayi shirin makaranta, tana ta zuba idon ganin Joy sai dai shiru shiru har ta gama ta fito gida ta kama hanya, yana ta tunanin ko zasu hadu a hanyar amma shiru har ta isa bakin get, bata kara shiga damuwa ba sai da ta isa class ta tarad babu joy babu me kama da ita, haka ta zauna jiki a sanyaye tana tunanin mekefaruwa ne yau, iya Sanin ta Joy bata fashin makaranta, can sa'insar daya shiga tsakanin joy da David ya fado mata, take gaban ta ya yanke ya fadi rassss..........
Me bukatar shiga group ya tuntubeni ta wannan lamabar *** [12/29, 2:32 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
*BY*
*AYSHA NALADO*
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
*LITTAFI NA ƊAYA*